*_________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*_________________________________*
بسم الله الرحمن الرحيم
_SHINFIƊA_
*BAYAN GAISUWA IRIN TA ADDININ MUSULUNCI DA FATAN KAI MAKARANCIN WANNAN LITTAFI KANA CIKIN ƘOSHIN LAFIYA ALLAH YA SA HAKA *AMIN* *KASANI CEWA WANNAN LITTAFIN ƘAGAGGEN LABARI NE BANYISHI DAN CIN XARAFI WANI KO WATA BA NAYI SHINE DOMIN FADAKARWA DA KUMA ILIMANTARWA IDAN KI KAGA/KAGA YAYI DAI DAI DA RAYUWAR KA TO SAI AYI HAƘURI BA ANYI SHI DAN CIN ZARAFI BA NAYI NE DAN KA GYARA ABINDA KAKE BA DAI-DAI BA ALLAH YASA MU DACE AMEEN*
*
**Mrs. Abdull ce*
```~JANNAT👱♀️```
_Labari mai taɓa zuciya_
🅿️1️⃣
Garin Gombe Gari ne mai tarin albarka da zaman lafiya, Garin da Allah ya sanya wa zaman lafiya da taron Masu zuciyar taimakon Wadda ya kasance bashi da hali,ƙabila da dama suna zaune cikin garin kowa na Yaren shi sannan kowa na addinin shi,
Cikin Gombe na leƙa ban tsaya a ko ina ba sai wani ƙauye da ake kira kashere a cikin wannan ƙauye Akwai wani ƙaramin gari da ake ƙira kaltanga,kaltanga a kauyen kashere 2 ce to niday ban sauka a kowace ba sai ta bare_bari(kanuri)wacce ta kasance tana dauke ne da bare_bare(kanuri) masu yawan gaske daga shiga ta Garin gida na farko dana fara arba dashi shine a farkon Garin madaidaicin gida ne wadda ya wadatu da jar ƙasa ade gidan Irin na ƙauye dai dai haduwa ya tsaru da alama gidan sunfi ƙarfin ci da sha da buƙatun yau da kullum sai day ba masu hali bane
A sukwane na shiga gidan agogon dake tsintsiyar hannu na na duba ƙarfe 8 saura yan mintuna yarinya ce tsaye gaban wata mata da alama mahaifiyar ta ce, Domin gyara mata hijabin makarantar dake jikin ta take yi ruwan omo da kuma riga irinshi Sannan da wando kalan ruwan omon day saiday ya shiga sosai shi(dark_blue)
Magana take mata a hankali kamar mai raɗa idan ba ka kasa kunne ba baza ka ji me take faɗa ba sai day ita yarinyar da ake faɗawan.
Cewa take kibi a sannu kinji JANNAT bari su su fito sai ku tafi tare kinji kar kiyi abinda zasu dake ki harsu ji maki rauni kinji?
Yarinyar da aka ƙira da JANNAT wacce batafi 7yrs ba ta girgiza kai alamar ta gamsu da abinda aka gaya mata.
Murmushi matar tayi sannan ta shafa kan yarinyar,
Ba tare da tayi magana ba sai g wata mata ta fito yara ne a gaban ta sanye Da Kayan makaranta irin day na Wannan yarinyar, maza ne guda biyu da mace 1 da gani itace ƙaramar su babban zaiyyi 13yrs sai mai bi masa 10 sai ƙaramar 7
Matar cewa take shamsu maza ku tafi ba sai kun jira annamimiyar yarinyar nan ba mai kama da Mayu babban da aka ƙira da shamsu ya girgiza kai sannan yace to inna
Ƙaramar ce ta ɓata fuskanta sannan tace kai inna ya za'ayi mu tafi mu bar JANNAT kuma kullum haka kike faɗa
Dungure kanta tayi sannan tace hindu ki kiyaye Ni wallahi nace maza ku wuce sai kun dawo shiday na tsakiyan bay ce komai ba sai harara da yake zabgamata da alama gaba daya yafi su jin haushinta da harara mamar Hindu ta bi mahaifiyar JANNAT Sannan ƴaƴanta suka fita we
Mahaifiyar JANNAT ce tace maza ki bisu ku tafi kinji? yanzu ma day girgiza kai ɗin tayi batace komai ba
Binsu tayi a baya da gudu bakin ƙofar gidan ta same su Hindu ce ta Kama hannun ta tana dariya sannan tace yawwa JANNAT mutafi ko mun kusa latti
Murmushi tayi ta girgiza kai sannan suka fara tafiya
Na tsakiyan ne ya zo ya finciko Hindu sannan ya kafa wa JANNAT wani wawan ranƙwashi da saida taji zafin har babban yatsu ƙafarta
Kallon ta kawai zaka yi ka tabbatar ba ƙaramar azaba ne ya rinsketa ba saboda yadda take rintse idanu hawaye na malala a idanun nata (Abin mamakin shine yadda kukan nata baya fidda sauti sai hawaye kawai niday nace to JANNAT bata magana ne to sai ku biyo ni readers don jin yadda abin yake)
Shamsu ne ya kama hannun Kabir Sannan yace zo mu wuce dan Allah kabar yarinyar can yayi maganar yana nuna JANNAT
Hindu ce ta riƙe ta tana hawaye tace sannu JANNAT Allah zai saka maki inshallah mu wuce, itaday hawayen ne ke ta malala a idanun ta tana girgiza kai tafiya Mai nisa suka yi sosi sanda suka wuce gonaki da dama sannan suka cigaba da tafiya har suka iso makarantar (makarantar nada nisa sosai da Cikin Mutane, matsalar da ake samu kenan a karkara babu makarantar kirki sannan yara sai sunci tafiya Mai nisa sannan zasu iso har ayi latti,irin dai Wannan matsalar da su JANNAT suke fuskanta,fatanmu dai Allah ya bawa shuwagabannin mu ikon sauke na uyin da Allah ya ɗora masu)
Suna isa makarantar aka fara taran latti wucewa suka yi aji da Hindu da JANNAT ajinsu 1 da Kabiru da shamsu ajinsu daban daban, aji suka shiga kowa ya zauna malami ne ya shigo sannan aka fara darasi
Sosai suka yi shiru suka maida hankali wajen darasin bayan malamin ya gama ya fassara da Hausa Sai da ya tabbatarwa kansa sungane sannan yace da mai tambaya shiru kowa yayi alamar Babu JANNAT ce ta ɗaga hannu alamar tanada shi
Murmushi malamin yayi sannan ya miƙa mata abin rubutu(alli) da Hausa ta rubuta tambayar a allo menene common noun a sauƙaƙe ya mata bayani ta gamsu da sauran yan ajin.
Haka dai malamai suka yi ta shiga wasu Lokacin darasin sune wasu kuma banasuba wasu suzo wasu basu zoba
Bayan an tashine daga makarantar shamsu yaja Hindu suka gudu gida suka bar JANNAT haka tayi ta tafiya cikin gonaki tana ratsawahar ta isa gida saboda da gida da makarantar ba ƙaramin nisa ne dashi ba
Godiya ga Allah innarta tayi da taga ta dawo lafiya
Bayan sunci abinci ne JANNAT mahaifinsu ya shigo dakin innar su shamsu ya wuce kai tsaye dan da alama bai san ma da wata uwar JANNAT Cikin gidan ba
Da yamma lokacin islamiyya nayi innarta ta shirya ta saiga Hindu innar JANNAT ke tambayar ta ke baza ki makarantar ba rau_rau da ido tayi sannan tace innar JANNAT inna tace ta ce wai mundena zuwa yayi nisa bokon ma day saboda baba ne Amma da bazamu ba Kuma Ni inason zuwa ta ƙarisa zancen hawaye na zuba JANNAT de kallon ta kawai take,innar JANNAT tace shike nan to kiyi haƙuri hindatu watarana sai labari nima bason zuwan JANNAT makaranta ita kaɗai nake ba Saboda hanyar ba kyau gare ta ba to Amma ba Yadda zanyi Dole taje makaranta
Hindu dai bata ce komai ba ta juya tabar wajen
JANNAT innarta ta qira sunanta ɗago Kai tayi ta kalli innar tata,inna tacigaba da cewa ki kula sosai ana tashi ki dawo gida banda wasa a hanya kina jinako? Girgiza kai ta yi sannan ta juya ta fita sai islamiyya a hanya ta haɗu da yan tafiya banda suka wuce tare,bayan an tashi daga makarantar islamiyya karfe 5 ta wuce nan tayo hanyar gida domin kuwa magriba ta gabato a ƙalla tayi rabin tafiya zuwa gida dayday gaban wata gona sai ga wasu samari su 2 da alama sun gama fakon mai zuwa ya wuce
Da sauri dayan yayi wo kanta sama ya ɗaga ta caɗak dayan na cewa wannan tayi ƙarama tanimu banda irinta amma ina ya suri JANNAT yayi wata gona da ita a ɓangaren JANNAT kuwa jin da tayi an ɗaga ta sama sai kawai ta fara kuka wadda hawayene zalla yake zuba ba sauti sannan sai ƙwacewa take Amma ya riƙe ta gam a jikinsa yayi wata gona
Kafin ya isa inda zai ajiyeta ma hijabin makarantar ya gama fita yana zuwa ya kwantar ta ya ya ga riga da wandon dake jikinta ya ɗaura mata nauyin sa nan yayi anfani da ƙarfin da yake da shi duk da hawaye da mutsimutsi da take yi Amma babu tausayi babu imani haka ya shiga keta mata haddiiiii
**Mrs. Abdull ce*
🅿️2️⃣
Ba tausayi ba imani haka ya shiga keta mata haddi,
Azaba,radadi,ciwo da wani irin azababben zafi ne ke ratsa JANNAT mutsu_mutsun da take yi ɗin ma ta gagara shikuwa wadda aka ƙira tanimu aikin da yasa agaba kawai yake ba tausyi ba imani haka yake Ratsa jikin yarinya yar shekara 7 a duniya yana shawagi tun JANNAT na gane me ake har tabar cikin hankalin ta ma'ana ta sume.
Ba ƙaramar dadewa tanimu yayi akanta ba sannan ya sauka a Lokacin kam JANNAT babu wani alamar rai a tattare da ita,zuwa kawai yake sharewa,haka ya taso ya fito da abokin nashi sukayi kiciɓus wani irin kallo ya jefe shi dashi sannan yace haba tanimu duk abinda zaka yi baza ka nemi budurwa ba sai ƙaramar yarinya irin wannan su shima malam ɗin bay ce ƙarama ba,shiday tanimu tafiya kawai yake yana gyara wandon sa yana cewa'' to shikenan Halilu ka tsaya a wajen idan yaso azo a kama mu'' Halilu yace to ay abinne da rashin tausayi Cikin sa.
Tanimu ya jawo hannun Halilu yace kana jina Halilu malamin nan cewa yayi idan har na bari asirina ya tonu to wallahi zanyi rayuwa mafi munin da bazai misaltu ba kai gwara na sa wuƙa na kashe kaina
Halilu ya zaro ido yace to wani irin abu ne haka kaje nema wajen sa'' dariya tanimu yayi sannan yace bazaka gane bane Halilu amma zan gaya maka daga baya.
Fita suka yi a gonar lokacin har anfara ƙiran sallar magariba.
Ɓangaren innar JANNAT kuwa da taga lokacin tashi yayi har ya wuce JANNAT bata dawo ba sai hankalinta ya fara tashi, musamman da ta tuna JANNAT ana tashi daga makaranta take dawowa bata tsaya wa ko ina dan haka ne ta dau mayafinta ta fito tsakar gida,kai tsaye dakin innar hindu tayi domin babansu shamsu yana can sallama tayi sau 2 sannan taji an amsa,innar hindu ce dan haka ta ɗaga labule tace babansu shamsu na nanne wata uwar harara ta zabga mata sannan tace lafiya,wani ɗaci ta haɗiye a maƙogoronta sannan tace ''dama JANNAT ce bata dawo daga makaranta ba shine nace barin gaya masa zan je na dubota.
Innar hindu ce ta kalli cikin ɗakin sai taga mijin nata ya ƙura wa innar JANNAT ido kamar mai don tuna wani abu,cikin sauri tace maza jekiya amince, sannan ta ƙara da fadin waya sani ma wannan bebiyar yar taki inda taje yarinya ƙarama da ita sai fi'ili da kisisina wata ƙila tana can tana wasa da maza yadda ta saba yarinya ga bebanci bata iya magana sai iskanci da bin yara maza ta ƙarisa maganar tana watsowa innar JANNAT harara.
Ita day tunda ance taje juyawa tayi ta tafi duk da mutum baya sabo da walaƙanci ko wahala amma ita zata iya cewa ya zama mata jiki a kullum fatan ta shine Allah yasa taga yarta cikin ƙoshin lafiya domin tana matukar tausayin JANNAT ga Rashin magana ga uƙubar matar uba
Hawayen da ya xubomata ta share sannan ta fita daga gidan kai tsaye makarantar ta fara nufa sannan har an kusa ƙiran isha sabida Akwai tazara sosai da gidan nasu gaba-daya babu kowa ita kanta Babba a lokacin tsoron wajen ya fara kamata sabida babu komai sai duhuwa da shuke shuke,duk inda tasan zata duba JANNAT ta duba Amma babu ita babu alamar ta bare mai kama da ita,
Tsaya wa faɗar irin tashin hankali da innar JANNAT ta shiga zai ɓata lokacin domin wani irin zafi take ji cikin ƙirjinta wani raɗaɗi ne ke mata yawo tunda ga yatsar ƙafarta har tsakar kanta,sai yau ta tabbatar wa kanta cewa idan kaga kana kuka da hawaye to a al'amarin ka Akwai sauƙi,idan kaga kana kuka to tashin hankali bayyi tashin hankali ba,kai tsaye gidan mai garin kaltanga ta wuce domin sanar da batan JANNAT don ita zuciyar ta na raya mata sace JANNAT tayi kuma tana mummunan hannu, saboda a duk Lokacin da ta tuna ta sai taji gabanta ya yanke ya faɗi.
Mai gari da tawagarsa suka sa salati domin kuwa kowa a garin yasan irin lalurar da JANNAT ke fama dashi tunda aka haife ta bata taɓa magana ba sai day komai za'a faɗa tana ji yanzu idan ɓata tayi taya zatayi bayanin gidansu
A take mai gari ya sa samari 2 da suje su duba ko ina a cikin garin sannan su tambaya ko da wadda ya ganta, sannan ya bawa mahaifiyar JANNAT hakuri akan ta koma gida za'a ganta inshallah itaday sai ido Domin tashin hankali da take ciki bazai kwatanta ba tasan ko ta koma gida ba lallai ta iya zama ba wannan wani irin tashin hankali ne, addu'a ta fara a ranta har ya fito fili''cewa take''ya Allah karka daura Mani abinda bazan iya ba ya Allah tun ina yar ƙarama ta kake daura Mani jarabawar rayuwa iri iri sannan ka bani iko nake cinye su ya Allah ina tawasalli da wannan ina roƙonka da ka kare yata JANNAT Allah kasa tana kyakkyawar hannu ta ƙarisa maganar da fashe wa da kuka mai gari ne ya ƙira yasa aka ƙura 1 daga cikin matansa ta shiga da ita gida da sannan ya tura a ƙira babansu shamsu saboda kowa yasan irin zaman da hindatu(mahaifiyar JANNAT)take a gidan,
Bayan yazo mai gari ya kwararo masa bayanin abinda ya faru,''zufa ce ta fara wanke shi tukun Sannan daga bisa Ni ya fara jera innalillahi sai da ya gama sannan Mai Gari ya fara masa nasiha,hawaye ne ya zubo masa sannan yace ranka ya dade ina matuƙar jin kunyar hindatu bansan da wanne ido zan kalleta ba idan ina gaban ameena rasa tunani na da natsuwa nake gaba 1 barin jikina suke sai na fita daga gidan sai abinda ya faru ya dawo min bansan ya zanyi ba yanzu idan JANNAT wani abu ya sameta da wani ido zan kalli hindatu,ya ƙarisa maganar da shesshekar kuka kowa a fadar ya tausaya mar sannan akayi ta Allah wadarai da hali irin na ameena(innar hindu)
Abinda ya faru a kauyen kaltanga kenan bayan shiga ta da safe ranar 6_3_2005
7_3_2005
Cikin birnin Gombe ban tsaya ko ina ba sai anguwar tunfure eckwa church babban gidane wadda wajen shi babu fenti flat house ne da zai yi a gina madaidaitan gidaje guda 8 a jefa ciki shiga gidan nayi inda na fahimci gidan wani ƙusa ne a siyasa ko kuma jami'in tsaro dan gidan ta ko ina police ne zagaye dashi.
Lokacin ƙarfe 7 na safe parloun na shiga sanyi da ƙamshi su suka fara gaidani zama nayi ina raba ido a gefe, nazarin parloun nake babu tarkace sosai sai maka makan kujeru da suka ƙawata parloun kujeru kalan pentin ne sai tv da ya cika bangon parloun daga dungu har dungu,dining space dauke yake da table da kujeru guda 12 komai na parloun farine da brown Ina cikin nazarin parloun ne naji hayaniya da alama jama'ar gidan ne ke tafe babbar mata ce da aƙala zata kai 50yrs riƙe da riga irinta lawyer sai atamfa a jikinta inda ta yafa mayafi kalan kayan da takalmi da kuma jaka,yara ne mata ke biye mata su 5 duk kansu daya sai day babbar tafi kama da matar, babban zatayi 20yr sai mai bi mata 15 sai mai bi mata 13 sai 11 sai 8 gaba dayansu uniform ne a jikin su banda babbar.
Matar ne tace Nafeesat zan wuce sai driver ya sauke ki sannan sai su faɗimatu inaga yau zan daɗe ba dawo ba dan kinsan Muna zuwa villages duk ƙarshen wata to wannan bamu samu zuwa ba sai yau bazan dawo da wuri ba'' wacce aka kira nafeesat tace to anty, ƙaramar su ce ta ɓata fuska sannan tace anty yanzu dan Allah kiga ya HUDAY bai fito ba kalan a shiga class yake so gashi yau maths first period fa,shafa kanta matar tayi sannan tace to AL_JANNATU ya zanyi da HUDAY sai day addu'a kawai yakai 2 yana kallo ya gagara tashi da safe tafiya skull shida yake da exams din fita daga secondry school baya karatu sai kallo Kinga nima zanyi latti domin way wani ƙauye yau zamuje can cikin kashere way kaltangan bare bari(kanuri) so bansan garinba yau zan fara zuwa kar muyi latti.
Kafin ta rufe baki akayi sallama aka shigo yaro ne da bazai wuce 17 uniform din international School ne a jikinshi fari ne tas har wata yellow yake gashi ne a tare a kansa dogo ne Masha Allah dashi yada da dara daran idanu da yalwataccen gashin gira bashi da jiki sai day daganinshi zaka san nan gaba
ba ƙaramin saurayi za a tayar ba a wajen don kuwa jiant ne mai madaidaiciyar fuska ma'abocin fara'a da dariya yana shigowa yayi kan matar zai rungume ta ja da baya tayi tana masa hararar wasa
Mu haɗu next Page
Mallakin
**Mrs. Abdull*
🅿️3️⃣
Duk da haka dariyar yake yazo ya rungume ta sannan yace sorry anty wallahi ban fito da wuri daga wanka ba that's why am sorry,dariya suka kwashe dashi gaba daya sakamakon yadda yayi maganar a ƙarshe yana kama kunne sannan ya sanyaya murya,kuma tun sa tana sannan tace is ok Yanzu day a wuce skull ansa su AL_JANNATU late jawo wacce aka kira da AL_JANNATU jikinshi yayi sannan yace sorry sister wlhi naɗan yi kallo jiya shiyasa ban kwanta da wuri ba,haka suka fita inda suka shiga babban jeep zuwa school driver ya jasu sannan matar ta shiga Mota ita ma ta wuce wajen ayki
Kai tsaye office ta wuce inda ta samu gaba daya an hallara ita kawai ake jira dan haka yan cike cike kawai tayi a takaddu suka kama hanya,yawancin su mata ne gaba daya masu ji da kansu wadda duniya ke damawa dasu waɗan da suka sha boko suka bugu ko wacce ka gani da wayewar ta take tafi mazan basu da wani yawa a tafiyar sai police mata 2 sai maza 3 haka suka kama hanya kai tsaye suka wuce kashere daganan suka shiga kaltanga.
Ƙarfe 10 suna ƙofar mai gari inda suka samu wajen a cike ana ta yan hayaniya kowa ka gani fuskar shi babu wata walwala,bayan sun sauka ne aka masu tarba mai kyau sannan aka tambayi me ke tafe dasu? wannan matar dai ita ta fara bayani kamar haka''to da farko dai mu nan da kuke gani ƙungiya ne ta lauyoyi masu zaman kansu muna bi gari gari ƙauye ƙauye domin wayar wa da iyaye musamman mata kayi akan yadda zasu ke kula da ƴaƴan su basai ƴaƴan sun kasance mata ba kawai a'a harda maza, sannan muna iya shiga gari domin mu ƙwata wa wadanda aka cuta hakkinsa kamar miji ya zalunci matarsa ko kuma saurayi yaci zarafin budurwa wannan shine maƙa shudin zuwan mu wannan gari,dafatan zamu samu karɓuwa muyi abinda ya kawo mu muga ma sannan a rabu Lafiya.
Duk da mai gari da sauran yan jama'a dake wurin suna cikin jimamin ɓatar JANNAT amma sunyi farin ciki wannan abu da ya faru sannan suna sa ran inshallah za'a ga JANNAT domin jiya da dare ba'a ganta ba haka suka dawo Kasancewar duhu,to Amma yau tun safe mai gari yasa samarin ƙauyen suka watsu domin gano inda wannan ƙanƙanuwar yarinya mai lalurar rashin iya magana ta shiga,hakanne yasa mai gari yace inshallah Allah Kun samu karɓuwa sannan Yanzu zan tura gaba daya ƙauyen nan kowa ya fito a haɗu anan dan muji cikakken bayani daga gare ku,
Kafin mai gari ya rufe baki saiga wani saurayi ya taho ya durƙushe gabansa idon shi kamar gauta da alama kuka yaci ya more,mai gari ne yace kai dan saurayi Yaya day kuka ne ya ƙwace masa kowa ya zuba masa idanu yana sauraren shi sai da yayi mai isarsa sannan yace ranka ya dade baka ganeni ba ko?mai gari yace kamar Halilu dan gidan musa na wajen tuƙa tuƙa girgiza kai yayi sannan yace nine yallabai,mai gari yace mai ke tafe dakai yaro? shesshekar kuka kaɗan yayi sannan ya fara kora masu bayani Kamar haka''
Yallaɓai jiya da yamma bayan an tashi daga makarantar islamiyya ta gangare muna zaune da tanimu dan gidan malam isa abokina shine yake gayamin wani bokan sa ya bashi laƙani da idan yayi anfani dashi to yarinyar da yake so yar wajen ka ko zaka yi yaya da ita zata ce sai shi zata aura
''tanbayar sa nayi wani irin laƙani ne wannan, shiru yayi kamar bazai sanar dani ba Amma sai yace mun waya bokan yace sai yayi wa mata 2 fyade zaro ido nayi zanyi masa magana kenan sai ga wata yarinya wannan yar gidan malam Abdullahi mai ruwa yarinya marar maganar nan tazo wucewa kafin nace kwabo kawai sai naga ya sureta ina mar magana Amma ina har yayi gona da ita ranka shi dade tunda abinnan ya faru na koma gida nake muggan mafarkai ba iya ka wallahi ranka ya dade nayi ƙoƙarin hana shi Amma yaƙi.......
Kafin ya rufe baki andau salati''dai dai lokacin ne kuwa wasu samari suka dauko JANNAT ranga ranga suka yiwo fada da ita dakyar suka sameta inda wadda ya dauko ta bashi da riga da alama tasa ya cire ya suturta mata jikinta dashi hawaye kawai samarin suke sabida yadda suka samu JANNAT ciki rigar janfar daya saka matan jini ne yayi kaca kaca da alama tun jiya da abin ya faru jinin yake zuba har izuwa Yanzu JANNAT kam rai yayi halinsa domin ƙirjinta kam ko alamar harbawa bayayi.....
Kowa miƙewa yayi a wajen daga baƙi har yan gari sabida ganin irin wannan baƙin zalunci domin kuwa fuskar yarinyar kumbure yake alamar duka da naushi da marin da tanimu yayi mata fuskan nan ta kumbura suntum kamar zata fashe.
Tanimu da aka tafi neman yarinyar da ta ɓata dashi sai ya fara ƙoƙarin guduwa samarin gefensa majiya ƙarfi irin ƙarfin nan su suka riƙe shi domin kuwa a labarin Halilu samarin da suke gurin sun tabbatar cewa tanimun da Halilu yake faɗa ne shikuwa baisan Halilu ya fasa ƙwai ba saboda ya tafi neman JANNAT a cewarsa.
Nan suka fara mishi wani irin duka na fitar hayyaci kafin yan sandan dake cikin mota su fito har wani ya ciro wuƙa irin masu zaman banza na ƙauye nan ne ya aika wa tanimu a maƙoshi(maƙogoro) nan fa waje ya kaure domin kuwa tanimu ko shurawa bai yiba ya faɗi a wajen shekakke,haba sai kayya kayya nan kuwa ƙofar mai gari ya hargitse domin kuwa har labari ya isa kunnen yan gari inda innar JANNAT ta fito ko takalmi babu
Dayday lokacin da wannan lawyer ta karɓi JANNAT daga hannun wannan mutumin tayi cikin 1 daga motocin da suka zo dashi, innar JANNAT tana zuwa ta sheda fuskar JANNAT duk da kuwa da canzawa da tayi kawai sai tayi motar tana rusa ihu sakamakon gani jini caɓa caɓa jikin yarta maimakon Ganin ta da kayan makaranta sai taga saɓanin haka kuma rigar jikinta duk jini,da gudu tayi kan motar inda wannan matar ke ƙoƙarin tayar wa tana ihu tazo day day bakin motar kawai sai ta daɗi sakamakon jiri da ya kwashe ta nan jini ya ɓalle mata itama kamar an buɗe fanfo duk da ta sume Amma jini ne ke zuba ba adadi, nanfa police mata guda 2 suka cicciɓeta suka sata a cikin wannan motar,matar nan ta tada motar kawai sai ta fashe da kuka ta gagara tafiya nan ta fito ta koma baya ta yiwa police namiji inkiya da ya riƙa motar.
Ba wani musu ya shiga ya tada motar inda ya sure ta kamar mai tashi sama yayi waje garin sauran police din kuwa suka shiga kwantar da tarzomar da ta tashi a ƙauyen inda babu wadda yabi takan tanimu balle ya yi niyyar kai masa ɗauki,
Mahaifin JANNAT yana zaune aka ayko yazo nan fa labarin yasha banban dan kuwa dama an riga an gaya wa innar hindu komai,nan tace babu inda zaije idan kuwa yace zai fita ga hanya, Amma wallahi ranka sai yayi mugun ɓaci ka futa,bashi da zaɓen da ya wuce komawa ya zauna domin kuwa yana jin ko uwarsa ce zata dawo duniya Yanzu indai ameena zata ga abinda take so to zai iya tsallake na wacce tayi numfashinsa ta kawo shi duniya(kai mata muji tsoron Allah, wallahi Allah kwanciyar kabari yana jiranmu zamuje mu gani da Allah duk wacce tayi mai kyau ta sani haka wacce tayi mummuna Allah ya datar damu)
Kai tsaye asibitin kwararru na cikin garin Gombe police din ya wuce dasu domin kuwa yasan ko ya tsaya a kashere babu abinda zai faru sai jagale sabida baza'a taɓa iya basu taimakon da suke buqata ba fedral medical center ya wuce dasu nan fa aka wuce dasu accident & emergency kowacce akayi inda ya kamata da ita.
Iya tashin hankali wannan matar ta shige shi domin kuwa duk wadda ya ganta zai tabbatar da yanayin da take ciki,tana cikin mawuyacin hali da damuwa ta rasa yadda zata kwatanta irin wannan baƙin zalunci da maza ke yiwa mata,nan abinda ya faru da ita shekara 33 ya faɗo mata arai wani irin zazzafar hawaye ne ya zubo mata a qunci(kumatu)
Aranta take jin da ba'a kashe tanimu ba sai ta dauko shi ta maka shi a kotu ta tsayawa yarinyar nan sannan ta ga mai tsaya mar taji haushin mutuwarsa domin kuwa ba yanzu ya kamata ya mutu ba sai ya ɗanɗana azaba da raɗaɗin da ya ɗanɗanawa yarinya yar ƙarama haka.
Tsawon awa 2 sannan likitocin da suka karɓi innar JANNAT suka fito, a lokacin har mai gari da sauran lauwyers da suka je kalatanga sun iso da mai gari da muƙarrabansa sakamakon aykawa da yayi a ƙira baban JANNAT Amma akace ace baya zuwa inji ameena, wannan dalili yasa mai gari ya taso da kansa ya taho,
Sakamakon turanci da likitan yake yasa mai gari baya ji dan haka matar nan ta matso ta goge hawayen ta sannan tace suje office din, da Hausa ta gaya wa mai gari inda tace ya biyosu
Bayan sun zauna likita ya fara yiwa matar bayani kamar haka da turanci''madam sakamakon bincike da muka yi ya nuna mana wannan matar ta samu kanta cikin wani mummunan yanayi ne yasa ta shiga wannan hali har zuciyar ta da ƙwaƙwalwar ta suka gagara dauka inda har yayi sandin zubewar abinda ke cikinta na tsawon watanni ukku.
Dafa kai kawai tayi tana salati da tasbihi ga Allah tana kuka sannan tace cikin kuka''yanzu ya jikin ta''murmushin ƙarfin hali likita yayi Sannan yace zata samu Lafiya da izinin Allah.
Nan tayiwaa mai gari bayani shi kanshi ya girgiza da irin wannan kwamacala domin kuwa ya dade yana tausaya wa Hindatu tun tana yarinya take ganin uƙuba domin shi abokin mahaifin ta ne babu Abinda bay sani ba game da rayuwar ta, yanzu gashi abin bay tsaya kanta ba har kan diyyar da ta haifa,shima tambayar matar yayi ya jikin ta tagayamasa yadda likita yace
Ita kuma yarinyar da cewar mai gari bayan sun fito daga office din likita yanzu zamu dubota cewar matar
Sai da suka ƙara share wasu awannin a wajen sannan likitocin da suka karɓi JANNAT suka fito fuskar nan tasu gaba daya babu annuri kowannensu ido jawur musamman ma matan likitocin
🅿️4️⃣
Matar da sauran lauwyers din ne suka yi kansu suna tambayar ya jikinta? Likita ya nuna matar da ta kawo su sannan yace ''na ganki a ofisoshi na mana ido jawur haka ta bishi mayafinta na zamewa
Bayan sun zauna ne ya kalleta sosai bayan ya gama Nazarin ta sannan yace kece mahaifiyar ta ''girgiza kai tayi alamar a'a sannan ta bashi labarin abin da ya faru a takaice, shiru yayi Sannan ya sauƙe ajiyar zuciya ya fara mata bayani kamar haka
''yarinyar da kuka kawo nan tana cikin mawuyacin hali Domin kuwa ko babbar budurwa akayi wa irin shigar da aka mata to lallai sai an kawo ta asibiti balle yarinya ƙarama sannan matsalan shine yayi yayi ya ratsa ta ya wuce Amma abin yaci tura saboda yarinya ce ɗanya wannan dalilin yasa yayi ta anfani da bakin al'aurarta yayi yadda yaso da ita domin kuwa daƙyar aka tsaida jinin dake zuba, sannan muka yi ƙoƙarin ceto rayuwar ta da izinin Allah daƙyar da taka tsantsan Allah ya dawo mata da numfashin ta,kafinnan kuma muka fara aiki akan ganin yadda zamu gyara ta wajen ya dawo dai dai alhamdulillah for now she is in best condition, domin kuwa munyi mata dinki sannan jinin ya tsaya numfashin ta ya dawo da izinin Allah zuwa nan da 3 hours zata farfaɗo''agogon hannunsa ya kalla sannan yace yanzu 6 zuwa nanda 8 ko 9 zata dawo hayyacinta inshallah a kula da ita dan Allah Madam yarinya ce ƙarama sannan ya ƙara da Allah ya bata lafiya
Kuka sosai take kamar me domin tasan irin wannan raɗaɗin tasan yadda mata suke fuskantar irin wadannan matsaloli tun suna da ƙananan shekaru shin ya zasu yi su tsaida irin wannan baƙin zalunci da maza kewa mata?share hawayen fuskanta tayi sannan tayiwa likita Godiya ta fito
Sauran lauwyers din sun tafi da police 2 mai gari kuwa sun tafi masallaci sallar magariba,itama zama tayi a ɗaya daga cikin kujerun bakin ɗakin tana maida numfashin domin kuwa duk ta fita daga hayyacinta duk tayi wani iri a rana 1 duk ta susuce
Suna dawowa daga sallar sai ga matar mai gari da yarsa bazawara daya don kuwa mai gari ne ya aika wani da suka zo tare akan ya dauko su daga kalatanga,gaisawa suka yi da matar sannan kowa yayi jugum jugum.
Mai gari ne ya kalleta yace baiwar Allah da kin tafi gida muma nan zamu tafi ynxu Amma zamu bar harira da Hafsah yata da matata ce zasu kwana wajen su,
Siririn hawaye ta share sannan tace mai gari ko zan iya ganin ka dan ALLAH''ba damuwa cewar mai gari dan haka suka fita can kujerun bakin emergency suka zsuna,
Kallon mai gari tayi sannan tace su waɗan nan yan uwanka''aa cewar mai gari''sai day Ni mai garin sune sannan ita Hindatu yar abokina ce''duk da bata san waye Hindatu ba Amma ta fahimci matar yake nufi'' dan haka tace su basu da yan uwane?ajiyar zuciya mai gari yayi sannan yace yarinya tarihin Hindatu da AL_JANNATU abin tausayi ne abin a masu kuka abin a yaba wa wannan yarinya Hindatu ne domin kuwa tasan tawakkali tasan idan Allah ya daura mata jarabawa ta karɓe shi da hannu 2 Yanzu nan zan gaya maki waye ce Hindatu ''to reader's muma ay sai mu gyara kunne musha labari
WACECE JANNAT
Sunan mahaifin Hindatu Nasiru mai arziki ne sosai irin namu na ƙauye ya mallaki gonaki na gyaɗa da sauransu kasancewar mu bare Bari yana da kudi sosai inda yawancin gidajen ƙauyen kaltanga na sane,aboki nane ko nace amini, su 3 babansu ya haifa shi kadai ne wajen mahaifiyar sa inda yake da yan uba mace da namiji a takaice dai Nasiru a kaltanga yayi aure inda ya auri Fatimah yarinya mai hankali da sanin ya kamata shekarar su guda ta haihu inda ta haifi mace aka sawa yarinya Hindatu(mahaifiyar JANNAT)sosai a irin rayuwar mu na ƙauye Hindatu tana cikin gata dayday gwargwado inda shekarar Hindatu biyu mahaifiyar ta Fatimah ta sake samun wani cikin
To rayuwa kana naka Allah yana tashi watarana da da dare''mudai a kaltanga ba wutar nepa gare mu ba balle muce ita ta kama haka wuta ta kama gidan Nasiru inda suka ƙone kurmus shida iyalansa ''a cikin daren kowa ya dauka babu wata sauran rai da ta saura'' to ikon Allah ya fi ganin wasa da asuba kawai saiga kukan yarinya ashe Hindatu ce sanyin asuba ya hura ta ta farka daga sumewar da tayi yarinya yar Kimanin shekara 2 a lokacin komai takan iya faɗa dan haka mukazo masu kuka nayi aka ƙira kanin Nasiru da suke uba daya nan ya karɓi hindatu yana kuka
''kawu daba baba ne ya wurgo ni da wuta ta kama shine yace yana zuwa shima kuma ina gani wuta na kamawa cikin inna ta da cikinta
Kowa a wajen kuka ya saka sabida tausayin Wannan ƙanƙanuwar yarinya haka dai muka watse inda Bello ƙanin mahaifin ta ya dauke ta ya Kaita gidan shi''to dukiya daya a Shari'ah na Hindatu ne dan haka aka dau komai na mahaifin ta aka danƙa wa kaninsa Bello da nufin ya riƙe amanar marainiyar Allah to kowa ya dauka hakance take kasancewa ashe Bello ya fake da guzuma ne yana harbin karsana
Gallazawa,bakar mugun ta shida matarsa da yayansa suke wa Hindatu sannan ya hau kan Dukiyar ta ya zauna yake abinda yake so,to ba wanda ya tashi sanin haka sai da Bello yazo da maganar auren hindu lokacin shekarar ta 15 sannan kowa ya gane abinda yake aikatawa zuwa wannan lokacin dukiya kam yaci fiye da rabi
Anan garin namu na kalatanga anan Abdullahi yake shima Maraya ne yana hanun kakarsa Amma shi yana cikin gata shekarar Abdullahi 25 yace yana son Hindatu sai dai yana da mata mai suna amina, duk da Bello yasan shikanshi Abdullahi bayanin dadin matar Amma yace dole Hindatu ta auri Abdullahi sabida baƙar mugun ta, Abdullahi yana son Hindatu sosai matslarsa daya yana matuƙar shakkar ameena lokacin itama ameenar bata haihu ba
''to a haka day aka samu akayi auren Hindatu wacce daƙyar Bello yayi mata tukwane da taburma aka kaita gidan Abdullahi Abdullahi sana'ar saida ruwa yake domin gado ne na mahaifin sa
Anan ne ameena tayi tsalle ta daure tace babu wadda ya isa ya zauna da mijinta''hindatu tana da faɗa sosai domin ana mata zata rama wannan dalili yasa daga farko ameenar ta shiga hayyacinta'' domin kuwa cewa Hindatu tayi tunda kika bari har na aure shi maganar zama dashi kuma dole
Wannan dalili yasa ameena ta shiga hankalin ta''to Hindatu na cika shekara gidan Abdullahi ta samu ciki lokacin ita ameena bata da komai'' nan fa hankalin ta inya yi dubu ya tashi da zugar shedan dana ƙawaye ameena ta faɗa bin bokaye''lokacin da Hindatu ta tashi haihuwa baƙar wahala ba wacce bata shaba haka ta haifi danta namiji ƙato dashi saiday babu rai tana haihuwa jini kuwa ya ɓalle mata in taƙaice maki labari,haka sai da Hindatu ta haifi yara biyar duka haka abin ke kasancewa, Lokacin ƴaƴan ameena 2 watarana tayi tafiya zuwa ƙauyen su deba way sunyi faɗa da Abdullahi bata san Hindatu nada cikin wata 5 ba sai da ameena tayi wata 5 sannan ta dawo lokacin ne kuma ameena ta dawo ta samu abinda ya ɗaga mata hankali abinda haryau ta tsana a duniya kamar mutuwarsa abinda har yau idan ta tuna dashi sai taji dama mana a wancan lokacin ta tsaya bata tafi ba, dama mana tana nan za'a hafi wannan cikin dama dama dama tayi ba adadi wannan ba komai bane face haihuwar Hindatu inda Allah ya azurtata da kyawawar ya mace wato AL_JANNATU dagowa matar tayi ta kalli mai gari don kuwa taji ya ƙura sunan yarta da take so cikin ƴaƴan ta mata itace mafi soyuwa a ƴaƴan ta idan ka cire HUDAY da take jinsa har cikin jiki da jini da ɓargonta
Mai Gari ya cigaba da cewa wannan dalili yasa ameena ƙara shiga bokaye inda abinnata yakai har ta asirce Abdullahi baya iya zuwa kusa da Hindatu a cewar ta basai ya je dakin ta bane sannan zai mata ciki ta haihu
Itaday Hindatu abin duniya ya dameta haka kawai sai taji kamar an dau tsoron ameena an daura mata ga kawu Bello daga mashi maganar kudi ya hauta da faɗa yace idan ta ƙas masa magana wallahi na lahira sai ya fita jin dadi
''to bata sake masa maganar ba haka ta ganganɗa ta haɗa kudin da ta samu a sunan yarta ta fara sana'ar cikin gida ,wata rana bayan komai na Bello ya ƙare mun tafi sallar asuba muna dawowa kawai sai muka samu gidan ya kama da wuta iyalan Bello kaf sun ƙone wannan dalilin yasa Bello hauka tuburan inda ya ringa tona asirin kansa cewa shi ya sa aka kunna wuta a gidan Nasiru domin su ƙone da iyalansa shi a bashi dukiyar haka dau yayi yawa kansa barbaɗe rayuwar Bello haka ta cigaba da tafiya cikin hauka da kazanta(ان الذين ياكلون اموا اليتاما ظلما انما ياكلون في بطونهم نارا)(innallazina ya'akuluna amwalal yatama zulman innama ya'akuluna fi buɗunihim nara)(lallai wadda yaci dukiyar Maraya in ji Allah da zalunci,to lallai yana ciwa kansa ko yana ɗorawa cikin sa wutane inji Allah subhanahu wata'ala) to me yasa zakuna cin dukiyar marayu kamata muyi wa kanmu karatun ta nitsu jama'a (suratul nisa'a aya ta goma)
Uƙuba da tashin hankali haka Hindatu da JANNAT suka dinga ganin shi a Wannan gidan sana'a Hindatu take tukuru domin ganin ta ciyar da rayuwarsu gaba shekarar JANNAT 2 a duniya akori kura ta buge Bello inda sai Kayan cikinsa suka zubo domin ta kashi tayi sai Lokacin Hindatu ta tabbatar wa kanta cewa ta zama cikakkiyar marainiya daga ita sai yarta watan JANNAT 1 ameena ta haifi Hindatu ashe itama tana da cikin tayi yaji ta tafi mace ta haifa wannan karon,
''ranan suna ne kuma wani rashin hankali ya faru amma wa ameena kawai Abdullahi yazo yace wa Hindatu da ameena sunar yarsa Hindatu ita yayi wa mai suna na ameena tayi tsalle ta dire tace wallahi ba'a isa ba babu wadda ya isa ya ƙira yarta da wannan sunan''miyasa da na haifi shamsu da Kabiru kace na zaɓa masu suna ka sa masu amma yanzu zaka ce sunan yata Hindatu to wallahi bazai yiwu ball
Amsan daya bata ne yasa har rana mai kama tayau bata ƙara tinkararshi da wannan maganar ba cewa yayi''shamsu da Kabiru banajinsu kamar yayana itadai wannan din ita nake ji ajikina jini na ce shiyasa na saka mata sunan da yafi soyuwa a gareni wato Hindatu su sai kawai ameena taji kanta ya sara shin meke shirin faruwa?ta tambayi kanta
Itaday Hindatu (mahaifiyar JANNAT)juyayi yau take salla domin bata taɓa farin ciki irin wannan rana ba daɗi ba wadda bata jishi ba har godiya tayiwa Abdullahi''
To haka rayuwar ke ta tafiya watarana dadi watarana wahala domin kuwa tun daga wannan rana ameena ta koma wajen bokan ta tace ayiwa Hindatu (mahaifiyar JANNAT)da Abdullahi farraƙu batason ko kallo ya ƙara hadasu bare kuma magana, haka akayi inda Allah yabawa bokan Sa'a asirin ya kama
Hindatu kullum cikin tashin hankali take to bayan shekara ne lokacin shekarar JANNAT uku a duniya wani tashin hankalin kuma ya ƙara bullowa Hindatu.......
Don jin wani irin tashin hankali ne sai ku biyoni fans takuce har kullum
🅿️5️⃣
Hindatu kullum cikin tashin hankali take to bayan shekara ne lokacin shekarar JANNAT uku a duniya wani tashin hankalin kuma ya ƙara bullowa Hindatu.......
Wannan abu ba komai bane face yadda ta lura da JANNAT kwara kwata bata magana sai day koji tayi ance JANNAT zata juyo, sannan irin gwara cin da yara suke yi dinnan ko arimga ƙiran Mama ko wani abu ita babu a bakinta saiday shiru.
Wannan abu ya ɗaga mata hankali aynun taso ta kai JANNAT asibiti a duba ta Amma kuma babu fuskar tambaya a wajen Abdullahi shiyasa tayi shiru amma kuma zuciyarta tana cikin fargaba da tashin hankali
Rayuwa haka tayi ta ganagarawa kwanaki na zama sati sati na zama wata watanni na juyawa su zama shekara har Allah ya kaimu inda JANNAT ta cika shekaru 7 lokacin kuma har ameena ta ƙara haihuwa inda aka sawa yarinyar suna A'isha (sabira)suke ce mata , amma ita Hindatu bata sake samun ciki ba,''to miji baya shiga dakinka ina zaka samu ciki?sai day ta cigaba da kula da kanta da yarta tana sana'a cikin gida basu fi ƙarfin komai ba inda ta dauki Abdullahi da ameena ta wasar.
Abinda ta lura dashi shine kaf cikin ƴaƴan ameena babu wadda ya tsani JANNAT sama da kabiru,Kabiru yaƙi jinin yarinyar ya tsane ta sama da yadda ya tsani barin shi duniya,cikin ƴaƴan ameena kuwa mai don JANNAT sai Hindatu tana matuƙar sonta ga kuma kama da suke kamar me domin kuwa idan ka kalli JANNAT kaga Hindatu zaka san tsatso 1 suka fito
Haka rayuwar take gangarawa Hindatu bazata ce bata da matsala ba Amma da yake idan Allah ya daura wa dan adam haƙuri to ya gama dace da komai na rayuwa a cikin duniya sai hakan ba ya damunta
JANNAT nada shekara 7 ne ameena ta shirya tafiya garinsu deba wata 1 tayi acan a kuma lokacin ne Abdullahi yaji kamar ancire masa wata rigar ƙara da ya daɗe da sawa.
Wata rana ya dawo gida yana shigowa ya samu Hindatu da JANNAT suna cin abinci bakin runfar ta
Tsayawa yayi ya kare masu kallo sannan yace Hindatu 🗣️ Muryar da ya kira dashi ne yasa wani kuka da faɗuwar gaba ya ziyarceta a take taji kuka ya kwace mata
Matsowa yayi kusa da ita sannan ya kamo hannun JANNAT su yana kama hannunta sai ta fara alamar shiɗewa domin kuwa duk duniya bayan inna ameena babu mahaluƙin da take tsoro sama da babansu
Hawaye ta fara tana kokarin ƙwacewa kawai sai ya jawo ta jikinshi ya rungume,tsakanin da da uba sai Allah kawai sai taji wata nutsuwa da tunda aka haife ta bata taɓa riskarta ba domin kuwa wata ni'ima ne ke ratsa ta yadda taji mahaifinta ya rungume ta
Be ce komai ba haka Hindatu dake kuka sai da bacci ya dauke JANNAT sannan ya ɗauke ta ya Kaita daki ya kwantar sannan ya dawo,kusa da Hindatu ya zauna sannan ya kamo hannun ta hawayen da yake riƙewa Tun dazu su suka fara masa shatata a kumatu(kunci) kafin ya fara magana da cewa
''hindatu idan na buɗe bakina nace kiyi haƙuri nasan ban miki adalci ba zai iya zama na raina ki ko na ƙasƙantaki Amma ki sani duk duniyar nan bakida wani masoyi da ya wuce Abdullahi ina matukar ƙaunar ki Hindatu da tausayin ki kullum nake kwana,nakan rasa natsuwa ta da tunani na idan ina gaban ameena takan bani tsoro takan mini kwarjini duk sai naji na fita hayyacina ,bana sanin abinda nake aykatawa dan Allah Hindatu ki yafemin kuma kisa aranki komai daren daɗewa ni Abdullahi baki ne kuma zandawo wajen ki da izinin Allah ke tawace Ni baki ne kuma kullum zan cigaba da ƙaunar ki har ƙarshen numfashi na.....
Idan Hindatu (mahaifiyar JANNAT)tace hankalinta bai kwanta ba yau tayi karya domin kuwa farin cikin dake ranta baya misaltuwa rabon ta da jin wadannan kyawawan maganganu a bakin wani mutum harta manta ranar sai yau,a take taji hawayen idanun ta sun ƙarfe wani sanyi na shiga cikin ranta
A Wannan ranar iyayan JANNAT sun ɗanɗana wa juna zumar soyayya wacce zaƙinta ke zama a harshe da baki da ƙwaƙwalwa da zuciyar wadda aka bawa, soyayya suka yi tsantsa a tsakanin su ,sai wajen Yamma komai ya natsu sannan Abdullahi ya dubi Hindatu yace ina Allah ya yarda da ajiyata wajen ki daga yau ki fara lissafi zan karbi abina nanda watanni 9 cib rufe fuskar ta tayi alamar kunya sannan tace nagode,buruntun JANNAT da suka ji a tsakar gidane ya sa su fitowa duka maimakon ta nufi mahaifin ta sai ta nufi mahaifiyar ta
Ita kanta Hindatu hakan bai mata dadi ba domin kuwa taga zuciyar Abdullahi ta sosu ''jeki wajen shi mana JANNAT''cewar innar JANNAT din
Batawa mahaifiyar ta musu dan haka ta fara tafiya jiki sanyaye tayi wajen shi ɗan hawayen kumatunsa ya share sannan ya kamota jikinshi
Hajiya ina taƙaice maki labari wannan iyalan Sai da suka kwashe sati 2 cir suna fuskantar dadi da kwanciyar hankali irin wadda suka daɗi basu samu ba a wannan lokaci ne kuma Abdullahi yasa JANNAT makaranta,mu kanmu yan gari saida muka gane canji daga Abdullahi domin kuwa duk inda yake yana fara'a,da kanshi ranar yake bani labarin kaf abinda ke faruwa bayan tafiyar ameena sosai na mishi murna kuma nayi mashi addu'ar Allah ya dawwamarsu haka,bayan dawowar ameena komai yakoma gidan jiya domin sabon shiri taje tayi inda bata fahimci komai ba game da abinda ya faru tsakanin Abdullahi da Hindatu
Ashe kuwa Kinga cikin da yake ta faɗa akwaishin,Akwai shi ashe saiday Allah baiyyi zai zauna ba gashi SANADIN tashin hankali ya zube
Wannan shine tarihin JANNAT da mahaifiyarta'''inji mai garin kaltanga''''
Matar nan da hawayen ma ya ƙafe mata sabida jin wannan ƙaddara rayuwa da Allah ya daurawa wannan baiwar Allah tabi mai gari da kallo
Tashi kawai tayi ta barshi wajen inda ta shiga dakin da aka kwantar da innar JANNAT ta farfaɗo itama gaban gadon ta ƙarisa sannan ta zauna
Kuka innar JANNAT tasa tace baiwar Allah idan ban manta ba kamar ke naga kunsa JANNAT jikin mota jiya ko
Dan Allah ina yata kuma nan inane,Ina son ganin JANNAT domin itace rayuwata banajin idan na rasa JANNAT akwai kuma wani sauran farin ciki da zanyi a duniya shin tana ina?tayi maganar tana ƙoƙarin miƙewa
Zaunar da ita matar tayi sannan tace ki kwantar da hankalinki tana nan cikin lafiya karki damu kema kinsamu ɓari ne(miscarriage)Dan haka ki kwantar da hankalinki kici wani abu zan kaiki kiga yarki JANNAT na miji alkawari Amma gaskiya sai kin kwantar da hankalinki,komawa innar JANNAT tayi ta kwanta sabida azaba da raɗaɗin dake cin zuciyar ta ,gashi kuma bata da wani zaɓi dan tanson taga yar tata
Tsananin tausayin innar JANNAT na cigba da azalzalar wannan matar
Fita tayi ta shiga office din likita ruwan zafi ta buƙata inda ta samu harda kayan tea nan ta haɗa wa innar JANNAT ta kawo mata,ba laifi tasha kaɗan kuma taji dadin jikinta,zama tayi tace zakiyi wanka yanzu ne
Bata rufe baki ba saiga yar mai gari da matarsa,matar ne tacewa matar mai gari baba Dan Allah ko za'a taimaka mata tayi wanka zanje na duba JANNAT din,matar mai gari tace bakomai to kema de yarnan Allah Ubangiji ya saka miki ya raya zuriya ya ranaku da duniya Lafiya ameen ta amsa sannan ta fita .
Sai Lokacin ta tuna da wani gida da ƴaƴanta da mijinta domin kuwa wannan abin duk ya mantar da ita komai
Motar ta ta nufa ta dauko jakarta da wayarta dake ciki ta samu missed call sunfi 40 na ƴaƴanta da ƙanwarta nafeesat da kuma mijin ta
Shiga motar tayi ta zauna sai kuma ta rasa wa zata fara kira cikinsu,mijinta ta fara ƙira yana dauka ta fashe masa da wani kuka mai tsuma zuciyar mai saurara zaune yake cikin parloun gidansa da yayansa yana ta ƙiran yan wurin aykinsu gaba daya lambar su yaƙi shiga kamar haɗa baki,sai ga kiran matarshi Hajiya sadiya kuma tana dauka ta fashe da kuka miƙewa yayi yana tambayar lafiya sadiya kike irin wannan kuka kina inane wasu ne suka kama ki ko yaya ki gayamin mana ,kukan da yaji ta cigaba da yine yasa hankalinsa ƙara tashi Amma sai ya dake ya zauna domin ya kwantar mata da hankali yama manta da ƴaƴan nata dake parloun nan ya fara gaya mata maganganun soyayya masu kwantar da hankali domin shi a zatonsa Shari'a tayi bayani dadint ba yasa take kuka,kafin ya gama magana ya juya yaga kaf ƴaƴan sun bar parloun murmushi yayi domin yasan kunya suka ji,ajikina yana ganin babu a inda bazai nuna wa sadiya so da ƙauna ba domin kuwa yana matuƙar so da tausayin ta irin su sadiya suna da tabon da dole sai ana lallashin irinsu shi kadai yasan halin kayansa dan haka kafin kace me tayi tsit sai nunfashi da take saukewa ''kina ina'' kawai yace ita kuma ta amsa masa da fthg(fedral teaching hospital Gombe)miƙewa yayi ya fito harabar gidan police din na ganinshi suka sara mishi wadda suke cikin mota har sun tayar sun buga sirin daga masu hannu yayi alamar a kashe sannan ya nufi motar da in zaifita ba tare da yan sanda bane yake hawa ita ya shiga
Police ne drivern,tada motar yayi suka fita daga wakeken gidan inda police suke da sara masa
Fmc zamuje cewar mutumin,kai tsaye medical center suka nufa
Hajiya sadiya kuwa tana gama waya da mijinta ta fita daga motar ta koma dakin JANNAT,karfe 9 da yan mintuna tana shiga kuwa JANNAT din ta farka ,da sauri ta isa wajen ta rike ta ta na mata sannu hawaye take tana kaɗa kai alamar to
Da JANNAT tana da baki abinda zata fara tambaya shine innar ta Amma babu hali,kallon da take wa Hajiya sadiya na rashin sani shine yasa ta fahimci innarta ta ke son gani ''innarki ko''cewar Hajiya sadiya da sauri ta girgiza kai , murmushin ƙarfin hali tayi kawai sannan tace zan kaiki nanma girgiza kan tayi,matar nan saura kadan ta fashe d kuka ganin irin wannan jarabawar da yarinya ƙarama ke fuskanta taji matuƙar tausayin JANNAT ga ba baki ga fyade domin kuwa ko bude bakin ma batayi kwatakwata, kwantar da ita tayi ta tashi domin kuwa taga jikin innar JANNAT din yafi sauƙin akan na yarinyar so gwara ita tazo da akai yarinyar
Tana bude kofar fita kuwa sukayi kiciɓus da mijinta kawai sai ta shige jikinshi tana kuka tana fadin ''abban HUDAY abinda ya faru dani ashe bakomai bane a tausayi zo kaga wani abin tausayin da ya fi na matarka zokaga waɗan da suke cikin halin wahala wadda yafi wadda matarka ta shiga abban HUDAY sun bani tausayi..saurin rufe mata baki yayi yana buga bayanta alamar rarrashi daƙyar tayi shiru sannan yace ina zaki
Zan dauko mata mahaifiyar tane cewar Hajiya sadiya girgiza kai yayi sannan ya sake ta ta fita yabi bayanta office din likitan taje ta gaya masa JANNAT ta farfaɗo kuma tanason a dauƙo mata innar ta.......
❤️️Mrs. Abdull❤️
