ADS HERE
Posts

ACHATING MUKA HAƊU PAGE 1


 *💖A CHATIING MUKA HAƊU💖*

       (Ƙalubale gareku mata)




®️🏝

 *ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻

[  ```Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.

Zafafa writers is a union to enlight women```]

*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/ 110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*



 _*Wannan labarin ƙirƙirarrin labari ne, ban yadda a sauyamin labari ba koda harfi ɗaya ba*🤗_ 


                *_Z• W• F•🏝_*


*SHAFI NA 1📑*



Wani fantamemen parlour ne Wanda yake dauke da kayan more rayuwa tsayawa baku labarin haduwar sa wani rubutu ne Mai yawa.


Wasu mutane ne zaune maza da mata amma mafi yawa maza ne dukan su jajayen kayane ajikin su zaune suke sun zagaye  wata ƙwarya wadda ita kanta Jace ,a hankali Wanda dagani shine babbansu ya dago da kansa ya faradubin su daya bayan daya har yakai ga wani matashin yaro sannan ya buda bakinsa yace,


"Mus'ab ya zancen matar nan da kuke chating da ita? ".


Saida ya ɗuƙar da kansa ƙasa haɗi da yimasa kirari irinnasu na matsafa sannan yace,


"ya shugabana banjima da kiranta ba naji wayanta kashe amma zuwa anjima zan sake gwadawa".

 

"A'a karka gwada saboda ɗazo nayi bincike akanta naga anɗauke wayar ta,kabari bayan kwana biyu sai kasa ke kira a lokacin tasake yin welcome back kuma a wannan lokacin mukeso ka aiwatar muna   da aikin mu akanta.

Saida ya ɗuƙar da kansa kana yace,


 "godiya nake ya shugabana".



Dariya mai ƙarfi yayi kana yace,


"ba godiya a cikin wannan aiki, fatar mu aiki yayi kyau dan wannan lokacin bazamu ɗaga maka ƙafa ba, kuma karka sake kanuna cewa kai namiji ne, dan tabbas kanuna haka to za'a samu matsala a cikin wannan aiki , kuma samun matsala a cikin sa, kamar samun matsala ne a rayuwarka".


Ina rantsuwa da kai  shugabana baza'a samu wata matsala ba".


 Kai ya jinjina sannan ya buɗa wannan ƙwaryar dake tsakansu tare da karanta wasu kalmumi na tsafi, jinine cike da ƙwarya sai tafasa yake kamar yana saman wuta, ɗauka yayi ya fara sha, sai da yasha mai isarshi sannan ya ba nakusa da shi, haka suka riƙa sha har ya ƙare sannan kowa ya tashi ya sauya kaya jikinsa suka kama gabansu, idan ka gansu sai ka rantse mutanin kirki ne.



   Bayan kwana biyu da ɓatan wayar ta, zaune take sai famar tunani take tarasa mike damunta saboda tunda aka ɗauke wayar nan ta koma wata shuru² kamar ba Sumayya sarki surutu ba, ƙaramar wayar tace tayi ƙara itace ta dawo da ita daga duniyar tunani da tatafi, a hankali ta ɗauke wayar dan taga wake kiranta, number tagani ba suna, da yake yanzu bata da number kowa dan haka sai ta ɗauka  haɗi da karawa a kunnin ta tare da yin sallama.



Bai ƙarɓa sallamr ba yace,


"Nayi fushe duk nakira waya kashe, ashe zaki iya kwana biyu batare da kin jini ba".


Murmushi tayi mai ɗan sauti kana tace,


"A'a my dear friend , mizai sa nayi kwana biyu ban nemiki ba kuma ina lafiya, a'a abinda yasa kika jini shuru wayana ne aka ɗauke shiyasa, ko yanzu welcom back ne nayi shiyasa yanzu kika sameni".


Anasa ɓangare murmushi yayi sannan yace cikin muryar ban tausayi yace,

"garin yaya haka ta faru?".


Sai da tayi murmushi mai ciyo kana tace,


"wallahi my sister nafita ne nasamu yaro yayimin cefenr koda na dawo banga waya ba, kuma koda aka kira kashe take".


"Laifin kene da kin rufe gida da hakan bata faru ba".

Cewar mus'ab kona ce sister mus'b.


"Haka ne dear amma na ɗauke haka yana daga cikin ƙaddara ta dan koshi mai gidana haka yace".


"Ba komai karkisa abin aranki".


"A'a nikam ban sa komai araina ba, yanzu ma jinake kamar ba'ayi ba".


"Da kyau my love". cewar dear mus'ab.


"To yanzu yaushe zakiyi waya dan gaskiya nayi kewarki sosai".


Murmushi tayi mai sauti kana tace,


"Wallahi dear ba yanzu ba dan yanzu ta ciki muke bata waya ba, amma idan Allah yacisheni Yayana ya sayamin wata waya zuwa ƙarshin shekarar nan".


"Mikikace!!!? a'a nikam ko kwana ɗaya bazan so kiyi baki da waya ba bare har wata shekara, wallahi da ace ina ƙasar nan bajimawa  zakiga na diro garin sokoto, amma ko yanzu bata ɓaci ba turumin account number ki in yaso kisaya ko ƙarama ce".


Tun kafin yarufe baki tace,


" dan Allah dear ki barsu wallahi zan samu wata ba jimawa".



Fuska ya haɗe kamar yana gabanta sannan yayi magana cikin rashin wasa yace,


"Baki ɗaukeni yadda na ɗaukeki ba, wallahi da bakice haka ba, kuma idan baki son musamu saɓani to ki gaugauta turumin number tun kafin raina ya ɓace".


Yana faɗar haka ya datse kiran batare da yaji mi zata ce ba.


Cikin sauri ya ɗauko kwaryar tsafin sa sai gata cikin kwaryar sai famar nazari take, ta tura ko karta tura?.


Aikuwa yana ganin haka ba ɓata lokaci yafara karanta wasu kalmumi wanda shi kaɗay yasan ma'anar su.


Kamar karya gama karanta waɗannan kalmumi sai ga wata kwalba ta bayyana a hannusa, murmushi yayi haɗi da fesa wannan turarin cikin wannan kwarya.


Lokaci ɗaya ya kece da dariyar su ta matsafa.....





 _Idan kunji daɗi naji comment sai muji gaba🤗_




*COMMEN, SHARE*




*UMMU JA'AFAR✍🏼*

Post a Comment

ADS HERE
ADS HERE