ADS HERE
Posts

BAZAWARA CE PAGE 1 to 5


 *🔥BAZAWARA CE🔥*



BY


*SUMMY M NA'IGE*

  (Ummu Ja'afar)



          *SADAUKARWA*

    *LEEMAT PINKY💞*




_Wannan labarin na kuɗi ne, ga mai ɓuƙatar karatun wannan labari zai iya tura katin waya na 200 ta wannan Number, 07062118047. Sumayya Almustapha.Accont:5154576019.Bank:FCMB. niger 250F_





      🆓 *Page 1*





Da gudu na shigo gidan mu, tun a soron gida na ke ƙwalawa Amma kira amma bata ƙarɓa ba, ɗakin mu na shiga ko sallama babu na faɗa jikin Amma, ajiyar zuciya na sauke kana na dube Amma  da kyau nace,


" Amma! Amma! Amma!".


Sai da ta girgiza kai kana tace,


" Sajida lifiya? waya taɓamin ke haka?".


" Ni ba wanda ya taɓani kawai na zo ne na shaida miki kije kiyiwa Baba magana wallahi aure nake so, yau watana biyar da ciki idda fa, amma ko an zo neman aure na sai Baba yace ba yanzu ba, to ba yanzu ba sai yaushe? ni fa bazawara nike ba budurwa ba,  dan haka bari kiji Amma, tabbas bazan iya zama yadda su aunty suka zauna gida  shakara da shekaru har tsofa ya fara taso musu babu miji kuma babu ɗa , amma in har Baba ya ce bazan yi aure ba Amma, to kisa ni! wallahi zan koma bazawara ta ai nahi kuma zanyi zawarci mai lasi-si!".


Ta na gama faɗar haka ta tashi daga jikin Amma da take kwance.


Hannu Amma tasa ta na lalubar Sajida amma bata jita kusa da ita ba, a hankali Amma ta buɗa baki tace,


" Sajida ki ƙara haƙuri da halin mahaifinku.....tun ba rufe baki ba taji kamar ana ihu tsakar gida, da sauri Amma tace,


"Sajida wa Baban ki ke duka tsakar gida? dubamin kiyi sauri ki fitar dani tun bai zo ya dake ni ba, wallahi yau ban da lafiya bazan iya ɗaukar dukan shi ba".

Ta faɗi haka jikinta na karkarwa.


" Kai tsaye Sajida tace,

" Mama Amarya ce ya ke duka, kuma wallahi bazam fitar da ke ba sai dai yazo ya da ke ki, amma ki sani!  yana dukan ki sai nasa zawarawa na sun ci ubansa".


Amma bata tsaya jin ƙarshin abinda Sajida ke faɗa ba ta laluba sandar ta tariƙa takawa a hankali har ta fita waje.


Tsaki Sajida tayi itama tamarawa Amma baya.


Koda na fita ƴan wahala duk sun fito waje sunyi layi ƙofar ɗakinsa, jikinsu sai karkarwa yake.


 Dukan ta yake yana faɗar,

" Ni zan faɗa kina faɗa, wallahi ba'ayi wata ƴa mace ba wadda zan faɗa ta faɗa ba, kafin na sanki har na aureki nasan irinki dubu, dan haka wannan ya zama shine na farko kuma shine ƙarshe".


Haƙuri ta riƙa bashi ta na kuka , sai da ya yi mata jagaf sannan ya kyleta .


Ko kallonsu Amma bai yi ba ya shega ɗakin sa kamar ɗan ƙaramin tawol ɗin da yake ɗaure dashi ya faɗi.


Yana shiga ɗakinsa na matso kusa da Amma nace,.

Amma Baba ya shiga ɗaki kije ki sanar dashi aure nake so wallahi, idan bakuyi min aure ba wallahi wallahi duk abin da naga dama shi zanyi".


Amma bata ce da ita komai ba ta ɗau sandar ta ta koma ɗakin ta.


Shigarta ke da wuya ya fito riƙi da kwarya wadda ke ɗauke da shinkafar towu.


" Kubura! Kubura! Kubura!.


Haka yariƙa faɗa da karfi, Kubura ita ce amarya a halin yanzu kuma itace wadda ya gama duka yanzu.


Jikinta na rawa ta isa gareshi ta durƙusa ciki da ladabi tace,


'' Gani Malam".


Ƙwaryar da ke hannunsa ya bata yace,


" Kiyi sauri ki kammala girki dan yau kinsan kece da baraya!".


Batare datayi masa musu ba tace,


" Tau Malam yanzu zan fara".


Jiki na rawa ta shiga kicing dan ta ɗaura sanwa, tukunya ta ɗauko zata ɗaura kan wuta a dai-dai lokacin na shigo, tukunyar na bi da kallo, saboda iya gani na ban taɓa ganin irin wannan tukunyar ta gidanmu ba, ita kanta wadda zata ɗaura tukunyar na bi da kallo, dan tas za'a saka irinta biyu a cikin tukunyar a dafe.


Kubura yarinya ce wadda bazata wuce shekara ashirin ba, yarinya ce kyakyawa son kowa ƙin wanda ya rasa.


Dubanta na sakiyi naga wace kaddarace ta kawo ta wannan gidan? oho, hawayen da ke zuba a idonta ta goge kana taci gaba da ɗaura sanwar.


Tsaki nayi kana nabar wajan, kai tsaye ɗakin zawarawa part 2 na nufa, da yake gidan da muke haya gida ne mai ɗaki takwas, huɗu na matan gida, uku kuwa namu ne zawarawa, ɗaya tsofafin zawarawa, ɗaya ko shine na tsaka, ɗaya kuwa shine namu sababin zawarawa, ɗaya ko na Babamu ne, sai tsoron gida inda ƙanninmu maza ke bacci.....




Taku har kullum




*SUMMY M NA'IGE✍️*

*🔥🔥BAZAWARA CE🔥🔥*





         *UMMU JA'AFAR✍️*



             *SADAUKARWA:*

     *💞LEEMAT PINKY💞*





_Wannan labarin na kuɗi ne, ga mai ɓuƙatar karatun wannan labari zai iya tura katin waya na 200 ta wannan Number, 07062118047. Sumayya Almustapha.Accont:5154576019.Bank:FCMB.nigar 250F_





 *SAFI NA 2*




Da sallama na shiga ɗakin, ƙarɓawa suka yi suna zaune kan gunton keso wanda zance shine makwanci kowace bazawara a gidanmu.


Fira suke hankali kwance, amma kallo ɗaya zakayi ma ko wace ka gane yunwar cikinta ta isheta, bare a zo ga zanci gyaran jiki, kuma wallahi duk ƴan gidamu kyawawa ne na ƙarshe.


Kallonsu nayi da kyau kana na ƙaraso kusa da su na samu waje na zauna haɗi da ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya sannan nace,


" Ƴan uwana, ko nace Yayu na zawarawa".

Nayi maganar tare da fitar da ido.


Basu karɓa ba sai dai ko wace ta ɗa go ido ta kalle ni ɗauke da mamaki a fuskarsu.


Murmishi nayi irin na zawarawa maso lasi-si kana tace,


" Dama zuwa nayi wajanku damon muyi wata ƴar magana wadda nake ganin zata anfane mu gaba ɗaya, kuma dan Allah kuyi duba mai kyau akan maganata dan Allah!".


" Ajiyar zuciya suka sauke kana suka ce muna jinki ƴar ƙanwarmu" .


Zama na gyara kana na dubesu nace,


" Mi zai hana ku zo mu fara sana'a, dan gaskiya na ga duk muna cikin neman taimako, ga zaman zawarci, kuma ga yunwa, uwa uba kuma gashi ko kafin ka riƙa nira biyar sai anfi wata biyu, kuma ba fita ku ke ba bare ku samu zawarawa da samari su baku, to shine nace ku futo mu fara sana'a muma mu nemi na kan mu har lokacin da Baba ya yarda kuyi aure".


" Atare suka ce kefa baza kijirashi ba?".


Murmushi nayi na gyafin baki kana tace,


" Kafin ya bani damar haka na mutu ko na tsofa na koma irin su Auntys zawarawa, shine nake so na fara sana'a mai haɗi da zawarci, wallah-wallahi na riga da na fito duk Baba yace ba zai min aure ba sai na sashi ya yi kukan safi da dare, ni ba dole sai na haɗa da sana'a zanyi zawarci  ba, a'a kune nake jiyema, gwara ku haɗa da sana'a idan kina so kiyi zawarcinki kiyi abinki hankali kwance batare da wani ko Baba sun samu ku ido ba, amma gaskiya zama haka babu daɗi, musamman in dare ya yi na rega naga yadda Baba ke holewa da matanshi".


A jiyar zuciya suka sauke a tare saboda an tuno musu abinda ke ci  ci musu towo a ƙwarya.


" To ke Sajida muda ba muda ko biyar ta ya ya zamu fara sana'a batare da mun samu kuɗin ba?".


Hafsat ta faɗi haka wadda ita da Sajida basu da wata tazara tsakanin su.


" Inda akan ƙuɗi ne babu damuwa, saboda yanzu haka akwai wani bazawari na da mukayi zai zo ya bani kuɗin bikin ƙawata to shine idan an kawo zan rarraba muku kowace ta yi jari koda kowa na sayar da sabolo ne, saboda a wannan tafiya ba'a sun bazawara mai aji ta kasance babu sana'a saboda kariya ce ga duk wata bazawara ba mu kaɗai ba!".


Godiya sukayi min saboda zaman gida ya zo ƙarshe, gashi ba wani jin daɗi bare so da ko wace ta san daɗin aure, kowa dai na faɗar albarkar  bakinta ta gaji da zama gidannan gida kamar gidan yari, gani suke ko ƴan gidan yari sun fiso ƴanci saboda so za su ci su ƙoshi, amma su fa? kuma wani lokaci ƴan gidan yari za'a fitar da su su ga gari amma sufa, da ga shekara sai shekara ko idan an yi mutuwa.


Kuma babban abin da ke ɗaure musu kai ace duk wadda tayi aure cikin su ba wadda ke da ɗa ko ciki, tabbas ko ka fito da ciki mutum baya sati da fitowa cikin zai zube.

            *******

Kubura na kammala aiki ta zubawa kowa nashi abinda ya samu sannan ta gyara gida kana tashiga ɗakin ta, da yake lokacin an fara kiran sallah magarb.


Wanka tayi kana tasa kananun kaya wanɗan da tasan ya na so, kana ta feshi jiki da turare sannan ta fito ta nufi ɗakin Babamu.

Har ta kusa ƙarasawo cikin ɗakin sai gashi ya fito riƙi da tabarma a hannunsa.


Cikin da ladabi ta zo ta karɓa tabarmar da ke hannunsa.


Tsoron gida ta kai ta shimfiɗa masa, bayan ta gama ta kai masa ruwa ban ɗaki ya yi wanka yana fitowa bai tsaya ko ina ba sai tsoron gida inda ta shimfiɗa masa tabarma, zama ya yi bai jima da zama ba sai gata ta zo riƙi da man shafawa a hannunta, zama tayi kusa da shi ta fara shafa masa mai sai lumsar ido ya ke.


Bayan ta kammala ta dawo kusa dashi ta zauna ta ɗauko abinci ta fara bashi har sai da ya ƙoshi, bayan ya yi gyatsa ne ya kwanta tare da janye ƙaramin tawol ɗin da ke jikinshi ya rage daga shi sai gajerin wando, tana gani haka a hankali ta ƙaraso gareshi ta ɗauko hannayenta ta ɗaura saman jikin shi, a hankali ta fara yi masa tausa, sosai ya ke jin daɗin abinda take masa har bai san lokacin da ya kai hannunshi ya fara zare mata kayan da ke jikinta ba, har sai da ya kai ba abinda ya rage na jikinta sai pant da bireziya.


Haka halin Babamu yake shiyasa da an idar da sallar isha'i ba mai sake fita gidan kuma ba mai saki shigowa saboda kada kayi mugun gani saboda haka ke kasancewa a girkin kowa ce daga cikinsu.. ......





*Dan Allah kutayani posting🙏*






*SUMMY M NA'IGE✍️*

*🔥🔥BAZAWARA CE🔥🔥*



         By


*UMMU JA'AFAR✍️*



         *SADAUKARWA*

*LEEMAT PINKY💞*





_Wannan labarin na kuɗi ne, ga mai ɓuƙatar karatun wannan labari zai iya tura katin waya na 200 ta wannan Number, 07062118047. Sumayya Almustapha.Accont:5154576019.Bank:FCMB.nigar 250F_





*SHAFI NA UKU*



Suna cikin haka sai na leƙo kai na na ga shin ko sunyi bacci kasancewar na daina jin mutsin su, abinda na gani ne nayi sauri na rufe idona ban shirya ba.


Ƙwafa nayi kana na ce,


" Shege Baba yanzu gashi sai jin daɗin aure  yake  amma mu gashi ya barmu zaune a gidan shi , in ya so mu mutu ! wallahi baza mu yarda ba!".

Tsaki nayi kana na ɗauko ƙafa a hankali dan wallahi ko zai dawo hayacin shi bai isa ya hana min  fita ba, haka na fara tafiya irin ta ɓarayi batare da nayi wani dogon mutsi ba bare yasa  ɗayan su ya san an fita.


Ko da na fita ba kowa a ƙofar gida, da hanzari na kama hanyar da zata kai ni gidan ƙawata itama bazawara ce, amma ita gidan kanta gareta dan ita zawarce ta ke mai tsaf ta, ba irin namu na wahala ba, da ya ke shi bazawarin nawa a can mukayi da shi zamu hadu.


Tun ban ƙarasa gidan ba na hango motarshi ƙofar gidan, gyara tafiya ta nayi da ga ta sauri zuwa ta zawarawa waɗan da suka san kan su, a ta ki na gyara ɗaurin kallabi na, ban duba madubi ba amma tabbas na san nayi kyau. a hankali na ɗau hannuna na fara ƙwanƙwasa glass ɗin motar.


Zaune ya ke yana dubin ta inda zan fito sai ya ji ana buga glass ɗin motar, a hankali ya mai da dubanshi zuwa ga inda ake buga ƙofar, ido huɗu mukayi dashi , lokaci ɗaya nayi masa wani kallo wanda shi kanshi ya kasa gane ma'anarsa,  cikin a zama ya washe haƙuran shi tare da sauri ya buɗe min ƙofar motar haɗi da faɗin,


" Bismillah hasken idaniya ta".


Murmushi nayi masa wanda sanadin haka yasa kumatu na suka lotsa. 


A hankali na buɗa baki nace,


" Kallon fa?".


Murmushi ya yi min kana yace,


" Wallah Baby sai ƙara kyau ki ke, wai miye sirrin?".


Ya faɗi haka shima a ɗan shagwaɓe.


Murmushi tayi saboda irin yadda ya yi maganar ta sani dariya kana nace,


" Ban da sharri, kai dai ka faɗi gaskiya, ko dai ka ga na ƙara muni ne?".

Na faɗi haka tare da tauna cingum ɗin da ke cikin baki na.


 Mun jima muna fira daga bisani nayi masa salma saboda na ga lokaci ya tafi ban kula ba saboda ni kai na na shiga shauƙin soyayya, saboda a rayuwata ina girmama soyayya, wallah shiyasa wani lokaci nake mamakin yadda mijina ya sake ni.


Ƙuɗin da zan saye kayan bikin ƙawata wanɗa da na ce masa su ya ɗauko ya bani, ban wani tsaya ƙirgawa ba nayi gaba cikin sauri haɗi da ɗaga masa hannu, alamar bye.


Sai da ya  daina ganina sannan ya ta da motarshi ya bar wajan.


    Yadda na barsu haka na dawo na same su, sai  dai yanzu bacci suke rungumi da juna, kai tsaye na shige cikin gida haɗi da antayawa Babanmu harara.

Sai da na shiga cikin gida nayi tsaki nace ƙaton banza ko kunya baya ji, warin jikarka a ce ita ce matarka.

Kai tsaye ɗakin Ammata na shiga, zaune na sameta kan sallaya da alamu yanzu ta gama wuturi, saboda ita Amma sai idan zata kwanciya take yin wuturi saboda ita haka ne tsarin ta, ko ba komai ta na son ta kwanta tana da alwala.

Ba sallama haka na shiga ɗakin, wajan da kaya na suke na nufa, aikuwa Amma na jin mutsin mutum ya shigo ɗakin ta lalabu sandarta haɗi da faɗar,

" Waye ya shigo! waye ya shigo! waye ya shigo min ɗaki?".

Ganin tana son ta tara min mutanin gida ne yasa na ja tsaki kana nace,


" Amma nice fa".


" Sajida lafiya mike damunki wanda ya hanaki bacci har yanzu?".


Ta faɗi haka ahankalin ta a tashe.


Baki na turu gaba nace,


" Amma kwantar da hankalinki ba abinda ke damu na, dama bazawari na ne ya kawo min ziyara yau".


Haka na faɗa babu wata kunya ko tsoro a tare dani, dan wallahi yanzu yadda na ke ji ko gaban sarki ne zan iya faɗar haka bare wani Babanmu.


A jiyar zuciya Amma ta sauke mai nauyi kana ta ce,


" Sajida mi ke ke son ki zama dan Allah? dan Allah ki rufamin asiri wallahi ban iyawa da halin mahaifinki, dan na san idan ya tashi hukunci ba ke kaɗai ba har ni sai ya shafa, kinga yanzu ba isassar lafiya da ni ba ,  dan Allah ki rufamin asiri Sajida wallahi ke ɗai ce zan ji naji daɗi a raina, ban san kowa ba sai Mahaifinki kuma sai ke, kuma sai Allah ya kawo min  jarabawa ta rasa ido, dan Allah ki taimaki rayuwata karki jamin abin magana!".


Yanayin da tayi magana ne yasa taban tausayi sosai, ajiyar zuciya na sauke,  sai da na kalleta tsaf kana na ce,


" Amma kin san shawar da zan baki gobe ki je ki sanar da Babanmu ki ce na ce aure na ke so, idan ya ban dama sai na turu mishi wanda ke so na, idan ki ka yi min haka kin gama min komai wallahi!.


Ina kai ƙarshin zancin na fice da ga ɗakin batare da na tsaya jin mi zata ce ba.

Ina ji ta na kirana na shareta, kai tsaye ɗakin zawara part 2 na nufa saboda ina so na gama da su tun a daren yau kafin na nufi ɗakin zawara part 1 saboda na san su part 3 basu da wuyar nuna musu hanya, saboda duk mune yara.


Koda na shiga wasu daga cikin su sunyi bacci, zama nayi haɗi da ƙwanƙwasa musu ƙofa na ce su tashi ina son nayi komai cikin sirri, bayan sun tashi ne na ɗauko kuɗin na rabawa ko wacin su dubu biyar-biyar na ce ko wace ta fara da ko da sayar da ƴan kunne ne, saboda na san tabbas nan gaba ko wacin ku zata samu jari mai yawan gaske, zama haka babu daɗi babu miji kuma ba bu cin mai kyau, dan haka mu tashi mu nemi na kan mu.


Sosai sukayi mata godiya akan wannan namijin ƙoƙari da tayi ace ita ce ƙaramarsu amma ita ke nuna musu hanyar neman kari mutuncin su.


Bayan sun gama shirya duk yadda abu zai kasance ta sa ƙafa ta koma ɗakin su.


Ko da tashiga ɗakin su, wato ɗakin zawarawa part 3 duk sunyi bacci, tsayuwa tayi ta bi su da kallo wai duk zawarawa ne su, ita abin ya ɗaure mata kai, miyasa duk suka zama zawara?.


Tsaki tayi saboda bata da amsar wannan tambaya dan haka ta je wajan da ƴar ƙaramar katifarta take ta kwanta idonta sai hango mata Babansu yake shida amarya sa.


   Kiran sallah asuba ne ya tashi duk wanda ke cikin gidan namu wanda ke ko mawa kamar ana cin kasuwa saboda duk sun tashi sai layi ake na shiga ban haya.


Tsaki nayi haɗi da ƙara gara kwanciya ta saboda na san ko na tashi sai na bi layin shiga ban hanya gwara nayi kwanciya ta.






*Kutayani posting dan Allah🙏*






*SUMMY M NA'IGE✍️*

*🔥🔥BAZAWARA CE🔥🔥*





       By


*SUMMY M NA'IGE✍️*




 


     

         *SADAUKARWA*

*LEEMAT PINKY💞*





_Wannan labarin na kuɗi ne, ga mai ɓuƙatar karatun wannan labari zai iya tura katin waya na 200 ta wannan Number, 07062118047. Sumayya Almustapha.Accont:5154576019.Bank:FCMB.nager 250F_


*🆓page 4️⃣*





Sai da gari ya fara haske har an kammala da ma kunun safe sannan Amma taji bata ji mutsi na ba, dan haka ta kira ɗaya da ga cikin mu ta ce su je su ce ta na ne mana.


Ko da aka je tashe ni sai bacci na ke mai ciki da jin daɗi sai mafarki na ke wai gashi nan nayi sabon bazawari har ya ɗauke ni zamu je hotel, ina cikin haka sai naji an tashe ni.


Tsaki nayi lokacin da na farka na ganin cikin mugun gidanmu wanda a yanzu na tsana kamar mutuwa ta, harara na afkawa na Na'imat wada na gani tsaye kuma da alamu ita ce ta tashe ni. sanin halina da tayi ne yasa ta buɗa baki tace,


" Amma ce tace na zo na ta sheki tana nemanki".


Tsaki nayi batare da na ce da ita komai ba na tashi na bar ɗaki,  toilet na shiga na kama ruwa haɗi da ɗaura alwala sannan na fito, sai da na gabatar da sallah kana na isa ɗakin Amma.


Zaune na same ta tayi ta gumi kamar wata marainiya, wannan abun da Amma ke yana ɓata min rai saboda ina lura da ita kamar tunani ne ta ke, a hankali na ƙaraso gareta bata re da nayi sallama ba, saboda ni hali na ne ban cika sallama ba idan zan shiga ɗakin Amma ba, kuma abin nan na ɓatawa Amma rai sosai, tayi min magana har ta gaji ta dai na.


A hankali na buɗa baki na ce,


" Amma wai mi ke damunki, wallahi ba na son na same ki ki na wannan ta gumi, kuma idan na ce tunani ki ke ki ce min a'a!".


Sai da ta jawo ni jikinta haɗi da shafar kaina kana ta ce,


" Ba komai Sajida,  kamar ina tuna wani abu ne mai mahimmanci a gareni  amma ban san miye shi ba, kuma ki ce ina tunani  to wani   tunani zanyi ni da ba gani nake ba?".


" To naji, lafiya aka ce ki na nemana?".


" Lafiya lau, gani nayi kowa ya tashi amma ke baki tashi ba, kuma malam ma har shigowa ya yi yace min ina ki ke na ce kina ɗakin ku, wai miyasa ki ke son ki kai wannan lokaci ki na bacci? baki san yawan bacci asara ne ba Sajida? dan Allah ki dai na kinji ƴar albarka".


Murmushi na yi haɗi da ƙara narkewa a jikin Amma kana nace,


" Zan daina wata rana in sha Allah. yanzu mi zan miki ki ka aika kirana?".


Har Amma ta buɗa baki tayi magana sai ga Baban mu ya shigo ɗauke da ƙwariya a hannunshi, ko yau shin kafar towu ce a ciki, sai da ya aje ƙwayar ƙasa kana na gaishe shi can ƙasan maƙoshi, Amma na jin haka ta yi sauri ta janye ni daga jikinta ita ma ta ƙara gaishe shi, kuɗi ya bata yace,



" Ga kuɗin ce fane nan saboda yanzu fita zanyi, kuma wata kila na kai yamma ban dawo ba, shiya sa na baki dan kin san yau ke ce da bara ya".


Murmushi tayi haɗi da kai hannu biyu ta ƙarɓa kana tace,


" Mu gode Allah an fana".


Da ameen ya ƙarɓa kana ya fita.


Yana fita nima na fita kai tsaye ɗaki zawarawa part 2 na nufa...


Ko da na shiga yanzu suke shan kunun da aka kawo musu, da hanzari na ƙaraso kusa da su nace,


" Yayu na, kuyi sauri ku shirya ku fita ɗaya bayan ɗaya saboda yanzu Baba zai fita wani taro, wata ƙila ma taron maula zai je, dan wallahi Baban mu ya ƙware ta wannan fannin" .


" Ko ina ya ke zuwa shi ya sani mu dai yau ta ki sallah a wajan mu".

Cewar Hafsat kenan.


Bayan sunyi wanka sun shirya sannan ko wace tasa hijab har ƙasa sannan suka fara fita ɗaya bayan ɗaya.....


Gidan ƙawata Ruƙayya nace su je, sai su sauya hijab zuwa mayafi ita zata ƙarasa musu sauran gyara kana su tafi kasuwa, har sun ce dubiyar ba zai iya kai su kasuwa ba, sai na nuna musu cewa ita bazawara ko budurwa mai neman abokin hulɗa, tabbas ko nera ɗari gare ta zata iya tafiya kasuwa, saboda ba yauwan ƙunɗin da zai ka riƙe ne matsala ba, a'a samun abokin hulɗa.


Sai da suka gama fita ɗaya bayan ɗaya sannan nima na bi bayan su.


Koda na isa gidan ƙawata Ruƙy suna zaune ta kawo musu abinci mai rai da mutsi wanda iya sanina marabin da su ci irinshi tun ranar sallah, da yake Ruƙayya itama bazawara ce amma bata nemi komai ta rasa ba, dan wallahi idan ka ganta ko wata matar aure bazata nuna mata komai ba, sana'a take mai haɗi da zawarici, to hakan da take mafi yawan muta ne basu gane cewa ita zawara ce mai lasi-si.



Bayan sun kammala sai muka rabo gida uku, ɗaya tare zamuje saboda na nuna musu kan gari, ɗaya ko tare da ƙawata Ruƙy za su tafi, ɗaya ko ta re da wata ƙawar Ruky.


Bayan mun isa kasuwa na nuna musu wajan da ake sayar duk wani abin da mutum ke so, a gurguje muka yi sayya kana suka dawo gida dan lokacin har yamma ta yi kusa.


Kuma cikin ikon Allah duk a ka  kasamu abinda aka je nema.



   **********


Amma ta jima zaune tana jiran Sajida ta zo a samu yaro ya sayo musi kayan abinci, gajiya tayi da jiran ta dan haka ta kira ɗaya daga cikin yaran gidan tace a kira mata sajida a tunanin ta ko tana ɗankin su, ko da aka je aka sanar da ita bata ɗakin su dan haka ta cewa yarinyar ta tafiyar ta saboda bata so ta ce taje waje kaza ta dawo tace batanan dan ta san tunda bata cikin ɗakin su ta ba shakka sajida bata gidannan , jikinta ne ya yi sanyi kar malam ya dawo ya tarar da bata nan, ko kuma kar watarana ya gane ta na fita, aikuwa ta san ranar idan ya gane ita da Sajida mai ƙarɓar su hannu malam sai Allah.


 jiran Sajida ta ga bashi ne mafita ba, dan haka ta tashi ta ɗauko sandar ta ta fara takawa a hankali har ta isa kicin ɗin gidan, itace ta ɗauko ta fara sakawo a kan murhu, duk da tasan zaman iccin bai yi ba, amma tana tsoron ta kira wani ya taimaka mata a gane cewa Sajida ba ta gidan, a hankali ta ɗauko ashana ta kunna wutar, cikin ikon Allah wuta ta kama, hakanan da lalube ta ɗaura sanwa, bayan ta kammala ne ta fito ta dawo ɗaki zuwa anjima sai ta zuba shinkafa.


Bayan ta dawo ɗaki ta kwatanci lokaci kaɗan sai taje inda take tunanin shinkafar take, tana cikin lalube sai taji kamar ta ta ke wani bu ya fashe da ƙarfi! gabanta ne ya fara dukan uku uku, cikin a zama ta durƙusa ta fara laubin mi nine ta taka, aikuwa tana lalubuwa taji ta taka shinkafa tuwon Malaman.







*DAN ALLAH KUTAYA NI POSTING🙏*



*SUMMY M NA'IGE✍️*

*🔥🔥BAZAWARA CE🔥🔥*





       By


*SUMMY M NA'IGE✍️*




     

         *SADAUKARWA*

*LEEMAT PINKY💞*


  


_Wannan labarin na kuɗi ne, ga mai ɓuƙatar karatun wannan labari zai iya tura katin waya na 200 ta wannan Number, 07062118047. Sumayya Almustapha.Accont:5154576019.Bank:FCMB._





*🆓  Page 5️⃣*




Ta jima tana lalabin shinkafar da ta watse tsakar ɗaki , jikinta sai dukun uku-uku ya ke, sosai ta shiga ta shin hankali kasancewar haka da tayi, ta jima zaune sai ta tashi ta ke kuma ta zauna duk ta kasa dugun mutsi, a halin da ta ke ciki taimakon Allah ne kawai ta ke nema sai na Sajida.


Bayan sun gama shiga maƙota suna nuna musu kayan da suke sayarwa ko da akwai mai nema zai iya aikawa a sayo masa cikin gidan su, ɗaya bayan ɗaya suka shiga har suka shiga gidan gaba ki ɗaya, zune suka yi tsakar ɗakin su sai farin ciki suke, ba komai ya hafar musu da wannan farin cikin ba sai fitar da suka yi, saboda wasu daga cikin su basu taɓa zuwa kasuwa ba, Hafsat da Rumaisat da Rayya sune suka ce baza su tsaya ga sana'ar gida ba, saboda a ganin su bata saurin kawo musu kuɗi da abokan hulɗa.


Hafsat ce ta tashi saboda ta kai wa Amma saƙon da Sajida ta sayo mata tace su kawo ma Amma kafin ta zo, ko da ta isa ɗakin Amma halin da ta sameta ya ɗaga mata hankali, cikin sauri ta ƙaraso gareta tana faɗar,


" Amma waya yi miki wannan ɗanyin aiki!?".


Jiki ta a sanya ye dan zuwa yanzu har zazzaɓi ya ta so mata kana Amma  tace,


" Dan Allah yau baki san inda Sajida ta je ba?".


" Amma gata zuwa bark nayi sauri na kwashe miki kafin Baban mu ya dawo, dan nasan halinshi tsaf zai iya baki hukunci mugun banza!".


Cikin ƙanƙanin lokaci Hafsat ta kwashi shinkafar kana ta ɗan gyara sannan ta wanke ta zuba, bayan ta zuba ne ta shiga ɗaki ta gaya musu halin da Amma take ciki dan haka suka zo aka taya ta, suna cikin haka sai suka ji sallamar Malam, aikuwa da hanzari suka koma ɗaki saboda gudun kar su jawo ma Amma wata fitina, saboda duk zaman da suke yi gida Babansu bai yarda wata ƴarshi ta taimaki matar gida ko da da sharar gida ba ce.


Amma ya samu a tsakar gida tana shirin kwasar abinci, baki ya buɗe saboda abin ya bashi mamaki, wai sai yanzu za'a kwashi abinci, ga yunwa ya kwaso saboda taron da ya tafi ko ruwa ba'a bashi ba kuma ba wai don babu ba ne, a'a sai manya mutane ake ba, ga baƙin cikin bai samu ya keɓe da kowa ne babba ba bare ya samu abin kaiwa bakin shi.


Ya jima tsaye yana kallon ta, lokaci ɗaya wani ƙololon baƙin ciki ya rufe shi, cikin ɗaga murya yace,



" Ki na nufin sai yanzu zaki ɗaura sanwa!?".



Jikina karkarwa tace,


" Dan Allah Malam kayi haƙuri wallahi yau na makara ne".


Ta faɗi haka kamar tayi kuka.


Bai tsaya jin me zata faɗa ba kai tsaye ɗakinshi ya shiga, babu ɓata lokaci sai gashi riƙi da durina mai baki biyu sabowa ƙal, cikin azama ya ƙarasa wajan da take ya fara zuba mata ita.


Tun tana iya shuru kar mutanin gida su jita har ta buɗa baki tana dan Allah Malam kayi haƙuri na tuba ka yafemin bazan sake ba!".


Ko saurarin ta ba ya yi haka ya riƙa zuba mata bulala kamar Allah ya aikoshi, ƙarar da ta ke ne na neman taimako yasa mutanin gida duk suka fito suka yi cirko-cirko suna kallon abinda ke wakana kamar yadda suka saba idan yana dukan ɗaya, saboda idan baka fito ba to bashakka kai ma kana da naka hukunci.


Tun Amma na zaune har ta tashi tana neman taimako dan gani take yau kasheta zai yi, aikuwa ya na ganin haka ya sa hannu ya jawota, wurin ya jawota ne ya janye mata zanin da ke ɗauri a jikinta, aikuwa tana jin haka ta ke ta buga wata ƙara wadda tasa ba yaran gidan ba har matan gida suka fara kuka, duk da haka da ya mayar da ita bai daina dukanta ba har sai da ya ga ta daina mutsi......


         ¤¤¤¤¤¤¤¤


    Sajida bayan sun dawo kasuwa ne ƙawarta tace ta rakata wajan mai ɗinki ta karɓo ɗinki ta, ba don  ta so zuwa ba sai dan mutunci da ke tsakanin su da Ruƙayya, kuma ba dan komai ta ƙi zuwa ba saboda wallahi duk abinda ta ke ƙarfin hali ne, amma hankalinta na ga Amma, bayan sun dawo ƙarɓar ɗinki ne ta kama hanyar gida har da ɗan gudunta saboda gabanta sai famar dukun uku-uku ya ke ta rasa miye dalili.



Tana kawo wa gab da gidan su sai taga shima Baban su ya fice da alamu masallaci zai tafi, cikin hanzari ta shiga gidan ko sallama babu, abinda idonta suka gani ne ya yi matuƙar ɗaga mata hankali..



Amma ta gani kwance a ƙasa matan gida sai ruwa suke zuba mata suna mata fifita, wata ƙara na saka , da gudu na zo kan Amma ina jijjigarta ina kuka ina faɗar,


" Amma karki mutu ki barni rayuwata tana cikin haɗari!!!".


Kuka ta ke sosai wanda duk wanda ke wajan sai ya zubar da ƙwalla, mutsin da Amma ta farayi ne yasa nayi saurin na dai na kuka haɗi da kiran sunanta, a hankali ta ɗauko hannuta ta kai ga fuskata haɗi da yin murmushi mai nuna alamumi da dama, ƙoƙarin tashi tayi dan haka muka kama mata ta tashi, ruwa ta ce na bata tayi alwala, cikin hanzari na ɗauko na bata kana na dube Amma da matan gida nace,


" Amma miya sameki?".


Tun basuyi magana ba tace,


" Faɗuwa nayi, kuma komai ya faru laifinki ne, dan haka kafin nayi sallah je ki kwashi abinci ki kawai malam na shi kafin ya dawo masalaci".


Tana faɗar haka ta ci gaba da alwalarta , bayan ta kammala Sajida ta kai ta ɗaki haɗi da shinfiɗa mata sallaya, sannan ta zo ta kwashi abinci ta kai wa kowa nashi kana ta shiga ɗakin zawara part 2, tambayar su tayi me ya same  Amma, ba wani ɓata lokaci suka kwashi komai suka sanar da ita, hawaye ta goge haɗi da yin murmushin gyafen baki, bata re da ta cewa kowa komai ba ta tashi kai tsaye waja ta fita , maganin ciyon jiki ta sayo mata sannan ta dawo gida, kai tsaye ɗakin ta ta numafa, ko da taje zaune ta same ta kan sallaya tana azkar.


Ku sa da ita na je na zaune tausayin ta ya kama ni sosai, hawayen da suka zuba a idona na goge kana nace,


" Amma ya jikin?".


" Na ji sauki Sajida, Allah yasa kin kwashi abinci kin kaiwa kowa nashi har malama?".


Ta faɗi haka hankali tashe.


Tsaki nayi kana nace,


" Eh duk nayi har sharar tsakar gida nayi".


Ajiyar zuciya Amma ta sauke kana tace,


" Allah ya yi miki albarka ya nuna min ƙarshin wannan zaman na ku gida ke da ƴan uwanki".


Murmushi wanda yafi kuka ciyo na yi kana nace ,


" Amma ashe Babanmu ya da ke ki, shine kika cemin zamewa kikayi kika faɗi?".


" Ba na son zancin nan fa, mi ruwanki tsakani na da mahaifinki eh!".



" To kiyi haƙuri Amma bazan sake ba".



Yauwa ko kefa, wai nace yau ina kika tafi?".


Mu ɗan fita ne Amma , na rake ƙawata ƙarɓo ɗinki kuma na je kasuwa".


" Sajida dan Allah ki rufamin asiri ki daina fita, in har kina son ganin farin ciki na!".


" Ni ko nake son ganin farin cikin ki Amma, wai Amma na tambayeki?".


" Eh amma idan ba tambayar shirme bace ina ji".



" Wai Amma nace ke baki da dangi ne, dube duk su Hasat da su Na'imat ina jin suna cewa ƙanwar Mamarsu, amma ni ban da su, dan Allah Amma idan ki na da su ki gaya min, wannan shine gata na farko da zaki fara yimin a raruwa!".


Jikin Amma ne ya yi sanyi, lokaci ɗaya kuma wani ɗan tunani ya zo mata amma ta kasa tuna komai dan haka tayi murmushi sai tace,



Ina ji ajikina nima inda dangi, amma ban san su ba Sajida, a salima ni wannan gidan kawai na tsinci kai na".


" To Amma in kina da su Allah ya bayyanar muna da su".


Da Ameen Amma ta ƙarɓa, tashi nayi na ɗauko mata abinci da na zo dashi gidan Ruƙayya na bata taci kana na bata magani tashi na haɗa mata ruwan zafi tayi wanka sannan na shafa mata wani magani a baya wanda zai sa ta daina jin zafin bulalar kuma wannan shatin na bulala ya ɓata, abu ga farar mace sai kunga yadda abi ya fito ɓaro-ɓaro, ina shafa mata magani ina shafe kwalla kuma wallah-wallahi duk bala'in da za'ayi sai nasa shi kuka fiye da wanda muka yi a yau.......






*SUMMY M NA'IGE✍️*

Post a Comment

ADS HERE
ADS HERE