Mahakurci........
*بسم الله الرحمن الرحيم*
®🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[ '''Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women''']
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*
*_Z• W• F•🏝_*
Writing* by_FARIDAT MOHD
Mmn rufy
Sadaukarwa na sadaukar da littafin nan ga qawata kuma aminiyata _FIRDAUSI HASSAN,inayinki besty Allah yakawo miji nagari musha biki.
*PAGE* *1 to 2*
Dijee dijee" bana rabaki da wannan baqin surutun ba kina yarinya qarama amma bakin ki be shiru kamar me bakin aku to wlh senasa madoki abakin nan naki, duo duo duo shekaran ki nawane da zaki shiqe daki da qawa kina bata labarin haihuwa agidan uwaki kika San yanda haihuwan take, to bari tunda auren kk so mallam xeshigo na fadamae".
"Wayo Allah ni dijen baba Gwago zata kasheni zata halakani, Gwago yaushe nace aure nakeso? Ni daga inaba balki labari shikenan se ace kuma aure nakeso".
" To danqaniya zaki rabamu da labarin masu haihuwa kokuwa?"
"Gwago wlh nadena ni Dije".
"To balki futo in aike Ku wajen yaya binto gidan megari saura kuma kuyo tsokana agari kamun kudawo".
" To Gwago ai bazamuyi ba insha Allahu, kawo sautun".
"Idan kinje kicewa Yaya tayi waya da shehu kuwa?"
"Haba gwago wlh Ku kuncika damuwa da wani shehuwa can shi yama manta daku qila amma Ku kullim kuna nemanshi awaya idan yana sane daku shixe neme Ku ai".
" To uwata dije kigamin fadan amma aike sekinjeshi kinjiniko, inaruwanki da damuwarmu tunda bataki bace, banda hauka ma irin naki ace Dan uwanka yana birni anranbu dajin duriyarsa shekaru biyar kenan amma baki damuba saboda bakida hankali ko dubi yanda uwar yaronan ke qaunarki amatsayinki na y'ar yayanta ko shehuwar batanunawa hakan ai amma kice bazami damuba,ko dabba katura kiwo bata dawoba wuni guda seka damu ballantana Dan mutum da yaje karatu binni shekara biyar ba labarinsa duo da betaba irin wannan dadewar bezoba amma shirun yy yawa kam, ke kam halinki seke dije ".
" Yo ni Gwago keda Innah saboda shehuwa ne kuke sami zarya kaman me tsohon dankanoman daya tashi. Haba Gwago inyi nan inyinan kullum fa se kin aikeni ko tauyin dijen baba bakuyi".
"Tausayo nace tausayo kinji, wlh dije akan shehuwa sena sasab'a maki kammani , maza kuwuce inda na aikeku.
'Daura hannu akai dije tayi tun kamin subar gidan " wayyo Allah ni dijen baba, Gwago bata tausayina saboda shehuwa, narantse da Allahn daya halliceni ya hallici shehuwan had'uwata da shehuwa bazatayi kyauba domin sena fanshe wahalata ta shekara biyar d'inan".
Balki ta qalqale da dariya "yasin dije baki iyawa da shehuwan innah, shimafa rigima ba daga baya ba abun namu duo gadone ai rigima ce mungadota wajen tsohuwa gwammah".
" yasin ni dije duo bala in Ku na fiku nadameku na shanye tass wai ko kin manta kirarin da yan qauyenan kemin ne, dejen baba dijen Gwago da innah dijen masu gari me siyen tsiya da kudinta idan ba kudi zakici bashi".
Balki ta sheqe da dariya "se dije tsiyarma har bashinta kk ci wlh dije kisauya saboda mace CE ke gidan wani zaki".
" Anqi acanja idan naje gidan wanin akasheni kinji"
"Allah yabaki hakuri dijen baba".
Ahaka dai aka isa gidan megari ankusa danbe a hanya.
" Assalamu alaiku innatah takainah innatah bata kowaba".
"Ho y'er innah karki karyani mana banga jikokinaba, ko bakison yaran da zaki Haifa su d'ana cinyar tawane?"
"Cab wannan cinyar ai dani kadai akayota inna ko na haihunma ba me hawa seni daya".
" yo ke se yaushe zaki girma ne? "
Har ki aurenma bazaki girman ba?"
"Nidai innah abar maganar aurenan, Gwago tace ansamu lambar shehuwan?"
"Hum had yanxu dai amma yaturo saqo tawajen wani Dan makotanmu dake can jiya yazo yace nan da watan gobe zezo makarntace ta riqeshi amma ya kammala yanzu cuku cukun aiki yake kuma yasamu yana tafe insha Allahu".
" Hum ni innah dama kada yazo, daya zo zewani takuramin da yi kaza gyara wancan ke banzace ke bakida hankali" tanayi tana kwaikwayon yanda yakeyi.
"Ho keda shehuwa kam ai seku tada gida, kome lokacine zaku dena ne ai.
Balki tace" dije da shehuwa innah basa dena rigima".
"Zasu dena balki lokacine ai".
" to innah Allah yasa".
"Ameen balki".
" Assalamu alaukum"
"Ha ah dijen masu garice agidan".
Cewar megari daya shigo.
" baba nice ya fama da mutane?"
"Lfy lau dijen masu gari,Ashe dijen tagirma tayi hankali ko?"
Rufe fuska tayi alamun jin kunya
Gaba dayansu sukayi dariya.
"Dijen masugari daga ina haka?"
"Inda ka aikeni me zuciyar kare".
" Haba dije daga ya tambayeki se baqar magana".
"To me zuciyar sahabai".
" yi haquri me zuciyar annabawa".
"To yasan ranka ne?, nifa wlh katakura min duk inda muka sa qafa sekasa shin wai ana dolene nace banayi banaso ka qi kyaleni, nayi maka kama da matar baqauye? Ko nayi maka kama da matar talaka dubenifa". Juyi tayi gaba da baya tasake cewa" dubafa kwalelenka wlh dangin mayu kurwata kur wlh rabe, Dan Allah kayi zuciya kabi wata hajar Dan wannan tafi qarfinka Rabe".
"Dije ni kike fadawa haka?.
" Eh mana ko akwai wani awajenan bayan ni da kai dakuma bilki?"
"Babu dije, koba kyasona ni inasonki kuma sena aureki".
" To wlh ko kana tsafi da baqar jaba bani aurenka".
"Maso Dan tsuntsu shike binsa dajifa ko dijeta".
" Naci uwar Dan tsuntsun kai harda dutsen jifar".
"Har da me jifar ko?"
"To lauya ni banceba, amma wlh nakusa cewa idan aka takura".
" To Allah ya huci zuciyar dijeta".
"Ashe kuwa zan luluqa maka zaki wlh ka qaracemin dijenka waya bakani wlh niba taka bace idan ka qara sena dirje ma baki da turb'aya bakansan dije ba labarinta kakeji mugunta kwando kwando gareni, wuce muje bilki".
Sororo suka barshi kamar lefen Sakara.
Suna tafiya bilki na fada " haba dije dankinga mazan garinan nadaga maki qafa shiyasa kike takasu yanda kk so to wlh ki takasu asanu ina jiye miki halinsu, yanzu miye aibun Rabe dan yace yana sonki gashi me hankali".
"Ko mahaukacine bazaki fidi ba ai saboda zuciyarki karyayah ce".
"To kiyi ke kam mijinki yabani wlh".
" yashiga ukku ma balki Dan ni ba sakarar mace bace ehem".
"Ho Dije".
" gani fa".
"Naganki ai".
" To yasan ranki".
"Babu".
" to ki Shafa min lafiya idan kika ga ina abuna ki kyaleni ninasan me nataka".
"Hum naji".
Yawan comment yawan typing
Ku biyoni acikin novel din mahakurci me cike da bandariya sarqaqiya ..............ngd
Faridat mohd
Mmn rufy ce
*بسم الله الرحمن الرحيم*
®🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[ '''Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women''']
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*
*_Z• W• F•🏝_*
3_4
Wacece Dijee ?
'Ya daya tilo awajen malam Ali da Gwago Rabi, Khadija Aliyu.
Yarinya me tsiwa shagwaba daukar magana bata gudun kota kwana, ba ilimin boko amma fa akwai na arabi
Burinta shine ta auri dangayu Dan birni Wanda yakeson ta fiyeda yadda zatasoshi idan tace bata Abu to batayi koda za akasheta mutum d'aya ne kesata dole bayan iyayenta shine,USMAN ABUBAKAR M/GARI,wato shehuwa, shekaranta 20 aduniya amma kyakyawar gaske ce danma batason kwalliya amma fa akwai wanka kamar kwad'uwa.
Wanene Shehuwa?
USMAN ABUBAKAR M/GARI, shine cikaken sunansa, su biyu ne wajen iyayensu shi da qanwarsa mariya,karatu yakaishi Nigeria amma asalinsu yan Niger ne. A wani qauye mesuna kahin qosau.
Engineering yakarnata yanzu haka yafara aiki. Kuma yanaganin bud'i sosai. Abu d'aya yarage mai wato aure kuma had yanzu be hadu da daidai shiba domin kuwa kutum ne shi meruwan ido da tsentseni.
Asalinsu
'Yan Niger ne cikin wani qauye kahin qosau, family nsu guda auren zumunci sukeyi yasu yasu.
Mahaifin shehuwa yayan mahaifiyar Dijee ne, mahaifiyar shehuwa yayar mahaifin Dijee ne.
Kakan shehuwa Dana Dijee ya da qani ne hakama kakaninsu mata suke dama nafada maku auren zumunci sukeyi.
Balki d'iyar anwar Gwago Rabi ne da tarasu ta ke hannunta.
Baban shehu shine megari.
Baban Dijee ma Nada nashi mukamin a fadar m/gari.
Cigaban labari
Zaune yake a ofishin ogansa yana neman izini domin yaje yagano mahaifarsa Dan shi kansa wlh yayi kewarsu sosai fa had yakanyi mafarki da mahaofiyarsa na cikin damuwar rashin ganinsa.
"Sir ataimaka wlh na kwana biyu rabona da kasarmu iyayenah sunansa bu atar ganina nima haka".
" To M/gari amma kasan akwai tarin ayuka dake jiranka ko?"
"Nasani sir, aikine bazanji dad'in yinsa ba batare Dana ganosuba".
" OK Allah yakaika lfy yaushe ne tafiyar?"
"Cikin week d'inan insha Allahu, kuma baze wuce sati biyu ba zandawo".
" OK idan zaka tadi seka biyo ta gida akwai saqon dazan baka ka kaiwa megari da dan uwansa domin zuwa na garin sunmin hallaci".
"OK sir godiya nake, Allah ya qara girma".
Bayan fitarsa bezame ko ina ba se gidansa dayake gini shirye shiryen tafiya ya keyi domin jibi yakeson wucewa, yayiwa kowa tsaraba amma banda Dijee, kuma bawai Dan babu wadatar hakan ba niyyace beyiba kuma yasan mudin beyinba qarshe ranshi ne ze baci wajen innarsa, idan bewa Dijee ba itama cewa take bata amsa, dole yayi ko ahanya ne.
" Dijee, Balki kuna ina ?"
"Gobe Yaya shehuwa zedawo".
" To aike yadama dalla can kin ishi mutane sbd shehuwa zedawo, kaman idan yadawo raga mana yake, bayan du wata tsohuwar muguntarsa kanmu take qarewa mtswww".
Mafici Gwago tajeho mata a baya,
"Ja irah kawai andai kusa yinta taqare muga idan kashe kanki zakiyi".
Balki ta kece da dariya.
Cakumota Dijee tayi," abiyar wasanki nake da zakimin dariya kamn kinga wawan zama yanzu na tumurmusaki Balki".
Ina tayo Kansu domin rabawa yayin da Mariya ta cakumi kwallar Dijee zata ramawa Balki.
"Ku kunci gidan Ku duka, INA rabaku kuna hautsinewa kaman kaji, kunzauna lafiya kokuwa".
Ganin ta da madoki yasa suka saki juna" Gwago munbari ai".
Sunsan duk girmansu tsab zata zanesu ballantana duka yaushe suka gama irgan dangi.
Washe gari gidan megari Dijee takwana itada Balki domin taya innah gyaran gidan da shirye shiryen taryan Yaya shehuwa.
Adafa wanca asauke wancan kamar shugaban qasane zezo cewar Dijee qasa_qasa dakada ajiyota.
"Laa Yaya shehuwan kk cewa haka, to yasin sena fadamai".
" jeki fadi aku me bakin magana suda uwar labari, kema be raga makiba ai idan ma kin fadi duo ze hadamu yazane,to miye ribarki?"
"Ba wani sena fadi," zaki min dad in baki Dan kar nafadi ko"hhhhhh to sena fadi Dijee".
"Mtsww idan baki fadi ba basunanki mariya ba nikuma idan ban dauki fansa ba ba sunana Dijee ba".
Innah CE ta raba fadan.
Tafiya yake acikin saharar qauyensu cike da annashuwa da far in cikin ganin iyayensa da zeyi.
Tunkamin motar shehuwa ta iso yara sun fallo da gudu gidan megari.
" Ga shehuwa nan ya iso". Suna rufe baki yana parking qofar gida da gudu Mariya da balki suka futo wajen ganin yayan nasu.
Kallo d'aya yayi masu suka fahimci na gargad'ine. Se alokacin suka tuna ba lulub'i ajikisu, da gudu suka sake juyawa gida, ita kam dama yar rigimar tana kan turmi zata shiga wanka Mariya ta saye mata takalmin zuwa qokar gida dole ta tsaya jiran dawowan su.
Suna shigowa d'aki sukayi da gudu domin tseren laifinsu.
Sororo tabisu da ido tana harare harare," aifa azara ilu yadawo dole Ku haukace haka".
"Watakan nine azara ilun ko?"
Tsamo tsamo tayi batayi tsamanin shigowarsa yanzuba.
Layancewa tayi " sannu da zuwa Yaya shehuwa anzo lafiya, ya hanya ya jama'a?"
"Bansaniba Dijee, zamu gauraya yarinya taki bazatayi kyau ba, badai nine azara ilu ba, to ta kanki zanfara zare rayuwan".
"Nifa ba dakai nakeba".
" koma dawa kike sekinfadamin yarinya, kwaila kawai".
Abinda Dijee bataso ace mata kwaila
To ga rigima ba kudin siye, koda kudinma shehuwa base saidaba, domin kuwa tana shakarsa wani lokacin.
"Murgud'e kawai tayi ta shige bayi.
Kwata yayi" me hali baya fasawa Allah ya shiryaki Dijeen innah".
Ashe tajiyo shi tundaga bayin "ameen dai idan da gaske kake".
Dakin innah yashiga da sallama" Oyo yo innata, I miss u a lot my momy ".
Kai da Allah d'agani kaida baka girma gaban qanenka zaka hayen cinya ka rumurmutseni bayan kazama tulele dakai".
Dariya yayi " ho innata yau kuma nine tulelen, ni bansan seyaushe za adena kunyar dan farinan ba anasona ana kaini kasuwa haba innata , shekara biyar kenan baki ganiba amma ana tutureni, ance labarin zuciya atambayi fuska fuskarki tanuna kinyi na am da zuwan d'anlelenki".
Dije dake shigowa gunguni tayi asa asa zata wuce ciki.
"Ke me kk cewa ne?"
" Nifa bance komai ba"
"Zaki fad'imin kosena taso".
" cewa nayi wai danlele kamr wani yaro ".
" hum wlh ina kiyiwa diyarnan taki magana ta ga tafara girmane ko , to Allah ni atafin hannuna take".
"To sarakan rigima kunfara ko, zamuga yanda zakuyi ai kuje Ku kashe kawunanku acan".
" Innah me kk nufi da muje can mu gane?"
"Me make ci na baka nazuba ai babu inda zaka qara komawa seda auren............
To kome innah teke nufi
Fans kome su innah suke kitsawane??????????"
Ku biyoni Dan jin meke faruwa.
Farida mohd CE
Mmn rufy
Maha urci*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
®🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[ '''Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women''']
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*
*_Z• W• F•🏝_*
*written by-*FARIDAT MOHD
*MMN RUFY*
~Sadaukarwa ga yan uwana da abokan arzi e~
*Bismilahir'rahmanir'rahim*
*Page 5_6*
Auren ka".
"Innah aure kuma, to dawa kuma?".
"Dame rabo a cikin family".
" haba innah har ni ban tsalake auren dole ba ".
" baka tsalake ba kuwa, ba auren dole bane auren zumuncine ai".
"To innah miye marabarsa dana dolen, tunda ni baso nake ba, abin haushin ma se wajen d'aurin auren zakasan wa aka aurama, innah sekace jahilliyah period".
" qaniyar ka, kaji muda akamana kenan zamanin jahilliya muke ko?"
"Haba innah ni bance ba".
" kace mana gashi ka fa e a gabana".
"To kiyi ha uri bazan sake ba ".
" ayiiiiiiiriiiiiiiiiii, Allah nagode".
"Ke kin haukace ne? Kikewa mutane buda kamar gidan biki?"
Mariya tayi carab ta amshe kamr da ita ake " yaya shehuwa wai dan da za a maka auren dole shine take murna".
"Innah kinji ko, sunfara rainani saboda za amin auren dole, meyasa kika fa e a gabansu innah?.
" hum shehuwa badai tamaka dariya ba ka kyaleta akwai ranar ramuwa gwanda kai kasani tun yanzu itako idan aka tashi auren bazata sani ba se ranar bikin".
"Kuma wlh innah tasake tace bataso ko bana kusa afadamin ta kwashi kashinta ahannu, ke wannan ma mijin da ze aureki ai yaga takansa wlh, mace har mace amma ba birki kwaila kawai, wannan saboda bala en ta seta orawa mijin hawan ruwa Allah".
" yasin aka auramin wanda banaso sena samai hawan jini ma ba ruwa ba gwanda ma kada afara , dan kada arasa dan mutane".
"Idan an auramiki sekiyi yanda zakayi ai sakarya yanda a kama kowa haka za amiki kwaila kawai fuska duo muni".
" wlh yy Shehuwa ni kyakyawace son kowa in wanda besamu ba".
"K'in kowa dai son me wahala".
" hum yaya shehuw wlh sekayi mamakin mijin da zan aura".
"Hum nagani ai".
"Innah bari naje na watsa ruwa sena dawo naci abinci".
" to a futo lfy, Dijee kaimai jakarsa dakin sa".
"Wayo innah dan Allah BAlki ko Mariya wata takai, yanzu danaje seya sani wani aiki".
" A a kece zaki kai mai suma aiki zasumin kije kidawo kihada mai a bincin annan".
Jakar ta auka tana tafiya tana mita" shikenan ni watan wahala ta yakama
tunda Shehuwa ya zo".
Bakin ofar akin ta tsaya kaman wata me nazarin, tada e tsaye a wajen.
" Shigomin da jakata zan canja kaya malama, kinwani min tsaye a dokin ofa ".
Da arfi ta tura ofar ta shige bata yarda sun hada ido ba ta aje kayan zata juya.
" Waye yai gyaran akin nan?"
"Balki".
" bemin yanda nakesoba, maza sake gyarawa".
"Haba yaya tafa gyara ".
" Eh nagani ai amma beyiba aikinsan kece me gyaran akin ko?"
"Ni Dijee nabani yaya Shehuwa na girma ma ban tsira ba, gwanda ma ayi ayi bikin kona huta wlh".
" ko anyi bazaki hutan ba inde ina garinan kome ke zakiyi shi yarinya sede in aure kikayi kinhuta da wahalata".
"To ita amaryar taka miye amfaninta ne da seni".
" Amfaninta base kinji ba mara kunya, oya zoki gyarashi zanje naci abinci nadawo kamin indawo ki gyara kisake wanke toilet dinma".
"Fita ofar aki zan canja kaya".
Fita tayi tana zunbara baki
" hum yarinya sena fashe miki lebuna kina zunbura ma mutane bakinan".
Fitowa yayi bayan ya canja kayan.
Ko kallonta beba yashige cikin gidan
Kwata tayi ta shiga akin, gyaran tafara.
" Innah ina abincin?"
"To me hada abincin ai tana wajenka ko?"
"Oh hakane fa".
" Balki hada mai".
"Ah barshi Balki jeki qirata tazo ta hada shi ".
Itama Innah daukar magana ne tasan idan yazo garin komanshi Dijee keyi, acewarsa horo ne yake bata akan rashin jinta, a zuciyarsa kuma ba haka bane saboda duk tafisu mariya tsabta ne da qwarewa gata dai a qauye amma wani abun idan tayi ko a birni se haka.
" Dijee Kizo ki zubawa Yy Shehuwa abin...........
"Dallah malama kije kice banzuwa nawa zan kasu ne wai, yace ingyara daki in wanke bayi, to ai ko aya bangama ba ko ballantane in yi na biyu sena ukku kije kice idan ze zuba da kansa yaci yazuba idan baze zuba ba kada Allah yasa yaci mtssssssw".
" inje in cemai hakan ko?"
"Eh kije mana".
" To aini ba ke bace, zan cemai dai kince kina zuwa da kingama gyaran".
"Kice hakan zamu gaurayane ai".
" ki kasheni kibarwa gwago gawata kinji".
Futa tayi zuwa akin innah
"Tace gata nan".
" OK".
Fira suka ci gaba dayi da innah inda yake cemata sati biyu zeyi yakoma saboda yabaro ayuka a ofice najiaransa.
"To amma Shehuwa ai na gayamaka da matarka zaka tafi ko, bazamu bari ka tafiba batare da aure ba".
" to innah ai anbari na koma na shirya inda zan ajeta ko?"
"Kanema idan kaje ai kanada kudin yi".
" hakane innah amma banfa shirya ma auren ba".
"Dama base kashirya ba ai".
Shigowar Dijee yasa yabar maganar.
Abincin ta hada mai ta aje,
" Innah zanje gidan gwago indawo".
"Haba yarinya guduwa dai zakiyi saboda aiki ko?"
"Kyaleta haka ai ta aikatu ita kad'ai kake sawa aiyukan ka, gaka da anbanzan sa aiki kaman mace me tsohon ciki ai dole tagaji, idan kinje kya gaisheta".
" Idan kunje kucewa Gwago ta nasauka lfy zanzo idan naqara hutawa".
"To".
Megari ne yashigo gidan cike da farin cikin dawowar d'ansa gida.
Bayan gaishe gaishe daya shiga tsakanin d'a da ubansa aka koma firar duniya aka gangaro ga maganar aure.
" Usman nasan cewa kasan yanda iyalanmu muke auren zumunci, kasan komai base na mai mai ta maka ba, hakan ce zata kasance a gareka kaima kuma ina fatan zaka amshi abun hannu biyu kuma ka ri e amana domin amana ce zamubaka kuma insha allahu jibi juma'a za a d'aura amasalacin jumu a dake ofar gidan nan".
Kansa a qasa yace" ranka shi dade na amsa hannu biyu Allah yabani ikon rike amanar da za abani, amma naso ace an dan bani lokaci naje nayi yan shirye shirye sena zo a daura auren".
"Allah ya albarkace ka Usman haqiqa ina alfahari dakai, maganar shiri bata taso ba kanada wayanda zaka wakilta acan a idasa maka ginin gidan ka, maganr kayan dakin amrya kuwa nine meyi sabida nine uban amarya zan bada kudi idan anje can asiya, amma aure insha Allahu jibi za a daurashi".
" To ranka shi da e 🅰 llah yanuna mana lfy, maganar kayan daki kuma zansa komai dakaina base kabada kudi ba".
"To Allah yayi maka Albarka".
"Sannan ina neman alfarma, koda sunan wadda za auramin ne fadimin".
" Usman idan lokacin yayi zaka sani nanda jibi ne fa 😀".
Kunya yaji ya du ar dakai
"Se wata alfarmar danake nema, ina son natafi da yaranan can nasasu makarantar boko tunda duo sun riga da sunyi saukar qur'ani, sbd karatun yanada mahimmanci".
" To suwa kenan kake magana?"
"KHADIJA da MARIYA da BILKISU".
"To Fitar da khadija a lissafi don ita wannan se yanda kace amma su se munyi shawara tukun, tashi kaje Allah ya taimaka".
Saqe saqe yake azuciyarsa to me hakan yake nufi da Dijee se yanda yace akwai alamar tambayafa???????????
Muhadu a page na haba
*Farida mohd*
*Mmn rufy ce*
