بسم الله الرحمن الرحي
*Mrs. Abdull ce*
```SARARIN KA
INUWA```
```~JANNAT👱♀️```
_Labari mai taɓa zuciya_
Abin tausayi, rashin imani, sadaukarwa,halacci,da tsantsan soyayya.
Domin sharhi,shawara,yabo,jinjina,qorafi,ko gyara(07059305867)
*_________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambitio n is to entertain & motivate the mind of readers}```https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*_________________________________*
🅿️6️⃣
Zan dauko mata mahaifiyar tane cewar Hajiya sadiya girgiza kai yayi sannan ya sake ta ta fita yabi bayanta office din likitan taje ta gaya masa JANNAT ta farfaɗo kuma tanason a dauƙo mata innar ta.......
Girgiza kai yayi alamar ya gamsu,wata nurse ya ƙira sannan ya gaya mata yadda za'a yi,tare suka fita da Hajiya sadiya a keken matarsa lafiya aka dauko innar JANNAT zuwa dakin da JANNAT take
Raba idanu kawai take don zata iya rantse wa da bata taɓa zuwa asibitin cikin birni ba sai yau iyakacinta a asibitin kashere.
Kai tsaye dakin da JANNAT take aka kai ta,ana shiga ta hango yarta makeken kan gado,wani irin faduwar gaba ya ƙara riskanta nan zuciyar ta tayi kamar ta faɗo,hargaban gadon JANNAT aka kai innar ta al'ajabi duk ya cika ta ganin fuskar yar Tata duk bendeji duk da ya saɓe Amma kamanninta sun dan sauya
Gaban gadon nurse din ta tura ta sannan ta fice Hajiya sadiya ce ta tsaya gefe jikin gadon tana kallonsu
Innar JANNAT ta kamo hannunta tace AL_JANNATU ya jikin ki me ya sameki a hanyar makaranta haka iyye,😭 innar JANNAT bata taɓa jin ciwon rashin maganar yarta ba irin na yau,inama JANNAT ta buɗe baki tace inn waje kaza ne ke min ciwo inama tace zansha ruwa ko zan i abinci😭hawayen daya ta cigaba dayi kafin ta tsaya d kukan ta juyi ta kalli Hajiya sadiya sannan ta fara tambayar ta ''baiwar Allah mai ya samu yata dan Allah hadari tayi ne ko buge ta kuka yi''
Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta fara mata nasiha kamar haka''kiyi hakuri Hindatu duk abinda kika gani ya faru da dan adam to mukaddarine daga Allah tun fil'azal an rubuta da zai sami mutum,sai day kuma Allah shi kawai yasan abinda yafi alkairi a rayuwar dan Adam,kar wai mutum yace nikam inaga ganin sharri a farkon rayuwa nasan har zuwa ƙarshen haka ze kasance, a'a ko kadan rayuwar dan Adam tana juyawa cikin ƙanƙanin lokaci masu so ka su koma ƙinka ,masu ƙinka kuwa su koma sonka haka rayuwar take ,kar in tayar maki da hankali ki kwantar da hankalinki inason kisa cewa aranki abinda ya faru da yarki kamar bai taɓa faruwa ba kisa hakan a ranki domin injin Ni kaina wannan yarinyar nake kawai zata zamo wa alkairi harda Ni da sauran jama'a duka,shiru tadan yi sannan ta cigaba da cewa'' a hanyar zuwan yarki islamiyya aka samu wani azzalumi ya kamata yayi mata fyade
Kamar an sauke mata araduwa haka taji wani rugugi na mata yawo a tsakar ka ta rasa gane ma matar me take daɗi bayan kalmar fyade d taji bata ƙara fahimtar komai ba a hankali take maimaita addu'ar nan cikin ranta kuma''allahumma ajirni fi musibaty wa'aklifni kairan minha, lahaulawalaquwwata illabilla, subhanallah, innalillahi wainna ilaihirraji'un,haka take ta daɗi kamar kuma me sai taji a hankali wata natsuwa na ratsa ko ina da ko'ina na sassan jikinta, hawaye ne ya fara bulbulowa a ido ta kamar an buɗe fanfo Hajiya sadiya bata hana taɓa domin kuwa tasan a irin wannan yanayin idan ma ba'a bar innar JANNAT tayi kuma ba an cucetane,
Sai da ta barta tayi mai isarta sannan ta kamo hannun ta tana ta bata baki da nuna mata mahimmancin hakuri ga rayuwar Musulmi , share hawayen ta tayi sannan tace,Nagode SOSAI baiwar Allah da kk tsaya mana tsayin daka Allah ya saka da alkairi kuma INSHALLAH zan cigaba da hakuri da rayuwa a yadda take zuwanmu ,komai nasan mukaddarine daga Allah idan Allah ya ƙaddara abinda zai faru babu wani mahaluƙi da ya Issa ya canza,miyasa muke amsa sunan musulmi?ay saboda mun yarda da Allah shi kadai sannan mun yarda cewa shi kaɗai ne zai iya dora mana abu sannan ya bamu hanyar fita cikinsa, Allah ya bata lafiya, Allah ya bata ikon cinye jarabawar da ya daura mata, shikuma wadda ya aikata Allah ya bi mata hakkinta akansa ,ta ƙaruwar maganar tare da goge hawayen fuskanta.
Da ameen Hajiya sadiya ta amsa sannan ta gaya mata ay an kashe tanimu a ranar sosai taji dan sanyi cikin ranta ko ba komai an rage mugun iri a cikin al'umma
Mijin Hajiya sadiya ne ya shigo gaisawa suka yi da innar JANNAT yayi mata ya jiki ,da sauki ta amsa domin kuwa ganin halin da yarta ke ciki yasa ita jinta ta warke
Kallon Hajiya sadiya mijinta yayi sannan yace hajiya mu wuce Ko zuwa da safe sai ki dawo don naaga kamar baki da shirin tafiya gashi dare ya na kara yi
Kallon shi tayi cikin fuskar tausayi sannan tace kai de...... Shiru tayi sannan ta gyara maganar ta da cewa kai Alhaji daga yanzu zamu tafi cewa yayi zuwa da safe sai ki dawo INSHALLAH su aljannatu anacan ana zuba ido ta ina anty zata dawo yanzu kam nasan sunyi bacci sai HUDAY iyayen kallo
Dan murmushi tayi sannan tace shikenan Hindatu zamu wuce Allah ya ƙara sauki ko zuwa da safe sai ina dawo tunda gasu Hafsah da harira ,sosai innar JANNAT ke mamakin yadda akayi matar ke ta ƙiran sunan su kamar ta dade da sanin su
Hajiya sadiya taje gaban gadon JANNAT ta kama kafadarta tace JANNAT Allah ya ƙara sauƙi ko,girgiza kai tayi alamar ameen sannan suka fita d mijin ta
Kai tsaye gida suka yi inda duk tayi shiru a mota domin gaba-daya tana cikin tension sosai , Alhaji Abubakar mijinta yana ta kwantar mata da hankali domin yasan sadiya da saka abu arai ,kuma likita ya gaya masa komai game da abinda ya faru haka suka koma gida gaba-daya sunyi bacci faɗimatu,aishatu,Hajara, aljannatu sai ƙanwar Hajiya sadiya ne nafeesat da HUDAY idaonsu 2 da shigowar su suka gane anty na cikin matsala gaidata kawai suka yi kowa ya tafi makwancinsa domin su bawa iyayensu privacy
Washe gari da safe Hajiya sadiya tayi sammako zuwa asibiti tare da break fast mai rai da motsi abinci ne kala kala masu dadin gaske da bada sha'awa ga marar lafiya , SOSAI tayi mamakin jikin innar JANNAT domin ta ware sarai , JANNAT dinne ma day da saura sosai amma innar ta kam da sauki kamar wani abu bai faru ba saiday da ka ganta zaka ga damuwa kwance kan fuskarta,.
Tunanin ta 1 shine idan zasu bar asibitin nan wa ze biya kudin jinya bazatace bata da kudi ba saiday suna kalatanga to wa zai dauko mata ,kuma tanason tunda Allah ya kawo su asibitin cikin gari a duba mata matsalar JANNAT domin tasan me ne ko yarta zata iya magana ko a'a
Haka dai Hajiya sadiya ta sameta tana ta tunani fada taɗan mata akan ta rage tunani sannan ta tambayi mai jiki murmushin ƙarfin hali tayi sannan ta amsa da ''da sauƙin '' Allah ya ƙara sauki inji Hajiya sadiya daidai lokacin JANNAT ta farka daga bacci
Bakin gadon ta nufa sannan tace daughter ya jiki '' JANNAT ta gane ya jikin Amma bata gane daughter ba ''girgiza kai kawai tayi alamar da sauƙi
Hajiya sadiya ne tace ''ya kamata a samu ruwan zafi tayi wanka da shiga ciki sannan a gasa mata jikinta ''tayi maganan ba tare da kallon innar JANNAT ba ''
Girgiza kai innar JANNAT tayi sannan tace to Hafsah yar mai gari ita ta haka mata ruwan a banɗaki,Hajiya sadiya ta daga JANNAT da kanta ta shiga da ita banɗaki domin mata wanka,bayan sun gama suka fito ,inda suka samu suna ta hirar kirkin Hajiya sadiya har suna mamakin dama a yan birni masu kudi Akwai irin wadannan mutane?
To break fast day suka yi sannan Hajiya sadiya ta wuce wajen aiki
''tsawon sati 2 cur suka dauka suna asibitin Hajiya sadiya ita taɗau nauyin komai nasu daga ci,sha da kuma buƙatar yaud kullum,harsu faɗimatu sunxo sun duba JANNAT² sunan da suka sawa JANNAT a cewar su JANNAT dinsu itace JANNAT ¹
Yau satin su JANNAT 2 a asibiti inda kuma yaune likita yake shirin sallamarsu JANNAT ta samu Lafiya dayday gwargwado saiday abinda ba'a rasa ba ,kamar raunukan da taji da kuma sata a ruwan zafi amsa kullum ya zamo wa Hajiya sadiya ta innar ta jiki ,haryau daga kalatanga babu wadda yazo su mai gari da muƙarrabansa ,amma baban JANNAT ko leƙe be yiba.
Bayan gama cuku² aka sallame su inda Hajiya sadiya da kanta da police guda2 da kawayenta guda 2 ta kwashe su a mota sai kaltanga maida su JANNAT
BARI MU KOMA KALATANGA*
Ameena ce gaban wani shahararren,ƙasurgumin,tantiri,hatsabibin boka inda take zuba masa kirari,shiko yana ta bushewa da dariya alamar kirarin na masa daɗi saida ta kai aya sannan ya murtuke fuska alamar ya dawo marar mutunci sannan yace ''yake ta hannun daman aljani zambaru me ke tafe dake''?
Gyara zama tayi sannan tace yakai mai share mana kuka mu((wa'iyazubillah mata mu ji tsoron Allah domin kuwa bamu da wani mai share mana kuka mu wadda ya wuce Allah ,dan haka mu koma gareshi d izinin Allah sai mu samu mafita))
Naji ana daɗi a gari cewar gobe wannan kidahumar matar zasu dawo ita da yarta inason kasa aljani zambaru ya shiga jikin Abdullahi idan sun dawo yace shi babu wadda ya Issa yasa JANNAT da uwarta zama masa a gida domin kuwa sun ja masa abin kunya dan haka kawai yace su tafi su bar masa gida,kai Sarkin sarakunan bokaye inason inda hali ma su ya fara yiwa Hindatu tsinannan duka sannan yace ta bar masa gida kuma ya ƙara mata d saki uku.......
Dariya ya bushe da ita sannan ya ce...
🅿️7️⃣
Dariya ya bushe da ita sannan ya ce
''hatsabibiya ta wajena Ni karan kaina tsoron irin baƙar zuciyar ki nake,karki damu za'a yi ayki kamar yadda kk buƙata Amma ki sani ba lallai bane ya iya koran matarsa Hindatu zai daya kori yarsa JANNAT wannan kam a rubuce yake ni Sarkin bokayen yankinnan na maki alkawari gaba daya ma garin yarinyar zata bari amma uwarta daƙyar ne tabar wannan garin''
Gyara zama tayi sannan tace'' yakai Sarkin sarakunan bokaye tayaya JANNAT zata bar gari ba tare da Hindatu ba ?babu abinda ke rabasu fa Ni ina shakku duk da nasan kana zartarwa zata kasance amma na shiga ɗimuwa''
Dariyar ya sake bushewa dashi sannan yace ''nima bansani ba amma ayki na yana nuna min JANNAT ce kadai zata bar garin banda Hindatu'' to ke miye na ɗaya hankalin ki idan tabar garin ita kaɗai uwar ma sai tafi jin tashin hankali ta rasa inda zata tsoma kanta karshe ma ta gudu da ƙafarta tabar mako gidan.
Washe jajayen haƙoranta tayi sannan tace Allah ya taimaki Sarkin bokaye
''murtuke fuska yyi sannan ya ce irin wannan ayki za'a yi da aka saba
Dan jimmmm kadan tayi sannan tace idan buƙata zata biya su shikenan mu shiga daga ciki
''washe ƙarin bakinsa yayi sannan ya tashi ameena ta shiga dakin shi kuwa boka yabi bayanta ''
Kafin ya shiga dakin har tayi zindir nan ya fara lashe baki kamar tsohon maye suka shiga aykata alfasha..
Bayan komai ya lafa ne suka fito ameena na daura zani boka ya na ta yar dariye² sa kallon ta yayi yace ki koma zakiga abin mamaki,ki gaidamin shamsu da kabiru yayana abin alfaharina
Gyaɗa kai tayi alamar fahimtar s sannan ta juya ta tafi ta mai masa yabo da neman Sa'a a wajensa....
''bokan ameena bazaka bada kudi ba aykinshi kawai ki bashi kanki yayi amfani dake shine ladarsa kuma baya bada magani daga wannan saduwar shikenan shi zai aykata Maki komai
WANNAN KENAN
''to bayan ameena ta koma ba daɗewa kuma su JANNAT suka iso kaltanga inda yara suka yi ta bin motar har ƙofar mai gari,dayday lokacin Hindu su dawo daga makaranta ita da shamsu da Kabiru,itama da gudu tabi motar sai gidan mai gari domin kuwa tana hango JANNAT a ciki sabida ba tinted bane motar, Kabiru na kwalla mata ƙira amma ina tayi nisa....
Suna zuwa kuwa mai gari ya fito daga gida nan ya masu iso har cikin gidan inda innar JANNAT da Hajiya sadiya da JANNAT suka fito daga motar suka nufi gidan mai gari,hindu na zuwa ta fara kiran JANNAT!!! Itama sai ta juya jin Muryar hindu tana zuwa ta rungume ta suka fara fara'ar ganin juna ita Hindu dariya take ita kuma JANNAT murmushi
''hindu ta gaida innar JANNAT (gaisuwa da Yaren kanuri) ''innar JANNAT ta amsa da murmushi a fuskarta,sannan tace ya innar ki da su shamsu,ɓata fuska tayi sannan tace lafiya,gaida Hajiya sadiya tayi itama ta amsa da murmushi domin ta gane wannan itace Hindatu mai sunan innar JANNAT ya kuma ga ameena,
Tare suka shiga gidan mai gari inda su harirah suka masu tarbar arziki
Bayan an gama gaisawa ne Hajiya sadiya tasa a kira mata baban JANNAT ,a cewar ta bazata gidan ameena ba ,mai gari da kansa ya aika a ƙura shi
'' yana zaune ameena ta dama masa kunu yana sha saiga sallama amsa wa yayi sannan ya dubi ameena yace barinje inga wanene cikin harshen kanuri''gyaɗa kai kawai tayi ''yasa kai ya fice
Bayan sun gaisa da saurayinne ya fara kora masa bayanin suka daga mai gari..
''shiru yayi domin shi harga Allah sai yau ya tuna da wata Hindatu da yarta JANNAT''
Baice komai ba ya wuce mutumin yabi Bayan shi
Har dakin mai gari aka masa iso yana shiga suka yi arba da JANNAT sai ya ƙara murtuke fuska domin ji yayi gaba-daya kansa ya sara''mai gari yace zauna mana Abdullahi''waje ya samu ya zauna sannan ya kalli Hajiya sadiya gaisawa suka yi cikin fara'a
Innar JANNAT ta daga masa gaisuwa ya amsa aɗan sake
Mai gari yayi gayaran murya sannan yace''abdullahi kamar yadda ka sani tsautsayi ya faɗa kan yarka JANNAT Wannan dalili yasa mahaifiyar ta shiga wani hali itama,Allah ya taimake mu wannan mata tana kusa kuma ta taimaka,matar arziki,mai son shiga ALJANNAH inda ta taimaka gashi yarinyar nan JANNAT ta samu Lafiya babu abinda zamu ce sai gdya''magana ta ta 2 shine Abdullahi anya kanason gamawa lafiya kuwa ,bazaka yi addu'a ba ba azkar balle ka tsare jikinka ,andawo dakai sai yadda akace ?yanzu ka duba yarka tunda suka kwanta a asibiti nan sai mu muke kewa a kansu sakon Allah ya ƙara sauki wannan ba ka taɓa bani na kai masu ba haka suka gama jinya suka dawo wani irin abu ne wannan kanason ka tashi ranar gobe kiyama ne gefenka 1 a shanye tunda ka gagara yin adalci a tsakanin matanka ya kamata ka gyara wallahi kasan mafita cikin rayuwarka...kai ka dawo sabaloto sai yadda mace tayi dakai duk abinda take so shi kake yi to inason ka sani bazan lamunci rashin adalci ba cikin ƙasa ta wallahi na gayamaka kuma kayi wa matarnan godiya ka tashi kaɗau yarka da matarka ku wuce gida,idan ka ga dama ka cigaba da rashin adalcin zandau mataki a kanka idan bandau mataki akanka a matsayin mai gari ba zandau mataki a kanka a matsayin na na abokin mahaifin matarka hindatu....
Haka mai gari yayi ta masa faɗa bayan ya gama yace su kama hanya su tafi
Abdullahi ya buɗe baki dakyar sannan yace ina yiwa wannan baiwar Allah godiya sakamakon ɗawainiya da tayi da matata a asibiti Nagode Allah ya saka da alkairi ,''hajiya sadiya ta amsa da ameen
''magana ta ta biyu shine...sai kuma yayi shiru''mai gari yace ina jinka shiru yayi daƙyar dai yayi magana kamar yana son yayi shiru sai kuma yaji ana masa amsa kuwa da ya furta abinda ke ransa
''gaskiya ranka ya daɗe Ni ALJANNATU bazata zauna min a gida ba domin kuwa tajamin abin kunya dan haka sai day ta naimi wani uban amma baniba domin kuwa baza'a ringa nuna Ni a gari ana ga baban wacce aka yiwa fyade ba,kuma ma ranka ya dade miyasa ba'a yiwa hindu fyade ba ba'a yiwa duk sauran yaran garinnan ba sai ALJANNATU kenan kaga ita ta kai kanta wajen sa har ya mata dama ameena tasha gayamin ALJANNATU tana yawan wasa da yara maza gashinan kuma abu ya tabbata dan haka niday kawai na sallama ta ta nemi wani uban ita kuma Hindatu ta tashi mu tafi...
Salati mai gari da Hajiya sadiya suka dauka sauran kawayenta kam ma sun gagara magana sabida ganin wannan abin al'ajabi wannan wace irin rayuwace mai gari ba abinda yake maimaita wa sai tasbihi ga Allah JANNAT kam baza ta iya gane abinda ya faɗa cikakke ba ita de taji tabarmai gida sai daɗi ya kamata domin kuwa wlh so take dama su bar gidan itada innarta, Hindatu kuwa kuka ne ya ƙwace mata inda ta shiga rera shi tana faɗin
''wannan wace irin jarabawa ce a dake ka a hana ka kuka to wallahi Abdullahi bazan koma gidn ka ba tare da JANNAT ba saiday ka sake Ni idan yaso in tafi da yata babu wadda ya isa ya raba i da JANNAT tayaya zaka ce way tabarma gida saboda kanason ka tozartani ka walaƙantani ka nuna min bani d wani sauran gata,yanzu idan kace JANNAT tabar gidan ka sai taje ina ko ina da wasu yan uwa ay bazan bar JANNAT ta koma gurinsu ba da raina d lafiya ta balle kuma bani da kowa daga ita sai Allah wallahi Abdullahi ka sake Ni kawai ta karisa Maganar tana gunjin kuka😭
Kowa yayi shiru a dakin yana sauraren ta idan kace baka ji tausayi Hindatu ba to lallai babu imani cikin ranka domin kuwa bar tausayi ce kwarai da gaske tana cikin wani yanayi mawuyacin marar misaltuwa
Tsawon minti 15 a dakin ba wanda yace komai sai kukan Hindatu dake tashi inda JANNAT ta fara tayata ''shi kuwa Abdullahi ko ɗar bai nuna yaji wani abu ba kuma yana kan bakan sa ,sai ma wata uwar harara da yake bankawa JANNAT wadda ya fara firgita ta
Mai gari ya kasa cewa komai haka Hajiya sadiya,wata kawarta ce tayi gyaran murya sannan ta fara da cewa ''amma kai dai bawan Allah baka da cikakken imani ko tausayi kamar ba yarka ta cikin ka ba to barin gaya maka babu yadda za'a yi wannan mata ta koma gidan ka idan ba tare da yarta ba idan sakin ta zaka yi zata tafi da yarta idan kuwa bazaka saketa ba to ya zama dole ka riƙe yarki abin kunya kam su ya riga da ya faru ,kuma duka kauyennan kowa yasan ba laifinsu bane ƙarfin su aka fi , wallahi wallahi wallahi kaji rantsuwar musulmi idan kace zaka walakanta matarnan da yarta yanzu zan maka ka kotu sannan in kwata masu yancin su kuma ina daureka inga kuma wadda ya isa ya kwato ka kaf garinnan ,ya ana lallashina kana wani bauɗewa kai a dole namiji ko to ko ka zaɓi daya ta koma gidan ka da yarta ko kuma ka sake ta kuma ka ringa biyan kudin ciyar da yarka da shayar da ita maza ka zaɓi 1 ko yanzu kaga mai zan maka anan...ta karisa Maganar tana nunfashi da alama idan aka barta tsaf zata iya dukan Abdullahi sabida ranta ya gama ɓaci ba kaɗan ba
Abdullahi yace wallahi na rantse da Allah ALJANNATU bazata zauna a gidana ba kuma banga wadda ya isa ya sani na saki Hindatu ba 'kuka innar JANNAT tasa tana cewa Wallahi Abdullahi saika sakeni gwara nayi yawo a jeji dana rabu da JANNAT a rayuwata ''wannan matar tace kima daina rantse wa dole ya sake kine indai inada numfashi sai an kwata mako yanci wannan wanne irin rayuwa ne haka wannan su zalincine kuma wallahi bazamu lamunci rashin adalci ba''
Nanfa faɗa yaso ɓarkewa tsakanin Abdullahi da kawar Hajiya sadiya inda ya kafe shi bazai saki Hindatu ba kuma wallahi JANNAT bazata zauna mar cikin gida ba
Daƙyar mai gari ya tsawatar sannan suka yi shiru '''mai gari ya kalli Abdullahi yace kana da dalilin ka na cewa JANNAT bazata zauna gidan kaba? Abdullahi yace ranka ya dade dalilinsa 1 ne kawai saboda taja min abin kunya kuma yanzu mutane ba damar na wuce sai ace ga baban wacce akaiwa fyade Ni shine dalilina
Mai gari ya girgiza kai sannan yace Abdullahi wannan ba dalili bane , dalili na na fadar haka kuwa shi ne kowa yasan JANNAT ta haɗu da tsautsayine ba yin kanta bane kaga kuwa bamai maka gori kuma Ni na maka alkawarin duk wadda ya nuna ka ya ce kaza kazo ka sameni ka gayamin zan ɗau mummunan mataki a kansa ko wa ye shi... Shikenan na gama Magana
Abdullahi yace ranka ya dade ameena fa ta gayamin ALJANNATU da kanta takai kanta akayi mata fyade Kum........
Kafin ya rufe baki ƙawar Hajiya sadiya ta kutuntumo ashar ta zabga sannan tace way wace yar abu kazancan ne ameena ku gayamin inda take naje naci mata uwa dan uba ta,toshe mata baki Hajiya sadiya tayi sannan tace haba Hajiya saliha calmdown mana komai zai tafi day day insha Allah
WACCE aka kira Hajiya saliha huci kawai take na baƙin ciki
Mai garine yace shikenan Abdullahi naji kuma ka nuna min matsyina ka tashi kaje zan neme ka amma ka sani ko Hindatu zata dawo gidan ka ba yanzu ba saina gama shawara tukunna zaka iya tafiy
Tashi yayi ya fita inda yake zabgawa JANNAT harara kamar wata babba,
Bayan ya fitane innar JANNAT tasa kuka ta kalli mai gari sannan tace baba kumin adalci dan Allah kar Abdullahi ya cuceni ynxu ina xan saka rayuwata
Hajiya sadiya nata bubbuga mata baya tana lallashina
Shiru kowa yayi sai can mai gari yace ''ni inaga abinda Zaifi shine Hindatu ta koma gidan ta tabar JANNAT wajensa harirah anan wajena nayi alkawarin daukar ɗawainiyarta har Allah ya dau raina insha Allah,tunda Abdullahi ba ruwansa da Hindatu inyaso kullum sai ta ringa zuwa tana ganin JANNAT anan wajena tunda itadinne baya son gani
Hajiya saliha tace haba baba mai gari wannan fa rashin adalci ne shin yafi ƙarfin hukuma ne shi da baza'a sashi dole ya sake taba?mata ga diri gata da kyan hali ga kyau ga sansanyar murya wallahi nayi imani idan Abdullahi ya saki Hindatu kaf kauyennan ma tafi ƙarfin mazan gaba 1 shin ita baza'a mata adalci bane.....
Guntun murmushi mai gari yayi sannan yace hajiya baƙi taki ba amma inason ki gane cewa Hindatu bata ci riban zama a gidan Abdullahi ba kwatakwata riba 1 ta samu shine na haihuwar yarta JANNAT amma babu wani dadi da ta lasa nasan babu abinda yazowa zama kuma ba ƙaramin so Abdullahi kewa Hindatu ba INSHALLAH da izinin buwayi gagara misali sarki Allah zai nuna wa ameena iyakarta ,ina nufin randa baƙin zaluncinta zai fito fili to dan haka banason kowa yace komai , Hindatu idan na isa dake ki tashi sadiya da saliha su taka ki gidanki ki cigaba da yiwa mijinki addu'a har Allah yasa ya gane kuma kullum ki ringa zuwa kina ganin yarki JANNAT Ni na dau alkawarin daukar nauyin ta har iya inda ƙarfina ya ƙare, Allah ya miki albarka ya baki abinda kike nema duniya da lahira Allah Ya tsare gabanki da bayanki Allah ya taimaka.....
Hajiya Sadiya ce tace ranka ya dade idan baza ku damu ba a bani JANNAT 😳
To fans ya kuke gani a bawa Hajiya sadiya JANNAT ko kuwa ina jiran shawarwarinku ta wannan number ga wadda basa group ɗin JANNAT suke son Magana dani*👇
07059305867
🅿️8️⃣
Hajiya Sadiya ce tace ranka ya dade idan baza ku damu ba a bani JANNAT
Tsit kake ji dakin yadau shiru kowa ya zurawa mai gari ido dan jin abinda zai faɗa
Shiru na kusan minti 6 sannan mai gari ya nunfasa yace''baiwar Allah bazance baki JANNAT yana daga cikin ganganci ba amma idan aka baki ita miye makomarta?kingade mu bamusan kiba,kin taimaka mana ne lokacin da muke bukatar taimako kin kyauta kam kuma kin nuna halaccin ki garemu, Amma a matsayinsa na asalin sarki mai son ganin farin cikin al'umma ta bazan iya daukan yarinya in Baki ba har sai na gudanar da binkice mai kyau sannan zan iya baki yarinyar, kuma sai naji ta bakin mahaifiyar ta sabida tana da hakƙi akanta idan ta yarda na baki to idan kuma ta nuna rashin amincewar hakan gaskiya ina mai baki haƙuri...
Kallon ne ya koma kan Hindatu dake ta kuka tana tunanin ita rayuwarta haka zai ƙare kenan kullum asirinta a tone wannan wanne irin Bala'i ne
Babu wadda ya hana ta kuka saida tayi mai isarta sannan mai gari ''yace Hindatu kiyi haƙuri kiyi shiru INSHALLAH inaji ajikina wataran kukan kinnnan zai zama dariya da izinin Allah ,babu abinda yazo wa zama cikin duniyar nan komai da kike gani mai wuce wa ne,''cikin shasshekar kuka tace to baba😭
Bayan ta gama kukan tane mai gari yace yanzu ya kike gani zaki iya bata JANNAT?
''share hawayen da ya zubo mata tayi sannan tace ''baba haka kawai naji zuciya ta ta aminta da matannan bansan dalili ba naji ta kwanta min arai duk da mugun bashi da kama Amma zuciya ta tana gayamin ba mutuwa bace bansan Dalili ba ?amma ina alaƙanta hakan da kulawa da ta ringa bawa yata JANNAT haka kawai naji tayimin kuma ina ganin soyayyar JANNAT cikin idanun ta sannan tana iya aikata shi a aikace bazan iya hana ta JANNAT ba sabida ina da buri SOSAI akan yata JANNAT sannan tunda kaji ameena ta fara wannan maganganu to idan JANNAT ta zauna a wannan garin ba daɗin shi zata jiba watakila ma idan ta fara girma tasan mai take yi abin ya riƙa damunta hakan kuma zai iya jamata naƙasu a Rayuwar ta bayan wadda take fama dashi ,ga bata gidan mahaifinta,abin zaiyyi yawa gwara kawai tabar kaltanga gaba 1 hakan zai sa hankali na yafi kwanciya nikuma sai na fuskanci yadda zan cigaba da zama da ameena domin kuwa ta kaini bango maƙurar kurewa ,dan haka babu komai kayi binkice akan ta idan kaga ya dace ambata JANNAT zanyi farin ciki da hakan idan kuma kaga wani aybi tattare da ita sai JANNAT din ta zauna nan wajen ka babu damuwa Allah yasa haka shiyafi zama alkairi a rayuwarta😭ta karisa maganar da fashewa da kuka...
Mai gari ne ya gyara zama sannan ya fuskanci Hajiya sadiya da Hajiya saliha da kawar su Hajiya Turai yace to kunji abinda Hindatu tace ,baiwar Allah ya nuna Hajiya sadiya ,tace na'am baba ,''yace zan baki JANNAT yanzu ku tafi sannan daga yau zanfara bin cikar halin da zata shiga a gidanki,ba Hindatu kaɗai taji kin kwanta mata ba a'a harda Ni domin kina da zuciyar tausayi kina nuna soyayyar yarinyar ƙiriƙiri a fuska
''dan haka zaku tafi da ita yau zamu tafi tare zanga muhallin ki da inda JANNAT zata zauna ,zamu tafi da harira matata da yara Hafsah ,kafin mu tafi inason ku raka Hindatu ta koma gidanta ta cigaba da zaman aure wannan shine masalaha tacan kuma ki tahowa da JANNAT kayanta domin kuwa ko komawa gidansa bazatayi ba ,kuma ku shaida Ni mai gari
''nayi alkawarin Abdullahi bazai sake ganin JANNAT ba sai ta zamo wani abu a rayuwa idan ma zai sake haduwa da ita sai yasan mahimmancinta tukunna....
''sadiya ya ƙuira SUNAN ta ''na'am ta amsa sannan ya cigaba''inason ki nuna mana halaccin waje rike yarinyar nan inason ki bata tarbiyya da ilimi dayday gwargwado kinga yadda take sannan Kinga lalurarta ''ki dauka cewa zaki raini marainiya ne marar uba ba mai uba saboda a halin yanzu JANNAT batada wani gata da ya wuce mahaifiyar ta da kuma ke a duniya dan Allah ki riƙe wannan amanar inason ko baki dauki JANNAT matsayin yar Cikin ki ba ki dauke ta a matsayin wani abu da zaki kula dashi don Allah ya baki lada.....
Allah yamiki albarka, Allah ya baki abinda kike nema duniya da lahira sannan ya miki jagora cikin lamuranki mungode Allah ya saka.....
Hawayen daɗi ne mai cike da murmushi da farin ciki ya zubo wa Hajiya sadiya nan ta shiga kwararowa mai gari da Hindatu godiya tana share kwallan farin ciki...
Allah ya gani tana matuƙar don JANNAT haka kawai taji yarinyar tayi mata bata sani ba ko dan tanajin itama abinda ya sami JANNAT din ya shafe ta ne oho amma harga Allah tana tausayinta musamman ma wannan lalurar Tata ta rashin magana da bata yi
Nagode ranka ya dade Allah ya saka da mafificin alkairi ina godiya Allah yabar zumunci yabar ƙauna Allah yasa mu dore har mutuwa a haka INSHALLAH nayi alkawarin kula da ita har iya inda zan iya kuma da izinin Allah bazata yi rashin uwa ko uba a kusa da ita ba Nagode ,su Hajiya saliha ne suka taya ta godiya inda suka taya ta samun wannan kyakkyawar Black beauty din yarinyaar.
Mai gari yace maza ku raka ta sai ku taho da kayanta mu kama hanya....
''tashi suka yi innar JANNAT ta riƙe hannun JANNAT game ji take kamar wannan ganin shine na ƙarshe da zata mata,cewa tayi'' ALJANNATU ''daga kai JANNAT tayi ta kalle ta sannan tayi murmushi cigaba tayi da cewa ''ki zauna gidan baba ga hindu kuyi wasa tunda taki tafiya gida barinje Yanzu indawo
JANNAT bayani komai ba sannan bata gane shiri bane tunda dama suna zuwa wasa gidan mai gari nan suka fita da yar uwarta hindu suna dariya sai wasan ƙasa
Siririn hawaye daya zubowa innar ta ta share sannan suka fita,da gidan mai gari da gidan su JANNAT ba nisa don haka da ƙafa suka taka zuwa can,yan gari kuwa sai kallon Mata masu kida kudi, ilimin boko dana addini,ga wayewa ko wacce tasha boko ta bugu ga kudi kamar me suke ,nan akayi ta ƙusƙus ganin Hindatu Cikin su ''to wasu sun gane Hajiya sadiya wasu kuma basu ganetaba ,daga masu cewa wacce taɗau JANNAT a mutane sai masu cewa a'a Sudan tafiyarsu kawai suke da police 2 na take masu baya har gidan su JANNAT
Da sallama dauke a bakin su suka shiga ciki ameena na zaune a tabarma da bombom stick gabanta tana jiran Hindu ta dawo taci uwrta sai taji Sallama innar JANNAT ce a gaba sai Hajiya saliha sai Hajiya Turai sannan Hajiya sadiya , innar JANNAT ta buɗe baki zata gaida ameena Hajiya saliha ta matsara da ita gefe sannan ta toshe bakinta tace'''munafuka annamimiya idan ma kin yi wani tsafinne bokan ki yace sai ta gaidaki ya kamata to ƙaryarki wlhi annamimiya kawai munafukai kuma kice tak yanxu insa ay maki shegen duka, Hindatu day gata ta dawo idan kin sa ya hana JANNAT zama cikin gidan ita tafi ƙarfin ki ta Allah kuma ba taki ba wallahi,idan zaki gane Annabi ya gamu ki gane idan kuma sai lokaci ya ƙure Mali to Bismillah....haka Hajiya saliha tayi ta yiwa ameena ɓarin masifa Ita kuwa tana shiru sai tsilli tsilli take da idanu domin kuwa ba tacewa ''🤣🤣🤣 ashe iskancin ma guri yake samu su ameena anji bosawa''' haka suka shige dakin ameena ,iya tausayin sun tausaya mata domin kuwa idan banda tabarma babu komai cikin dakin sai tarkacen kwanuka ta da ameena ta hana ta ajiye su a kuxin Dan haka ta kawo su daki ,sai kayan ta dana JANNAT dake haɗe cikin ghana most go haka suka zauna a tabarman hindstu ta buɗe randar kasan ta ta debo masu ruwa mai Bala'in sanyi sosai kowacce tasha
Sai zuciyar Hindatu ta kwanta sabida ta dauka bazasu shaba nan fa ta ƙara tabbatar wa kanta insha Allah yarta JANNAT zatayi rayuwa babu tsangwama....
Tashi tayi ta fara haɗa kayan JANNAT a leda gari yayi zafi...
''hajiya Turai ne ta dakatar da ita sannan tace ''ni zan siya wa JANNAT kayan sawa gaba daya idan mun shiga Gombe na dau wannan nauyin baza'a yi aykin lada babu niba Ni na dau wannan fannin dan haka kiyi kyuata da kayanta ''murmushin farin ciki innar JANNAT tayi sannan tayi mata gdya
Basu wani daɗe ba sabida yau zasu koma dan haka suka dan mata nasiha da baza'a rasa ba na tayi haƙuri sannan Hajiya sadiya ta ciro wata karamar itel waya (inuwa gida gida😅)ta bude cikin purse dinta ta dakko wani dadadden simm ta sa ka mata sannan ta bada tace Hindatu da wannan zan ringa kiranki kullum zakuna Magana d JANNAT sannan ki riƙe a hannun ki duk wata matsala zaki iya ƙirana ta wajen ba damuwa dan koya mata tayi kawai saboda number 2 ne kawai cikin wayar daga na Hajiya sadiya saina ɗanta HUDAY shikenan
Godiya tayi ta masu sannan Hajiya saliha ta bata dubu ashirin ta riƙe wajenta ko wani abu zai taso mata''ƙin karɓar tayi a cewar ta ba komai dama dawainiyar JANNAT ne kuma sun dauke ''daƙyar suka sata ta karɓa akan ta ƙara karin sana'ar ta
Dan ɓata fuska tayi alamar damuwa sannan tace ay ameena ma tasa baban su shamsu ya hana mutane shigowa siyar kunun da kayan miyar da nake siyarwa ,Hajiya saliha tace ƙarni day kekam karki damu.....
Godiya tayi sosai harda kwallanta sannan su Hajiya sadiya suka fito da niyyar tafiya ameena ta tattara koli ta ta wuce daki domin kuwa ba ƙaramin tsoro saliha ta bata ba
Suna fita daga gidan Hajiya saliha tace tayi matuqa bari ta dauko su wuce tana zuwa ''hajiya Turai tace Baida'u mu kiranki ki ɗauko''a'a cewar saliha kubaemin Ruth sai mu taho tare (yar sandan da suka taho da ita )ok cewar Hajiya sadiya....
Komawa gidan suka yi kai tsaye dakin ameena saliha ta wuce ,ameena na zaune dasu shamsu kabiru na kwance kan tabarma sai ganin mutane suka yi a kansu''ni yar gida barau cewar ameena tana zare idanu,
Hajiya saliha ta kalli Ruth tace ''slap her very well''wani gigitaccen mari Ruth ta sauke wa ameena saida taga Stars nan fa ta kurma ihu ta faɗin na shiga 3 Ni yar gidan barau (ku kuke gani mu bamu muke ganinku ba ,dan girman Allah baiwar Allah kiyi hakuri mai na miki )Ruth ta doke Bakin ameena da bayan hannunta sai jini nan tayi shiru ta fara hawaye su shamsu kuwa sun rakuɓe da gini suna wulli wulli da ido(🤣🤣🤣 Wallahi iskanci ma wargi ya samu)
Hajiya saliha ne ta ɗora yatsanta kan bakin ta tace shiru tana zare wa ameena ido ''hannunta tasa ta riƙe bakinta tana hawaye domin kuwa harga Allah ta tsorata ga azaba dake damunta baki sai jini yake haka ta riƙe shi tana hawaye (ga Ruth irin zabga zabgan matan nanne masu nonuwa da uwawu😅 ga gashin kanti akanta shine abinda ya ƙara firgita ameena)''hajiya saliha tace miye Dalilin ki na hana Hindatu yin sana'a cikin gidannan?kafin tayi magana Hajiya saliha ta cigaba da cewa ko gidan ubankine dake aka gina gidanne ? girgiza kai kawai ameena take tana kuka ... Ina magana bazakice komai ba?kafin Hajiya saliha ta rufe bakinta Ruth ta sake hanɓare ameena 🤣
Ah ahh uhmmm mmmm Dan Allah kiyi hakuri wallahi babu ko 1 kuma nayi alkawarin zata dawo sana'ar ta bazan ƙara sa mata idanu ba, ta faɗa cikin kuka
Dariya Hajiya saliha tayi sannan tace mijinki na dawowa ki gaya masa Hindatu zata cigaba da sana'a ke kuma ki je ki gaya mata ta fara sana'ar ta zuwa gobe zan dawo idan baki gaya mata ba wallahi na lahira su ya fili jin sumul kinji Ni?Hajiya saliha tayi maganar tana kama kunnen ameena
Uhmmmmm uhmmmmm nji ki Hajiya Ni yanzu ma zangaya mata kafin ki tafi ....
Hajiya saliha tace to maza miƙe muje ki gaya mata kafin ranki ya kuma ɓaci ''minewa ameena tayi suka fito inda Hindatu take tsaye a tsakar gida tana mamakin kamar Muryar Hajiya saliha take ji cikin dakin bayan kuma sun fita da har zata shiga sai taga faɗa da ba ruwana dadin kallo garai kawai sai ta tsaya''tunaninta ne ya tsinke ganin fitowar ameena tana hawaye baki a fashe sai jini yake har ya fara kumbura Hajiya saliha na biye da ita ga kuma yar sanda
Gaban Hindatu ameena take tace Hindatu ki fara sana'ar ki go e dan Allah ki e su rabu sani Ni daga yau ma babu ruwana dake Alqur'an... Dariya ne ya kusa kashe innar JANNAT saiday ta danne ta girgiza kai alamar to kawai sannan ta juya ta shiga dakin yana tuntsira dariya🤣
Hajiya saliha kuwa fita suka yi ay kawai sai ameena ta fashe da kuka tana faɗin na shiga uku Ni yar gidan barau yau ban tashi da Sa'a ba yau nice gani ga yar sanda hartana dukana oh Ni diyarsu jikar dan Sambo🤣🤣
Shamsu da kabiru ne suka fito suna sheka dariya Kabiru harda riƙe ciki sabida mugunta na cinsa....
Hajiya saliha suna isa suka samu har su mai gari sun fito cikin shirin su dan haka kawai mota suka shiga...
Harirah ce tacewa hindu kije ki cire kayan makarantar ki sai kisa na gida ki gayawa innar JANNAT ta fito mu tafi sai mu tafi tare dake .....
Da gudu hindu tayi gida tana murna tana cewa JANNAT , JANNAT barinje nasa kaya irin naki da innar ki ta ɗinka mana sai mu tafi ko ku Ku jirani fa nan ta falla a guje
Kowa sai da yaji tausayinta nan suka shiga Mota suka tayar sai cikin Gombe nan JANNAT ta fara kuka,hawaye kamar an buɗe fanfo da tana da baki cewa zatayi ku kaini wajen innata 😭...
*COMMENTS DINKU NA SANI NISHADI YAN JANNAT FANS GROUP ADDUO'INKU NA MINI DADI INA MATUKAR GODIYA HAKA SHINE YAKE NUNA MANI ANA BALA'IN TARE KU CIGABA DA BIBIYATA ZAN CIGABA DA BAKU NISHADI KU KUMA KU CIGABA DA SUBURBUƊO DA RUWAN COMMENTS DA ADDUO'INKU NA FATAN GAMAWA LAFIYA* 🙏
🅿️9️⃣
Sosai driver ke gudu cikin 1 hour 30 minutes suka iso Gombe kai tsaye aka fara sauke Hajiya saliha da Hajiya Turai sannan aka yi tunfure gidan Hajiya sadiya
Tunda aka shiga layin eckwa church su mai gari ke bawa idonsu abinci dankon gidajene iya ganin ka suday kallo kawai suke inda JANNAT tasha jikanta hartayi bacci tana da ajiyar zuciya
Tangamemen gare din gidan mai gadi ya bude inda wakeken filin gidan na farko ya bayyana tafiya aka ƙara yi sannan aka bude gare na 2 duka police ne ta ko ta Ina suke ta yawo ,gare na uku aka bude wadda ya kasance ƙaramine shi to anan ne fa asalin cikin gidan ya bayyana''zuwa wannan lokacin mai gari ya gama saddakarwa yanka kansu za'a yi sabida shi ko a labarai be taɓa jin gida mai gare uku ba nan aka yi parking a parking lot din da akalla zai dau mota 30 saiday guda 15 ne a wajen
Motar da mai gari da harirah suke aka buɗe masu suka fito su su dauka nazama suga Hajiya sadiya ba sun saddaqar da kayukansu kawai za'a yanke da suka hangota sai suka taho da sauri wajenta domin kuwa idan ka kalli gidan ta ko ta ina police ne kuma kinsan dan ƙauye da tsoron police ,hajiya sadiya kawai suka sani dan haka suka tsaya tsamo tsamo
Dauko JANNAT tayi a kafadarta inda police mai tsaronta tazo zata karɓi JANNAT ta hana ta
''kallon mai gari tayi sannan tace bana mu shiga ciki to Hajiya ''dan murmushi tayi sannan tace ka daina cemin Hajiya baba Ni yarka cefa kace sadiya kawai girgiza kai yayi shiday har yanzu ya kasa gaskata a duniya yake ko a ina...😅
Hajiya sadiya ta kalli wani police cikin harshen turanci tayi Maganar da alama bayanin Hausa (ka kai shi dakin baki) police din ya girgiza kai tare da rusunawa alamar girmamawa ''kallon mai gari yayi yace let's go'' hajiya sadiya ce tace baba kuje zai kaikai ka huta kayi salla la'asar tayi sai ka ci abinci za'a kawo maka
''girgiza kai mai gari yayi yace to police din ya wuce gaba inda mai gari yabi Bayan shi yana waigen su harirah😅''hajiya sadiya tace wa su harirah muje ko? Hafsah yar mai gari ta karɓi JANNAT daga hannun Hajiya sadiya suka bi bayanta
Parloun gidan suka shiga nan fitsari ya kusa kufcewa harirah domin kuwa ita harga Allah ta tsorata wy wannan gudanar kuma a duniyar nan yake anya mijinta bay kawo su ga halaka ba kuwa ''haka daya tayi hakuri ta ƙara da shiga ciki''
Hajiya sadiya ta cire hijab din dake jikinta sannan tace wa Hafsah sauketa ki kwantar da ita kan kujerar nan to Hafsah tace sannan ta kwantar ta
Ƙofa ta nuna masu cikin parloun tace ku shiga akwai banɗaki ciki sai kuyi alwala la'asar tayi to harirah tace''wani tunani ne ya faɗo wa Hajiya sadiya kuma su tace ina zuwa ''kiran suna ta fara yi tanacewa Hannah Hannah '' da sauri wata budurwa da kayan uniform alama maaikaciya ce ta fito ta durƙusa gaba Hajiya sadiya (cikin turanci ta gaisheta ta amsa sannan itama ta gaya mata da turancin)'' ki kansu toilet ki nuna masu yadda ake anfani dashi sai ki basu sallaya sannan ki fito ki basu abinci Ni zan yi wanka nayi salla zan fito yanzu a kai masu abinci'' mai kuka dafa?ta tanbayeta ''white rice nd stew , coslow nd chekean'' ok ki basu Amma yanzu ki nuna masu toilet da yanda zasuyi anfani dashi''
Hafsah ku bita zata nuna maku banɗaki da yadda zakuyi amfani dashi zanyi wanka inyi salla ina fitowa
To Hafsah ta amsa sannan Hajiya sadiya ta wuce su kuma suka bi wacce aka kira Hannah kamar raƙumi da akala
Ƙaton bedroom ne da zai iya daukan maka makan gadaje guda 3 sannan space ya saura katin gado ne guda 1 a ciki sai Waldrop shima ƙato sai madubi babu wani tarkace kasancewarsa ɗakin baƙi.....
Harirah aka fara nuna wa yadda zata using toilet din Sannan Hafsah ita Hafsah da yake yaɗa yi boko sannan tayi aure a kashere auren ya mutu to taɗan san wasu abubuwa amma ita kanta sai da wannan gida ya ruɗa ta
''to bayan sun idar da Sallah ne harira ta kalli Hafsah tace hafsatu🤔 gaskiya idan wannan mata ta riƙe JANNAT tsakani da Allah lallai ba ƙaramar mutum za'a tayar ba a wajen kiga gida sai kace ba a duniya muke ba kina gani ƙofa kawai saida muka wuce tafi nawa sannan muka zo cikin gidan ''to ga cikin gidan ma kawai kamar aljanna
''kafin Hafsah tayi magana saiga Hajiya sadiya ta shigo da kanta tace su fito suci abinci ''
Fitowa suka yi sai suka yi turus a tsakiya parloun Hajiya sadiya tace Bismillah tana nuna masu dining kowa taja kujera ta zauna Kamar wadda take kan ƙaya
''hannah da wata mata itakam da gani musulma ce su suka zuba masu abinci shinkafa da coslow da yaji naman rago sai paper chekean a gefe
Zagee wa suka yi sosai suka ci abinci amma ba wacce taci coslow a cikinsu da alama bai masu ba
Lemo da zoɓo suka sha sannan kowa tayi hamdalah, sauƙowa suka yi a dining din suka dawo parloun say day nan JANNAT ta farka tashi tayi ta zauna tukunna sannan ta fara ƙarewa inda take kallo kanta ne ya kulle dan haka tayi ta raba ido ta gagara tuna komi kuma
Harirah ta hango dan haka ta tashi da gudu tana murmushi taje ta riƙe ta Hafsah tace JANNAT kin tashi?ɗaya kai tayi alamar eh ''day say lokacin Hajiya sadiya ta fito da fara'a fuskanta ta kalli JANNAT tace JANNAT² riƙe hannunta JANNAT tayi alamar gaisuwa ''kumatunta yaɗa ja itama sannan ta nemi waje ta zauna
JANNAT nason cewa ina innarta amma ta kasa faɗa haka dy tayi shiru sabida aɗan zama da suka yi a asibiti ta saba da ita sosai da yake kullum tana cikin kawo mata kayan zaƙi tana sha kuma zuciya tanason mai kyautata mata
Mangariba ta kusa dan haka su harirah suka fara shirin tafiya domin yau zasu koma driver zai me da su inji mai gari
Dakin da aka sauke mai gari nan suka je suka same shi ya gama cin abinci nan ya ƙara yiwa Hajiya sadiya nasiha da gdya sannan suka mike da niyyar tafiya....
Fitowa sukayi harabar gidan nan Hajiya sadiya ta cika su da goma ta arziki harirah da Hafsah dubu 10 10 ta basu mai gari 30 sannan ta bawa Hafsah waya mai kyau ƙaramar tecno softtouch kasancewar Hafsah tayi boko tace duk lokacin da take son yin magana da innar JANNAT vedio call zata ƙira idan yaje ta nemi wadda ya iya setawa ya sets mata Kasancewar lokaci ya ƙare
Haka day suka shiga Mota inda JANNAT take ƙoƙarin binsu Hajiya sadiya ta riƙe ta nan fa ta fara kuka tana fisgewa amma ina driver yaja su'' dayday nan kuma mota ta shigo inda aka dawo da su faɗimatu daga islamiyya
Dukkan su suka fito kawai sai suka ga JANNAT² a gidan su nan suka zo kowa ta riƙe ta tauri tsuru JANNAT tayi domin kuwa babu bakin kuka kam
Cikin gida suka wuce inda HUDAY yayi part dinshi daban
Nafeesat ƙanwar Hajiya sadiya ce take tanbayar Hajiya sadiya ''anty JANNAT din ta dawo gidannanne? girgiza mata kai tayi alamar eh nan suka sa ihun dadi kowa ya rungume JANNAT itakuwa ido yayi tsuru tsuru.....
''to bayan anyi sallan isha HUDAY ya shigo parloun duk suna parloun ana kallo itaday JANNAT tana dari dari domin kuwa kewar innar ta ke damunta da tana da baki abinda zata fara tambaya shine ina inna ta sannan ina ne nan to amma babu halin hakan dan kuwa babu baki....
Zama yayi suka dan fara hira da yan'uwansa anan Hajiya sadiya take basu labarin kaddarar JANNAT da mahaifiyar ta sannan fyaɗe da rashin iya magana
''wani tausayin JANNAT ne ya tsufa wa nafeesat, HUDAY,faɗimatu aishatu kam da ALJANNATU basu fahimci komai ba sabida yara ne ƙanana
HUDAY kam jiyayi maza ma Allah wadaran su yanzu yar yarinyar nan an ɓata mata rayuwa ya hayyu ya qayyum Allah ya kare mana zuri'a cewar HUDAY hira suka yi SOSAI anan bacci ya kwashe JANNAT ² saida suka gama sannan kowa ya nufi makwancinsa sai 11 mai gidan ya dawo.......
Nan Hajiya sadiya ta yi masa bayani tare da bashi haƙuri akan hukuncin da ta ɗauka bada izinin shiga ta ƙara da cewa ''yarinyar ta bani tausayi shiyasa kuma abban HUDAY kai kadai kasan irin raɗaɗi danake ji cikin raina basai na faɗa maka ba inason ka bani ƙarfin gwiwa na taimakawa yarinyar nan domin inaji a jikina watara zata zama wani abu
Rungume ta yayi yana lallashi sannan yace sadiya sani da dukiya ta d abinda na mallaka duk nakins kiyi yadda ki so dashi wallahi sadiya ko kare kk dauko kk kawo gidannan yafi ƙarfin walaƙanci a wajena bare ɗan mutum ,duk abinda kk San uba na wa yarsa Ni ki daura min zsnyiwa JANNAT shi nayi alkawarin daga sutura,skull fees,kayan sawa ,buƙatun yauda kullum ni zan ɗaukewa JANNAT ke kuma ki cigaba da kula da taribiyya kamar yadda kike kula da nasu faɗimatu......
Wata runguma Hajiya sadiya tayiwa mai gidanna ta tana dariyar farin ciki .....niday da sauri na fito domin zuwa gurin nasa mijin sai kuma zuwa da safe kwa jini da ci gaba mu kwana ƙalau🏃
Kuyi hakuri da wannan na yanke a yatsa ta babba wadda nake typing shiyasa yyi kadan ayi manage.....
_INA ROKON KU DA KUSANI CIKIN ADDU'O'INKU INA DA BUƘATU ALLAH YA BIYA MANI_
🅿️_1️⃣0️⃣
To washe gari da safe haka suka tashi gaba daya kowa yana shirin tafiya school masu shirin zuwa ayki nayi anty (Hajiya sadiya)da kuma abu,sai nafeesat dake shirin tafiya hau(Gombe State University)sai su ALJANNATU da za'a je a sauya wa makaranta su faɗimatu kuwa da aishatu da Hajara international suke, ALJANNATU da JANNAT za'a saka tare ita ALJANNATU za'a canza mata ne ita kuwa JANNAT za'a sata(matrix) to haka dau gaba daya kowa ya gama shirya wa
''7 dayday kowa ya fito domin shine lokacin break fast ɗin su da suka cire
Masu zuwa makaranta kowa da uniform a dining suka zauna inda JANNAT taja ta tsaya tana kallon kowa
HUDAY ne yace JANNAT zo mana ki zauna kujerar kusa dashi ya nuna mata matsowa tayi ta zauna sannan Hannah ta fara serving ɗin su ''dining din yayi shiru sai ƙaran cokala kake ji da plate kowa ya maida hankali ga abinda ke gabanshi
Sosai abu ya lura da JANNAT ba cin abincin take sosai ba tafi shan tea kuma shima a hankali ya fuskanci rashin sabo ne to amma yasan a hankali zata saba..bayan sun gama ne suka mike abu zai wuce wajen ayki anty zata kai su JANNAT makaranta sannan ta wuce ayki su nafeesat da su HUDAY driver zai kai su school
Haka suka fito kowa ya kama gabansa inda su anty suka shiga Mota da su JANNAT, kai tsaye matrix suka wuce tunda ga bakin ƙofar school ɗin securities ne suke gadi, motar kai tsaye ta kutsa ciki ,bayan sun fito suka wuce ofishin shugaban makarantar bayan yan gaishe gaishe ta gabatar da su JANNAT cikin dakin fuska yace ba komai ay hajiya sunayensu za'a bayar sai registration, uniform,da littattafai,da islamiyya ne ko babu Hajiya sadiya tace duka zasu shiga'' a take akayi komai aka basu komai ta cika kowacce aka saka sunan ta ALJANNATU ABUBAKAR da ALJANNATU Abdullahi
Hajiya sadiya ta gaya masa lalurar JANNAT inda yace babu damuwa zai rubuta cikin Form sannan ya sanarwa malamai tunda tanajin kuma tana gani zata iya rubutawa su karatu bazai zama mata matsala ba sai day wadda ba'a rasa ba''gdya tayi masa sannan ta biya gaba ɗaya kudin da ake buƙata
Daganan ta maida su gida sannan ta wuce wajen ayki
''to haka rayuwa taci gaba inda bayan wata 3 JANNAT ta gama sabawa dasu Hajiya sadiya da ƴaƴanta kai kowa yana jin dadin zama d ita rashin maganar tane kawai yake ci masu tuwo a ƙwarya basajin dadi, HUDAY ne yace to anty akai ta mana asibiti a duba ta ,anty tayi murmushi tace HUDAY ban fita son shiga hurumin Ubangiji ba kasan dalili na na faɗar haka? girgiza kai yayi alamar a'a ,tace da JANNAT bayan an haife ta ta samu wannan lalurar da ko ina zankaita na sama mata magani domin kuwa nafison naga tana magana fiye da kowa a duniya bayan mahaifiyar ta to amma haka aka haife ta ,ta iya yuwuwa haka ita kuma Allah yake don ganinta SHIYASA ya halittota haka kaga kuwa nema mata maganin zai zama kamar shiga hurumin Ubangiji ne, girgiza kai HUDAY yayi alamar gamsuwa
''to kullum Hajiya sadiya suna waya da innar JANNAT kuma komai lafiya ta cigaba da sana'o'in ta Kamar yadda take yi da ,sai day Abdullahi babu ruwansa da ita haka ameena ,dama akan JANNAT ne su shamsu suke dauke haushin uwar ta to kuma batanan shiyasa kowa yake harkarsa,amma a hakan ma kamar ameena zata jefata wuta take ji.....
Yau ma kamar kullum suna waya da Hajiya sadiya innar JANNAT tace antyn JANNAT Hajiya sadiya tace na'am,uhmmm uhmm dama kuma su tayi shiru , murmushi Hajiya sadiya tayi sannan tace ina jinki,
Uhmmm dama cikin yana nan bai fa zube ba,wani irin daɗi ne ya kama Hajiya sadiya da farin ciki ta ringa nanata Masha Allah Allah buwayi gagara misali , Allah yayi sai wannan ɗa ya sahaƙi iskar duniya kai Masha Allah Allah ya raya shi ya kawo shi lafiya,da ameen innar JANNAT ta amsa sannan suka ci gaba da hira ,washe gari kuwa Hajiya sadiya da kanta da Ruth da driver suka je har kaltanga suka kaiwa innar JANNAT kayan masarufi iri iri wadda masu ciki suke bukata da kuma kayan sawa dana abinci,har da kuka saida innar JANNAT tayi tsabar daɗi , sannan Hajiya sadiya ta roƙe ta dan Allah karki bari ameena tasan da cikinnan duk yadda za'a yi nasan zai kara watanni amma ki kula sosai sannan nakƙuda na tashi ki kira Hafsah a waya sai ta gayawa inna harira sai suzo kinga ameena ma bata sani ba...
Karɓar wayar tayi ta sa mata number hafsah ta ɓata tace number ukuce a ciki daga tawa sai ta HUDAY dana sai ta Hafsah dan Allah innar JANNAT ki kula da to ta amsa
Kai tsaye gidan mai gari ta wuce a tsaitsaye suka gaisa sannan suka kamo hanyar dawowa
HUDAY sun fara jarabawar fita daga secondry skull inda faɗimatu take shirin shiga babbar sakandare,sai aishatu da take aji ukku sai Hajara dake aji daya a karamar sakandare sai su ALJANNATU dake firamare 5 kowa yana karatunsa cikin kwanciyar hankali ,suna islamiyya amma JANNAT ba'a ƙara mata hadda ta bayar sai day akaranta mata ta haddace sabida ba halin bayarwa idan anƙara mata tazo gobe akace ta iya idan ta iya a kara wani idan bata iyaba sai ta koya,,,,
''haka rayuwa take ta gudu inda su HUDAY da anwar ɗan GIDAN Hajiya saliha suka yi jarabawar gama sakandare , Sa'anni ne su wajen tare suka haifesu tun suna ƙanana suke matuƙar don junansu , Hajiya Turai Allah bai bata da wuri ba danta na fari julaibib sa'an faɗimatu ne yanzu yake 16 sukuma suke 18 amma duk da haka komai tare suke inda basa ware shi a matsayin sun fushi.....
Haka rayuwa keta juyawa inda kwanaki suke juyawa su dawo sati ,sati ya juya ya koma watanni,a ciki. Wadannan watanni ne kuwa cikin innar JANNAT ya fito sosai domin kuwa yana wata na goma ne yanzu haka da sabida matsalan da aka samu ne yasa ya ƙara watannin
''to yau ne kuma da misalin 9 na dare baƙi da ya tashi wa innar JANNAT dama wayarta na kusa dan haka ta lalubota jini ne yake ta zubo mata kaɗan kaɗan abin ya fara bata tsoro Domin kuwa ance zubar jini yayin naƙuda babban illa ne ga mai haihuwa
''harta fara galabaita ta ɗau waya ta danna ƙira, HUDAY na zaune shida anwar da julaibib a gidan Hajiya saliha sai ga ƙura waya ,sabuwar nanba daya gani yasa yaƙi dauka ,ƙara kira akayi dan tsaki yaja sannan ya dau wayar domin bai ma san da wannan number ta mom dinshi ba dayake bata taɓa kiranshi dashi ba kafin yayi magana ta katse aka sake ƙira daga wa yayi ,yayi shiru magana yaji ƙasa_ƙasa sai da ya kasa kunne sannan yaji tana faɗin antyn JANNAT ce ko Hafsah zan mutu dan Allah ku taimake Ni ba kowa kusa dani
Da sauri HUDAY ya katse layin jikin shi na tsuma domin ya gane mai magana innar JANNAT ce sai yanxu ya tina anty ta gaya masa ta bata waya sabida idan haihuwa ya tashi mata,,,,
Number anty ya ƙira ,bugu 1 ta dauka jikinshi na ɓari yake cewa anty anty , na'am cewar Hajiya sadiya domin ta fara Bacci inajinka ,am anty dama wata number aka Kirani da ita to inaga innar JANNAT ce way a taimake ta zata mutu ba kowa.....
Kafin ya ƙarisa Hajiya sadiya ta kashe wayar domin kuwa tana ta lissafin cikin yau wata goma da kwana goma kenan kuma ta fahimci tazo kiran tane ko Hafsah ta kira HUDAY''da sauri ta ƙira Hafsah (yar mai gari)tana dagawa tace Hafsah kuke gidan su JANNAT innarta ba lafiya naƙuda take ku tafi da inna harirah dan Allah kuyi sauri nima zuwa da safe ina tafe ,kinga zan turo mota ynxu ku wuce asibiti kar a ɓata lokaci dan Allah ku kula kinji Hafsah?cikin ruɗewa Hafsah tace INSHA ALLAH Hajiya bari muje mugani...''hafsah ta sanar wa inna harira (matar mai gari) a take suka wuce gida su JANNAT kai tsaye dakin ta suka wuce ba kowa a tsakar gida ''samunta suka yi yashe tana ta nishi gaciki a sama yayi tsini sai haɗa gumi take nan inna harira ta fara taimaka mata tsawon minti talatin babu haihuwa suna a haka sai ga ƙaran waya Hafsah na ɗagawa Hajiya sadiya tace ku kamo ta ku fito da ita ga mota a ƙofar gidan sai ku wuce asibiti ko ta haihu ne?cikin ruɗu Hafsah ta amsa da a'a ''nan suka kama innar JANNAT suka fito da ita police mata 2 ne sai day 1 da personal dress days da uniform sai driver dake tuƙa motar sata suka yi a ciki sannan suka shiga dayday lokacin ameena ta fito jin motsi tsakar gida kawai sai taga an cusa innar JANNAT cikin mota an tashi jeep din da gudu sun yi hanyar barin gari(ga wadda ta karanta LITTAFIN tun farko na gaya maku gidan su JANNAT shine a farkon gari)budar bakinta sai cewa tayi Allah yasa sace tsinanniyar nan aka yi har abada kar a ganta 🙄niday ban tsaya jin ta ameena ba babu motar da gudu
Kai tsaye asibitin kashere suka wuce ,suna zuwa kan ɗa ya fara leƙowa nan likitoci suka rufu a kanta (inda Ruth take gayawa Hajiya sadiya meke faruwa ta waya) Ruth yar kashere ne to kuma tazo gida weekend kasancewar ranan Saturday ne kawai sai Hajiya sadiya ta ƙirata tace taje police station ta samu wanda take duty da kuma driver suje gidan da suka je ranan shine Ruth din suka dauko ta''
Sai ƙarfe 1 sannan Allah ya sauki innar JANNAT lafiya inda ta samu ƙatuwar yarta mace ''farinciki baya misaltuwa wajen Hajiya sadiya da su inna harirah sai lokacin Hajiya sadiya ta rintsa ay kuwa asuba nayi ta tashi Kasancewar abu baya gari da wuri ta shirya tasa su faɗimatu da su JANNAT shirya wa tace zata musu bazata kasancewar Sunday ce ba makaranta, nafeesat kuma taje gida zata kwana, flaks da warmers a cike da lafiyayyun break fast haka suka dau hanya
Suday su faɗimatu suna don ganin wannan surprise din domin su ga ana ta shiga ƙauye dasu saida suka ga sun iso cikin gari an nufi asibiti suka fara harsashi wani abu basu ce komai ba suka yi shiru, saida aka faka cikin asibitin sannan suka fito yar sanda ɗaya ce kawai suka tafi da ita sai police 1 mai tuƙa su ,,,a can suka samu mai gari
''bakin Hajiya sadiya ya kasa ruhuwa sai murmushi take sun samu har akai ta gado ma nan fa aka ringa matsa wa kowa sai ƙare wa wannan mata da yaranta kallo ake , suna zuwa Hajiya sadiya ta rungume innar JANNAT tana wa Allah gdya bayan sun gaisa da mai garine kuma ya miƙo wa Hajiya sadiya yarinya a towel duk na siyayyan da Hajiya sadiya tayi masu ne na haihuwa ,mai gari ya miƙo mata yar sannan yace ansamu yata SADIYA yana murmushi...... Wani hawayen daɗi ne ya zubo wa Hajiya sadiya ta rungume yarinyar a ƙirjinta tanajin wani daɗi na ratsa ta lallai haɗuwar su da wannan mutanen alkairi ne saida ta gama ganin yar sannan ta bawa su JANNAT ALJANNATU ce ta fara karɓar sakamakonsa mai don yara itakam JANNAT ta tafi wajen innar ta innarta nata shafa fuskar ta tana murmushi tana sake yiwa Allah gdya daya kare mata yarta ba dabara ta ba ba wayon taba
Hajiya sadiya ta ƙura JANNAT ta ɗaura mata yar a hannun ta tace ƙanwarki........
To haka day suka wuni a asibiti aka sallame su duka suka ɗunguma suka yi kaltanga''ameena sai ganinsu kawai tayi gaba ɗaya inda basu zo da JANNAT gidan ba aka kaita gidan mai gari''nan ameena ta ci mamaki kamar ya kashe ta way Hindatu ta haihu to yaushe tayi cikin kuma ma su bata ganshi ba ya akayi haka lallai tayi sake ko shine taji ana cewa tayi ɓarinsa ashe bai ɓare ba,😭aukuwa wlh da tasan dashi da ta daɗe da kwarara shi a rariya kai taji baƙin ciki kam''abu daya ne zai hana ta tada balbalin Bala'i a gidannan shine Ruth da ta gani fuskar ta babu alamar rahama kuma bata manta dukan da tasha a hannunta ba har bakinta yayi dogo🤣🤣
RANAN SUNA.........
*_GAYYATA GAYYATA GAYYATA_*
_**HAJIYA SADIYA TANA GAYYATAR FANS NA JANNAT WAJEN TARON SUNAN INNAR JANNAT WADDA AKA SAKA MATA MAI SUNA WADDA ZA'A YI
A RANAR ASABAR IN ALLAH YA YARDA A KALTANGA GIDANSU JANNAT_**😉 _ALLAH YA BADA IKON HALARTA_
To FANS ga wacce take son ankon suna sai ta min magana domin Hajiya sadiya tace a tabawa kowa kyauta albarkacin mai suna
Sai na jiki😜
Kar ku gaji yanxu ne za'a shiga asalin labarin domin kuwa JANNAT bata fara ganin rayuwa ba tukun wannan soman taɓine kudai ku biyoni masoyan asali son so fisabillillah
_INA ROKON KU DA KUSANI CIKIN ADDU'O'INKU INA DA BUƘATU ALLAH YA BIYA MANI_
❤️Mrs. Abdull❤️
Mallakar
❤️Mrs. Abdull❤️
More comments more typing
Yawan sharhi yawan rubutu
Mu haɗu next page don jin yadda za'a kaya kardai ku ƙagu domin ba'a ma fara labarin ba tukun kudai masoyan asali ku biyo NI kawai domin sharhi, shawara,ko yabo👉07059305867
❤️️Mrs. Abdull❤
