*💖A CHATIING MUKA HAƊU💖*
(Ƙalubale gareku mata)
®️🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[ ```Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women```]
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/ 110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*
_*Wannan labarin ƙirƙirarrin labari ne, ban yadda a sauyamin labari ba koda harfi ɗaya ba*🤗_
*_Z• W• F•🏝_*
*SHAFI NA 2📑*
________📖 Shigar turarin ke da wuya cikin ƙawaryar jikinta ya fara ƙarƙarwa ji tayi idan bata turama ta number ba ba ta kyauta ba, dan haka ba ɓata lokaci ta rubuta ta turamata batare da ta shirya hakan ba.
Turawar ta ke da wuya saƙo ya shigo, jiki na rawa ta ɓuɗa saƙon ta gani, ido ta zare lokacin da taga ƙuɗin da ta turumata wanda a iya tunaninta ko mijinta bai taɓa samun dubu ɗari biyar ba a shekara bare ma ita.
Tana cikin wannan tunanin wayar ta ta fara rura, da sauri ta dawo daga duniyar tunanin da ta tafi sunan ƙawarta taga ya bayyana, dan haka ta ɗauka cikin hanzari tare da faɗi,
"Dear waɗannan ƙuɗin fa? ko dai mistek ne kikayi?".
"Sun miki ƙaɗan ne na sake turu wasu?".
"aa wallahi sunyi yawa dear kirage....tun bata rufe bakin taba taji tace,
"Idan har baki son musa mu matsala kafin yamma na ganki onlie".
Tana faɗar haka ta datse kira tare da sanya dariyar mugunta.
Kai da kawo ta farayi a tsakar gida tana faɗin,
"Oho ni Sumayya ya zanyi da waɗannan kuɗi sai kace wadda ta sayar da mutum".
Tana faɗar haka sai yayi murmushi kana yace,
"Ai kin kusa sayar da kanki Summy gaye".
Yana faɗar haka ya sanya dariya mai ban tsoro.
Tunani ta fara ya zatayi da waɗannan kuɗi kuma gashi dear tace idan bata son su samu matsala to ta saya wayar kafin yamma, kuma ita bata son su samu matsala ko ƙaɗan dan sosai take ganin mutunci ƙawarta dan ko bata bata kuɗi ba tace tana son ganinta onlie dole tasan yadda zatayi ta samu arun waya bare har ta turu mata kuɗi, tana kai ƙarshin wannan tunanin ta tashi jikin na rawa ta shirya batari neman izinin mijin ta ba ta fito, kai tsaye P.0.S ta taje ta ciro dubu ɗari, ba ɓata lokaci ta tsayar da mai napep ya kaita shagon yaro goberawa, tana shiga ta gaya musu waya ta keso mai ɗan dama, nuna mata wajan da manya wayoyi suke akayi , isarta ke da wuya idonta ya ganomata kamfanin snmsung, da sauri ta ƙarasa wajan da wayar take ta ɗauko, sosai waya tayi mata dan haka ta koma wajan manaja tace a gaya mata kuɗin wayar, ba ɓata lokaci aka gaya mata kuɗin waya dubu ɗari da ashirin, ido ta zari haɗi da sake dubin wayar da akace dubu ɗari da ashirin wayar tayi sosai, dan duk inda waye ke zuwa to wannan zata je, A.T.M. ta ɗauko ta basu, dan kuɗin da zata zaro basu kai ba, karɓa sukayi suka zare kuɗin wayar sannan suka sa mata a leda wadda ke ɗauke da yaro goberawa haɗi dayi mata godiya tare da faɗin Allah ya tsare.
Da Ameen ta karɓa kana ta tafi, mai napep ta sake tsayar dashi tace ya kaita unguwar mabera, ba ɓata lokaci ta shiga yaje, har ƙofar gida ya kawota, ɗari biyar ta bashi ya ciri kuɗinsa ya bata canji.
Sai da tabari ya bar wajan sannan ta buɗe gida ta shiga, wutar nepa taga an maida, aikuwa cikin zumuɗi ta ƙarasa ɗaki ta buɗe wayar ta sanyata chaji, har faɗin bismillahi lokacin da za'a saka chaji.
Tana ganin wayar ta fara chaji lokaci ɗaya ta sanya wani murmushi tare da faɗin,
"Alhmdllh".
Aikin da bata ƙarasa ba shi tazo ta farayi, bayan ta gama tsaftace gida tazo tayi cefane, dan yau bazata jira har mijinta ya dawo ba tunda ta samu kuɗi yau koshi sai yasan ta samu kuɗi , cifene tayi naji da faɗi harda naman miya, shinkafa da miya tayi masu rai da lafiya har da haɗa masa lemo ko ba komai yau tana son taga farin cikin mijin ta da tajima bata gani ba, kuma idan yace ina ta samu kuɗi sai tace Yayana ne yazo ya kawomin waya harda haɗimin da kuɗi, tana jin ta samu mafita natsowa ta shige ta dan haka ta sake jiki ta cikigaba da aikin sai walwala take tana jin wani sanyi na ratsa zuciyar ta.
Duk abin da take yana ganinta cikin kwaryar tsafinshi, har wayar da taje sayi, murmushi yayi lokacin da yaga tana cikin farin ciki haɗi da faɗi,
"Zan kamaki Summy lokack kaɗan".
Ya faɗi haka tare da kinne ido ɗaya.....
*COMMEN and SHARE*
*UMMU JA'AFAR✍🏼*
