ADS HERE

SO SHU'UMI. PAGE 1 NA MRS BREAKER

 *SO SHU'UMI💞*


_✍🏽MRS BREAKER_


         001


*_WANNAN LITTAFIN HABIBATIES BA FREE BOOK BA NE NA KUD'I AKAN KUD'I NAIRA 300 KACAL, NASAN KO MILLION NACE ZAKU IYA BIYA SABODA KUN SAN ALK'ALAMINA DA ZA'KI YAKE😅 KATIN MTN ZA'A TURO TA WANNAN NUMBER 09138224709 SAI SHAIDAR BIYA TA WANNAN NUMBER 08122188717_*


Zaune suke a farfajiyar gidan akan kujerun roba babu abinda kake jii sai kukan tsintsaye ga wata iska da take kad'a su wacce take k'a rasa su jin sauk'in soyayyar junan su, kafe shi da kyawawan idanuwan ta tayi kamar wacce bata tab'a ganin sa ba sai yau, wanda kuma kullum sai yazo gidan nasu dan kaf dangin ta babu wanda bai san Abdul ba, saboda rasiyya bata da wata magana sai ta Abdul ko kawayen ta ma dukan su sun san sa, shima a bangaren sa dangin sa sun san rasiyya saboda irin tsananin son da suke yiwa junan su, wanda suke ganin ba za su tab'a rayuwa ba, ba tare da juna ba.


Abdul ya kirawo sunan ta cikin muryar sa mai dad'in sauraro 

"Rasiyya"

"Na'am my Abdul" tayi maganar tana mai sakar masa wani irin murmushi wanda yake nuna alamun tsantsar soyayyar sa

"Wallahi a duk sanda nazo wajen ki sai naji wata nutsuwa tana kara shiga ta, ko da ace ina cikin damuwa sai na nemi damuwar ta wa na rasa ta, a kullum a kowane second sai naji son ki da kaunar ki yana kara shiga ta"

Kara fad'ad'a murmushin ta tayi tana tare da cewa "Hmm ai baka kai ni ba, nifa idan ina tare da kai sai naji kamar nafi kowa dacewa wallahi Abdul idan bada kai ba bazan tab'a iya rayuwa ba, ka zama wani b'angare a rayuwa ta,zan iya yadda na rasa komai nawa amman ba zan tab'a jure rashin ka ba Abdul i really love you"tayi maganar cikin wani irin yanayi wanda na rasa na dad'i ne ko a kasin haka.


"I Love you too Rasiyya Allah ubangiji ya bar mu tare har abada cikin so da kaunar junan mu" Abdul ya fad'a


"Amin ya rabbil'alamin".


Daga nan suka cigaba da hirar su ta masoya sai da aka kira sallar Azahar sannan Rasiyya taje ta zubo masa ruwan alwala a buta, sai da ta tsaya yayi alwalar sannan  ya d'ago yana kallon ta "Rasiyya daga masallaci zan huce kasuwa saboda Akwai kayan da za'a kawo mana kuma akwai bukatar ace ina gurin za'a saka su a shago".


Rasiyya tayi shuru dan sam bata son Abdul ya tafi, "kuma dan za'a kawo musu kaya sai ace sai dole yana gurin bayan akwai wasu wad'anda kin san ko ce musu yayi su tsaya a zuba kayan a gaban su zasu bii umarnin sa",duk wad'annan zantuttukan zuciyar ta ce take raya mata wata zuciyar tace "to kila ya gaji da hira dake ne shiyasa".


Abdul bai jira jin abinda zata ce ba yayi hanyar fita daga gidan dan kada ya rasa sallar, wannan abin yayi matuk'ar b'atawa Rasiyya rai wato kenan ya tabbata ya gaji da hira da ita ne, haka ta juya takoma gida d'akin ta ta nufa ta shiga toilet tayi alwala sannan ta dawo ta shimfid'a dadduma tayi sallah tana idarwa bayan tayi addu'o'i sannan ta koma kan gado ta kwanta tana cigaba da tunanin Abdul da kuma abinda yayi mata yanzu a haka har bacci ya kwashe ta, ba ita ta farka ba sai wajen karfe 4:30pm tana duba wayar ta taga missed calls d'in Abdul ya kai guda 30, cikin sauri ta dauki wayar da niyyar ta kirawo sa, sai abinda da yayi mata na dazu ya fad'o mata tayi wurgi da wayar tare da jan tsaki.


Toilet ta shiga tayi alwala sannan ta dawo tayi sallar la'asar ta fita zuwa kitchen domin ta taya mama aikace_aikacen gida duk da tasan a irin wannam lokacin mama ta gama duk aikin gidan, tana zuwa kuwa ta tarar mama ta gama aikin gidan jollof d'in shinkafa da taliyar da akayi da d'iba takoma d'akin ta tana cii tana ganin kiran Abdul yana ta shigowa wayar tayi banza tana gama cin abincin kiran Abdul d'in ya sake shigowa wayar kallon wayar tayi wacce ta wurga ta chan karshen gado, hannu ta saka ta dauko ta, ta d'aga kiran tare da karawa a kunnan ta, ba tare da tace komai ba.


Cikin muryar tashin hankali Abdul yake magana "Rasiyya menayi miki komai nayi miki bai kamata kiyi min irin wannan horon ba sai ki fad'a min gaba sai in gyara kin san dai ina tsananin son ki, wallahi da baki d'aga kirana ba to komai zai iya faruwa dani koma na rasa rai na" 

Cikin tsoron jin yace zai rasa ran sa Rasiyya ta shiga bashi hakuri da kawo masa dalilin da yasa bata d'aga kiran nasa ba saboda baccin da take yii, amman bata fad'a masa cewa saboda yace zai je a zuba kaya a gaban sa bane shiyasa tayi fushi saboda wannan kullum sai tayi masa mita amman sai yace wai idan bai je an zuba a gaban sa ba, ana samun matsala, ita kuma tana ganin kawai gajiya yayi da ita shiyasa da yazo sai yace zai je shago.


A hankali ya sauke ajiyar zuciya tare da cewa " kin tashi lafiya da fatan kin ci abinci dan bana so kina zaunawa baki ci abinci ba dan nasan da zaki kwanta baki ci ba"


Murmushi tayi tare da cewa "Wallahi my Abdul naci abinci yanzun nan kaga ma plate d'in a kusa dani"


"To masha Allah sallah fa, duk da nasan bakya wasa da sallah amman yau kam baki yi ta akan lokaci ba"


"Wallahi my Abdul bacci ne ya kwashe ni amman sai da nayi ta ma sannan na zubo abinci"


"Alhamdulillahi har naji dad'i dan nafi son matata ta kasance ita ce farko farko a b'angaren sallah"


Wani irin murmushi ta saki kamar yana ganin ta dan har sai da gefen kumatun ta ya lotsa (dimples) sannan tace "nima haka my Abdul"

Sun kwashi kusan awa daya suna waya dashi sannan daga karshe kowannan su ya kashe wayar da niyyar anjima sai k'ara yin wayar.


*'BANGAREN FATIMA*


Fatima macece kyakkyawa bafulatana ce, ba za'a kirata da doguwa ba kuma baza'a ce mata gajera ba zaune take akan kujerar d'akin ta ta zabga tagumi tana tunanin farhan ta rasa ya zata yi da zuciyar ta tana tsananin son farhan amman shi kuma duk duniya babu wacce ya tsana irin ta, ko yana zaune a guri tazo wucewa tashi yake ya bar gurin saboda a cewar sa, ko ganin ta ma baya son yii komai suna fatima ya gani sai ya dinga jin haushin su, babu irin wulakancin da ba ya yii mata amman sam tak'i ta rabu dashi.


Kawayen ta har zaunar da ita sukayi akan ta rabu dashi ta dena kula shii amman bud'ar bakin ta sai ce musu tayi "ita duk abinda farhan yake mata kara son shi take kuma ko kashe ta yace zai yii zata yarda kuma zatai farin cikin ace masoyin ta shine ya kashe ta da hannun sa, kuma zata bada wasiyya akan kada a hukumta shii akan wannan laifin domin hukumta shi akan kashe tan da yayi babban zunubi ne" 

Basu iya ce mata komai ba saboda takaici haka suka kyaleta suka zuba mata idanuwa.


Hoton sa da ta roki abokinsa fahad da ya turo mata ta shiga kalla tana zooming d'in hoton hawaye na zuba daga idanuwan ta "Farhan wallahi ina son ka bazan tab'a iya rayuwa ba tare da kai ba, ni nasan wata rana zaka fahimci irin abinda nake jii akan ka kuma zaka so ni, Farhan zan iya sadaukar da rayuwa ta indai akan ka ne domin saboda kai nake rayuwa a cikin duniyar nan, wallahi ni nasan kai ne miji na banda wani miji in ba kai ba, Farhan kai ne zab'i na ina kaunar ka fiye da yadda kake tunani haka tayi ta sambatun ta kamar wata mahaukaciya kamar an tsikare ta tayi zumbur ta tashi bayan ta ajiye wayar ta shiga toilet Alwala tayi sannan tazo tayi sallah raka'a biyu tayi addu'o'i ta dade tana rokon Allah ya bata Farhan sannan ta koma ta zauna tana cigaba da koke_koken ta kamar ko yaushe.


Tana zaunan kawai sai ta tuna yau su Farhan d'in suna da lecture karfe 4:00pm na yamma da ta duba agogon wayar ta sai taga 4:50pm tasan dai yanzu sun kusan fitowa daga lecture d'in kiran Fahad tayi dan shi Farhan d'in bashi da tsayayyar number dan duk layin da aka bata nashi indai yasan tasan shi to karya shi yake ya chanza wani ringing daya biyu ya d'aga "Assalamu alaikum Fahad kuna makaranta ne?" 

"Wa'alaikumussalam wallahi Fatima bama makaranta mun tashi tun karfe 4:30pm domin bamu dad'e a lecture d'in ba".

"Kana tare da Farhan ne?"

"Kinga yanzun nan kuka rabu dashi ya tafi gida"

"To shikenan sai anjima" ta fad'a tare da kashe wayar ta saki kukan takaici, Amman babu komai akwai gobe ta fad'a tare da goge hawayen ta.


*'BANGAREN SU RASIYYA*


Yau ta kama ranar lahadi Abdul yana gida bai fita ba saboda basa fita kasuwa ranar lahadi, jallabiya ce a jikin sa marun colour yana kwance kan makeken gadon d'akin nasa, tunanin Rasiyya ne ya cika masa zuciya tabbas yana tsananin son Rasiyya bama zai iya kwatanta irin son da yake mata ba amman ya fuskanci ita Rasiyya kwata_kwata bata bashi kulawar da ta dace shiyasa har ya fara tunanin ko ta samu wani ne amman wani bangare na zuciyar sa yana raya masa inda ta samu wani ai baza ta tsaya kula shi ba, haka dai yayi ta sake_sake har bacci mai nauyi yayi awan gaba dashi.


Kamar wanda aka mintsina ya tashi a firgice sakamakon mafarkin Rasiyya da yayi tana cikin mawiyacin hali sai kuka take tana kiran sunan sa.

"Rasiyya! Rasiyya!! Rasiyya!!!" abinda yake fad'a kenan babu shiri ya fad'a toilet yayi wanka ya dora alwala ya tada ikama domin gabatar da sallar magriba yana idarwa ya shirya cikin shaddar sa blue ya dauki makullin mashin din sa, ya fita daga gidan duk jikin sa sai rawa yake masa.


Tuk'i yake amman gaba daya tunanin sa da hankalin sa yana gurin Rasiyya irin yadda yake shararar gudu akan titi kadai zaka fahimci ba lafiya ba, burin shi kawai yaje yaga Rasiyya a wane irin hali take ciki duk da irin gudun da yake yii amman shi gani yake sam baya sauri.


Yana isa gidan su Rasiyya kuwa ya shiga jerawa mai gadin gidan hon kamar zai tashi duniyar, malam bala wanda shine mai gadin gidan su Rasiyya ya bud'e gate d'in gidan tare da mamakin wannan wanene yake yin wannan hon d'in kodai babu lafiya ne?.

Ai ba idar da yin tambayar ba yaga mashin din Abdul ya danno cikin gidan nan mamakin sa ya k'aru kuma ya tabbatar babu lafiya dan yasan Abdul mutum ne mai nutsuwa kuma bai tab'a zuwa gidan nan yayi irin wannan hon d'in ba haka ya tattara yakoma d'akin sa.


Yana zuwa wajen da aka tanada dan ajiye motoci yaja wani mugun burki ji kake 'kiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiii.......


A dai_dai lokacin da yasa kafa ya fito daga cikin motar Rasiyya tana fitowa daga cikin gida jin hon d'in motar sa ce yasa ta fito babu ko takalmi sai wani d'an karamin mayafi nasu kausar riga da siket ne a jikin ta.

Karasowa gurin da yake tayii tana zub'ar da hawaye tana fad'ar sunan sa shima yana fad'ar nata.

"My Abdul"

"Rasiyya"

Sai kuma ta fashe da kuka tana fad'ar ashe daman zaka iya wuni guda ba tare da kazo kaga lafiya ta ba ka barni a cikin damuwa asa zuciya ta a cikin wani irin hali, duk na rud'e nayi tunanin wani abin ne ya same ka.

A nan Abdul ya kara rud'ewa ya rasa ta ina zai fara farin handkey ya dauko a aljihun sa ya bata tare da cewa "Baby kiyi hakuri nasan ban kyauta miki ba amman kiyi hakuri dan manzon Allah nima kamar yadda kika wuni cikin damuwa haka nima na wuni".

Kallon sa kawai take ta shiga raya abubuwa da yawa a cikin zuciyar ta "ta yaya ma za'a ce wai ya wuni yana tunanin ta to mai ya hana shi zuwa ya ganta kuma me yasa bai kira ta ba kuma ta kira shi wayar sa a kashe wannan shine soyayyar daman".


Amman kawai ta nuna masa komai ya huce dan yanzu da ta fara yi masa korafi akan haka zai ce ta fiya yawan korafi bata da hakuri.

Haka ta dauko musu kujerun robar suka zauna suna fuskantar junan su.

"Rasiyya" ya kirawo sunan ta akaro na biyu 

"Na'am" ta amsa masa a takaice

"Baby wai har yanzu baki hakura ba, dan Allah ni na yarda kiyi min kowane irin hukunci ne amman Dan Allah karki hukunta ni ta wannan sigar" yayi maganar cikin muryar rarrashi.

Murmurshin yake tayi tare da cewa "Haba my Abdul ai nace maka komai ya huce, ya gida ya mamana da Abba"

"Duk suna nan lafiya kalau alhamdulillahi"

"Masha Allahu har nayi farin ciki, Allah ya kara musu lafiya da nisan kwana"

"Amin ya Allah, yau zan shiga in gaishe dasu mommy kam".

"Laaaa ai kuwa ka makaro yanzun nan mommy da Abba suka fita babu kowa daga ni sai su kausar"


"Wayyo Allah sai dai idan na kara dawowa".

"Haka ne kam"

"Rasiyya wallahi kullum bani da buri irin naga na mallake ki a matsayin matata uwar 'ya'yana farin cikin raina".


Hannayenta dukkansu ta saka ta rufe fuskar ta, cike da jin kunyar sa.


Murmushi yayi yana fad'ar "chabbb baby me zan gani kunya ai kuwa gwanda ki ajiye wannan kunyar fa domin zata hanani ganin kyakkyawar fuskar matata"


Bud'e fuskar tata tare da langwab'ar da kanta tana fad'ar "My Abdul to ai kai kasa naji kunyar amman na bud'e fuskar yanzu to"


Irin yadda tayi maganar cikin wani irin salon shagwab'a sai da yasa zuciyar raurawa.


Haka suka cigaba da hirar sannan sukayi sallama suna masu kewar junan su.


*'BANGAREN FATIMA*


Tun k'arfe 7:30am ta gama shirin zuwa makaranta ta zauna tana jiran k'arfe 8:00am tayi ta shiga school d'in tunanin mahaifiyar ta ya fad'o mata a cikin ranta "Allah sarki ummata insha Allahu ranar Asabar zanje inga ya lafiyar ki take". 

Kiran wayar da ya shigo wayar ta ne ya katse mata tunanin mahaifiyar tatan ta d'aga tare da yin sallama

"Assalamu alaikum"

Daga chan bangaren ya sauke ajiyar zuciya tare da amsa mata sallamar.

 "Wa'alaikumussalam wa rahmatullahi ta'ala wa barakatuhu malama Fatima bintu ya kike" .

"Lafiya alhamdulillahi" ta bashi amsa cike da mamakin wannan waye tunda ya ambaci sunan ta, tasan ya santa sosai, ta dora da cewa amman ban gane mai magana ba dan Allah idan babu damu kayi min bayani.


"To yanzu dai lokacin shiga makarantar ki yayi, idan kin dawo gida mayi magana sai anjima ki kula da kanki" yana ga fad'ar haka ya kashe wayar.

"Hmmm to koma waye dai shi ya sani" ta fad'a tare da daukar jakar ta, ta nufi school bayan ta kulle gidan.

Sai da suka kammala lectures d'insu gaba daya ta fito ta nufi ajin su Farhan, tana zuwa ta tarar da malami a ajin dan haka ta tsaya har sai da yaga yi musu lecture d'in ya fita sannan ta shiga ajin da sallama kallon ta gaba daya 'yan ajin suke tare da tausaya mata saboda kaf makarantar babu wanda bai san irin son da Fatima takewa Farhan ba shi kuma duk duniya babu wacce ya tsana sama da ita, Fahad ne ya amsa mata sallamar tare da yi mata sannu da zuwa.

"Ahhh Fatima kece kika kawo mana ziyara to sannun ki da zuwa" 

Murmushi tayi tare da cewa "Yawwa Fahad ya karatu"

"Hmm karatu gashi nan muna tayin sa"

"Allah ubangiji ya taimaka"

"Amin"


Duk wannan hirar da suke yii Farhan na jin su, takaici da bak'in ciki suka kamashi wato shi wannan Fahad d'in har tsayawa yake yana magana da wannan kucakar yarinyar duk sai yaji ya kara tsanar ta kuma yaji Fahad d'in ya bashi haushi.

"Farhan gurin ka nazo" yaji muryar Fatima ta daki dodon kunnan sa, kallon ta yayi tare da jan tsaki kamar bazai ce komai ba sai kuma yace "To 'yar wahala ai kin saba wahala daman, zuwa gurin wanda duk duniya babu wacce ya tsana sama dake, wai ke Fatima kike kowa baki da zuciya ne, ke wace irin yar dak'ik'iya ce, dabba mara hankali, nace bana son ki bana son ki ko ana dole ne soyayyar 'yar gidan talakawa kawai shashasha wacce bata san mai take yi ba" yana gama fad'ar haka ya tashi zai tafi.

Ta sha gaban sa tana hawaye ai kuwa babi wata_wata ya kama kanta ya gara da tiles d'in bangon ajin da karfe jii kake gauuuuuuuuuuuuuuuuuuu..........


Anan take jini ya fara ambaliya ta fad'i kasa sumammiya, shi kuma ya tsallaketa yayi tafiyar sa.

Gaba daya 'yan ajin sukai kan Fatima suna kiran sunan ta amman inaaaaaaa....

Haka yammatan ajin suka ciccib'eta sukai asibitin dake cikin makarantar suna kiran "Nurse! Nurse!! Nurse!!!"

Sai ga nurse nan tare da gadon da ake dora mara lafiya idan ankawo su, suka shiga da Fatima cikin asibitin *(EMERGENCY ROOM)* suka nufa da ita likitoci suka shiga bata taimakon gaggawa.


Yammatan suka juya suka tafi nasu gurin ya rage Fahad ne kadai bai iya tafiya ba.


Fahad kuwa ya kasa zaune ya kasa tsaye sai zagaye yake a cikin asibitin ya kafe kofar emergency room d'in da ido so yake doctor ya fito ya fad'a masa halin da Fatima take ciki, fatan sa dai Allah yasa bata mutu ba.


An kwashi kusan awa d'aya sannan yaga ana kok'arin bud'e kofar *Emergency* d'in doctor Nabil ne ya fito tare da wata nurse tana biye da shi a baya, da sauri Fahad ya k'arasa har yana tuntub'e yana fad'a "doctor ya Fatima take da fatan bata mutu ba dan Allah doctor ka sanar dani ko hankali na ya kwanta" yayi magana muryar sa na rawa cike da tashin hankali.

Kallon sa yayi sannan yace "ka biyo ni office" yana gama fad'ar haka ya rab'a ta gefen sa ya huce, shima Fahad ya rufa masa baya ita kuma nurse d'in ta koma bak'in aikin ta.

Suna shiga office d'in doctor Nabil ya huce kujerar sa ya zauna, shi kuma Fahad ya zauna a kujerar da ake ganin likita gaba daya ya nutsu akan jin me doctor d'in zai ce, shi kuwa doctor nabil sai da yayi 'yan rubuce rubucen sa a takada sannan ya mik'awa Fahad tare da cewa "gashi wad'annan magungunan zaka je ka siyo mata, domin bayan irin gagarmayar da muka yi da taimakon ubangiji mun samu jinin ya tsaya munyi mata allurar bacci domin ba k'aramar buguwa tayi ba dan irin wannan buguwar na iya haifar da mutum ya sami matsala a kwakwalwar sa, yanzu a kowane lokaci zata iya farkawa".


Wata sassanyar ajiyar zuciya Fahad ya saki tare da furta "Alhamdulillahi" ya fita bayan yayi wa doctor Nabil d'in sallama *Pharmacy* ya huce yaje ya siyo magungunan sannan ya nufi d'akin da aka kwantar da Fatima, ya k'arasa bak'in gado yana kallon yadda aka had'e mata goshin ta, da bandage "Allah sarki Fatima Allah ya saka miki" ya fad'a cikin muryar tausayawa.


Zama yayi a gefen gadon sai da aka kira sallar Azahar ya tashi ya fita zuwa masallacin dake cikin makarantar.


*BANGAREN RASIYYA*


Yau ma kamar kullum suna zaune ita da Abdul suna hirar su ta masoya.

Rasiyya ta kalli Abdul d'in cikin marairaicewa tace "My Abdul yau fa wak'a nake so kayi min"

Murmushi yayi sannan yace "To badamuwa wace iri ya kike so"

"Ni ba ta mawak'a ba, yanzu nake so ka k'irk'ira sai kayi min"

"Wayyo my ni da ban tab'a yin wak'a ba, amman tunda kece zan gwada yin ta yanzun nan kuwa, amman....."


Kiran wayar da ya shigo wayar Abdul ne yasa shi yin shuru bai k'arasa maganar ba.

Shuru yayi yana kallon screen d'in wayar number ce babu suna, ya d'aga tare da yin sallama

"Assalamu alaikum"

 daga chan bangaren aka amsa sallamar 

"Wa'alaikumussalam baby na"

Yayi mamaki sosai jin tace masa "baby na" dan haka cikin mamaki da neman sanin wacece yace.

 "Ban gane mai magana ba wacece" 

"Masoyi amman nayi mamaki da kace wai baka gane ni ba amman bakomai" tana gama fad'ar haka ta kashe wayar.


"To ikon Allah" Abdul ya fad'a cike da mamaki


Rasiyya kuwa kishi ya gama tirniketa dan taji duk yadda sukai, kenan Abdul yaudarar ta yake yana da wata budurwar bayan ita.


"Abdul bai tab'a tunanin zaka tab'a yi min haka ba amman nagode nagode sosai idan halin ka haka yake to wallahi baka da hali mai kyau banza mayaudari".

ta k'arasa maganar cikin sarkewar murya bata jira jin abinda zai ce ba ta tashi ta shiga gida da gudu tana kuka tare da dana sanin, sanin Abdul a rayuwar ta.


Shi kuwa Abdul tashi yayi a gigice yana kiran sunan ta.

"Rasiyya! Rasiyya!! Rasiyya!!!" 


Amman ina tuni ta shige gida, haka ya samu ya nufi motar sa jiri na kokarin yarda shi, bude motar yayi ya shiga ya kasa tafiya ya kifa kansa akan sitiyarin motar zuciyar sa tana mai yin zafi, wato kwata_kwata ya fuskanci Rasiyya ita sam duk kok'arin nuna mata soyayya da yake bata gani, yaga a gaban ta ya nuna bai san yarinyar ba amman ita tana tunanin yaudarar ta yake.


Haka dai ya samu yayi addu'o'i sannan ya ja motar, tuki kawai yake amman kwata_kwata baya ganin gaban sa Allah ne kawai ya tsare shi ya isa gida lafiya.


Yana zuwa kai tsaye bangaren sa ya shiga a falo ya nemi kujera ya kwanta tare da lumshe idanuwan sa wadanda sukayi jajahur kamar an watsa barkono.

Haka ya wunii cikin wani irin yanayi wanda Allah ne kadai yasan abinda yake ji a zuciyar sa, a wuni daya duk ya fita a hayyacin sa dakyar yake iya motsi.


Ita ma Rasiyya tunda ta shiga gida ta tarar da mama na falo tana kallon wani film d'in hausa a tashar arewafly t.v ta fad'a kanta tare da rushewa da wani irin wahalallen kuka tana fad'in .


"Wayyo Allah mama Abdul ya cuce ni ya yaudare ni daman ba tun yau ba nake fuskantar ba ya bani cikakkiyar kulawar da ta kamata amman saboda shi mayaudari ne kullum cewa yake yana sona ashe mama Abdul yana da wacce yake so zai aura".


Mama ta d'ago ta cike da mamakin abinda take cewa "Kai Rasiyya! Duk irin son da Abdul yake nuna miki kice yana da wacce zai aura karfa wasu ne, suke son raba ku kike son ki biye musu, su kai ki su baro ki, amman ni ban yarda Abdul zai iya yaudarar ki ba".


Rasiyya ta zauna sosai a kujerar da maman take tare da yin wani irin murmushin takaici tana fad'ar "mama babu wanda yake ziga ni yanzun nan muna tare dashi wata ta kira shi kuma harda ce masa baby, amman yake son raina min wayo wai bai san wacece ba bayan da kunne na naji, mama kinsan inda wani ne ya fad'a min wallahi bazan tab'a yarda ba kinsan yadda nake son shi" ta k'arasa maganar cikin muryar kuka.


A nan mama ta shiga rarrashin ta da maganganu masu dad'i tare da kwantar mata da hankali anan ta kwanta a jikin maman ta shiga sauke ajiyar zuciya ta shiga karanta addu'ar da idan mutum yana cikin damuwa yake karantawa "Allahumma la sahala illa ma ja'al tahu sahala wa'anta taja'alul hadhna idha shiita sahla" Allah ya datar damu baki daya.


Anan take bacci b'arawo yayi awan gaba da ita, mama ta gyara mata kwanciyar akan kujera sannan ta shiga kitchen domin ta d'ora musu abincin dare, fried rice tayi sannan ta dawo falon ta cigaba da kallon ta.


Sai wajen karfe 8:30pm Rasiyya ta farka bayan tayi addu'ar tashi daga bacci tare da salati ga annabin mu, annabi muhd (s.a.w) Allah ya taimaka duk wani bak'in ciki da bacin ran da take ciki taji duk ya ragu daga cikin zuciyar ta.


Kok'arin bud'e kofar falon da akayi ne yasa gaba daya suka mayar da hankalin su ganin waye zai shigo, daleela k'awar Rasiyya ce ta shigo cikin shigar ta ta kamala hijabi ne har k'asa a jikin ta, dauke da sallama a bak'in ta.


"Assalamu alaikum"


 Suka amsa sallamar gaba d'ayan su a tare.


"Wa'alaikumussalam"


ta k'ara so ta tsugunna har k'asa ta gaisar da mama.


"Ina wuni mama"


Cikin fara'a ta amsa mata.


"Lafiya kalau daleela ya su maman naki da 'yan uwa  ki"


"Suna nan lafiya mama, mommy ma tace tana gaishe ki kafin tazo"


"To ina amsawa"  


Mama ta fad'a tare da tashi ta nufi d'akin ta

 

Kallon Rasiyya sosai daleela tayi tare da cewa.


"Besty ko ba'a fad'a min ba nasan kina cikin tsananin damuwa"


Anan fa daleela ta, tab'o mata inda yake mata k'aikayi Rasiyya tayi raurau da ido hawaye yana kok'arin fitowa daga idanuwan ta.


Cikin tashin hankali daleela tace "me yafaru besty kodai baki da lafiya ne?"


Cikin rawar murya Rasiyya ta fara magana "Aa besty lafiya ta kalau, besty Abdul ne, Abdul ya cuce ni ya yaudare ni a lokacin da ya bari na kamu da tsananin son sa"


Cikin mamaki daleela take tambayar Rasiyya "Me Abdul d'in yayi miki" 


Anan ta kwace duk abinda ya faru dazu ta fad'a mata tare da cigaba da kuka.


Daleela ta tausayawa Rasiyya sosai saboda tasan irin yadda k'awar ta ta, take son Abdul d'in kamar ran ta.


Cikin muryar rarrashi ta shiga bawa k'awar ta ta baki bayan ta zauna kusa da ita.


"Besty yau dai ina son ki bani labarin yadda kuka had'u da Abdul d'in nan naki dan ni ban san had'uwar ku ba, amman nasan soyayyar ku"


"Eh besty gaskiya kam ba za kisan had'uwar mu dashi ba, dan lokacin da kika tafi gidan aunty maryuda ne a satin muka had'u"


"Ahhh dole kam dan kuwa na kusam shekara a gidan aunty maryuda"


Cikin dasasshiyar muryar ta wacce kana jii kasan tasha kuka ta fara bawa Daleela labarin yadda suka had'u da Abdul d'in.


"A ranar wata labara na fito daga super market ina ta sauri saboda irin hadarin da ya had'u lokaci guda a koda yaushe za'a iya tsinkewa da ruwa, gashii idi driver tunda kai ni yace yana da uzuri zai je ya dawo, amman har na gama shopping d'in na fito bai dawo ba gashi duk wani mai napep da zan gani a cike yake da mutane.


Tafiya nake dan a lokacin duk a rud'e nake kar ruwa ya sauko gashi babu wanda nasani a gurin.


Ban ankara ba kawai najii an dauke ni da mari, jijicewa iya jiji cewa nayi a wannan lokacin dan har shopping d'in da nayi sai da suka fad'i a k'asa suka tarwatse, ina d'ago kai naga wata budurwa ce wacce bata wuce sa'a ta ba, ta fara magana cikin isa da kasaita.


"ke daga ganin ki 'yar gidan talakawa ce, kina ganin zan wuce amman kina kok'arin bangare ni shashasha wacce.........."


Ai bata k'arasa maganar ta tan, ba sai gani nayi wani kyakkyawan saurayii ya dauke ta da mari wanda sai da ta tafi taga taga kamar zata fad'i.


Kallon sa nake kawai iya had'uwa ya riga ya had'u ta ko'ina cikin muryar sa mai dad'in sauraro ya fara magana.

"ke daga ganin ki baki da tarbiyya kawai saboda wajen uban ki ne ya bud'e shi, shine zaki dauke ta da mari ba tare da tayi miki komai ba, kawai dan zaki wuce saboda ke dabba ce"


Duk tsiwar yarinyar da jiji da kanta sai gashi tayi tsit ta kasa magana.


Haka ya tsugunna ya kwashe min kayan da na zubar na shopping d'in sannan ya d'ago ya miko min.


Karb'ar ledar nayi tare da yi masa godiya "Nagode sosai yaya na"


Murmushi yayi tare da cewa "babu komai" .


Ruwan da aka fara ne lokaci d'aya kamar da bak'in kwarya ya sakani cewa "na shiga uku ni Rasiyya yanzu ina zanje"


"baki shiga uku ba idan babu damuwa zan iya ragewa k'anwar tawa hanya"


Ban san sanda nace masa "ai kuwa da babu abinda zan ce maka saboda idan na shiga ruwa zazzab'i nake yi"


Cikin sauri yace shine baki fad'a min ba "kizo mu shiga mota" magana yake cikin rud'ewa


Haka muka nufi motar tasa shi ya bud'e min mazaunin gaba na shiga shi kuma ya zagaya gurin driver ya zauna.

Har ya tada motar muka fara tafi ina kallon wannan yarinyar tana ta faman kallon motar.


A haka ya fara tuki muka hau kan titi muna hirar mu kamar irin mun dad'e dashi gaskiya Abdul babu ruwan shi ko zaman mintine daya kayi dashi sai ya shiga ran ka, gashi da wasa da barkwanci, da kwatancen da nake masa ya kainii gida ko dana ce masa zan sauka a bak'in gate sai yace.


"Aa Rasiyya bazan yarda ki sauka anan ba saboda wannan ruwan kina ganin shii da k'arfin shi kuma keda bakya son ruwa"


Ban yi mamakin yadda yasan sunana ba saboda lokacin da muke gurin shopping da ruwan ya fara saukowa na ambaci sunana.


Har cikin gida ya shiga dani yayi parking, a gurin da aka tanada domin yin parking, sai da muka yi musanyar number sannan na bud'e motar na shiga gida, tun daga ranar soyayya mai k'arfi ta shiga tsakanin mu kullum sai ya kira ni a waya kuma yazo.


"To daleela kinji yadda muka had'u da Abdul"


Daleela dai tunda Rasiyya ta fara magana ta kafe ta da ido har ta gama sannan ta numfasa tace.


"tabbas labarin had'uwar ku da Abdul yana da ban mamaki"


Anan dai ta shiga jan Rasiyya da hira har tadan saki kadan, amman ita daleela akwai abinda take tunani a zuciyar ta game da matsalar da Rasiyya da Abdul d'in suka samu amman dai tabar shii iya zuciyar ta.


Sai wajen isha'i bayan sunyi sallah suka ci abinci Daleela ta shiga tayiwa mama sallama tafito Rasiyya ta rakata har bakin gate sannan ta dawo d'akin ta kai tsaye ta shige ta kwanta zuciyar ta na cigaba da suya.



*B'ANGAREN FATIMA*


Fahad yana zaune ya kafe ta da ido duk hankalin sa ya tashi saboda doctor yace ba za ta dad'e ba zata tashi amman tun karfe 11 har karfe 5 yanzu Fatima bata farka ba zuwan sa uku gurin doctor nabil yana ce masa korafin bata farka ba, yana bashi hakuri akan cewa zata farka akwai bukatar ace ta samu hutu sosai ne, saboda lafiyar kwakwalwar ta.


A zuwa na ukun ne ya saka kuka "yana fad'ar doctor dan Allah dan Annabi idan Fatima mutuwa tayi ka sanar dani domin na sani"


Doctor nabil yayi matukar tausayawa Fahad cikin muryar rarrashi ya fara magana "malam Fahad ya kamata ka kwantar da hankalin ka, inda Fatima ta mutu bazan tsaya ina bata maka lokaci ba, Fatima tana raye kuma a yau d'in nan da ikon ubangiji zata tashii saboda buguwar da tayi ne shiyasa tana buk'atar samun hutu ta haka ne kwakwalwar ta ba za ta samu matsala ba"


"To shikenan doctor hankali na ya tashi ne sosai da naga an kwashi awanni bata farka ba"


"Wannan duk ba matsala bane, amman dan Allah tana farkawa kazo ka sanar dani domin muk'ara duba ta sosai"


"Insha Allahu doctor tana farkawa zanzo na sanar da kai"


Haka ya tashi ya nufi kofar fita daga cikin office d'in, ya cikaro da k'awayen Fatima, Fadila da Faleela suna kok'arin shiga office d'in.


Suna ganin Fahad dukan su suka fara tambayar sa cike da rud'ewa  "Fahad ya Fatima take"


"Muje d'akin da take" ya fad'a tare da yin gaba suka rufa masa baya cikin sauri.


Suna shiga d'akin suka yii gurin gadon da take Fadila ta zauna a wajen kan ta ida kuma Faleela ta zauna wajen kafafuwan ta.


Shi kuwa Fahad kujerar robar da aka ajiye domin kula da mara lafiya anan ya zauna yana fuskantar su.


"Allah sarki Fatima, Fahad to me doctor d'in yace" 

Fadeela tayi maganar cikin muryar tausayawa.


Bai b'oye musu komai ba saboda yasan irin amincin da yake tsakanin su, ya kwashe duk abinda doctor yace masa tun daga farkon zuwan su asibitin har zuwa yanzu.


Faleela wacce ita tana da saurin kuka, tuni ta fara zubar da hawaye tare da yiwa K'awar tasu addu'ar Allah ya gashi kafad'unta.


Fadeela kuwa wani irin haushin Farhan ne ya turnike zuciyar ta.


"To shiii wanda yayi mata aika_aikan yazo ya duba ta" ta fad'a cikin muryar dake duba tsantsar haushin farhan d'in


Girgiza kai fahad yayi alamar "A'a"


"Gaskiya Fahad kayi hakuri da abinda zan fad'a nasan Farhan abokin ka ne amman wallahi ban tab'a ganin mara imani mara tausayi kamar sa ba"

Faleela ta fad'a cikin kuka.


Fahad bai iya cewa komai ba, saboda shii kanshi yafara tsora ta da lamarin Farhan d'in bai tab'a tunanin haka daga gurin sa, kenan zai iya kashe Fatima kamar yadda kullum idan yana masa maganar Fatima yake ce masa.


Maganar da suka yii jiya ce ta fad'o masa suna zaune a d'akin su bayan sun dawo daga makaranta.


Fahad ya kalli Farhan wanda yake kwance rik'e da littafi yana karantawa.


"Abokina wai meyasa ba zaka yarda kaso Fatima bane, wallahii yarinyar tana tsananin son ka, ba zaka tab'a samun irin wacce zata so ka haka ba, musamman a wannan zamanin da yammata suka saka yaudara a zuciyar su"


Wani irin wawan tsaki ya ja cike da haushin abokin nasa 


 "Wai dan Allah Fahad meyasa idan mun zauna baka da magana sai na wannan shegiyar yarinyar wallahi da ina da dama Wallahi kaji na rantse maka kashe ta zan yi na tsane ta ban tab'a tsanar wani a duniya irin yarda na tsani yarinyar nan ba, amman kai na fuskance ka kana son yii min maganar ta, to wallahi idan kana so mu shiri kadai nai min maganar ta"


Muryar Faleela ce ta dawo da Fahad daga tunanin da ya tafi.


"Alhamdulillahii Fatima ta fara motsi da hannun ta".


Cike da murna Fadila tace "Alhamdulillahii Allah mun gode maka"


A hankali Fatima ta shiga farfar da ido alamun tana son da bud'e su, tun tana ganin dishi~dishi har ta fara ganin sosai.


"Farhan!"

"Farhan!!"

"Farhan!!!"


Abinda take cewa kenan muryar ta a shak'e.


Gaba d'aya tausayin ta ya lillib'e su Faleela da Fadeela saboda shii Fahad tunda Faleela tace Fatima ta fara motsi da hannun ta ya fita domin ya kirawo doctor nabeel.


"Yanzu duk irin abinda yayi mata ace wai ta farka tana kiran sunan sa"

Faleela ta fad'a cike da alhini


"Hmmm Faleela kenan irin wannan son ne ake kiran sa da mugun so, sai dai fatan mu Allah ya yaye mata muku ma Allah ya raba mu da irin wannan ya kare mu daga son naso wani"

Fadeela fad'a tare da rik'e hannun Fatiman.


"Amin ya rabbil'alamin"

Faleela ta fad'a tana cigaba da kallon fatima wacce har zuwa yanzu kiran sunan Farhan take.


Doctor nabeel da Fahad ne suka turo kofa suka shigo dauke da sallama a bakin su.


"Assalamu alaikum"


Amsawa suka yi gaba dayan su.


"Wa'alaikumussalam"


Tashi suka yi domin su bawa doctor daman duba Fatiman sosai.


A nan dai doctor nabeel yayi mata gwaje gwajen sa Sannan yace.


"Kun bata wani abun ne da ta tashi"


"A'a babu abinda aka bata"

Fadila ta fad'a


"To yanzu ku bata koda ruwan tea ne sai ku bata magungunan ta sha"


Faleela tace "to bari inje in had'o mata tea d'in in kawo"

Bata jira cewar su ba ta fita da sauri.


Ba'afi mintune 2 ba sai gata ta dawo rik'e da dan karamin cup mai murfi.


Fadeela ce ta karb'a tak'arasa gurin Fatima wacce take kwance tana kiran sunan "Farhan".


Da taimakon Faleela ta tallafo ta, suka jinjina ta da gadon asibitin, Fadeela ta shiga bata tea sai da ta sha rab'in kofin sannan ta "Girgiza kai" alamar ya ishe ta.


Suka bata magungunan sannan suka kwantar da ita, a hankali ta lunshe idon ta.


"Allah ubangiji ya yaye miki wannan mugun son Fatima"


Doctor nabil ya fad'a domin kuwa kaf makarantar su har 'yan asibitin sun san irin yadda Fatima take son Farhan d'in.


"Amin ya Allah" suka fad'a gaba d'ayan su har da Fahad.


Doctor nabeel ya fita daga d'akin ya nufi office d'insa.


Ganin har k'arfe 8:00pm Fahad bai da niyyar tafiya yasa Fadeela tace "Fahad ya kamata kaje gida ka huta mu zamu kwana da ita"


"To shikenan Fadeela mu kwana lafiya" ya fad'a tare da tashi ya nufi kofar da zai fita daga d'akin.


"Amin Fahad mun gode Allah ubangiji ya kare ka da kariyar sa ya baka duk abinda kake nema, kai d'in na daban ne, ba kamar abokin ka ba"

Faleela ta fad'a cike da yaba abinda Fahad d'in yayi yau.


Juyowa yayi yana murmushi yace "Amin Faleela nagode"


Yana fada ya juya ya fita daga d'akin, sai da yayi sallar ihsha'i sannan ya nufi hostel d'in maza d'akin su ya nufa kai tsaye.


Yana shiga ya tarar da Farhan yayi d'ay_d'ay akan katifa yana baccin sa hankalin sa kwance.


Mamaki da takaici suka kama shi.

"wato yaje ya kusan kashe 'yar mutane amman yazo har ya iya kwanciya bacci"

 Ya fad'a a fili yana cigaba da kallon sa, tsaki ya ja ya shiga toilet yayi wanka sannan yazo ya kwanta a katifar sa batare da ya k'ara kallan gurin da Farhan d'in yake ba.


*BANGAREN RASIYYA*


Wani irin nishi yake wanda dakyar yake iya fitar da numfashi, dan jin numfashin sa yake kamar zai dauke, yau ya kira Rasiyya kusan sau d'ari amman bata d'aga ba daga karfe ma ta kashe wayar.


Wasu zafafan hawaye ne suka fara ambaliya akan kyakkyawar fuskar sa, wacce tayi jaaa sosai saboda irin kukan da yasha daga jiya zuwa yau, kansa na wani irin sara masa kamar zai fita daga gangar jikin sa.


Wayar sa ce wacce take kan fridge ce ta shiga ruri ko kallon inda take bai yii ba, sai kuma yayi tunanin kodai Rasiyya ce take kiran sa, a haka ya tashi a daddafe ya zauna akan kujerar  yana cigaba da yin nishi kamar wanda yayi tsere, ya dauki kusan mintune 5 a haka kafin ya saka hannu ya dauko wayar har kiran ya katse.


Kallon number yayi sosai tabbas wannan number da ita aka kira sa jiya lokacin da yake wajen Rasiyya.


Wani kiran ne ya shigo, kamar bazai dauka ba dan har ta kusan katsewa sai kuma ya dauka.


"Baby ka hau whatsapp d'inka na turo maka sako"


Abinda aka fad'a kenan aka kashe wayar.


Babu shiri ya bud'e data ya shiga whatsapp d'in, number da aka kira shi da ita, ita ya gani an turo masa hotuna guda goma amman duk basu bud'e ba anan ya shiga bud'e hotunan daya bayan daya.


Wata iri yar razana yayi lokaci d'aya kuma gaban sa yayi wani irin bugawa, Rasiyya ya gani tare da wanii saurayi gaba daya hotunan kana kallo zaka san akwai soyayya a tsakanin su.


 wani hoton wanda Rasiyya ta dafa kafad'ar wannan saurayin shi kuma yana zaune ita kuma tana tsaye ta leko da fuskar ta tana kallon sa tana murmushi.


Abdul bai san sanda yayi wurgi da wayar ba, tayi watsa_watsa a kasa, wani irin tari ne ya sark'e shi haka ya shiga yin tarin yana dafe k'irgin sa.


A dai_dai lokacin kuma abokin sa Shamsidden ya shigo yana ganin irin yanayin da abokin nasa yake ya fita da sauri yaje ya kirawo mummy wacce take bangaren ta ita sam bata san duk abinda yake faruwa ba dan Abdul d'in ya saba zama a d'aki shi kadai.


Mummy tunda ta shigo taga halin da d'an nata yake hankalin ta yayi mugun tashi, wayar ta ta dauko ta lalubo number doctor d'in gidan da yake duba su idan wani bashi da lafiya bugu d'aya biyu ya d'aga tare da yin cikakkiyar sallama.


"Assalamu alaikum"


"Wa'alaikumussala doctor hafeez dan Allah komai kake yii ka bari kazo ka duba Abdul kaga yanzun nan shamsudden ya shiga d'akin sa ya ganshi cikin wani irin hali shine ya kira ni kaga maganar da nake maka ma bai san suwa nene akan sa ba".


"Subhanallahi to gani nan yanzun nan zan k'ara so daman ina hanyar komawa gida ne"


"To shikenan nagode sai ka k'araso" mummy tana gama magar ta kashe wayar.


Ko mintune 5 ba'a yi ba sai ga doctor hafeez ya danno hancin motar sa cikin katafaran gidan, Shamsuddeen ne ya fita ya shigo dashi har bangaren Abdul d'in, anan take doctor hafeez ya shiga duba Abdul d'in bayan ya gano cewa yana cikin tsananin damuwa kuma zuciyar sa lokaci daya tayi muguwar razana allurai yayi masa sannan ya cewa shamsuddeen.


 "Dan Allah taikama min mu daga shii kuma inda sosa mune a kwantar dashi a inda zai wataya saboda wannan kujerar tayi masa kad'an"


Cikin sauri mummy tace "to shamsuddeen mu shigar dashi bedroom d'in sa"


"To mummy" shamsudden ya fad'a cike da ladabi.


Haka suka kamashi suka kai shi har kan gadon sa sannan suka dawo falon inda mummy take zaune ta zabga tagumi tana tunanin irin halin da d'an nata yake ciki.


Zama suka yi gaba d'ayan su a kujerar da take fuskantar mummy doctor hafeez ya fara yiwa mummy bayanin rashin lafiyar Abdul d'in.


"A gaskiya hajiya Abdul yana cikin tsananin damuwa, wanda a gwaje_gwajen da nayi masa na gano kuma zuciyar sa tayi wata iri yar razana lokaci d'aya wanda indai aka ce mutum yayi iriyar razanar nan to hakan na iya jawowa mutum ya rasa rayuwar sa amman Alhamdulillahi nayi masa allurai wacce a cikin alluran da nayi masa har da ta bacci zai dan dad'e yana bacci hakan ne zai saka ya farka lafiya kalau amman sai an kula dashi saboda indai bai dai na shiga cikin damuwa ba za'a iya samun babbar matsala Allah ubangiji ya kiyaye"


Mummy da Shamsudden sunyi matukar girgiza da jin abinda doctor yace "Innalillahi wa inna ilaihi raju'un nii haulatu meya damu Abdul da har ya bari hakan na kok'arin raba shi da rayuwar sa" sai kuma ta fashe da kuka.


Cikin tashin hankali shamsudden yace.


 "Haba mummy ki dena kuka nan Dan manzon Allah so kike in rasa inda zan saka rai na kuma yanzu ba lokacin kuka bane saboda babu abinda kuka zai yi mana Dan Allah ki de na"



"Hajiya ki dena kuka indai kuka bii abubuwan da nace muku kuka kiyaye shi daga shiga damuwa zai warke kamar bai tab'a yin cutar ba"


Shuru tayi tare da goge hawayen ta.


Tashi doctor hafeez yayi bayan ya bawa Shamsudden takardar magungunan da ya rubuta yace "To ga wannan aje a siyo yana tashi idan aka bashi abinci sai a bashi ya sha".


"Hajiya ni zan huce"

Kudi ta bashi masu yawa sannan tayi masa godiya, shamsudden ya daukar masa jakar sa, yana fad'ar


 "Mommy zan raka shi daga nan zan huce in siyo magungunan"


"To shikenan bari in baka kud'in magungunan"


"A'a mummy ba sai kin bada ba, ai Abdul komai nayi masa ban fad'i ba dan aboki ne nagari"


"Hakane to shikenan sai ka dawo"


Bin bayan doctor hafeez yayi wanda tuni ya fita sai da ya raka shi har motar sa  ya bashi jakar sa sannan ya juya ya shiga motar sa domin zuwa siyo magungunan.


Ita kuma mummy bedroom d'in Abdul ta shiga ta zauna kusa dashi tana kallon sa cike da tausayin d'ana ta.


Yau da wani irin matsanancin zazzab'i ta tashi ga wani irin sarawa da kanta yake yii kamar zai rabe gida biyu, kwana tayi tana tunanin Abdul a cikin ran ta, tana ganin kiran shi amman kishi da haushin abinda yayi mata ne yasa ta k'in d'aga wayar, amman duk kiran da yake mata sai taji har cikin zuciyar ta, zuciyar ta sai tayi mata wani irin bugu tare da harbawa, kuma gashi wani irin sabon son Abdul d'inne yake k'ara ratsa ta, daga jiya zuwa yau son shi ya k'ara ninkuwa a cikin zuciyar ta.


Dakyar ta iya tashi ta shiga toilet a daddafe jiri na neman yarda ita, wanka tayi sannan tazo ta sha tea saboda irin yunwar da take jii tana kok'arin yi mata illa, maganin zazzab'i da ciwon kai tasha takoma ta kwanta akan gadon, wayar ta ta jawo ta shiga wajen image folder guda ta ware da hotunan Abdul ta danna folder ta shiga kallon hotunan tana kuka take da sambatu iri_iri


"Haba my Abdul meyasa kayi min haka sam hakan bai dace ba, nice fa babyn ka Rasiyya kasan ina son ka fiye da yadda nake son kai na, zan iya yin komai indai akan son ka ne, kasan kai ne habibin zuciya ta, kaine kadai zuciya ta ta amince dashi ina son ka ina kaunar ka, ban chanchanci haka daga wajen ka ba" ta k'arasa maganar take da fashewa da kuka ta rumgume wayar kuka take sosai zuciyar ta na cigaba da zafi gami da tsantsanr son Abdul d'in.


Ta dauki kusan 45 tana cikin wannan halin, amman abin mamakin kuma lokaci d'aya ta mike zaune tare da share hawayen fuskar ta, ta maida duban ta kan wayar ta wanda har yanzu hoton Abdul yake bayyane a jikin ta.


Kallon sa take kamar baza ta dena ba sai kuma ta shiga murmushi tare da fad'ar "My Abdul baka san irin yadda nake son ka bane, ina sonka fiye da yadda uwa take tsananin son d'an ta ina kaunar ka fiye da yadda jariri yake tsananin kaunar mahaifiyar sa, meyasa ka zab'i ka tarwatsa min farin ciki na, meyasa ba zaka duba irin tsananin son da nake maka ba, kasan bazan tab'a iya rayuwa ba, ba tare da kai ba, kai ne muradi na haka zalika kai ne farin ciki na" duk wannan maganganun da take yi tana kuka kuma fuskar ta dauke da wani irin murmushi wanda ake masa lak'abi da murmushin yak'e kafi kuka ciwo.


Turo kofar d'akin aka yi tare da yin sallama aka shigo mama ce, k'arasowa tayi da sauri tana tambayar ta.


 "lafiya Rasiyya tun daga falo nake jin kukan ki"


Bata iya cewa komai ba, sai hawayen da suke ambaliya daga idanuwan ta kamar famfo, zama mama tayi tana kallon 'yar tata cike da tausayawa.


"Rasiyya meyasa bazaki zama mai daukar k'addara ba, wannan fa fad'in Allah madaukakin sarki ne duk wani musulmi ya kamata ya rumgumi kowace iriyar k'addara mai kyau ko akasin ta saboda haka shine yake nuna cikar imanin mutum"


"Ma....ma....mama nayi iya kar kok'ari na gana na manta da irin yaudarar da Abdul yayi min amman nakasa mama a duk lokacin da na tuna wannan abin ina jin zafi, zafi sosai a cikin zuciya ta, ban chanchanci haka daga wajen Abdul ba, bai yi min adalci ba, kullum idan yazo waje na maganar sa d'aya ce Rasiyya ke kadai ce wacce nake so a cikin zuciya ta bana tunanin akwai wacce zata iya maye gurbin ki a zuciya ta, mama ashe duk wannan kalaman duk yaudara ce nii kuma na riga da na yarda dashi na bashi zuciya ta gaba d'aya mama wallahi nii nasan lokacin mutuwa ta yayi domin bazan iya tab'a rayuwa ba tare da Abdul ba, mama shine rayuwa, shine rayuwa" duk cikin kuka take yin maganar.


Da sauri mama ta janyo ta tana fad'ar "baki da hankali da har zaki dinga fad'ar wani zaki mutu saboda shine rayuwar ki baza ki iya rayuwa ba sai dashi, lokacin da baki had'u dashi ba mai yasa baki mutu ba, kar in k'ara jin kin sake fad'ar irin wannan maganganun"


Ta bud'e baki zata yi magana ta toshe mata baki "bana son kice komai indai kina son mu shirya to kidai na wannan koke_koken da bashi da amfani".


Jin gina bayan ta tayi da gadon, ta lumshe ido hannayen ta na cikin na mama ajiyar zuciya ta shiga yi, sai da mama ta tabbatar ta dawo cikin hankalin ta sannan ta koma b'angaren ta, ita kuma mama na fita ta zame tayi kwanciyar rigingine ta dan samu sauk'i kadan a zuciyar ta, tabbas wani lokacin idan kana cikin damuwa mahaifiyar ka ta zauna tare da kai kana jin sauk'in ta, Allah ubangiji ya barmu da iyayen mu, wadanda suka mutu kuma Allah ya jikan su.


*'BANGAREN FATIMA*


Fahad yau da wuri ya tashi yayi wankan sa yayi shirin zuwa makarantar sa tsab,amman abin mamaki bai tashi Farhan ba kamar yadda ya saba kullum shi yake tashin sa domin zuwa makaranta saboda haushin abinda yayi shi har yanzu abin nan ma yana k'ara bashi mamaki wai har ya kusan kashe yarinya ya kwanta yana baccin sa ko a jikin sa.


Jakar sa ya dauka ya nufi hanyar fita daga d'akin, daga bayan sa ya ji Farhan ya kira sunan sa cike da mamaki.


Fahad!

Fahad!!


Bai jiyo ba, sai da kawai tsayawa yayi cak yana jiran yaji abinda zai ce masa kuma yau.


Tasowa yayi daga kan katifar yazo ya tsaya a gaban sa suna kallon kallo.


Farhan d'in ya fara magana cike da mamaki gami da bak'in ciki.


"Fahad ashe daman akwai lokacin da zaka juya min baya saboda wata shegiyar yarinya wacce kwata_kwata bata da kamun ka, nayi mamaki matuk'a ban tab'a tunanin zaka iya min haka ba".


Kallon sa Fahad yayi cike da takaicin maganganun sa.


"Hmm wato kaine ma kayi mamakin abinda nayi, kai sam baka yi mamakin abinda kayi jiya ba, kuma ko kadan babu alamar nadama a tare da kai wai Farhan me Fatima tayi maka ne haka kasan irin halin da ka kusan jefa ta kuwa wato ma kai idan ta mutu baka damu ba, baka damu da cewa duk wanda ya kashe wani dan adam ba, to shima baza'a barsa ba kashe shi za'ai ban yi tunanin zaka iya aikata abinda kayi jiya ba"


Mtswww Farhan ya ja wani dogon tsaki.


"to idan na kasheta sai me, ni fa na farko ita ta fara shiga gona ta, wai tsaya ma in tambaye ka menene had'in ka da Fatimar nan kullum kai shikenan maganar Fatima, Fatima dan Allah Fahad idan kana jin haushin abinda nake mata kaje ka aure ta nidai bana kaunar ta na tsane ta"


Fahad bai iya ce masa komai ba ya rab'a ta gefen sa yayi tafiyar sa, shi kuma Farhan wannan abinda Fahad d'in yayi shi ya k'ara kona masa rai, toilet ya shiga yayi wanka shima ya shirya ya dauki jakar sa ya kulle d'akin ya nufi cikin makaranta.


Fahad kuwa yana fita asibitin ya nufa sai da yaje ya duba Fatima yana shiga d'akin da aka kwantar da Fatimar ya ganta a zaune tana shan tea da kanta.


"Alhamdulillahi Fatiti"


Murmushi tayi tare da kiran sunan sa.


"Fahad sannun ka da kok'ari"


 zama yayi a kujerar robar yana tambayar ta ya jikin 


"Fatiti ya jikin naki"


"Jiki alhamdulillahi naji sauki sosai"


"To Allah ya k'ara sauk'i"


"Amin Fahad su Fadila sun fad'a min irin hidimar da kayi da ni nagode sosai Allah ya bar zumunci"


"Amin ai Fatima kin fi k'arfin haka kawai dai fatan mu Allah ya baki lafiya"


"Amin" Fadeela ta fad'a


"Hajiya Fadila da Falila bamu gaisa ba ina kwanan ku"


"Lafiya alhamdulillahi" suka amsa a tare 


"Fahad ina Farhan"


"Yana cikin hostel shiryawa yake zai shiga makaranta"


"Hostel kuma kun dawo hostel ne, eh Fatim mun dawo hostel saboda kullum zuwa da dawowa da sassafen nan da akwai wahala shiyasa muka ce bari mu kama d'aki a hostel"


"Gaskiya kam dan Allah idan kaje kace ina gaisheshi kuma ina sonshi har yanzu"


Kallonta yayi cike da tausayawa yace "insha Allahu zan isar da sak'on ki gurin sa"


Mikewa yayi yana cewa "zan huce makaranta idan na dawo zan shigo inga jikin ki kafin in huce hostel"


"To dan Allah Fahad idan zaka dawo ku taho tare da Farhan"


Cike da takaici Fadila tace "kema kinsan wannan mai zuciyar kamar ta kare ba zai tab'a zuwa anan asibitin da sunan yazo wajen ki ba"


Fatima dai ba tace komai ba, Fahad yace "insha Allahu zan iya kok'ari na roke shi yazo"


Murmushi tayi tace "nagode sosai Fahad"


Fita yayi kai tsaye cikin makarantar ya nufa yana zuwa ya shige ajin su, bai jima da shigowa ba Farham d'in shima ya shigo a kusa dashi yazo duk da irin haushin sa da yake ji amman hakan baya nuna cewa zai iya rabuwa dashi.


*_WANNAN LITTAFIN NA KUD'I NE BA FREE BOOK BA NE ZAKU IYA SIYANSA AKAN KUD'I NAIRA 300, DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI ZAKU IYA TUNTUB'ATA TA WANNAN NUMBER 08122188717  KO KUMA TURA MIN DA KATIN WAYA DOMIN SIYAN LITTAFIN TA WANNAN NUMBER 09138224709 SAI A TURO MIN SHAIDAR BIYA TA WANNAN NUMBER 08122188717_*


*MRS BREAKER😍*


Post a Comment

ADS HERE
ADS HERE