ADS HERE
Posts

BANI NA KASHE SHI BA PAGE 1 to complete


 *بسم الله الرحمن الرحيم*

 


        *😭BANI NA KASHE SHIBA*😭


           *Story and wrtten*

                       *By*


       *FATIMA UMAR KAS*

                 *_(MUMMYN MIHAL_ )*



*PAID BOOK*

 _(Littafin kud'i_) 



*LABARI MAI TAB'A ZUCIYA*_😔

ya k'unshi soyayya,tausayi, cin amana, hassada, munafirci _



*Dedicated to LEEMAHT pinky*💕💞💕



®🏝

 *ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻

[  ```Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.

Zafafa writers is a union to enlight women```]

*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*



      *Gyara da kanki*👌🏻


_Ki samu kankana ki markaɗa ki tace, ki zuba minannas da madara ki zuba zuma ki juya, insun haɗe jikinsu sai kisha, yana da kyau sosai_


 

 *_Z• W• F•🏝_*



*🆓page two*



Mutane ta hango dank'am a waje, sai hayaniya sukeyi, da sauri ta juya ta ziro hijab ta fito, duk yadda taso ganin meke faruwa kasawa tayi, dan an cika gurin sosai mutane sai dad'uwa sukeyi a gurin dan tini labari ya bazu anyi kisa a lungun.


    Da sauri ta juya tasami leda ta k'ulle gidan, sannan ta dawo gurin, so take taga meya faru, hakan ne ya sanya ta dinga kutsawa ta cikin mutane tana shiga wajen, harta fara hango mutum a zaune a k'asa.


    Daidai lokacin jami'an tsoro suka iso gurin, kai tsaye gurin suka shiga dan tini aka dare aka basu hanya ganin hukuma ne, a kanta suka tsaya dukkansu gami da zagayeta, d'aya daga cikin su ne ya d'auko Waya ya fara d'aukar hotuna, har lokacin bata motsaba daga gurin ba, d'ayan ne ya durk'usa yasaka kyalle dan karb'ar wuk'ar daga hannunta, saidai ta damk'e wuk'ar tak'i saki, duk yadda yaso amsa bata sakarmai ba.


    Zuciya ce ta ciwoshi ganin ta aikata laifi kuma tana shirin b'ata musu lokaci, hannu ya d'aga ya zabga mata wani gigitaccen mari, saukar marin ne ya sanya ta saurin dawowa hayyacinta, hannunta ta kallah, da sauri ta saki wuk'ar tana ja da baya ganin mutanen dake gabanta, sai kuma ta kalli gawar dake kwance a gabanta, 


    Sai lokacin kwakwalwarta ta tino mata abinda ya faru, jitai ance "ku kamata." kafin ta tantance abinda ake nufi taji an mik'ar da ita tsaye gami da sanya mata Abu a hannunta, 


    Tayar da ita tsayen da akayi ne ya sanya mama ganota, ido ta zaro ganin 'yarta ce akaiwa Wannan taron, so take taga me tayi, dan haka tai saurin isa gunsu ganin sun fito daga cikin gurin, 


    Gabanta ne ya yanke ya fad'i ganin jinin dake jikinta. "IKLEEMAH jinin mene ajikinki.? Yallab'ai ina zaku kaita me ta aikata.?" ta fad'a jiki na rawa, Kamar bazai bata amsa ba sai kuma ya daure yace, "Mai laifice, kisa tayi, baki ganiba.?" 


    Ya fad'a yana nuna mata Wanda aka shigar cikin motor Ambulance, kallonta ta maida kan mutumin sannan ta juyo da kallonta kan Leemaht, ita kuwa kai kawai take girgiza mata dan bakinta ya gaza furta komai, haka idonta k'amas yake Ko d'igon hawaye babu, dan zuciyarta a bushe take.


     Itama mama sandarewa tayi a tsaye jin abinda akace, saida taga an shigar da ita motar sannan ta dawo hayyacinta, da sauri ta isa bakin motar, tana fad'in. "Yallab'ai ku tsaya ku saurareni, dan Allah karku tafi da ita, ninasan ikleemah Ko dabba bazata iya kashewa ba balle mutum, ku tsaya ku binkita acikin mutanen gurin nan dan Allah." 


    "In munje can zamu tantance Ko tanada laifi Ko batada laifi, kai tayar da motar mu tafi", ya fad'a yana bawa Mai tuk'asu umarni, aikuwa tayar da motar yayi, da sauri mama tayi baya ganin zaija tana jiki, 


    Da azama tayi bayan motar inda aka shigar da Leemaht d'in dan ta shiga Itama, saidai kafin ta isa anja motar, aikuwa da sauri tabi bayansu, har tana hard'ewa, haka ta dinga bin motar gudu gudu sauri sauri, amman duk da haka saida suka fara b'acewa ganinta. 


     Azama ta K'ara dan so take tasan inda za a kai mata 'Yar tata, ita kanta batasan  inda take Jefa k'afarta ba dan hankalin ta a mugun tashe yake.


    Can ta hango sun tsaya, azama ta k'ara har ta isa gurin, gaba d'aya k'afafunta sun gaji, nan ta fahimci ashe division ne agurin, a lokacin har an shige da ita Ciki, Shikuwa asibiti wasu 'yan sanda suka nufa dashi, 


    Tana shiga ta hango leemaht d'in a cikin cell har an rufeta, juyawa tayi gurin Wanda ke rubutu a wata paper, tana shirin magana ya d'aga mata hannu, sannan yaci gaba da abinda yakeyi, durkushewa tayi agurin daman k'afafunta har wani rawa sukeyi saboda tafiyar da tasha, cikin kuka tahau fad'in.


     "Innalillahi wa'innah ilaihirrajiun, Wannan Wacce irin k'addara ce ke shirin fad'owa cikin rayuwarmu,? Muna cikin wata jarrabawar gashi ubangiji ya aiko mana da wata, ya ubangiji ka sauk'ak'a mana, ka fitar da Wannan baiwa taka daga iftila'in dake tinkarota, bamuda Kowa sai kai ubangiji, Muna da rauni kai mana agajinka ya Allah. " ta fad'a tana cigaba da kukan, 




_____________________________

Wata hamshak'iyar mata na hango sanye cikin kaya na Alfarma, zaune take a wani katafaren falo da yaji kayan more Rayuwa sai zuba ƙamshi yakeyi, tabbas ta had'u iya had'uwa, dan da ganinta kasan naira ta zauna a gunta, 


      Wayace a hannunta tana ta Kiran wata number amman a kashe, wurgi tayi da wayar kan kujerar tana dafe kanta da dukkan hannunta.


   Wata had'aɗd'iyar matashiyar matace ta shigo cikin falon Itama fuskarta cike da damuwa, a hankali ta k'araso Ciki, a k'asa ta zauna sannan tace.


     "MAMY barka da hutawa." d'agowa tayi ta kalleta, amsawa tayi sannan ta d'ora da fad'in, "ZULAIHAT Ko AMMAR ya sanar dake zai biya wani gurin inya dawo sallahr juma'a.?" 


    Girgiza kai tayi sannan tace, "Nima mamy abinda na shigo in tambayeki kenan, naga har yanzu bai dawoba, kuma yacemin inyi mai farfesun hanta in ya dawo zaici, gashi har magriba ta kusa amman shiru, wayoyinshi ma a kashe suke." ta k'arasa fad'a cike da da damuwa, 


    "A'ah! to ina yaron nan ya shiga ne.? nifa hankalina ya fara tashi, tin wajen hud'u nake kiran numbobinshi duka hud'un a kashe suke, kuma na kira security na tambayesu sunce shi kad'ai ya fita, ashe duk juma'a inzaije sallahr juma'a baya tafiya da Kowa shi kad'ai yake tafiya?bansan sanda ya fara wannan gangancinba," ta k'arasa fad'a hankali a tashe...........✍🏻





_Comment and share pls_

*😭BANI NA KASHE SHIBA*😭


           *Story and written*


                       *By*


       *FATIMA UMAR KAS*

                 *_(MUMMYN MIHAL_ )*



*PAID BOOK*

 _(Littafin kud'i_) 



*LABARI MAI TAB'A ZUCIYA*😔

_ya k'unshi soyayya, tausayi, cin amana, hassada, munafirci_



   *NA SADAUKAR DA LITTAFIN NAN GA SHUGABAR K'UNGIYARMU TA ZAFAFA WRITTERS, WATO AUNTY LEEMAHT, LEEMAHT PINKY,💞💕 HAZIK'A KUMA FASIHIYAR MARUBUCIYA, SHUGABA TA GARI, ALLAH YA TAYAKI RIK'O, YA BAKI ZURI'A TA GARI, YA BIYA MIKI DUKKAN BUK'ATUNKI DUNIYA DA LAHIRA, INAYINKI MY LEEMAHT  IRIN SOSAI D'IN NAN🥰😍😘*



®🏝

 *ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻

 

             

     *_Z• W• F•🏝_*



       *Gyara da kanki*👌🏻


_Ki sami sassaƙen ɓaure ki zuba kanunfari citta ki ɗaura a wuta ki dafasu, insun dahu sai ki sauke ki tace, sai ki maida ruwan kan wuta ki zuba zuma da mazar ƙwaila a ciki, ki maida kan wuta, in sun gama narkewa sun dahu kenan sai ki sauke, ki barshi yasha iska sai ki sha, wannan haɗin yana da kyau, ki gwada ƴar uwa._



*Bismillahir'rahmanir'rahim*



*🆓page one*


     Tafiya takeyi sannu a hankali cikin nutsuwa, duk da daman haka tafiyarta take, amman Yau silo d'in tafiyar da takeyi har ya zarce yadda take tafiyar koda yaushe.


    gaba d'aya Yau d'in jikinta a sanyaye yake, tin tashinta da safe zuciyarta ke yawan tsinkewa, haka da taje makarantar ma, komai a sanyaye take yi shi, tin safe suka tafi amman sai yanzu biyar saura aka tasosu kasancewar tahfeez ce a can suke wuni, 


    Karyo kwanar da zata sadata da layinsu take shirin yi, saidai da sauri tayi baya ganin motar da ta fafaro da uban gudu, Kamar zatabi ta kanta, fitt! ta wuce ta gabanta. k'irjinta ne ya buga da k'arfi dan ta tsorata sosai, da kallo tabi motar har ta harba kan titin bakin layin ta b'acewa ganinta, juyawa tayi dan shiga layin nasu har yanzu k'irjinta bugawa yakeyi.



   Tana shigowa Layin tai saurin ja da baya gami da dafe k'irji, idanunta duka ta zaro ganin abinda ke gabanta.


   Mutum ta gani kwance cikin jini baya motsi, ga wuk'a data gani an cakamai a cikinshi, tini jikinta ya d'au rawa, ita kanta batasan sanda ta isa gurin ba, sai ji tayi hannunta na k'ok'arin ciremai wuk'ar daga cikinshi, 


    K'ok'arin ciremai takeyi amman tak'i fita kasancewar an cakata can ciki, ganin tanayi a hankali bata ciriba shine ya sanya ta cirota da k'arfi. "Ahhhhhh!". taji ya furta, sai kuma jikinshi ya saki numfashinshi ya d'auke cak!.


     "Innalillahi wainna ilaihir rajiun, LEEMAHT me zan gani haka.?" wani saurayi ya fad'a yana d'ora hannu a kanshi. mutanen da suka fara dawowa sallahr juma'a ne sukaji sukaji hargagin saurayin, tini suka fara tururuwar shigowa cikin lungun dan ganewa idonsu meke faruwa?.


   Abunda suka gani ne ya sanya suka firgita, Masu d'aura hannu aka nayi, masu sallallami ma nayi, sai masu d'auka a Waya, ita kuwa mutuwar Zaune tayi ta kasa motsawa daga gurin, gaba d'aya ido ta zubawa wuk'ar hannunta ta kasa ajiyewa, 


      Can na hango wani mutum ya fito da waya yana kira, kan kace me lungun ya cika da jama'a, aikuwa Ko minti biyar ba ayiba jiniyar motar 'yan sanda ta karad'e gurin, 


   Jin jiniyar ne ya sanya MAMA dake firfita wuta a cikin gida tai saurin mik'ewa, gami da nufo hanyar waje,.... ✍🏻




 *D'AND'ANO DAGA LITTAFIN BANI NA KASHE SHIBA*

*SUBSCRIBE*

_DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV_


https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ


🏝️ *ZAFAFA WRITERS FORUM*✍🏻


        *_Z. A .W_*🏝️


*بسم الله الرحمن الرحيم*

 


        *😭BANI NA KASHE SHIBA*😭


           *Story and wrtten*

                      

                  *By*


       *FATIMA UMAR KAS*

                 *_(MUMMYN MIHAL_ )*


_Marubuciyar_👇🏼

*BAK'IN CIKIN KISHIYATA*

     *RAYUWAR MIHAL*

*ABINDA ALLAH YA NUFA*

    *SILAR ABAYA*

*'YA'YAN MIJINA NE*

     _AND NOW_

*BANI NA KASHE SHIBA*



*PAID BOOK*

 _(Littafin kud'i_) 



*LABARI MAI TAB'A ZUCIYA*😔

_ya k'unshi soyayya, tausayi, cin amana, hassada, munafirci_



*Dedicated to LEEMAHT pinky*💞


         

    *Gyara da kanki*


_Ki samu kankana ki ɓulata, sai kisa cokali ki caccakata sai ki zuba madara ki shanye. Hummmm! sai kin gwada😊_



🆓 *page Three*


    

    Itama damuwar tace ta ninka ta da, cikin tsananin tashin hankali tace. " Wai daman Mamy duk juma'a baya fita da excot shi kaɗai yake fita? To ai ni ban taɓa sanin hakan ba sai yanzu a bakinki."


   Wata nannauyar ajiyar zuciya Mamy ta sauke sannan tace. "Nima Zulaihat ban taɓa sanin hakan ba sai yanzu, wallahi gabana faɗuwa kawai yake tayi na rasa meke yimin daɗi, Ya ubangiji ka sanya muji Alkairi, kasa ɗana yana cikin ƙoshin lafiya, tabbas bazan iya jure wani abu ya samu tilon ɗana ba." ta ƙarasa faɗa idonta na kawo ruwa.


   Ita ma jitai zuciyarta ta karye ganin yanayin Mamy, jiki a sanyaye ta ƙarasa ta zauna a kan carfet  kusa da ƙafar ta tace. " Dan Allah mamy ki kwantar da Hankalinki insha Allah zamuji Alkairi, wata ƙil ya biya wani gurin ne, mu ɗan ƙara jira mu gani."


   Kai ta gyaɗa sannan ta kuma ɗaukar wayar tata, kiran nashi taci gaba dayi amman amsar ɗaƴace a kashe, number mai gidan ta shiga nema, taci sa'a tana kira ta shiga, tanajin An ɗaga tai saurin faɗin.


    "Alhaji dan Allah kayi azama kazo gida yanzu yanzu".

     "Me ya faru?." ya tambaya a kiɗime jin muryar tata kamar tana cikin damuwa.


    "Maganar bazai yiwu a waya ba kazo dai ɗin yanzu dan Allah." tana gama faɗa ta kashe wayar. Miƙewa yayi da sauri ya fara tattara takaddun kan teburin dake gabanshi ya juya ya fice. Kulle office ɗin yayi sannan ya nufi motarshi, yana shiga ya tasheta ya fice daga gurin.



     Yana isa katafaren  gidan yai horn, mai gadin ne ya wangalemai get ɗin, nan ya shiga ya samu guri yai parking, ko gama daidaita parking ɗin bai yiba ya kashe motar ya shige ciki.



     A tsaye ya tarar dasu sunyu cirko cirko, dan dukkan ma'aikatan gidan Mamy ta tara agurin tana tambayarsu, tana ganin shigowarshi tai saurin isa gurinshi tana faɗin.



     "Alhaji Ammar ne har yanzu bai dawo ba, ga kuma wayoyinshi duk basa shiga." cike da rashin fahimta yace. "Kamar ya baya nan ina yaje, Ai naga baya zuwa office duk friday hutu yakeyi."


    "Eh duk juma'a yake hutu maimakon lahadi da kowa keyi, Amman ya tafi sallahr Juma'a ne gashi kuma har magriba ta kusa bai dawoba, kuma tin ɗazu nake kiran wayoyinshi ɗuka ba wacce ta shiga."


   Cike da Damuwa shima yace. "A'ah to ina masu tsaron lafiyarshi da yake fita dasu, naga duk motocin suna nan inda suke a rufe."


  Hawayen idonta ne ya silalo nan tace. "Sunanan su ai, sunce shi kaɗai ya tafi masallacin wai duk juma'a baya bari su bishi zuwa masallaci, yanzu dai nasa su bi bayanshi duk masallatan da suka sani su dubo, suma kaji su shiru har yanzu basu dawo ba." ta ƙarasa faɗa muryarta na rawa dan kukan dake neman kufce mata. Shi kanshi hankalinshi ne ya soma tashi amman saboda kar ya kuma karya mata zuciya,sai ya daure yace.



     "Kinga HAJIYA JAMILA ki kwantar da hankalinki insha Allah zasu dawo tare, may be ko motar ce ta lalace musu a hanya, Ammar fa ba yaro bane duk inya yake shima hankalinshi yayo gida yanzu, kuma wayoyinshi wata ƙil ba caji ne shiyasa basa shiga."


   Girgiza kai tashiga yi sannan tace. "Ku ku kewa Ammar kallon babba, Amman ni har gobe kallon yaro ƙarami nake yimai, shi kaɗai fa na mallaka taya zan iya jure wani abu ya sameshi? Wallahi bakaji yadda ƙirjina yake min zafi ba, zuciyata kuma bugawa kawai takeyi."


   Cikin kwantar mata da Hankali yace. "Na faɗa miki zasu dawo tare, yanzu kije kiyi Alwala kiyi sallah kiyimai Addu'a,Amman dan Allah ki cire komai a ranki ki dunga hasasho Alkairi kinsan dai kinada Hawan jini." kai ta gyaɗa sannan ta juya ba musu ta shige ɗakinta.


     Itama Zulaihat jiki a sanyaye taja ƙafafunta ta doshi nata sashen har wani tangaɗi takeyi saboda jirin dake ɗiɓarta, tana isa ɗakin nata tai wani irin.......!, suma duk cewa yai suje suyi sallah, a hankali suka fara fita a falon har suka fice, shima fita yayi dan zuwa yai tashi sallahr amman shi kanshi zuciyarshi tsinkewa takeyi dauriya kawai yake tayi.



___________________________________


Ita kuwa tana zaune a cikin cell ɗin ta haɗa kai da gwiwa tayi zurfi cikin tinanin ƙaddarar dake kunno kai cikin Rayuwarta,


   Ƙarar buɗe ƙofar ne ya maido ta hankalinta,taji an buɗe ƙofa an shigo, amman bata ɗagoba har yanzu, wata tsawa da aka daka mata ce ta sanya tai saurin ɗagowa ba shiri.


     Wani baƙin mutum ta gani tsaye akanta fuskarshi babu Alamun fara'a aciki, sanye yake cikin kayan ƴan sanda, fuskarshi a murtuke, guri ya samu ya zauna ya zuba mata jajayen idanunshi sannan ya soma faɗin. 


   "Tambaya ɗaya zanyi miki, inason ki  faɗamin gaskiya hakan zai sa ki samu sauƙin Azabar da zamu gana miki a gurin nan, inason ki sanar dani waya sakaki ki kashe Ɗan gidan ALHAJI BILYAMIN NAIRA?."


   Kanta ta shiga girgizawa hawaye na silalo mata sannan tace. "Babu wanda ya sakani."


   "Kenan kece kikai niyyar kasheshi da kanki, to wanne laifi yayi miki har kika zaɓi rabashi da Rayuwarshi.?"


    Shiru tayi ta kasa magana,saukar wani Azababben mari taji a fuskarta take jinta ya ɗauke na wucin gadi, danshi taji a gefen bakinta, tana saka hannu ta dangwalo nan taga ashe jini ne dan marin har bakinta ya taɓa. Wannan karan Hawayen nata cak! Ya ɗauke.


    "Bazaki buɗe baki kiyi magana ba.?" ya kuma daka mata tsawa. "Wallahi BANI NA KASHE SHIBA, nima a haka n..."


    "Bazaki faɗi gaskiya ba kenan."? Ya katse mata maganar, juyawa yayi ya fara kiran wani daga waje, ba jimawa ya shigo.


   "Kirawo min su SA'ADATU ita da SAFIYYA." Amsawa yayi sannan ya juya ya fice.  Can jimawa sai gasu sun shigo. Ɗaya ya kalla daga cikinsu yace. "Kije inda muke ajiyar kayayyakin nan ki ɗauko min Akwatin nan."


  Rissinawa tayi sannan ta juya ta fice, dawowa tayi ɗauke da wani Akwati a hannunta ta ajiye, janyo Akwatin yayi gabanshi ya buɗeshi, wani ƙaton Almakashi ya ciro mai ɗan karan tsini, ajiyeshi yayi a gefe sannan ya maida kallonshi kansu yace.


    "Sa'adatu ɗauramin hannun damanta akan nan." da azama ta matso ta tsugunnan gabanta, ita kuwa batai Aune ba sai ji tayi an danƙam mata Hannu. Bata gama tantance me za a yi mata ba saida taji ya kuma cewa. "Safiyya  riƙemin ita, ke kuma Sa'adatu ki riƙe mata Hannun sosai."


    Nan kuwa suka rirriƙeta kamar wacce za'a yanka, cike da rashin Imani ya ɗago Almakashin ya seta yatsun Hannun nata.


    Wani gigitaccen ƙara ta saki dan ta fahimci abinda ake son yi mata, take ta soma kiciniyar ƙwatar kanta, Amman riƙon da sukai mata bana wasa bane, gashi daman dukkansu lukutaye ne, Hakan ne ya sanya duk ƙoƙarinta ta kasa ƙwatar kanta..............✍🏻




_Comment And share_

*بسم الله الرحمن الرحيم*

 


        *😭BANI NA KASHE SHIBA*😭


           *Story and wrtten*

                       *By*


       *FATIMA UMAR KAS*

                 *_(MUMMYN MIHAL_ )*


_Marubuciyar_👇🏼

*BAK'IN CIKIN KISHIYATA*

     *RAYUWAR MIHAL*

*ABINDA ALLAH YA NUFA*

    *SILAR ABAYA*

*'YA'YAN MIJINA NE*

     _AND NOW_

*BANI NA KASHE SHIBA*



*PAID BOOK*

 _(Littafin kud'i_) 



*LABARI MAI TAB'A ZUCIYA*😔

_ya k'unshi soyayya,tausayi, cin amana, hassada, munafirci_



*Dedicated to LEEMAHT pinky*💞



®🏝

 *ZAFAFA WRITTERS FORUM* 


             

  *_Z• W• F•🏝_*



    *Gyara da kanki*👌🏻

   

  *Kwai*

*Tumatir*

*Tattasai Albasa,* *Attarugu*

    *Maggi mai*.


_Ki kaɗa kwanki mai ɗan yawa, sai ki niƙa tumatir shima da yawa, sai ki juye akan ƙwan nan, sai ki yanka Albasa attarugu tattasai kaɗan aciki, sai ki sanya maggi shima kaɗan, saiki kaɗa sosai, in sun haɗe jikinsu sai ki ɗaura mai ki soyasu sama sama,in kin zuba sai kiyi ta juyawa, karki bari ya soyu sosai ya ɗanyi ruwa-ruwa, sai ki sauke in ya ɗan sha iska sai kici, yana saukar da Ni'ima sosai da kuma ƙara lfy, sai kin gwada zaki tabbatar ƴar uwa😊._



   🆓 *page four*


Jin ƙarar ne ya sanya Mama dake durƙushe a waje tin ɗazu tai saurin miƙewa, ƙirjinta ta dafe jin yana bugawa da ƙarfi. Dan ta fahimci akwai abinda akeyi wa ƴar tata.


   Ɗan sandan ɗazu ne yai saurin nufar bakin cell ɗin ya tsaya sannan ya soma faɗin. "Yallaɓai ka dan Dakata." ya faɗa da sauri,   shi kuwa da ya gama niyyar Aiwatar da ƙudirin shi juyowa yayi ya watsa mai wani kallo sannan yace. "Wane kai kake ƙoƙarin dakatar dani zanyi aiki na? Ƙaramin expector irinka har kakai ka hanani yin abinda nai niyya? Me kakeson faɗamin."?


   Shi kuwa sunkuyar da kai yayi cike da girmamawa yace. "Yallaɓai kayi haƙuri karkaga nayi maka shishshigi cikin lamuranka, saidai ƴar  Shawara ce daman zan bayar, a ganina ya kamata mu jira a gama duba yaron tukunna a tabbatar yana da rai ko ya rasu, a lokacin ne za a san hukuncin daya dace da ita, yanzu in ka cire mata yatsu akazo batada laifi fa,? Kuma ya dace ka kirawo shi mahaifin yaron tinda kanada number shi dan ina ganin kamar gidan su basu san meke faruwa ba."


    Shiru yayi yana nazarin maganarshi, sai can tukunna ya nisa yace."Naji to sai ka kama gabanka."


  Juyawa yayi ya fice daga gurin, gaba ɗaya tausayin yarinyar yakeji da kuma mahaifiyar tata dake kuka tin ɗazu. Gurin da yake tsaye ya koma ya cigaba da rubuce rubucen da yakeyi,


    Mama ce ta iso gurinshi da sauri tana faɗin. "Ɗan Allah ɗana karku cutar min da yarinya ita kaɗai na mallaka,  karkuyi mata wani abu ba akan laifin taba,  ninasan bata Aikata komai ba."


     "Ki dena kuka Ba'ba, kuje kuci gaba da Addu'a sai ubangiji ya sauƙaƙa muku." ɗan sandan ya faɗa, tana shirin magana wata budurwa ta faɗo cikin division ɗin kamar an jefota, kai tsaye gurin  ta nufa, a ruɗe ta soma faɗin. " Mama yanzu nan na samu labarin wai Leemaht tana tsare a nan an kamata  wai tayi kisa, wannan wacce irin magana ce da hankali bazai ɗauka ba, taya za a ce wai tayi kisa, ta kashe babban mutum haka.?"


   Ta ƙarasa faɗa cike da damuwa, itama Hawayen fuskarta ta goge sannan tace. "SADIYA ya zamuyi da Abinda Allah ya tsaro? Ƙaddara ce ta Afko cikin Rayuwarmu ba zato bare tsammani, sai dai ku tayamu da Adduar ubangiji ya kawo mana komai da sauƙi."



      Kai Sadiya ta shiga girgizawa sannan tace."Aradun Allah ko za a bani Al'qur'ani zan dafa akan Leemaht bazata iya kashe dabba bama balle mutum, insha Allah zata kuɓuta, ni dawowa ta kenan  daga Aiken da Umman mu tayimin na tarar da unguwar a hargitse, ina fara tambayar me ya faru ake faɗamin, anan na tambayi wanne police station aka kaita shine akacemin kuna nan, Banyi mamakin ganin babu wanda ya biyo bayanku a maƙota ba dan nasan irin ƙamar da suke yi muku, yanzu ina ita leemaht ɗin take."?


   Ta faɗa cikin muryarta ta fulani.


   "Tana ciki a tsare, ɗazu ma na jiyo ƙararta fata na ba wani mugun Abin sukai mata ba, sun hanani in ganta kuma."


      Tini Hawaye ya ciko idon Sadiya, nan tai ƙoƙarin maidasu sannan tace. "Kiyi Haƙuri mama kizo mu koma gida yanzu kinga magriba tayi, kuma ba bari zasuyi ki ganta ba, mu tafi gida da safe sai mu dawo."


     Ta faɗa cikin kwantar da murya, kai ta gyaɗa sannan tace. "Shikenan muje ma dawo goben."  riƙe mata hannu Sadiya  tayi ganin jiri na shirin kayar da ita suka fita a gurin.


*** Shi kuwa exfector mudi ɗan sandan na fita ya juya ya Ajiye Almakashin Hannunshi sannan ya juya yace musu su saketa. Suna sakinta ta shiga yarfe hannun tana cije leɓe da runtse idanunta jin Azabar zafin da yatsunta ke yi mata, ɗago hannun tayi tana kallon yadda yatsun sukai jajir suka kumbura, ji take kamar ba a jikinta hannun yakeba. Shi kuwa miƙewa yayi sannan ya zabga mata wani kallo yace. "Karkiga na rabu dake yanzu haɗuwarmu ta gaba bazatayi kyau ba, dan sai kin ɗanɗani Azaba a gurin nan kafin kije ki karɓi hukuncin laifin da kika Aikata."


   Yana gama faɗa ya juya ya fice, suma matan juyawa sukai suka fita, kwaɗo yasa ya garƙame cell ɗin sannan ya nufi office ɗinshi. 


   Ita kuwa hannun nata ta cigaba da matsawa ko zata samu sauƙin zugin da suke yi mata.


     Yana shiga ya ɗauko wayarshi sannan ya shiga laluben Number Alhaji Bilyamin Naira.


.....

Shi kuwa fitowarshi kenan da niyyar yin Alwala ya tafi masallaci yaji wayarshi na ring, zaro ta yayi daga Aljihu sannan ya ɗaga gami dayin sallama, Amsawa yayi daga ɗaya ɓangaren sannan yace.


   "Alhaji Barka dai, Kana magana da Expector Mudi daga police station ɗin gwagwaladawa."


  "Ok inaji meya faru.?"

Ya tambaya a ɗan ruɗe, shima daga can zama ya gyara sannan yace. "Alhaji munason ganinka a Division ɗin namu yanzu bada jimawa ba, magana ce akan yaron wajenka AMMAR."


   "Me ya faru! me ya sameshi."? Ya faɗa ƙirjinshi na bugawa.


   "Maganar bazata yiwu ta waya ba sai kazo dai ɗin."


   "Ok yanzu Zanyi sallah ne inna idar zanzo insha Allah."


"ok sai kazo ɗin nima sallahr zamuyi yanzu."


   Sallama sukai sannan suka kashe wayar, masallacin ya juya ya nufa gabanshi na yawaita faɗuwa.


***A cikin gidan kuwa koda Mamy ta idar da sallahr falon ta dawo tana cigaba da daddan na carbin hannu dake yatsanta, tagumi ta zuba tana zaman jiran tsammani. Sallama taji a bakin shigowa falon nan ta bada damar shigowa.


    Wasu mutane ne suka shigo su biyar sanye da kaya iri ɗaya, tsayawa sukai gami da sunkuyar dakai An rasa mai magana acikinsu. Zuba musu ido tayi, jin basuce komai ba ya sanya A tsawace tace.


    "Ya na ganku ku kaɗai ina yake Ammar ɗin.?" jikinsu ne ya ɗau rawa, da ƙyar ɗaya daga cikinsua ɗarare yai ƙarfin halin furta. "H..Hajiya b..bamu sameshi ba iya motarshi kawai muka samu gefen titi ba kowa a ciki gata nan ma motar mun zo da ita tana waj...."


  "Me kace!?, kace motarshi kaɗai kuka tarar shi baya cik..."


Banko ƙofar da akayi da ƙarfi shiya dakatar da ita da maganar da takeyi, gaba ɗaya ƙofar suka zubawa ido, wani mutum ne ya shigo, zubewa yayi a kan carfet ɗin yana maida Numfashi sai haki yake zubawa.


     "Lafiya Babawo meye hakan ka shigo a guje bako sallama.?"


    "H..H...Hajiya Hajiya mai gida ne na ganshi a h.h.h..."

   Haki kawai yakeyi ya kasa furta abinda zai faɗa. "Ka nutsu kayi magana mana meya sameshi.?" ta faɗa a ruɗe. Baki ya kuma buɗewa Amman ya kasa cewa komai dan Haka ya miƙa mata wayar Hannunshi. Da sauri ta karɓa, tana dubawa taga a cikin Facebook yake, post ɗin da akayi ta ƙurawa ido tana kallo. Bata gama gane fuskar wanda aka ɗauka ba, dan haka ta zuƙo hoton. "Ammar!" ta furta a hankali, Rubutun ƙasan hoton ta soma karantawa tini jikinta ya ɗau rawa batasan sanda wayar ta siɓice a hannunta ba ta faɗi a ƙasa, gaba ɗaya idonta ta zaro waje sai ƙirjinta data dafe da dukkan Hannayenta, jiri ne ya soma ɗiɓarta take ta yanke jiki ta faɗi.........✍🏻







_Comment and share_

*SUBSCRIBE*

_DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV_


https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ


*بسم الله الرحمن الرحيم*

 


        *😭BANI NA KASHE SHIBA*😭


           *Story and wrtten*

                      

                  *By*


       *FATIMA UMAR KAS*

                 *_(MUMMYN MIHAL_ )*


_Marubuciyar_👇🏼

*BAK'IN CIKIN KISHIYATA*

     *RAYUWAR MIHAL*

*ABINDA ALLAH YA NUFA*

    *SILAR ABAYA*

*'YA'YAN MIJINA NE*

     _AND NOW_

*BANI NA KASHE SHIBA*



*PAID BOOK*

 _(Littafin kud'i_) 



*LABARI MAI TAB'A ZUCIYA*😔

_ya k'unshi soyayya, tausayi, cin amana, hassada, munafirci_



*Dedicated to LEEMAHT pinky*💞



®🏝

 *ZAFAFA WRITTERS FORUM* ✍🏻


             

  *_Z• W• F•🏝_*



    *Gyara da kanki*


_Ki samu garin kuka ki zuba acikin Ruwa ki gauraya sosai, sai ki juye madarar ruwa a ciki ko ta gari kisha_

   _Zaki iya yin na garin bushashshiyar kuɓewa amman sai kin daure zaki iyasha . Ki gwada ƴar uwa_



🆓 *PAGE Seven*


    "Yanzu shi Ammar ɗin yana ina?". Yai ƙarfin Halin tambaya duk da zuciyarshi bugawa takeyi. Kanta kawai take girgizawa ta gaza furta komai sai Hawayen dake Ambaliya a kan fuskarta.

   "Sun kashe mana shi".

Tai ƙarfin halin furtawa.


    "Innalillahi wa inna ilaihirrajiun". Ita kawai yake maimaitawa. "Shikenan yanzu ki zauna ki kwana da ita anan ɗin ni zan koma gida insha Allah gobe da Sassafe zan dawo in ga jikin nata."


    Kai kawai ta gyaɗa mai, juyawa yayi ya fita kanshi na wani irin juyawa da ƙyar ya iya kai kanshi motarshi, koda ya shiga ma ɗaura kanshi yayi kan sitiyarin motar yai shiru yana jinjina Al'amarin, ganin dare na kumayi shiya sanya ya tashi motar ya fice a cikin Asibitin.


  A wannan daren babu wanda ya Rintsa a cikinsu, *Zulaihat, Amir, Daddy, Sadiya Fillo, Mama.*


    Gaba ɗaya mama ta rasa meke yi mata daɗi a duniya mafita kawai take nema, babban tashin hankalinta batasan wanda zataje gurinshi ba akan ya taimaka mata duba da yadda kowa yai watsi dasu saboda Talauci, tasan a Dangin mijin nata akwai masu halin da zasu iya taimaka musu amman tasan tsanar da sukai mata bazai bari su taimakesu ba, Gatansu shine Allah, a yanzu a gurinshi kawai zasu nemi taimako, tashi tayi ta ɗauro Alwala tazo ta fara jero nafilfili.

.....

Itama a wannan daren idanunta a bushe suke babu alamun bacci, a yanzu hawayen ma sun tsaya cak sun dena zubowa, Sauro kuwa tin tana dokesu in sun cijeta har ta haƙura ta barsu sunata Hidimarsu a jikinta, ga kukansu dake ta addabar kunnuwanta.


   

  Ita kanta bazata ce ƙarfe nawa ba a yanzu dan garin yayi tsit bakajin motsin komai sai haushin karnuka, ɗakin dunɗum yake ko tafin Hannunta bata iya gani, ga wari da zarni da suka cika mata ciki. 


   A yanzu ba kanta take jimantawa ba, gaba ɗaya tausayin mahaifiyarta ne ya cikata, tasan duk inda take a yanzu hankalinta ba akwance yake ba, tinaninta ya zata kasance in aka kasheta? Dan ta tabbatar itama kasheta za ayi.


   Waɗannan tinane tinanen su suka Addabi zuciyarta, wani tinani ne ya faɗo mata tinawa batayi sallahr Magriba da isha'i ba, juyawa tayi a cikin duhun ta soma taimama a jikin bangon da take zaune. Tana gama taimamar ta cire ɗan kwalin kanta ta shimfiɗa ta miƙe ta tayar da sallahr, ganinta data zauna batayi ba gwara tayi a duk yanayin data samu.


.....

Sai wajen Asubahi sannan Mamy ta farfaɗo, a hankali ta soma buɗe idanunta, dishi dishi ta soma gani har idan nata ya washe, gefe ta kallah nan taga Zulaihat nata jera sallah. 

Sai lokacin abinda tagani ya faɗo mata a rai, da sauri ta soma kiciniyar tashi saidai ruwa ne jone a hannunta. Jin motsinta shiya sanya Zulaihat saurin sallame sallahr da takeyi, da sauri tazo ta riƙe mamyn tanayi mata Sannu . Mai makon ta Amsa sai cewa tai.


    "Zulaihat da gaske ne abinda na gani cewar An kashemin Ammar.?" Shiru tayi ta kasa magana saima sunkuyar da kai da tayi.


   "Tambayarki nakeyi ki bani Amsa mana ta kuma faɗa a Hargitse. Turo ɗakin akayi aka shigo da sallama, kallon bakin ƙofar sukayi dukkansu. Amir ne ya shigo kai tsaye gurin Mamyn ya nufo yana yi mata sannu.


   "Amir da gaske an kashe Abokinka.?" shima ta jefo mai tambayar, girgiza kanshi yayi sannan yace.

   "A'a bai mutu ba yanzu ma daga Asibitin da yake nake, likitoci sun tabbatar yana raye yanzu hakama na baroshi yana bacci." Wata ƙarƙarfar Ajiyar zuciya ta sauke sannan tace. "Inason in ganshi yanzu ku kaini in ganshi sai hankali na yafi kwanciya."


   Ta faɗa tana ƙoƙarin fizge Ƙarin ruwan dake Hannunta. Da sauri ya matsa yana faɗin. " Ai mamy babu wanda ake bari ya ganshi yanzu yana buƙatar hutu ne, kuma kinga kema bakida lafiya ko kinje bazaki samu ganinshi ba, dan Allah ki kwantar da hankalinki kar ciwonki ya tashi dan Allah Mamy badan muba."


   Tabbas maganganunshi sun ɗan kwantar mata da hankali dan haka ta koma ta kwanta. Ajiyar zuciya ya sauke shima ganin ya shawo kanta, kallon Zulaihat yayi yace tazo yana da magana da ita.


   Miƙewa tayi ta fice a dakin, kallon Mamyn yayi yace. "Bari taje ta siyo miki magungunan da aka rubuta miki inyaso ni sai in zauna kafin ta dawo."


   Kai ta gyaɗa tana lumshe idanunta, juyawa yayi ya fice a ɗakin gami da ja mata ƙofar, saida suka fita daga kwanar sannan ya dubeta yace........✍🏻





_Comment and share pls_

*SUBSCRIBE*

_DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV_


https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ


*بسم الله الرحمن الرحيم*

 


        *😭BANI NA KASHE SHIBA*😭


           *Story and wrtten*

                      

                  *By*


       *FATIMA UMAR KAS*

                 *_(MUMMYN MIHAL_ )*


_Marubuciyar_👇🏼

*BAK'IN CIKIN KISHIYATA*

     *RAYUWAR MIHAL*

*ABINDA ALLAH YA NUFA*

    *SILAR ABAYA*

*'YA'YAN MIJINA NE*

     _AND NOW_

*BANI NA KASHE SHIBA*



*PAID BOOK*

 _(Littafin kud'i_) 



*LABARI MAI TAB'A ZUCIYA*😔

_ya k'unshi soyayya, tausayi, cin amana, hassada, munafirci_



*Dedicated to LEEMAHT pinky*💞



®🏝

 *ZAFAFA WRITTERS FORUM* ✍🏻


             

  *_Z• W• F•🏝_*



    *Gyara da kanki*


         *KANUN FARI*


_Ƴar uwa ki riƙe kanin fari shi kaɗai ma ya isheki, in kin riƙeshi ba ruwanki da wasu tarkacen magunguna. Ki samu kanunfari ki jiƙashi a robar faro ki zuba mai tsaftataccen ruwa ki barshi ya jiƙu, inya jiƙu sai kisha da safe kafin kici komai, da rana ma kisha da dare ma kisha, sannan zaki iya ɗibar garwashi ki zubashi a kai sai ki tsugunna akai, har maganin sanyi yakeyi, Shi kaɗai ma inkin riƙe ya isheki, ki gwada😊._



🆓 *Page Five*


   Faɗuwar Mamy yai daidai da shigowar Zulaihat cikin falon, da wani mugun gudu ta ƙarasa tana ƙoƙarin tareta amman saida taje ƙasa, da Azama ta ƙarasa ta shiga girgizata amman bata motsi ta suma, a ruɗe ta soma faɗin.


   "Me ya sameta? Tsaiwar me kuke a nan ku kuma bazaku taimakamin ko da ruwa bane.?" da Azama ɗaya daga cikinsu ya nufi frige ya buɗe ya ɗauko ruwa yazo ya miƙa mata. Buɗewa tayi ta shiga yayyafawa mamyn.


Ajiyar zuciya Mamy ta sauke mai ƙarfi Alamar ta farfaɗo, saidai har yanzu bata gama dawowa hayyacinta ba Still kuma idonta a rufe yake. Sannu suketa jera mata amman ba Amsa.


   "Wai me ya faru ne ina tambayarku kun ƙaleni." ta faɗa a tsawace."


   "Babawo mai gadi ne ya nuna mata Abu a waya muma bamusan mene ba tana gani ta faɗi." Babban ya faɗa.


    "Me ka nuna mata a wayar." ta maida tambayar kan Babawo da jikinshi keta ɓari ya jiƙe sharkaf da gumi. Wayar dake yashe a ƙasa ya nuna mata, da sauri ta ɗauki wayar  tana kunnawa ta kawo. Allah ya sa akan kafet ne da ba carfet a gurin ba abinda zai hanata yin tararatsa.


 

     Hannu takai ta ɗauki wayar, take taga abinda ya kusa tarwatsa kwanyarta. Ammar ne kwance cikin jini gaba ɗaya farar Shaddar daya sanya tayi kaca kaca da jini gefe ɗaya budurwa ce durƙushe a gabanshi da wuƙa a hannunta sai mutane dake tsaye a kansu. Rubutun ƙasa ta soma karantawa.


   _"A yaune da misalin ƙarfe 5:45 Aka kama wata budurwa da laifin kashe ɗan gidan Alhaji Bilyamin Naira ta Hanyar luma mai wuƙa a cikinshi, yanzu haka dai ƴan Sanda sun kamata sun tafi da ita, yayinda shi kuma aka wuce dashi Asibiti dan yimai gwaje gwaje ko da sauran numfashin shi."_


     Ɗaga Wayar tayi ta makata a bango sannan ta silale a gurin ta durƙushe duk Adduar data zo bakinta ita kawai take yi, gaba ɗaya Duniyar ce keta juya mata kanta yayi mata wani duuuuum! Shiru falon yayi bamai magana ga Mamy dake ta sauke numfashi da ƙar da ƙyar sai Zulaihat data dafe saitin Zuciyarta jin tana bugawa ba bisa ka' ida ba, su kuwa duk sunyi jigum jigum ko ƙwaƙwƙwaran motsi sun gazayi.


   Suna cikin wannan Halin Alhaji Bilyamin ya shigo falon a hargitse, dan da ƙar ma ya iya kawo kanshi gida dan da yaje ba,abinda Ɗan sandan ya ɓoyemai har wacce tai Aika Aikar a cewarsu saida ya nuna mai, shi kanshi ƙarfin Adduar da yake tayi ita ta sanya bai fita hayyacinshi Amman hankalinshi a matuƙar tashe yake jin Abin kamar Al'mara wai An cakawa ɗanshi wuƙa.


   A lokacin Aka haɗashi da wanda zai Rakashi Asibitin da aka kaishi saidai yace dole sai ya koma gida ya taho da iyalan gidan.  Yayi matuƙar ƙoƙarin saita kanshi kar Mamyn ta fahimci wani abu amman kana ganinshi zakasan ba a daidai yake ba.


  Adduarshi Allah yasa bata samu labari ba ya fiso yayi mata bayani a nutse, saidai yana shigowa cikin falon yai turus, ganin yadda Zulaihat keta rusar kuka tallafe da Mamy da numfashinta ke fita Sama-Sama. Yana kallon fuskokinsu yasan mai faruwa ta faru, 


   Da sauri ya ƙarasa yana  jijjiga Mamyn Amman shiru, Baya buƙatar ƙarin bayani yasan dai Sunji komai yanzu. kanshi ya dafe sanin Abinda yake gudu dai sai da ya faru da ƙar ya iya furta.


   "Je ki ɗauko mayafinki mu kaita Asibiti". Kai kawai ta iya ɗagawa sannan ta miƙe da ƙyar ta fice. Sashinta ta shiga.  

  Tana fita ya cicciɓi Mamyn ya fice da ita, da sauri Direba yazo ya buɗe mai motar ya sakata, zagayawa yayi ya tayar da motar yana shirin Ja Zulaihat ta fito sanye cikin cikin ƙaton Hijab tazo ta buɗe motar ta shiga idonta kuwa ya kaɗa yayi wani irin mugun Jaaa! Hawaye ne kawai ke tsiyaya a cikinsu, saidai tasa gefen hijab ɗinta ta goge.


    Ita ta zauna a baya ta riƙe Mamyn yayin da shi kuma ya zauna kusa da Direban, tini mai gadi ya buɗe musu get suka fice, ko basu faɗa ba Direban yasan Asibiti zasu je dan haka kai tsaye Asibitin da suke zuwa ya nufa dasu.



   Suna isa Akayi saurin karɓarta nan aka  sanyata a kujerar ɗaukar marasa lafiya akayi wani ɗaki da ita. Gefe suka koma sukayi jigum jigum kowa da tinanin da yake a ranshi.


    Sunanan tsaye har dare ya soma yi ba wanda yazo yace musu wani abu, nan Hankalinsu ya kuma tashi. Sai can tukunna wani Likita ya fito.


   Da sauri suka isa gurinshi suna tambayar ya jikin nata.?


     "Da sauƙi mun samu ta dawo hayyacinta, yanzu inason ganin ka a office ɗina." ya faɗa yana yin gaba. Ba musu yabi bayanshi shima. Nan suka bar Zulaihat zaune inda take ta rafka uban tagumi.


    Suna shiga ya nemi guri ya zauna, shima zaman yayi sannan likitan ya soma faɗin. "Alhaji Me kuka bari ta gani daya ɗaga mata Hankali har Hawan jininta ya tashi? Ni dakai fa nasha faɗa maka kar ai mata wani Abu da zai saka ta shiga damuwa har  ciwonta ya tashi. Gashi yanzu jininta ya hau fiye da da. Amman dai munyi iyakar iyawarmu mun samu komai ya daidaita, yanzu munyi mata Allurar bacci dan ta samu hutu insha Allah inta farka ba wata matsala, yanzu ga wannan takaddar magungunan da za a siya ne."


    Ya faɗa yana miƙa mai wata  takadda. Amsa yai sannan yace. "Shikenan mungode zan siyo magungunan yanzu inta farka sai tasha, Allah ya bata lafiya."


   Ya faɗa a taƙaice sannan ya miƙe ya fice daga office ɗin, da kallo likitan ya bishi yana tinanin meke faruwa ne? yaga shi kanshi ba a nutse yake ba.


   Yana fita ya fito da wayarshi a Aljihu dan tin ɗazu aketa kiranshi yana ciki. Yana dubawa yaga Number ɗazu ce, bin kiran yayi sannan ya kara a kunnenshi yana jin An ɗaga ya soma faɗin.


    "Ya, ya farfaɗo kuwa daga dogon suman.?" magana akayi mai daga ɗaya ɓangaren. Kai ya shiga gyaɗawa sannan yace. "Shikenan ganinan zuwa Asibitin yanzun nan." yana faɗa ya kashe wayar, kallonshi ya maida kan Zulaihat sannan yace. "Kije ki kula da Mamyn naku nina tafi inda aka kai Ammar ɗin sunce in je in samesu a can yanzu."


   Kai ta gyaɗa sannan ta miƙe jiki a saluɓe ta nufi ɗakin da aka kwantar da Mamyn, shima juyawa yayi ya tafi.


.....

Yana isa Asibitin ya tambayi inane Emergency room? Nan aka nuna mishi kai tsaye can ya nufa, yana zuwa ya tarar da ɗan sandan suna magana da likita.


   "Yawwa ga Mahaifin yaron nan ya iso muje ɗakin da yake." ɗan sandan ya faɗa. Ba musu suka rankaya ɗakin, tura ɗakin sukayi suka shiga.


   Karaf! Idonshi ya sauka akan wanda ke kwance samɓal an lulluɓeshi da likkafani har fuskarshi. Jiyai ƙafafuwanshi sun gaza ɗaukarshi sai rawa sukeyi, durƙushewa yayi a gurin yana maimaita Innalillahi wa inna ilaihirrajiun.! Ji yake kanshi kamar zai rabe biyu, wannan shine Tashin hankali da ba a saka masa Rana, tinaninshi ne ya rabu biyu ga mutuwar tilon ɗanshi rana tsaka ga kuma Mai ɗakinshi itama Rai a hannun Allah, wani irin Zafi yakeji a Zuciyarshi ya rasa me ma zaiyi yanzu...........✍🏻






_Comment and share pls_

*SUBSCRIBE*

_DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV_


https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ


*بسم الله الرحمن الرحيم*

 


        *😭BANI NA KASHE SHIBA*😭


           *Story and wrtten*

                      

                  *By*


       *FATIMA UMAR KAS*

                 *_(MUMMYN MIHAL_ )*


_Marubuciyar_👇🏼

*BAK'IN CIKIN KISHIYATA*

     *RAYUWAR MIHAL*

*ABINDA ALLAH YA NUFA*

    *SILAR ABAYA*

*'YA'YAN MIJINA NE*

     _AND NOW_

*BANI NA KASHE SHIBA*



*PAID BOOK*

 _(Littafin kud'i_) 



*LABARI MAI TAB'A ZUCIYA*😔

_ya k'unshi soyayya, tausayi, cin amana, hassada, munafirci_



*Dedicated to LEEMAHT pinky*💞



®🏝

 *ZAFAFA WRITTERS FORUM* ✍🏻


             

  *_Z• W• F•🏝_*



    *Gyara da kanki*


          *ZUMA*


_Ki riƙe zuma da kyau ƴar uwa, kisha cokali uku da safe, uku da Rana, uku da dare. Kullum ki dinga yin hakan  zaki sha mamaki, sai kin gwada._



🆓 *PAGE Eight*



     "Jiya bayan na bar nan na kira Daddy a waya na tambayeshi a wanne Asibiti suke in zo, sai yacemin Ai dare ya riga yayi in bari yau sai inje can gidan naku yace shima da Safe zasu wuce da gawar. Amman ya umarce ni da in tafi  dake saidai kar mu taho da Mamy kuma kar in nuna mata cewar ya rasu."


   Kai kawai take gyaɗawa alamar gamsuwa dan bakin nata ya gama kullewa saidai Ambaliyar Hawaye da take tayi tin jiya sunƙi tsayawa. 


   A lokacin likitan ya iso gurinsu yana tambayar ta farka? Nan yace mai ta farka amman saidai ya kuma rubuta musu wani maganin dan waccen takaddar ta ɓace.


  Ba gardama likitan ya buɗe Office ɗin nashi ya shiga, magungunan ya kuma Rubuta mata ya kawo mai, amsa yai yaje ya siyo ya biya kuɗin sannan suka koma cikin ɗakin, kasancewar harda Ruwa ya siyo shiya ɓare magungunan sannan ya miƙawa Zulaihat ɗin ta bata, Amsa tai ta zauna ta bawa Mamyn.


    Zama taci gaba dayi har saida taga Mamyn ta soma bacci dan a magungunan nata harda na sa Bacci sannan ta miƙe ta fice, tana fita taga yana jiranta a bakin ƙofar.


   Gaba yayi yace ta taho su tafi. Ba musu tabi bayanshi, a motarshi suka tafi, ko a hanyama Nasiha yaci gaba dayi mata da kuma bata haƙuri akan ta rage zubar mai da Hawaye.


    Suna karyo kwanar Layin suka ga unguwar danƙam da mutane, rasa gurin yin parking ɗin ma yayi sai baya ya koma ya ajiye motar sannan suka fito, Ƴan jaridan da suka cika gurin suna ganinsu sukayo kansu da Tambaya musamman ita. Ƙalilan ne keyi mata gaisuwa amman yawancin su Bayanin nata suka fi buƙata.


    Haka Amir ya dinga tuttture su suna samun hanya har sukai nasarar danganawa da get ɗin gidan, turawa sukayi suka shiga shima Harabar gidan cike yake da jama'a, saida yai mata Jagora har cikin falon sannan ya juyo ya fito.


   Anan ma ƴan uwa da Abokanan Arziƙi da maƙota su suka cika falon. Tana ganin ƴan uwanta ta kuma rushewa da kuka, wata Auntyn tace tazo ta riƙota ta zaunar da ita tana Rarrashinta.


   A lokacin ne Daddy ya shigo falon, nan ya kalli Zulaihat yace. "Ƴata taso kiyimai Addu'a za a rakashi gidanshi na gaskiya. Miƙewa tayi tabi bayanshi, kai tsaye Masaukin baƙi suka nufa,  tana shiga ta tarar nan ma ƴan uwa ne duk a ciki sunzo tayasu Alhini.


   Durƙusawa tayi ta soma zubomai Adduoi duk da muryar tata bata fita Amman kana kallonta kasan Addu'a take yimai duba da yadda Bakinta ke motsi.


   Bata ƙarasa ba kuka ya kufce mata, miƙewa tayi tsaye, Juyawa tayi ta fice daga ɗakin da gudu ganin za a fita da gawar. Nan manyan dake cikin ɗakin suka ɗauki gawar suka fice da ita.


   Dandazon mutanen dake waje suma juyawa sukayi dan raka gawar makwancinta. Koda ta koma ciki ma cukuikuye kanta tayi cikin Hijabi tana kukan.


   "Kiyi haƙuri lokacinshi ne yayi muma nan duk jiranta mukeyi, ki dena yi mishi kuka kiyimai Addu'a." Taji matar dake gefenta ta faɗa, ɗago fuskarta tayi sannan ta shiga goge Hawayen fuskarta.


   Aunty Salma ce ta taso ta dawo kusa da ita sannan tace. "Ina ita Mamyn na ganki ke kaɗai.?"


    "Mamy nacan an kwantar da ita Rai a hannun Allah, mukam duk wanda Ya aikata hakan a garemu ya cucemu ya rusa mana farin cikinmu, Amman ya dace Wani yaje ya kula da Mamy a Asibiti dan ni bani da damar kuma fita tinda Takaba ta Riskeni."


   Ta ƙarasa faɗa tana sheshsheƙa. Itama girgiza kai tayi cike da tausayinsu sannan tace. "Bari ga ƙanwar tanan bari inyi mata magana sai taje ta zauna da ita a Asibitin, Allah dai yai muku sakayya."


   Da Amin duk masujin maganar tasu suka Amsa, Tashi tayi taje tayiwa Hajiya Zainab bayanin Halinda Yayar tata take ciki a asibiti. Nan ta tambayi wanne Asibiti? Ana faɗa mata ta miƙe ta fuce a sukwane. Kasancewar duk an tafi Rakiyar gawa tana fita taga ba kowa dan haka da Azama ta fice daga ciki ta nufi titi dan samun Abin da zata hau zuwa Asibitin.



Acan kuwa sanda suka isa An riga da Anyi Haƙar kabarin dan Haka suna isa aka fara ƙoƙarin shigar dashi ciki.


   Daddy Amir sai wasu mutum biyu su suka kama gawar suka sanyata a ciki. Suna Ajiyeta aka fara ƙoƙarin

 Rufeshi da ƙasa.


*"Ku dakata!."* Amir yai saurin katsesu, juyowa sukayi suka zubamai ido suna jiran jin mai zaice.?

    "Ku kalla ku gani yana ɗan motsi ƙirjinshi na ɗagawa." juyawa sukayi dukkansu suka zubawa gawar ido dan tabbatar da Abinda yace........✍🏻







_Comment and share_

*SUBSCRIBE*

_DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV_


https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ


*بسم الله الرحمن الرحيم*

 


        *😭BANI NA KASHE SHIBA*😭


           *Story and wrtten*

                      

                  *By*


       *FATIMA UMAR KAS*

                 *_(MUMMYN MIHAL_ )*


_Marubuciyar_👇🏼

*BAK'IN CIKIN KISHIYATA*

     *RAYUWAR MIHAL*

*ABINDA ALLAH YA NUFA*

    *SILAR ABAYA*

*'YA'YAN MIJINA NE*

     _AND NOW_

*BANI NA KASHE SHIBA*



*PAID BOOK*

 _(Littafin kud'i_) 



*LABARI MAI TAB'A ZUCIYA*😔

_ya k'unshi soyayya, tausayi, cin amana, hassada, munafirci_



*Dedicated to LEEMAHT pinky*💞



®🏝

 *ZAFAFA WRITTERS FORUM* ✍🏻


             

  *_Z• W• F•🏝_*



    *Gyara da kanki*


        *KANIN FARI*


_Ki sami kanunfari ki zuba a mazubi sai ki zuba mazar ƙwaila akai, ki kawo ruwa mai tsafta ki zuba musu, sai ki barsu su su jiƙu na tsawon kwana 6, inyai kwana shida sai ki ɗauko zakiga ya zama tsimi ya haɗe jikinshi sai kisha shima yana da kyau ki gwada._


🆓 *PAGE six*

 


    Dafashi ɗin da akayi shi ya dawo dashi cikin Nutsuwarshi. "Kayi Haƙuri Alhaji dukkan mai rai mamaci ne, ka ƙaddara shi tashi silar Tafiyar kenan, ku bishi da Adduar samun dacewa da Rahamar Ubangiji."


   Ɗagowa yayi da idonshi daya kaɗa yai jajawur ya kalli Doctor ɗin dake yimai wannan bayanin, kanshi kawai ya gyaɗa sannan ya fara ƙoƙarin miƙewa, bakin gadon ya nufa ya tsaya a gaban gawar, buɗe likkafanin da aka rufeshi yayi, da sauri ya mayar mai rufin jin zuciyarshi na kuma karyewa ga jikinshi daya ɗauki Rawa. 


  Baki ya buɗe da niyyar yimai Addu'a saidai yaji kuka ya taho mai, kanshi kawai yake girgizawa na tausayawa dukkansu akan Babban Rashin da sukai. Baisan ya mahaifiyar mamacin zata kasance ba intai tozali da gawar tilon ɗan nata, gefe ɗaya kuma ga matarshi da ko shekara basu rufa da Aure ba ta zama ƙaramar Bazawara.


   "Kuyi Haƙuri Alhaji Nayi maka Alƙawarin bazamu taɓa ƙyale wanda ya Aikatawa yaron nan wannan Rashin Imanin ba, kamar yadda nayi maka bayanin wacce ake Zargi in har ya tabbata ita ta Aikata wannan ɗanyen Aikin dolene ta karɓi Hukunci daidai da Laifin data Aikata."



    Esfector Mudi ya taɗa. Sai Lokacin Bakin Alhaji Bilyamin ya iya furta wani Abu, cike da ƙunar rai ya soma faɗin. "Wannan Wacce iriyar Rayuwa ce ace An maida Ran mutum ba a bakin komai ba? Kamar Dabbobi haka akeyi wa mutane kisan Gillah? Yanzu me Ammar ya tsarewa mutane har sukaga gwara su Rabashi da duniyar gaba ɗaya? Ammar ni kaina zan shaideshi akan Sauƙin Hali da tausayawa na ƙasa dashi, Dukiyarshi bata rufe mishi ido ba duk wani na ƙasanshi yanajin daɗin mu'amala dashi, ashe akwai waɗanda ke Farautar Rayuwarshi bamu sani ba, Tabbas bazan taɓa ƙyale wanda ya rabani da gudan jini naba koda zan ƙarar da duk Abinda na mallaka sai naga An yankewa wanda yai mana wannan yankan ƙaunar Hukunci."


   Kai suka jijjiga dukkansu alamar gamsuwa, sai can tukunna ya kuma Nisawa yace. "Yanzu inason Abani gawar mu tafi da ita aje ayimai sitira."


   "Eh muma hakan muka yanke daman, Amman ni a ganina mu barwa Safiya mana? Yanzu a samu wanda zai kwana da gawar a nan, Alabashi in gari ya waye sai a sanyata a mota a kai gida, Amman yanzu dare yayi yawancin ma aikatan duk sun tafi gida."


   Likitan ya faɗa. "Shikenan Allah ya kaimu goben, Dole ni zan kwana dashi anan ɗin dan mahaifiyarshi na cikin mayuwacin Hali Haka ma matar tashi zamanta anan zai kuma ɗaga mata Hankali, dan Haka ni zan kwana dashi a nan ɗin."


   "Shikenan Hakan ma yayi." Cewar Ɗan sandan. Nan suka fice suka barshi a ciki cike da Alhini, suna fita ya tashi ya dawo ya zauna gaban gadon gami da zuba tagumi, nan ya shiga tinanin yadda Duniya ta lalace yanzu wannan Rayuwa mai cike da Ruɗani.



    Acan kuwa isowar *AMIR* kenan Asibitin yaci karo da likitan dake shirin kulle office ɗinshi dan tafiya gida, kasancewar dare ya soma yi.


   AMIR shine babban Aminin mamacin tin ƙuruciya har girma, da sauri ya ƙaraso ya miƙawa Doctor ɗin Hannu suka gaisa, nan ya ƙara da faɗin.


    "Ance min Su Mamy duk suna wannan Asibitin, yanzu suna wanne ɗakin ne."? Ya gane wacce yake nufi dan haka yace.


    "In kabi hanyar nan kayi kwana zakaga  ƙofar tana kallo ka to a nan ɗakin aka kwantar da ita, yanzu haka tana ciki.Shima mai gidan tinda na bashi takaddar magungunan da za a siyo mata tasha in ta farka har yanzu bai dawo ba gashi ni har na tashi."


   "Wai bata farfaɗo ba har yanzu? To inashi Ammar ɗin ance min duk suna wannan Asibitin ne, inason ganinsu dukkansu."


   "Wane kuma Ammar? Ai ita kaɗai kawai suka kawo bayan ita ba wanda sukazo dashi nan mara Lafiya." kanshi ne ya kulle dan shidai har yanzu bai gama tantance meke faruwa ba dan Haka ya juya ya nufi ɗakin da Likitan ya nuna mai.


  Shima juyawa yayi ya tafi da sassarfa ganin Dare na kumayi.


    Knocking yayi jikin ƙofar, tasowa Zulaihat tayi tana haɗa Hanya tazo ta buɗemai, Ganin yanayin ta saida gabanshi ya yanke ya faɗi, fatanshi Allah yasa ba Raɗi-Raɗin dayaji a gari bane ya tabbata.


   "Sannu Zulaihat ya jikin Mamyn meya same ta wai."?


   "Faɗuwa tayi". Ta faɗa da muryarta data dishashe ko fita batayi, shi kanshi bakinta kawai ya kalla yasan me tace.


   "Garin yaya ta faɗi, me likita yace ina fatan dai Hawan jini ta bai tashi ba."


    "Nima ban sani ba, Da Daddy likitan yai magana, kuma daya fito bai cemin komai ba yace dai inzo in kula da ita shi zai je ya dawo, gashi shima shiru har yanzu bai dawo ba."


    Shiru ya kumayi har yanzu ƙirjinshi na bugawa, gaba ɗaya fargaba ce ta gama cikashi, dan ganin yadda Idanun Zulaihat suka kumbura sukai jawur Alamar taci kuka ta ƙoshi, ga kuma Mamy kwance ba lafiya shi ka

ɗai ya isa ya tabbatar mai maganar da yaji ya kuma gani a Media Gaskiya ce ba ƙarya ba........✍🏻






_Comment And Share_

*SUBSCRIBE*

_DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV_


https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ


*بسم الله الرحمن الرحيم*

 


        *😭BANI NA KASHE SHIBA*😭


           *Story and wrtten*

                      

                  *By*


       *FATIMA UMAR KAS*

                 *_(MUMMYN MIHAL_ )*


_Marubuciyar_👇🏼

*BAK'IN CIKIN KISHIYATA*

     *RAYUWAR MIHAL*

*ABINDA ALLAH YA NUFA*

    *SILAR ABAYA*

*'YA'YAN MIJINA NE*

     _AND NOW_

*BANI NA KASHE SHIBA*



*PAID BOOK*

 _(Littafin kud'i_) 



*LABARI MAI TAB'A ZUCIYA*😔

_ya k'unshi soyayya, tausayi, cin amana, hassada, munafirci_



*Dedicated to LEEMAHT pinky*💞



®🏝

 *ZAFAFA WRITTERS FORUM* ✍🏻


             

  *_Z• W• F•🏝_*



    *Gyara da kanki*


*Ruwan kanunfari*

*Kankana*

*Zuma*

*Madara*


_Ki yanka kankana cikin kofi sai ki kawo ruwan kanunfari ki zuba ki kawo madara da zuma kizuba sai ki damesu ki ɗaga ki shanye. Hmmmmm! Sai kin gwada_


🆓 *PAGE Nine*


  Gaba ɗaya kallonsu suka maida kan gawar, kowa tsayar da idanunshi yayi a kan gawar amman basu ga wani motsi da tayi ba, Daddy ne ya maido da kallonshi kan Amir, dafa kafaɗarshi yayi yace.


    "Amir idanunka ne keyi maka gizo, Amman baya motsi ya riga ya mutu saidai muyi hakuri mu bishi da Addu'a." Kanshi kawai ya gyaɗa badan ya yarda ba dan shidai tabbas yaga sanda ƙirjinshi ya ɗaga saidai kamar yadda Daddyn ya faɗa wata ƙil gizo ɗin idanunshi ke yimai.


    Umarnin Rufeshi Daddyn ya bayar, nan aka shiga tilamai ƙasa akanshi har aka rufeshi ko ɓula ɗaya ba a bari ba, Ana gamawa mutane suka juya da makarar, nan akabar Daddy da Amir suna kuma yimai Adduoi, Miƙewa Dadɗyn yayi dan tafiya, ganin har lokacin Amir bai gama Adduar ba ya sanya ya juya yabi mutane ya barshi a gurin, dan yasan bayansu duk wanda zaiji mutuwar Ammar ba kamar Amir ba da suka taso kamar ƴan biyu.

.......

A safiyar ranar ne su Mama suka kuma yin sammako zuwa Station ɗin itada Sadiya ƴar fillo, dan dukkansu basu runtsaba, yanzu ma satar jiki Sadiyan tayi ta fito ba tare da Momyn nata ta sani ba, dan tin jiya taja kunnenta akan kar ta sake ta kuma zuwa police station ɗin wai kar taje laifin Leemaht ɗin ya Shafeta, amman bazata iya barin Aminiyar tata a wannan Halin ba dole suna buƙatar ta musamman Mama.


    Tana shigowa gidansu tace suyi sauri su tafi kafin momyn ta tasa a biyo bayanta, itama Mama cike da fargabar Tijarar mahaifiyar Sadiyar ta fito ta kulle gidan suka tafi. Ko ba komai sun samu mutum guda daya nuna Alhinin Abinda ya samesu, dan kaf Unguwar babu wanda ya iya ko leƙowa yayi musu jaje saima Tsegumi da suke tayi akan Lamarin.



    Suna isa Suka tarar an buɗe gurin, kutsa kai sukayi ciki, suna shiga suka tara da ɗan sandan jiya mai ɗan kirkin yana Rubuce Rubuce. Sunji daɗin ganin Office ɗin Espector Mudi a kulle da Alama bai riga yazo ba.


   Matsawa sukayi suka gaisa dashi, nan ya ɗago yana Amsawa. "Dan Allah ɗana inason ka bani damar nayi magana da Ikleemah ko na minti biyar ne." Shiru yayi yana tinani sai can tukunna ya nisa yace.


   "Gaskiya Innayi hakan zai iya jawomin matsala gurin yallaɓai."


   "Don Allah ka taimake mu mu ganta tinda gashi bai zoba har yanzu." Sadiya  ƴar fillo ta faɗa cikin muryarta ta fulani. Shiru ya kumayi sai kuma ya juya ya nufi cell ɗin.


   Tana zaune ta zuba uban tagumi dan a safiyar ma dai taimamar ta kumayi tayi sallahr Asubahi, yanda taga Rana haka taga dare, jin an taɓa gurin ne ya sanya tai saurin kallon ƙofar.


   "Ki taso ga mahaifiyarki tazo zakuyi magana."

Yana faɗa ya juya yakoma. "Kuje kuyi maganar da zakuyi amman minti biyar kawai na baku." Kai suka gyaɗa gami da yimai godiya sannan suka nufi kofar.


   Tana ganin su tai wata iriyar Zabura ta taso, tana zuwa ta zuro Hannu ta riƙe Hannun mahaifiyar tata ƙaƙam, sai kuma kuka ya kufce mata, itama Mama kukan ne ya taho mata take ta somayi, Hawayen tausayi ne ya silalowa Sadiya fillo na tausayin uwa da ƴar. Cikin kuka Leemaht ta soma faɗin.


   "Mama kinga inda ƙaddarar Rayuwa ta kawo ni koh?. Mama wallahi ban Aikata Abinda ake zargi na dashi ba, Na Rantse miki da Allah *BANI NA KASHE SHIBA* A haka naganshi a kwance nima taimaka mai kawai nayi, amman kinga An dawo da Laifin kaina."


    Ta ƙarasa faɗa tana ɗora goshinta  kan Hannun maman dake manne da nata  taci gaba da kukan. Tini tausayinta ya kuma kamasu cikin Rarrashi Mama ta soma faɗin.


   "Wallahi Ikleemah koda za a bani Alƙur'ani zan dafa akan bazaki taɓa iya kashe mutum ba, Nina haifeki nasan Abinda zaki iya da wanda bazaki iyaba,  Wannan jarrabawa ce kawai daga ubangiji, inaso ki sani.


  Ita ƙaddara a Rayuwar mutum Abun dubawa ce ga kowanne musulmi mai Imani, dan Haka kowa yana tafiya ne akan tafarkin ƙaddarar dake Rubuce cikin Littafin Rayuwarshi, dan haka muke Addu'a a matsayinmu na musulmi Allah yasa mu cinye jarrabawar Rayuwarmu, Amman igiyar ƙaddara tanada tsawo ba inda bazata  ja mutum takaishi ba, dan haka in kaga mutum ya Afka cikin wata Rayuwa to Addu'a ya kamata ka rakashi da ita bawai Aibatashi ba, dole sai mun toshe kunnuwanmu akan duk abinda mutane zasu faɗa akanki.


   Saidai ina mai Tinatar dake ki dage da Adduar ubangiji ya baki ikon cinye wannan  jarrabar, ki yawaita maimaita Innalillahi wa inna ilaihirrajiun, Allahumma Ajirni fi musibati min kairi Haulin minni wala ƙuwwati, Allahumma lah'Sahala illah ma ja'al tuhu sahala, wa anta taj'al iza shita Sahala, Lahaula wala ƙuwwata illah billahil azizul hakim, kiyi ta maimaitasu ba iyaka, insha Allah zaki ji sanyi a zuciyarki."


   "Nagode Mama insha Allahu zanyi yadda kikace." gurin Sadiya ƴar fillo ta juya sannan tace.

    "Sadiya nagode da ƙaunar da kika nunamin tabbas ke ƙawa ce ta gari a gareni dan Allah ga Amanar mahaifiya ta nan na baki ki kulamin da ita in kin samu damar hakan."


   Baki Sadiya ta buɗe da niyyar magana saidai tsawar da sukaji a bakin ƙofa ita ta katsesu. "Su waye waɗannan suka shigo mana nan."?........✍🏻










_Comment and Share pls_

*SUBSCRIBE*

_DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV_


https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ


*بسم الله الرحمن الرحيم*

 


        *😭BANI NA KASHE SHIBA*😭


           *Story and wrtten*

                      

                  *By*


       *FATIMA UMAR KAS*

                 *_(MUMMYN MIHAL_ )*


_Marubuciyar_👇🏼

*BAK'IN CIKIN KISHIYATA*

     *RAYUWAR MIHAL*

*ABINDA ALLAH YA NUFA*

    *SILAR ABAYA*

*'YA'YAN MIJINA NE*

     _AND NOW_

*BANI NA KASHE SHIBA*



*PAID BOOK*

 _(Littafin kud'i_) 



*LABARI MAI TAB'A ZUCIYA*😔

_ya k'unshi soyayya, tausayi, cin amana, hassada, munafirci_



*Dedicated to LEEMAHT pinky*💕💞💕



®🏝

 *ZAFAFA WRITTERS FORUM* ✍🏻


             

  *_Z• W• F•🏝_*



    *Gyara da kanki*


_Ki samu gyaɗarki ki soya ko ki jiƙa ki saka kayan ƙamshi a ciki da dabino kikai a markaɗa miki, sai ki zuba Peak da Zuma da garin zogale kisha safe da yamma hmmmm! Sai kin gwada._


 🆓 *PAGE TEN*


    Da sauri dukkansu suka kai kallonsu bakin ƙofar nan sukai tozali da Espector mudi fuskar nan a turɓune kamar kullum. Wani kallo yake makawa Ɗan sandan, shi kuwa tin shigowarshi cikin shi ya ɗuri ruwa tini ya sadda kanshi ƙasa ya kasa cigaba da Rubutun da yakeyi. 


    "Waya basu ikon shigo mana har cikin wajen, komene ma bazasu tsaya a waje ba shine zasu shigo mana har nan?". Ya faɗa cikin faɗa, sai lokacin Mama da suka iso gabanshi tace.


   "Haba ɗana, yanzu ganin ƴar tawa ma bazaku bani damar yi ba,? Karka ka manta kaima kana da ƴaƴa, kuma ko ba kada su bazaka rasa ƴan uwa mata ba, yanzu ka ƙiyasta in ƴarka ce wannan Ƙaddarar ta faɗo cikin Rayuwarta zakayi watsi da ita kenan? Yanzu sau nawa ina zuwa gurun nan amman kun hana in ganta, sai yau ɗaya dan nayi magana da ita ya zama laifi.?"


    Shiru yayi yana saurarenta har ta gama, Tabbas jikinshi ya ɗanyi sanyi da maganganun data faɗa. Nan ya gyara tsaiwa sannan  yace.


   "Ai Ba'ba ni ganina ba tsayawa ya dace kuyi anan ba, ya kamata kuje ku gana da iyayen mamacin sannan kuma ku soma ƙoƙarin ɗaukar lauya dan An riga an shigar da ƙara Anayin Sadakar bakwai za a shiga kotu. Dan haka tin yanzu ya dace kusan abinyi." yana gama faɗa ya wuce zuwa office ɗinshi, nan ya barsu cike da tashin Hankalin jin Wai har an shigar da ƙara, juyowa Mama tayi ta kalli Sadiya ƴar fillo tace.


  "ƴar nan kinji wai har an shigar da ƙara kuma dole sai mun ɗau lawyer? To ni yanzu ina zamu samu wanda zai tsaya mata? Koda mun samu ma ina nake da kuɗin da zan iya ɗaukar lawyer a yanzu, shikenan nasan ƙarshen Rayuwar mu ne yazo, dan na tabbatar in aka kashemin Ikleemah nima bazanyi tsawon rai a duniya ba."


   Ta ƙarasa faɗa idonta na kawo ruwa, Cike da Tausayawa Sadiya tace. "Mama dan Allah karki karaya babu abinda zasuyi wa Leemaht, Ni naji a jikina Baza a kashe taba, Akwai Wani tsohon Saurayi na dana taɓayi nasanshi ƙwararran Lawyer ne, zamuje gurinshi insha Allah zai taimaka mana in mukayi mai bayani, sannan kamar yadda yace muje mu samu iyayen mamacin ya dace muje ɗin, mu nemi suyi mana kwatancen gidan sai muje yanzu daga nan." kai Mama,ta gyaɗa Alamar gamsuwa,


 Juyawa Sadiya tayi gurin ɗan sandan ta nemi daya daure ya basu Adrees ɗin gidan Alhaji Bilyamin Naira, nan take yai musu kwatancen gidan.


   Godiya sukai mai suka tafi, sun gane wajen kasancewar shiɗin sanannen mutum ne a garin.


......

Acan kuwa koda Hajiya Ruƙayya ta isa Asibitin batasha wahalar gano ɗakin da Mamy take ba, bakinta ɗauke da Sallama ta tura ɗakin ta shiga, har lokacin Mamy bacci takeyi. Guri Hajiya Ruƙayya ta samu ta zauna gami da zuba tagumi idonta akan yayar tata, cike da tausayawa take kallonta ganin kwana ɗaya kawai Amman ta zabga uwar Rama.


A hankali Mamy ta fara motsa Hannunta, ganin Hakan ne ya sanya ƙanwar tata miƙewa da sauri ta fice, likitan taje ta kirawo akan yazo ta farka, Tare suka taho ita da shi, shigowa yayi da kayan gwaje gwaje nan ya hau gwadata, yaji daɗin ganin Hawan jinin nata ya sauka, nan ya fara ƙoƙarin cire mata drip ɗin.


   A lokacin ne ta buɗe idonta sosai tana kallansu. "Sannu Yaya." Hajiya Ruƙayya ta faɗa, kai ta gyaɗa alamar amsawa, shima likitan cewa yai. "Sannu Hajiya ya jikin naki.?" 


    "Da sauƙi." ta fada a hankali. "To Allah ya ƙara sauƙi, Anci sa'a Hawan jinin ya sauka yanzu  saidai ki rage saka abu a ranki saboda ciwonki, Taci wani abu ne.?." ya faɗa yana  maida kallonshi kan Hajiya Ruƙayya, girgiza kai tayi sannan tace.


    "A'a gaskiya bana tinanin taci wani abu."


  "Ok Amman ya kamata taci wani Abu yanzu sai tasha magungunanta insha Allah zataji daɗin jikinta, Allah ya ƙara lafiya." 


   "Amin mungode insha Allah zan samo mata wani abu taci yanzu sai tasha maganin."


  "Nasha magani ɗazu su Zulaihat sun bani, ina take ita yanzu."?


   Ta tambaya, Wani huci ƙanwar tata ta fesar mai zafi sannan tace. "Tana gida Ana cigaba da karɓar gaisuwa, kinsan yanzu bazai yiwu ta kuma fitowa ba tinda takaba takeyi, Kema dan Allah ki ɗauki dangana ki ƙaddara lokacin shi ne yayi shiyasa ya tafi saidai mu bishi da Addu'a."


    "Wane ya rasu."? Likitan ya tambaya. "Ɗanta ne wallahi wasu marasa imani suka caka mishi wuƙa yanzu haka dai ya rigamu gidan gaskiya."


   "Badai wanda ke kawo ta wannan Asibitin ana duba taba." ya tambaya a Ruɗe. Kai ta gyaɗa sannan tace. "Wallahi shine, shi kaɗai ne yaron ta ai."


   "Allahu Akbar!, Allah ya jiƙanshi da Rahama yasa ya huta, Allah kuma ya toni Asirin waɗanda suka Aikata hakan gareshi. Sai Haƙuri Hajiya, Allah ya sanya muku dangana da haƙurin jure Rashinshi."

   ya faɗa yana tattara kayan shi dan fita a ɗakin.


   "Amin Amin." Hajiya Ruƙayya ta Amsa, banda Mamy datai shiru tana saurarensu, saida taga yana shirin fita sannan tai ƙoƙarin furta.


   "Ka bani sallama gida zamu wuce." cike da mamaki yace. "Gida kuma yanzu? Ki ɗan bari jikin naki ya kuma warwarewa."


   "A'a ko minti ɗaya Bazan ƙara a nan ba gida zan tafi, in kuma baka bani ba saidai ka dawo ka tarar na tafi." Mamyn ta faɗa a kausashe.


   "Shikenan ina zuwa." ya faɗa yana ficewa, ba jimawa ya dawo ya basu takaddar sallama sannan ya fita, nan suka soma shirin tafiya. Babu wasu tarkacen da sukazo dashi iya ledar magungunan kawai suka ɗauka suka fito, ita ta riƙo mamyn har suka fito waje, nan ta tare musu Napep suka hau sukayo gida.


   A lokacin ne suma su Mama suka iso ƙofar gidan da tambaya suka gane gidan, tsayawa sukai suna tinanin ta yadda zasu shiga gidan sai ga Adaidaita ya Ajiye Su Mamy.


   Fitowa sukayi daga ciki nan Hajiya Ruƙayya ta fito da kuɗi ta biyashi, hannun Mamyn ta riƙe da niyyar su shiga ciki. Ƙaraso wa gurinsu sukayi, saida suka gaisa sannan Sadiya ƴar fillo tace. "Dan Allah gidan Alhaji Bilyamin Naira muke nema."


    "Ai kunzo gidan, Ga matar gidan nan ma." ta faɗa tana Nuna musu mamy. Ƙarasawa gurin ta sukayi nan Mama tace. "Sannu Hajiya, ya mukaji da Alhinin abinda ya faru Ya ƙarin Haƙuri kuma.?"


   "Haƙuri mun gode Allah." Mamyn ta daure ta faɗa. "To Allah ya jiƙanshi da Rahama yasa ya huta. Dan Allah inason magana da ku ne akan rasuwar yaranku in ba damuwa."


   "Shikenan ku shigo ciki." Hajiya Ruƙayya ta faɗa sannan ta juya suka tura get ɗin suka shiga. Cike Harabar gidan take danƙam da Mutane, suna shigowa aka fara yiwa Mamy Ta'aziyya, Hannu kawai take ɗaga musu dan ita kaɗai tasan me takeji a zuciyarta.


   Har falon suka shige nan ma gaisuwar dai ake ta zubowa, kai tsaye bedroom Ƙanwar tata ta kaita, zaunar da ita tayi bakin gadon tace  ta kwanta ta huta bari taje ta haɗo mata ko ruwan tea ne.


    Fitowa tayi daga ɗakin nan taci karo da Alhaji Bilyamin daya biyo bayansu dan yaga shigowarsu. Kai tsaye cikin ɗakin ya shiga shima.


   Saida ta haɗo mata Shayi mai kauri ta ɗauko Bread sannan ta nufo ɗakin, sai lokacin Idonta ya sauka kan su Mama dake Rakuɓe a gefe.


    "Oh! Kuyi Haƙuri An barku a tsaye ku ƙaraso ciki." Ta faɗa tana ƙarasa shiga ɗakin, Ba musu suma suka bi bayanta, shiga sukayi bakinsu ɗauke da Sallama.


    Har yanzu Mamyn na zaune inda take shi kuma yana tsaye yana ta bata baki amman batace komai ba. "Ga waɗanda keson Magana da ku na shigo dasu." Hajiya Ruƙayya ta faɗa tana Nuna su Mama.


   A lokacin itama Zulaihat ta turo ɗakin ta shigo,Zama tai tana yiwa Mamyn Sannu. Alhaji Bilyamin ne ya kallesu sannan yace.


   "Muna Saurarenku meke tafe daku." Ya faɗa yana maida Hankalinshi kansu, zama Mama ta gyara sannan ta soma faɗin. " Alhaji daman zuwa mukai muyi muku gaisuwa da tayaku Alhinin Abinda ya faru, Nice Mahaifiyar Ikleemaht yarinyar da ake zargi da kashe yaron wajenku, Daman Munzo Neman Alfarma ne akan ku taimaka ku janye Ƙarar da kuka shigar akanta, Wallahi Alhaji ƴata bazata iya Aikata kisan kaiba, Mu talakawa ne ba muda ƙarfin da zamu iya yin Shari'a daku,  kuma bamu da wanda zai iya Tsaya mana, Dan Allah Kusa a saki Ikleemaht ko waye ya aikata Laifin ma Allah bazai barshi ba dan Allah Alhaji da Hajiya."


    Ta ƙarasa faɗa tana durƙusawa kan gwiwowinta tare da Haɗa hannayenta guri huda Alamar Roƙo ga kuma idonta dake tsiyayar Hawaye.


    Wani irin Tausayin ta ne ya kamasu dukkansu, Nan Daddyn yace. "Ba'ba tashi,daga tsugun nan dan Allah, Za a sakar miki ƴarki insha Allah."


    Cike da jin daɗi tace." Dan Allah da gaske za a saketa.?"

   Kai  ya gyaɗa mata cike da ƙarfin Hali. Itama Mamy wata irin dauriya tare da tawakkali gami da dangana su suka dirar mata lokaci guda dan dattijuwar ta bata tausayi sosai, Sai yanzu bakinta ya buɗe, Cike da Jarumta itama tace.


   "Ki dena kuka mun yafe, Allah ya jiƙanshi yasa Halinshi na gari ya bishi."


    "Amin mungode Hajiya Allah ya....!"

   "Dena saurin godiya gyatuma!." Zulaihat dake binsu da wani irin mugun  kallo tin ɗazu ta katse Mama sannan taci gaba.


    "Akan me zaki zo ki marairai ce mana ki cucemu? Ƴarki ta Aikata wannan babban laifi kuma har kiyi tinanin Haƙuri  ya isa yasa A ƙaleta a ƙiyi mata Hukunci?. Ran mutum fa ta kashe ba dabba ba kuma duk mutane sun gani sun shaida amman kice musa a saketa.? Ta salwantar da ɗan babban mutum a garin nan ta rusa mana duk wani Farin ciki da jin daɗin Rayuwarmu amman har kiyi tinanin bamu haƙuri mu haƙura.? To Wallahi tin wuri ki cire a ranki cewar ƴarki zata tsira yadda ta kashe mana shi itama sai an binneta a ƙasa. 


   Me yasa tin farko baki tsaya kika bata Tarbiyya ba har ta taso da kwaɗayin son Abin duniya? Dan na tabbata wani ne ya bata kuɗi akan ta kashe mai shi shine ta aiwatar saboda son Abin duniya irin naku, daman ku Talakawan nan  bakusan komai ba sai son abin duniya makwaɗaita kaw....!


   "Ya isa haka Zulaihat!. Babbar mace haka kike faɗawa waɗannan maganganun? Wannan ko batai jika dake ba tayi ƴa dake, kar ɓacin rai ya sanya Hankalinki ya gushe mana.?"


   Mamy ta katse Zulaihat ɗin daga maganganun da take ta yaɓawa Mama. Cikin Kuka itama Zulaihat ɗin tace.


   "Wallahi Mamy Bazamu bar jinin Yaya Ammar ya zuba a banza ba, yadda ta kasheshi itama sai an kasheta, dan ko ku kun yafe ni bazan yafe ba, Wallahi a yau ɗin nan zanyi magana da Lawyer na akan wannan cest ɗin." tana gama faɗa ta juya ta fice a ɗakin tana sharar Hawaye.


   Gaba ɗaya bin bayanta sukayi da kallo cike da mamakin abinda tayi, Daddy ne ya maido da Kallonshi kan Mama dake sharar Hawaye yace.


   "Ba'ba kiyi haƙuri da Kalaman da yarinyar nan ta faɗa miki, Sam ba halinta bane Hakan, Zulaihat yarinya ce mai hankali da Nutsuwa da kuma haƙuri, ga kuma girmama na gaba da ita kawai Zafin Rashin mijin nata da tayi ne ya sanya har ta faɗa miki Hakan, Ku tashi kuje zamuyi magana da ita in ta huce."


    Kai kawai ta gyaɗa sannan ta fara ƙoƙarin miƙewa, Sadiya ƴar fillo ce ta kamata ta miƙar da ita tsaye suka fice, Zuciyar Sadiya kuwa tafarfasa kawai takeyi na Abinda Zulaihat tayi musu ji take kamar taje ta Rufeta da duka ko zataji daɗi.


   Ko a hanya ma bamai magana kowa da Abinda yake tinani,Abinda yafi tsayewa mama a rai shine Makwaɗaita masu son Abin duniya da Zulaihat da kirasu dashi, Yanzu duk yadda suka kai da Riƙe talaucinsu da tsayawa iya matsayinsu amman yau gashi An kirasu da waɗannan kalmomin. Maganar Sadiya ce ta katse mata tinanin data tafi.


    "Mama ki kwantar da Hankalinki insha Allah Zan ɗau Lawyer ɗin dazai tsaya mata, gobe insha Allah zanje har office dinshi na sameshi nayi mai bayani nasan zaitaimaka mana."


   "To Sadiya Allah ya taimaka ya shige mana gaba." Amin Amin." ta amsa, haka suka cigaba da tattauna Al'amarin har suka iso bakin layin, sauka sukai suka biyashi sannan suka shiga lungun, Kunce ƙullun gidan Mama tayi ta shiga gami dayi mata godiya sannan itama ta wuce nasu gidan.


   Tana tura get ɗin ta shiga, gabanta ne ya yanke ya faɗi ganin Mummyn nasu tsaye a ƙofar shiga cikin gidan."Daga ina kike." ta jefo mata tambayar. dabircewa tayi ta rasa me zata ce mata nan ta hau kame kame.


   "Yauma komawa kikayi inda nai miki kashen karki kuma zuwa ko? Ban ce karki saka kanki cikin wannan masifar ba shine zaki shiga. To wallahi bazaki jawo mana ba dan ko mu bazamu iya ja da gidan Alhaji Bilyamin Naira ba balle kuma su da talauci yai musu katutu, Dan haka daga yanzu ko bakin get bazaki kuma leƙowa ba balle fita kuma na ɗauke wayarki da kika jona a caji ko ita bazaki kuma ɗauka ba na ƙwaceta daga yau wuce ciki ki bani guri."


    Ta daka mata matsa, da sauri tazo ta shige ciki jikinta na ɓari, ita babban tashin Hankalinta da Mahaifiyar tata tace bazata kuma fita ba to yanzu taya Zata Haɗu da Lawyer ɗin da take shirin ɗaukarwa Leemaht ɗin???...........✍🏻





*Kamar yadda kuka gani tin farkon labarin, Wannan littafin na kuɗi ne akan Naira 200 kacal ga mai buƙatar cigaban wannan littafin har zuwa ƙarshe zai turo 200 ta wannan Accaunt ɗin👇🏼*

  *Fatima Umar First Bank 3178565252*


   *Sai kiyimin screen short in kin tura ki turomin in gani ta wannan Number 09036257038. In kin biya sai in sakaki a group ɗin kici gaba da karanta littafin BANI NA KASHE SHIBA.*



   *Ina Alfahari daku masoya na A duk inda kuke. NAGODE🥰*

*SUBSCRIBE*

_DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV_


https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ


*بسم الله الرحمن الرحيم*

 


        *😭BANI NA KASHE SHIBA*😭


           *Story and wrtten*

                      

                  *By*


       *FATIMA UMAR KAS*

                 *_(MUMMYN MIHAL_ )*


_Marubuciyar_👇🏼

*BAK'IN CIKIN KISHIYATA*

     *RAYUWAR MIHAL*

*ABINDA ALLAH YA NUFA*

    *SILAR ABAYA*

*'YA'YAN MIJINA NE*

     _AND NOW_

*BANI NA KASHE SHIBA*



*PAID BOOK*

 _(Littafin kud'i_) 



*LABARI MAI TAB'A ZUCIYA*😔

_ya k'unshi soyayya, tausayi, cin amana, hassada, munafirci_



*Dedicated to LEEMAHT pinky*💞



®🏝

 *ZAFAFA WRITTERS FORUM* ✍🏻


             

  *_Z• W• F•🏝_*



    *Gyara da kanki*


_Ayaba, kwakwa,madara pk. Zaki haɗesu duka kiyi blenɗing sai ki tace kisa madara kisha. Hmmm!._


🆓page


No.12 


   "Alhaji ka manta yadda duniya ta lalace yanzu? Sai a ɗauki ƙanƙanin kuɗi a bawa mutum akan anason ya kashe wani kuma ya kashe ɗin, Nima Dattijuwar matar taban tausayi sosai, Tabbas Akwai buƙatar a tsananta Binkice sosai dan gano ko su waye suka kashe mana shi. In ma ita ɗince to akwai dalili mai ƙarfi daya sanya ta Kashe shiɗin."


    "Kai!Bana tinanin yarinya ƙarama haka zata iya wannan babban gangancin. Tabbas Akwai Sarƙaƙiya cikin Wannan Lamarin. Zan je gobe can police station ɗin naji inda aka kwana a maganar. Sannan ita kanta akwai tambayoyin da nakeson yi mata."


   Cike da ƙwarin gwiya ya ƙarasa faɗa, itama ta gamsu dan Haka tace. "Inason Zuwa goben Nima in ga ita yarinyar, Sai muyi sammako kafin mutane su soma zuwa."


   "Shikenan Allah ya kaimu goben, da fatan dai kinci Abinci kinsha magungunanki."?


   "Eh Ruƙayya ta bani ɗazu nasha."


  "Shikenan to saida safen." ya faɗa yana miƙewa ya nufi ƙofa. "Allah ya tashemu Lafiya." ta Amsa mai, fita yai yaja mata ƙofar. Ita kuwa cigaba tayi da Lazimin da takeyi saidai Zuciyarta a Cunkushe take, Har yanzu bata daina jin zafi da Raɗaɗin kashe mata Yaron ta da akayi ba.


   Shi kanshi Alhaji Bilyamin daya kwanta Tinani ne danƙare a Zuciyarshi ya rasa meke yimai daɗi, Yana ɗaurewa ne kawai dan ya ƙarfafa musu gwiwa Amman a ganinshi duk wanda zaiji mutuwar nan bayan shine Haka tinane tinane suka Addabeshi suka Hanashi bacci ya matsu gobe tayi yaje Police station ɗin.


   Washe gari kuwa a falo suka Haɗu. ita Mamy ta fito ta tasoshi shima ya fito ya ce ta fito su wuce, yana kallon Idonta yasan taci kuka ta ƙoshi, ita ma Ganin idonshi yai ja kuma ya kumbura sai ta ɗauka shima yayi kukan. Baice mata komai ba ya juya ya fice.


   Itama Bayanshi tabi suka fita bayan tace da mai Aiki duk wanda yazo neman ta ace ta fita bazata jima ba zata dawo. A motar shi suka tafi can ɗin.


    Bayan sun isa a buɗe gurin yake dan Takwas ta kusa lokacin, Shiga sukayi ciki nan suka tarar duk yawancin Police ɗin sunzo kowa da Abinda yakeyi, suna ganinshi suka fara gaidasu. Amsawa yayi sannan yace.


   "D.P.O yana ciki ne?."

      "Eh yana ciki shima bai jima da Zuwa ba bari ayi mai magana." Wani ɗan sanda ya faɗa yana shigewa ciki.


     "Knocking yayi jikin ƙofar nan aka bashi damar shiga, turawa yayi ya shiga da sallama, saida ya ƙame ƙam! Alamar girmamawa sannan yace. "Yallaɓai kana da baƙi ne awaje sunzo gurinka."


    "Ok ba Matsala kace su shigo." ya faɗa yana cigaba da Abinda yakeyi. Kuma ƙamewa yayi sannan ya juya ya fice a ɗakin. Gurin su ya koma sannan yace. "Yace ku shiga ku sameshi a ciki."


   Miƙewa sukayi suka shiga office ɗin nashi, shi kuwa ganin sune saida ya miƙe tsaye sannan ya nuna musu gurin Zama, Cike da girmamawa suka gaisa, saida suka gama gaisawa sannan Daddy ya Nisa yace.


   "Daman munzo ne akan Cest ɗin yaro na da aka kashe, inason Ganin yarinyar da ake zargi akwai Tambayoyin da zanyi mata."


   Kai ya gyaɗa alamar gamsuwa sai kuma ya miƙe ya leƙa wajen, wani ɗan sanda ya kirawo, yana zuwa yace mai yaje yacewa Espector mudi yanason A fito da Yarinyar nan ya kawota nan gurinshi. Amsawa yayi sannan ya juya ya nufi wani corridor.


   Ba jimawa sai gashi sun taho dashi, har yanzu fuskar nan a turɓune take da Alama shi ba ma'abocin fara'a bane. Kai tsaye Cell ɗin yaje ya buɗe sannan yace ta taso. 


  Miƙewa tayi daƙyar dan jikinta gaba ɗaya yayi tsami. Haka ta taho jiri na ɗibarta Saboda yunwa ga kuma leɓenta daya bushe da Alama ko Ruwa baiga Bakinta ba.


   Kanta a ƙasa ta nufi inda ya nuna mata tana haɗa hanya, a baya ya bita har suka shiga Office ɗin D.p.o ɗin. Shima saida ya ƙame ya saramai sannan yace."Yallaɓai gatanan na kawo ta." kai ya gyaɗa sannan ya kalli su Mamy yace. "Ga Yarinyar nan.


   Ido Mamy ta zuba mata  tana Nazarinta, sai kuma ta maida idonta kan Uniform ɗin dake jikinta, ita kuwa ta sunkuyar dakai ta kasa ko ƙwaƙwƙwarar motsi, Alhaji Bilyamin ne ya katse shirun ta hanyar furta."Yarinya mene Sunanki." ɗagowa tayi ta kalleshi sannan tace.


    "Sunana  *Ikleemah B. Abubakar.*"


     "Ina mahaifinki yake."?


   "Mahaifina ya rasu Tsawon shekara guda kenan. Yanzu haka tare muke nida Mahaifiyata a unguwar Bubbugaje."


   "Mene gaskiyar Zargin da ake yi miki? Kiyi mana bayanin yadda Lamarin ya faru shin da gaske ke kika kasheshi da Ra'ayin kanki ko kuma wani ya sakaki Aikata hakan.?"


   Nan ta shiga girgiza kai Hawaye na silalo mata sannan tace."Wallahi Alhaji *BANI NA KASHE SHIBA* ni taimaka mai kawai nayi."


   "Kamar ya taimaka mai.?" Mummy ta jefo mata tambayar tana tsatstsareta da ido ganin tayi shiru. So take taga yanayin ta a yayin da zata bada Amsa. Hawayen idon nata ta goge sannan tace. 

   "A lokacin dana dawo daga makaranta ne ina shigowa cikin lungun namu shine na ganshi a ƙasa da Wuƙa a cikinshi shine na cire mai ita, bayan Haka babu abinda na Aikata."


   Shiru sukayi dukkansu, sai can tukunna Alhaji Bilyamin yace. "Kin tabbatar da abinda kika faɗa Hakane babu ƙarya a cikinshi.?" kai ta gyaɗa sannan tace. "Wallahi iya gaskiya ta na faɗa muku."


   "Maganar Banza maganar wofi, wannan ta shirya ƙarya ne kawai dan ta fitar da kanta, Amman ta yaya Za ai tace wai A haka ta ganshi itama taimaka mai tayi.? In har taimakon ne mai yasa bata kira hukuma ko wani a cikin unguwar ba dan yazo ya zame mata Shaida? Kuma Ai da mutane a cikin layin ya akai ba wanda yaga Sanda aka Ajiye gawar sai ita? Kawai tanason tayi wasa da Hankalin Hukuma ne shiyasa take wannan Marairaicewar ku barmu da ita in taji uwar bari zata faɗi gaskiya."


   "A'a Karkuyi mata komai ku ƙyaleta. Ai yaronmu ne aka yiwa Hakan ko? To mun yafe ku saketa ta tafi bazamu tsaya Shari'a da suba." mamy ta faɗa. Gaba ɗaya cike da mamakin Abinda Mamyn tace suka tsaya suna kallonta. Shima Daddy wani irin kallo yake yi mata yana ganin kamar baiji daidai ba. Sai can tukunna D.P.O ɗin ya gyara zama sannan yace.............✍🏻




-


*HILFAT*

*SUBSCRIBE*

_DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV_


https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ


*بسم الله الرحمن الرحيم*

 


        *😭BANI NA KASHE SHIBA*😭


           *Story and wrtten*

                      

                  *By*


       *FATIMA UMAR KAS*

                 *_(MUMMYN MIHAL_ )*


_Marubuciyar_👇🏼

*BAK'IN CIKIN KISHIYATA*

     *RAYUWAR MIHAL*

*ABINDA ALLAH YA NUFA*

    *SILAR ABAYA*

*'YA'YAN MIJINA NE*

     _AND NOW_

*BANI NA KASHE SHIBA*



*PAID BOOK*

 _(Littafin kud'i_) 



*LABARI MAI TAB'A ZUCIYA*😔

_ya k'unshi soyayya, tausayi, cin amana, hassada, munafirci_



*Dedicated to LEEMAHT pinky*💞



®🏝

 *ZAFAFA WRITTERS FORUM* ✍🏻


             

  *_Z• W• F•🏝_*



    *Gyara da kanki*


        _Ƴar uwa ki sami kankana ki yanka ta ƙanana ki zuba a kofi, ki kawo peak milk ta ruwa ki zuba, sai ki saka ruwan kanun fari da zuma cokali ɗaya kisha. Hmmmmm!_


🆓page


No.11


   Ita kuwa Mama ko da ta shiga cikin gidan ƙoƙarin dafawa leemaht ɗin wani abu ta soma dan tasan tin da aka kaita can bataci komai ba, ita ba ta kanta take ba dan har manta bata ci abincin bama take dan ba tashi take ba yanzu.


   Mai sauƙi ta samu ta girka mata sannan ta kuma kulle gidan ta fice. Kai tsaye station ɗin ta koma, tana shiga ta tarar dasu suna ta Aikace Aikacensu. Wata mace ta gani tana Rubuce Rubuce , gurinta ta nufa tai mata Sannu sannan tace.


    "Dan Allah Abinci na kawowa wacce ke tsare anan ko zaki taimaka ki miƙa mata.?" Kallonta tayi a raine sannan ta kalli kwanon Abincin gami da yatsina fuska tace. "Ki ajiye akan bencin nan za'a miƙa mata." Ba musu Ta ajiye ɗin kuwa. Ganin ta tsaya ne ya sanya tace.


   "Kije kawai za a kai mata." Ba tare da Tinanin komai ba ta juya jiki a saluɓe ta fice a cikin gurin. Daga nan kuwa bata  koma gida ba Napep ta hau ta nufi  gidan wani kawun Leemaht ɗin.


   A daidai get ɗin gidan aka sauketa, tana sauka ta miƙa mai Hamsin ɗin datai saura a hannunta ta tura get ɗin ta shiga. Taci sa'a kuwa tana shiga sai gashi ya fito da Alama fita zaiyi.


  Yana ganinta kuwa yai saurin haɗe rai kamar bashi ke murmushi ba yanzu. Ƙarasawa Mama tayi tana gaidashi kasancewar Yayan mai gidan tane.


   Amsawa yayi a takaice sannan yace."Meke tafe dake? da fatan dai ba wata buƙata kika zo min da ita ba."


  Sunkuyar dakai tayi sannan tace."Daman akan maganar Ikleemah ce da ƴan sanda suka kama akan zargi, naga ba wanda yai maganar a cikin ku balle kuje can ɗin inda aka tsareta shine nazo inji ko bakusan me ya faru ba."


    "Ni kuwa nasan me ya faru dan tin lokacin na samu labari hasalima har gurin naje, to yanzu ni mene nawa a ciki Tsuntsun daya ja Ruwa ai shi ruwa kan doka, ni babu ruwa na acikin wannan Maganar karma ki sakoni aciki."


 Ya faɗa yana Nufar motarshi. Cikin sauri Mama ta tareshi da faɗin. "Dan Allah kar kuyimin Haka, in kuka zame kuka barni ciki Abin zai yimin yawa bazan iya ɗauka ba. A yanzu fa Ikleemaht bata da kowa sai ku kune dolenta tinda kune dangin mahaifinta, taya zan iya da wannan Al'amarin ni kaɗai nifa macece ina da Rauni, dole muna buƙatar Namiji a cikin wannan Ƙaddarar data faɗo mana. Dan Allah ku taimaki Ikleemaht a yanzu bata da wasu iyaye bayan ku."


   "Au! Sai yanzu kikasan mu iyayenta ne mun isa da ita? Sanda mukeson tanƙwarata tayi abinda mukeso ai ke kika ɗaure mata gindi ta bijire mana, tin yaushe naso Aurar da ita amman duk wanda na zaɓa mata sai ta bijire bata sonshi kuma ki goyi bayanta, Sannan sau nawa muka so Amsar ta bayan Rasuwar mahaifinta amman kika ƙi bamu ita saboda bamu da daraja a gurinku? Sai yanzu da taje tai Aika Aika sannan zaki nufo gurinmu wai muje musa baki. To wallahi babu inda zanje karki sake ma ki sakani cikin wannan maganar, kuma karki kuma takowa nan da sunan wai kinzo neman taimako dan bazan taimaka ba. Sanda naso ta taimake ni nima ai ƙi tayi."

   


   Yana gama faɗa ya faɗa motar tashi ya tasheta ya fice agidan. Nan yabar Mama tsaye tana mai binshi da kallo har ya fice. Jiki a sanyaye ta juya ta fita itama.


   Koda ta fita ma gidan ɗaya Ƙanin mai gidan nata ta nufa, sai dai shima kusan Abinda ya faru a inda ta soma zuwa shiya faru, dan shima tin tini yaso Haɗa Leemaht ɗin da yaron wajenshi amman ta ƙi kasancewar yaron  yana shaye shaye kuma kowa yasan hakan, tin daga nan suma kejin Haushinsu.


   Haka shima ta baro gidan jiki a saluɓe, daga Nan gida ta koma, gaba ɗaya ƙafafunta Rawa kawai sukeyi saboda gajiya dan taci tafiyar ƙasa sosai gashi bata samu abinda taje nema ba. Abu ɗaya ke ɗan ƙarfafa mata gwiwa in ta tina Sadiya fillo zata taimaka musu kuma zata  ɗauka musu lawyer.


.....

A can kuwa Haka aka cigaba da zaman makoki wasu na fita wasu na shiga. Mamy ma ta ɗan samu ta fito falon ana karɓar gaisuwa, yawanci duk wanda yazo sai ya shigo yayi musu gaisuwa kana ya koma wajen.


  Ana Haka wasu maza biyu suka shigo suna Rizgar kuka kamar zasu shiɗe, gaban daddy sukazo suka zube suna cigaba da kukan, shi kuwa kansu kawai yake shafawa alamar Rarrashi, mutanen wajen kuwa Haƙuri aka shiga basu dan da Alama suma mutuwar ta dakesu, sai can tukunna ɗaya ya tsagaita da kukan sannan ya soma magana.


  "Allah sarki Abokinmu mutuwa ta Rabamu dakai a sanda bamu zata ba, mutuwa mai yankan ƙauna, Ashe ganin ƙarshe mukayi maka shekaran jiya.? Tabbas munyi Rashin Aboki na gari Abokin dake Rufa mana Asiri, Allah ya jiƙanshi da Rahama."


   "Ameen!." aka Amsa, shima ɗayan cewa yai. "Tabbas mutuwar Ammar Ammar ta dakeni dan Lokaci ɗaya naji mutuwar tashi, Allah yasa ya huta." ya ƙarasa faɗa yana matsar ƙwallah. Da Amin nan ma aka Amsa.


    "Bari mu shiga muyiwa su Mamy gaisuwa." suka faɗa suna miƙewa dan shiga ciki."  cikin falon danƙam yake da mutane hakan ne ya sanya suka tsaya a bakin ƙofar, dubawa suke ko zasu hango Mamyn Amman basu gano taba, Hakan ne yasa suka juya suka fice  zuwa wajen. Zama sukayi suma ana cigaba da karɓar gaisuwa.


   Sai yamma liƙis sannan  mutane suka ɗan Rarragu. Da yawan mutane sai da sukai kukan Rashin Shi musamman waɗanda kecin abinci a ƙasanshi. Duk wanda zai buɗi baki saidai ya faɗi Alkairi a kanshi kuma yace Allah ya toni Asirin waɗanda suka kasheshi.


    Ƴan jaridan da suka Nace suka ƙi tafiya ana suka ɗan samu waɗanda suka tattauna dasu akan wanda aka kashe ɗin, saidai ko mutum ɗaya a iyalen gidan basu samu magana dashi ba.


    Sai magriba aka Naɗe tabarmi aka shigar ciki, a lokacin ne Shima Daddy ya samu shiga cikin gidan dan duk an tattafi. Kai tsaye ɗakin Mamy ya shiga. Idar da Sallahr ta kenan tana lazimi ya shigo. Guri ya samu ya Zauna har ta shafa Adduar.


  "Ya jikin naki?." ya tambaya. "Da sauƙi". Ta bashi Amsa. Ajiyar Zuciya ya sauke Sannan yace. "Ɗazu  Yaran nan sun bani tausayi Matuƙa yadda suka dinga kuka saida suka taɓamin Zuciya."


    "Waɗanne yara kenan?". Mamy ta Tambaya, "Yaran nan Abokan Marigayi mana MA'ARUF da MARWAN, kinsan Akwai Shaƙuwa mai ƙarfi tsakaninsu daman. Sun karyawa kowa zuciya Wallahi. Ai sun shigo Nan ma ko?."


    Ya ƙarasa faɗa cike da Rauni, girgiza kai tayi sannan tace."A'ah bangansu ba kasan falon a cike yakene."


    "Eh to wataƙil sun shigo da sukaga mutane suka koma. Nifa Akwai abinda ke ɗan damuna tin ɗazu. maganar kisan Yaron nan. Gaskiya Yarinyar da aka Nunamim a matsayin ita tayi kisan ban gamsu ba, dan daga yanayin ta kaɗai dana gani na fuskanci ba ita bace. Sannan data kalleni iya gaskiya na Hango a idonta banga Saɓanin Hakan ba. Saidai tayaya Jinin yazo jikinta wuƙar ma ta kasance a Hannunta? Shiyasa da Mahaifiyarta  tazo ɗazu nace mun yafe dan Na fuskansu su ɗin suna da Rauni sosai."


   Itama Mamyn Ajiyar Zuciya ta sauke mai ƙarfi jin An taɓo mata inda keyi mata ƙaiƙayi Nan tace..........!✍🏻




*HILFAT*

*SUBSCRIBE*

_DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV_


https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ


*بسم الله الرحمن الرحيم*

 


        *😭BANI NA KASHE SHIBA*😭


           *Story and wrtten*

                      

                  *By*


       *FATIMA UMAR KAS*

                 *_(MUMMYN MIHAL_ )*


_Marubuciyar_👇🏼

*BAK'IN CIKIN KISHIYATA*

     *RAYUWAR MIHAL*

*ABINDA ALLAH YA NUFA*

    *SILAR ABAYA*

*'YA'YAN MIJINA NE*

     _AND NOW_

*BANI NA KASHE SHIBA*



*PAID BOOK*

 _(Littafin kud'i_) 



*LABARI MAI TAB'A ZUCIYA*😔

_ya k'unshi soyayya, tausayi, cin amana, hassada, munafirci_



*Dedicated to LEEMAHT pinky*💞



®🏝

 *ZAFAFA WRITTERS FORUM* ✍🏻


             

  *_Z• W• F•🏝_*



    *Gyara da kanki*


_Aya, gyaɗan mata, pick ta ruwa, mazar ƙwaila._

  _Zaki haɗesu duka kiyi blending sai kisha._


🆓 Page


No.13


   "Hajiya Ai koda kun yafe akwai Haƙƙin shari'a akanta na kisan Rai. Bazai yiwu abar maganar ba, mu tini ma muka tura maganar zuwa kotu, zamu cigaba da tattara bayanai har Allah ya kaimu ayi Sadakar Bakwai ɗin  yaron washe gari za'a fara sauraren ƙara."


    Ajiyar Zuciya mai ƙarfi Mamy ta sauke tana gyaɗa kai Saidai ita ba Haka taso ba. Alhaji Bilyamin ne yace. "Shikenan To Allah ya kaimu Lokacin da rai da Lafiya, saidai ya kamata ku ƙara zurfafa Binkice dan gano gaskiyar Al'amarin."


   "Insha Allahu Alhaji." Cewar espector mudi. Tashi sukai da Niyyar tafiya, a lokacin shima D.p.o ɗin yace a maidata inda take, juyawa tayi dan bin bayan ɗan sandan daya juya ya fice. Tana ɗaga ƙafarta jiri ya kwasheta ta faɗi a ƙasa.


   "Subhanallah!." Mamy da Idonta ke kanta ta furta, da sauri taje ta ɗagota tana mata Sannu. Kai kawai ta ɗaga sannan ta kuma yunƙurin tafiyar, wata Hajijiya ce ke shirin kuma kayar da ita. Da hanzari ta kuma tare ta. "Kinci Abinci kuwa.?" ta faɗa tana ƙarewa fuskarta kallo. Ita kuwa girgiza kai tayi alamar A'a. "Ruwa fa?." ta kuma tambayarta ganin yadda Bakinta ke bushe, shima girgiza kai tayi. Ƙarƙarfar ajiyar Zuciya Mamy ta sauke tana kallon Expector mudi sannan tace.


    "Wai daman in mutum na tsare anan ko Ruwan sha baku bashi.? Kalli fa yadda jikinta ke rawa ga jiri da takeyi saboda yunwa, yanzu in ta mutu a haka me zaku cewa Allah.? Ai ko me ta Aikata bazaku barta baci ba sha ba." Mamyn ta faɗa Rai a ɓace.


   "Ayi Haƙuri Hajiya ba Laifin mu bane, laifin mahaifiyar ta ne tinda har yau bata taɓa kawo mata komai ba, ta zazzo gurin nan amman ko sau ɗaya bata kawo mata komai ba. Mu kuma bamu da abinda Abincin da zamu bata anan."


   "Mahaifiyar ta bazata ƙi kawo mata wani Abu da gangan ba saidai in ta Sha'a fane. Ga wannan in masu Abinci sun fito a siyo mata a bata taci haka Ruwa ma."


   Ta faɗa tana zuge jakarta ta fito da kuɗi ta miƙamai. Zuruf ya Amshe yana godiya kamar shi aka bawa."


   "ya kamata mu koma gida fa yanzu dan Nasan mutane nacan suna jiranmu.".Alhaji Bilyamin ya faɗa. "Shikenan muje." Ta faɗa tana bin bayanshi ganin ya fice. Da kallo itama Leemaht ɗin tabi bayan Mamy tana ganin ƙimar matar a idonta na taimakon data yi mata yanzun.


   "Muje to." ya Katse mata tinanin data tafi. Juyawa tayi tana dafa bango suka  fice a office ɗin. "In ka maidata kazo inason Magana dakai." D.P.O ya faɗa. Kai Expector mudi ya jijjiga alamar Alamar amsawa sannan suka fice.


   Saida ya maidata ya mayar da wajen ya kulle sannan ya koma kiran daya yimai. Tura office ɗin yayi ya shiga da sallama, ƙamewa yayi a tsaye saida  ya bashi ikon zama sannan ya Zauna. Shima Hankalinshi ya maida kanshi kanshi sannan yace.


    "Kamar yadda iyayen Yaron nan suka Nemi mu ƙara tsananta binkice ya kamata a ƙaraɗin. Dan gaskiya maganar yarinyar nan akwai ƙamshin gaskiya a ciki. Inason ka maida Hankalinka kan Aikinka. Dan na fuskanci baka fiya tsananta binkice ba kafi gane Azabtar da mai laifi. Inason  Ka ɗebi ma'aikata ku koma unguwar tasu inda akayi kisan ku kuma binkitawa". Cike da girmawa yake Amsawa. "Kuma kamar yadda Hajiya tace a dinga sai mata Abinci to kullum ka dinga sai mata. Na baku daga yau zuwa gobe ku kawomin abinda kuka gano a binkicen naku."


   "Insha Allah ƴallaɓai." ya Amsa, bashi damar tafiya yayi nan ya juya ya fice daga   Cikin office ɗin. Yana fita shima yaci gaba da abinda yakeyi.


......

  Su kuwa su Mamy suna tafiya a hanya Ya kalleta sannan yace. "Me yasa Kikai saurin cewa mun yafe mun janye Shari'ar da za'a gabatar? Karfa ki manta gudan jinin mu tilon ɗanmu aka salwantar mana da Rayuwarshi  amman sai mubar jinin shi ya zuba a banza.? Ammar ɗinki fa!Ammar fa!." Runtse idonta tayi da ƙarfi tanajin yadda ƙirjinta ke bugawa, Adduo'i ta soma yi a fili take taji ɗan sanyi a zuciyarta, buɗe idonta tayi sannan cike da Rauni tace.


    "Jinin Ammar bazai zuba a banza ba, domin ko ba'a yiwa wanda ta kasheshi Hukunci a nan ba za'ayi mai a Ranar gobe ƙiyama. Jiki na ya riga ya bani ba Yarinyar nan bace ta Aikata Laifin, domin kana kallon yanayin ta zaka fuskanci bata Aikata ba, duk maganganun da take faɗa iya gaskiya nake Hangowa a idonta, babu wani Alamun Rashin gaskiya da suka bayyana gareta, Sannan ka duba ka gani Uniform ne jikin ta na Islamiyya taya zatayi kisan kai dasu jikinta kuma a unguwarsu.?"


   Ta faɗa tana kallonshi, Shiru yayi Yana saurarenta, tabbas maganar ta abar dubawa ce dan duk abinda ta faɗa Hakanne, cike da gamsuwa yace.


   "Allah dai ya kyauta in anje kotu ko mene ma zai bayyana gaskiya zata fito." Shiru Mamy tayi saidai a Zuciyarta ta gama yanke abinyi. A haka suka ƙarasa gida. 


  Yauma gidan cike yake da Jama'a, Shigowarsu ta sanya aka shiga yi musu gaisuwa, Shi anan ya zauna ita kuwa Mamy ciki ta shige kai tsaye. Bata zauna a gurin ba kawai ta wuce Zuwa ɗakin ta. Hajiya Ruƙayya ce tabi ɓayanta. A zaune ta tarar da ita ta zuba uban tagumi."


    "Yaya ya jikin naki." ta cewa Mamyn. Kai kawai ta gyaɗa mata. Ganin kamar batason magana ne ya sanya ta juya ta fice ba tare da tayi mata Tambayar inda taje ba.


.....

Yau Akayi Adduar Ukun marigayin, A safiyar ne kuma Jami'an tsaro suka cika unguwar Bubbugaje suna gabatar da Binkicensu, duk Mazan unguwar saida suka tara suna yi musu tambayoyi. Sun ɗan samu wasu Amsoshin sannan suka tafi.


    Mama kuwa Abin duniya duk ya taru yai mata yawa, dan tin Ranar da suka Rabu da Sadiya akan zata ɗauka musu Lawyer har yau bata kuma ko ganinta ba, ƙarfin gwiwar data,samu a da yanzu duk ya gudu, gaba ɗaya jikinta ya mutu ganiin basu da wani mataimaki sai Allah, saidai duk da Hakan kullum cikin faɗawa ubangiji Halin da suke ciki take, tana Roƙon ya kawo musu Mafita........✍🏻

*SUBSCRIBE*

_DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV_


https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ


*بسم الله الرحمن الرحيم*

 


        *😭BANI NA KASHE SHIBA*😭


           *Story and wrtten*

                      

                  *By*


       *FATIMA UMAR KAS*

                 *_(MUMMYN MIHAL_ )*


_Marubuciyar_👇🏼

*BAK'IN CIKIN KISHIYATA*

     *RAYUWAR MIHAL*

*ABINDA ALLAH YA NUFA*

    *SILAR ABAYA*

*'YA'YAN MIJINA NE*

     _AND NOW_

*BANI NA KASHE SHIBA*



*PAID BOOK*

 _(Littafin kud'i_) 



*LABARI MAI TAB'A ZUCIYA*😔

_ya k'unshi soyayya, tausayi, cin amana, hassada, munafirci_



*Dedicated to LEEMAHT pinky*💞



®🏝

 *ZAFAFA WRITTERS FORUM* ✍🏻


             

  *_Z• W• F•🏝_*



    *Gyara da kanki*


_Kaninfari minannas,Dabino._

  _Zaki haɗesu duka a turmi ki daka su sai ki tankaɗe, zaki dinga sha da madara pick._


🆓page


  No.15


         *KOTU*


Kotun a cike take maƙil tayi danƙam da mutane, tin daga Harabar kotun zuwa ciki. Ƴan jarida kuwa sai turereniya sukeyi kowa nasan ya ɗauki rahoto. A lokacin ne kuma motar da aka kawo Leemaht ta tsaya a gurin. Wata ƙatuwar mota ce da ƙofa a cikinta an kulleta ta ciki banda mutum biyu dake zaune a ƙofar suna gadi. Motar na tsayawa aka buɗe gurin, a lokacin ne ta fito hannayenta sanye cikin Ankwa, da ƙyar ta iya sakkowa daga motar saboda tana da ɗan tsayi ita kuma jikinta sam ba ƙwari.


   Fitowarta ya sanya ƴan jarida yi mata caaaa! A ka, kowa da Abinda yake tambayarta, ita kam sam taƙi yarda ko fuskarta ta ɗago balle aga fuskarta, Haka jami'an tsaron suka dinga ture mutane suna samun hanya har suka wuce cikin kotun. Nan kuwa akabi bayansu yuuuu! Har ciki.


   Kai tsaye inda ake tsayar da waɗanda ake tuhuma aka shigar da ita, hayaniya ake tayi saida Alƙali ya bubbuga guduma sannan kotun tai tsit. 


  Wani dake ƙasan inda Alƙali ke zaune ne ya miƙe da wata takadda a hannunshi sannan yace.              "Ayau zamu saurari shari'a ne akan kisan ɗan gidan Alhaji Bilyamin Naira wanda aka kashe a ranar juma'a ta hanyar luma mai wuƙa a cikinshi. Ga kuma wacce ake zargi tsaye a gaban kotu". Tini kotun ta kuma kaurewa da Hayaniya kowa na faɗar Albarkacin bakinshi, yanzu ma gudumar Alƙali ya bubbuga sannan akayi shiru.


   Juyawa yayi ya miƙawa Alƙali Takaddar, miƙo hannu yayi ya karɓa ya duba. Alƙalin ne ya maida Hankalinshi kanta sannan ya soma magana ta hanyar furta.


   "Malama Ikleemah kinji zargin da aka karanta miki.?"


    "Eh naji ya mai girma mai shari'a."


  "To me zakice game da zargin kin aikaata laifin ko baki Aikata ba."?


   "Ban Aikataba yamai girma mai shari'a. *BANI NA KASHE SHIBA*."


    "Kinsan shine daman."?


   "Bansan shi ba Ranar na fara ganinshi shima cikin mawuyacin Hali taimaka mai kawai nayi."


 Sunkuyar da kanshi yayi yai rubuce rubuce sannan ya ɗago yace. "Ko Lawyern masu ƙara yana da tambayar da zaiyiwa Ikleemah.?"


   Miƙewa wani Marashi dake sanye da shigar lauyoyi  yayi sannan yace."Eh ina da ita ya mai girma mai shari'a."


  "Kotu ta baka dama."

Alƙalin ya faɗa. Godiya yayi sannan ya juya yana mai fuskantar ta yace.

   "Ikleemah kin taɓayin kisan kai."?


   Ɗagowa tayi ta kalleshi sai kuma ta kalli dandazon mutanen dake cikin kotun, anan ta hango Mama da Sadiya da iyayenta sai sauran ƴan unguwar tasu, gefe kuma Ƴan makarantar sune suma tsaye kowanne fuskarshi cike da damuwa.

  


   "Ina tambayarki kinyi shiru nace kin taɓayin kisan kai." maganar lauyan ta maido ta tinaninta, girgiza kai tayi sannan tace.


   "Ban taɓa ba, ni ko dabba ban taɓa kashewa ba balle mutum."


    "Wannan shine karo na farko da kika taɓayin kisa kena...!"


    "Objection my Lord. Mai tambaya yana nuna kamar itace tai kisan Alhali tuhumarta akeyi har yanzu ba a tabbatar ba."


    "Barrister Leerwan ya faɗa."


   "Ƙorafi ya karɓu, lauyan masu ƙara ka gyara kalamanka." Alƙalin ya faɗa. Kai ya gyaɗa sannan ya kuma juyawa yana kallonta yace.


    "A wannan Rana mutane da yawa sun ganki sanda kika ciro wuƙar, dan da yawa sun ɗauka a wayarsu, kuma wanda ya fara ganinki a lokacin ɗan unguwar kune, sannan har jami'an tsaro suka iso gurin baki ajiye wuƙar ba Anyi haka ko ba a yi haka ba."?


     "Anyi hakan amman...!"


   "Iya abinda na tambayeki kenan." ya katseta. "Objection my lord, mai tambaya ya karya dokar kotu gurin katse wacce ake tuhuma yayinda take bada Amsa."


   "ƙorafi ya karɓu,Barrister Yusuf ka kiyaye. Ikleemah cigaba da Bayaninki. " Alƙali ya faɗa.


   Wani kallo ya juya ya makawa Barrister Leerwan sannan ya juya gurinta jin taci gaba.


   "Eh mutane sun ganni da wuƙa a Hannuna,Amman ni kawai na cire mai itane dan ceton Rayuwarshi amman *Bani na kashe shiba* saidai lokacin dana shigo cikin lungun namu naga wata mota ta fita da gudu daga cikin layin." shiru ta kuma yi ƙanta a ƙasa. Juyawa Barrister Yusif yayi gurin mai Sharia sannan yace.


    "Ya mai girma mai shari'a inason kotu tai Nazari a kan maganar data faɗa na cewa wai taga wata mota ta fita a lungun, wannan magana ƙanzon kurege ce kawai tana son ɓatawa Kotu lokaci ne bayan kotu nada wasu shariar da zata saurara bayan wannan. Tanason yin Amfani da wannan damar dan ta zame kanta daga tuhuma shiyasa tace taga wata mota ta fita a lokacin saboda ai tinanin na cikin motar ne yai kisan ya gudu. Bayan mutane duk sun shaida ita suka gani haka wuƙar ma da aka Auna shatin yatsu yatsunta ne suka fito raɗau akan wuƙar.Dan haka nake Roƙon wannan kotu mai Adalci ta yanke mata Hukunci daidai da Laifin data Aikata, Nagode ya mai girma mai shari'a.


   Ya faɗa yana komawa ya zauna. Rubutu Alƙali ya yayi sannan ya kuma ɗagowa yace. "Ko lauyan wacce ake zargi yana da magana.?"


     Miƙewa Barrister Leerwan yayi sannan yace. "Eh akwai ya mai Sharia."


   "Kotu ta baka dama."

"Nagode." ya faɗa yana matsawa gabanta sannan yace."


   "A lokacin da kika cire mai wuƙar yayi motsi ne.?"


   "Eh yayi motsi lokacin kana daga baya jikinshi ya saki."


    "Kafin ki kai ga  cire mai wuƙar akwai wanda ya ganki ne?."


  "Gaskiya Bansani ba ko wani ya ganni saboda a lokacin Hankali na ya tafi ga son taimaka mai ne, ganin jinin ya tadamin Hankali sosai hakan ne ya sanya bansan sanda mutane suka cika gurin ba har saida naji saukar mari a fuskata sannan Hankali na ya dawo jikina."


    Kai ya gyaɗa alamun gamsuwa sannan ya juya gurin Alƙali yace. "Ya mai girma mai shari'a wannan bayanin kaɗai ya isa ya gamsar da kotu Leemaht ba ita tai kisan ba, ganin ta da wuƙa bashi ke nuna ita ta kashe shiba.mahaifiyar Leemaht da sauran ƴan makarantarsu sun tabbatar da Leemaht hatta ƙadangare tsoronshi takeji haka ko ɓera bata taɓa gwada kashewa ba, sannan a binkicen da nayi na gano Mamacin ada duk inda zaije yana tare da masu tsaronshi baya fita shi ɗaya, Amman gashi a ranar da aka kasheshi baya tare dasu shin su suna ina har aka kasheshi basu sani ba.? Dan Haka nake roƙon wannan kotu data sa azo da waɗannan excort ɗin nan dan su Amsa tambayoyi a gaban kotu. Nagode mai shari'a."


   Ya faɗa yana komawa ya zauna, yanzun ma rubutun Alƙalin ya kuma yi, sai can tukunna ya ɗago sannan yace........✍🏻





_Comment and share pls_

*SUBSCRIBE*

_DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV_


https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ


*بسم الله الرحمن الرحيم*

 


        *😭BANI NA KASHE SHIBA*😭


           *Story and wrtten*

                      

                  *By*


       *FATIMA UMAR KAS*

                 *_(MUMMYN MIHAL_ )*


_Marubuciyar_👇🏼

*BAK'IN CIKIN KISHIYATA*

     *RAYUWAR MIHAL*

*ABINDA ALLAH YA NUFA*

    *SILAR ABAYA*

*'YA'YAN MIJINA NE*

     _AND NOW_

*BANI NA KASHE SHIBA*



*PAID BOOK*

 _(Littafin kud'i_) 



*LABARI MAI TAB'A ZUCIYA*😔

_ya k'unshi soyayya, tausayi, cin amana, hassada, munafirci_



*Dedicated to LEEMAHT pinky*💞



®🏝

 *ZAFAFA WRITTERS FORUM* ✍🏻


             

  *_Z• W• F•🏝_*



    *Gyara da kanki*


_Ki samu zogale ki shanya ya bushe sai ki daka shi ki riƙa sha da madarar ruwa ko ta gari_


🆓page


No.16


Ɗagowa Alƙalin yayi sannan yace. "Kotu ta saurari dukkan jawaban da aka gabatar a gabanta dan Haka kotu ta  ɗage wannan zama sai nan da ɗaya ga watan da zamu shiga sati na sama kenan za a dawo dan cigaba da saurarar wannan ƙarar, Saidai za a cigaba da Tsare Ikleemaht har zuwa ranar da za a dawo Sharia, Sannan Kotu tana umarnin a zama na gaba azo da Excort ɗin dake tsaron marigayin da kuma sakamakon gwajin yatsu da aka ce anyi." ya ƙarasa  faɗa yana buga gudumar Hannunshi kan bencin dake gabanshi.

 

  "Kotuuuuuuuu!."

Jama'ar gurin suka faɗa sannan suka fara miƙewa dan fita daga ciki. Su mama na tsaye a waje sukaga an kuma fito da ita an tisa ƙeyarta zuwa motar data kawo ta.


     Tini Zuciyar su ta kuma karyewa ba kamar Ƙawayenta na makaranta dan su kuka suke sosai na tausayin Halin da Ƙawar tasu take ciki, ganin uniform ɗin jikinta shi ke kuma karya musu zuciya. Mama idanunta nakan ƴar tata, wani irin tausayinta ne ke ratsa ko ina na jikinta ganin yadda tabi ta lalace tai baƙi ƙirin ga kuma wasu ƙuraje duk a fuskar tata banda uwar Ramar data zabga sai idanu.

    Maganar da akayi a kusa da ita ita ta maido ta tinanin data tafi. Tana waigowa,suka Haɗa ido da Sadiya ƴar fillo itama idonta cike taf da hawaye.


   "Mama Sannu." Sadiyan ta faɗa cike da tausayin Mama ganin yadda idanun Maman suka ƙanƙance sukai ja da Alama sun fara yi mata ciwo ma. "Yawwa Sadiya." tai ƙoƙarin furtawa.


    "Dan Allah Mama kiyi Haƙuri na rashin jina tin ranar da muka rabu. Wallahi fitar ce bana samun damar yi kwata kwata gashi wayana bata Hannu na balle nayi magana da Barrister ɗin dana faɗa miki. Saidai kullum ina saka ku cikin Addu'ata. Amman naji daɗin ganin Ashe kin samu  Wanda ya tsaya mata. Allah ya taimaka."


    "Amin amin Sadiya. Ni kaina bansan wanda ya ɗauka mata Lawyer ɗin da zai kare taba, dan ko da yaje gurina na zaci ke kika turashi saida na tambayeshi yace ba ke bace, kuma ba'a bashi damar ya faɗi wanda ya ɗaukeshi ba, ubangiji ne ya dubi zuciyarmu shiyasa ya turo mana dashi dan ya taimakemu, Allah dai yasa muyi Nasara." 


   Ta ƙarasa faɗa tana goge Hawayen idonta, Sadiya na shirin magana Mahaifiyarta ta iso gurin. Tana zuwa tace. "Ke daman kina nan muna ta nemanki wuce mu tafi."


    Ba musu ta juya tabi ta tana waigen Mama, itama bin bayansu tayi da kallo a ranta tana Ayyana yawancin ƴan unguwar tasu tsegumi ne ta kawo su kotun dan tin faruwar abin babu wanda ya leƙa da sunan tayata Alhini amman yau gasu duk sunzo kotun, Hatta dangin mahaifin Leemaht ɗin sunzo da iyalensu suma ana gama shariar sukai tafiyarsu ko ta kanta basu biba kuma sun ganta. Ajiyar zuciya ta sauke gami da kawar da kanta daga garesu. tana waigawa gefe ta Hango Barrister Leerwan yana shirin shiga motar shi.


   Da sauri taja ƙafafuwanta da suka mata tsami ta isa gurinshi. "Ɗana." ta kira sunanshi. Yana shirin shiga motar ya ji maganar. Dakatawa yayi sannan ya juyo. Ganin Mama yasa ya ɗan duƙa yana gaidata. Cike dajin daɗi take Amsawa nan ta ƙara da faɗin.


   "Barrister Mungode fa Allah ya biyaka yasa ka gama da duniya lafiya."


  "Amin amin Mama ba komai ku dai ƙara dagewa da Addu'a akan lamarin nima zan yi iya yina dan ganin ta kuɓuta."


    "Insha Allah." Maman ta faɗa tana gyaɗa kai alamar gamsuwa, Sallama yayi mata ya juya ya shiga motar tashi ya tasheta, ta ɗan samu ƙarfin gwiwa jin maganar Barrister ɗin.


   Tana nan tsaye har motar da aka sanya Leemaht ɗin ta ɓacewa ganinta, A lokacin duk mutane sun watse sai ƴan tsiraru, Haka taja ƙafafuwanta dake mata ciwo ta tafi, 


   Kwanan nan sun matsa mata da ciwon kasancewar zirga zirgar da take tasha, gashi maganin da take sha shima ya ƙare kuma babu kuɗi a hannunta balle tasai wani. Dan wankau ɗin da take ɗanyi  take samun wanda suke rufawa kansu Asiri yanzu  bata da Kwanciyar Hankalin da take samun damar yi.  Haka taci gaba da Tafiyar tanayi tana Hutawa a hanya dan da ɗan tazara tsakaninsu.


.......

Su Mamy kuwa tinda suka fito a kotun jikinta ke a matuƙar sanyaye dan yau Shariar ta taɓa mata zuciya kuma ta tina mata tilon ɗan nata data rasa lokaci ɗaya, tin a kotun take fakar idon mutane tana share Hawayen dake silalo mata. Yanzun ma suna tafiya Daddy ne dake lura da yanayinta tin ɗazu ya maida kallonshi kanta sannan yace. "Kinsan dai Kinada Hawan jini kuma ciwonki bayasan damuwa amman naga kina son dawo da Tinani cikin ranki. Kefa da bakinki kikace kin yafe kar ma ayi shari'ar, amman gashi yau duk kin ɗaga Hankalinki naga ma har kuka kikayi ɗazu. Gaskiya in haka zaki dingayi saidai ki dinga zama a gida na ɗinga faɗa miki yadda akayi."


   Ƙarƙarfar Ajiyar Zuciya Mamy ta Sauke sannan tace."Kamar yadda nace na yafe to har a zuciyata Hakanne, mudai yanzu tinda har an fara Sharia saidai mu zubawa Sarautar Allah ido muga abinda zai hukunta. Nikam akwai abinda ya ɗan dameni a raina magana ce ban yiba, Nifa tin Ranar da Nake Asibiti da naga *AMIR* har yau ban kuma ganinshi ba. Ko a kotun nan ma naga duk sauran Abokan nasu sunzo amman shi ban ganshi ba."


    Shima Daddyn ɗan tinani yayi sannan yace."Nima fa nayi wannan tinanin dan nima rabona dashi tin Ranar da aka kai Marigayi makwancinshi ban kuma sakashi a ido naba har akayi zaman makoki aka ƙare bai zo ba su  Safwan kuwa kullum dasu muke karɓar gaisuwa."


    "A'ah! To shi ina ya shige yana ina kenan?." Mamyn ta faɗa.........✍🏻



  _Comment and share pls_

*SUBSCRIBE*

_DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV_


https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ


*بسم الله الرحمن الرحيم*

 


        *😭BANI NA KASHE SHIBA*😭


           *Story and wrtten*

                      

                  *By*


       *FATIMA UMAR KAS*

                 *_(MUMMYN MIHAL_ )*


_Marubuciyar_👇🏼

*BAK'IN CIKIN KISHIYATA*

     *RAYUWAR MIHAL*

*ABINDA ALLAH YA NUFA*

    *SILAR ABAYA*

*'YA'YAN MIJINA NE*

     _AND NOW_

*BANI NA KASHE SHIBA*



*PAID BOOK*

 _(Littafin kud'i_) 



*LABARI MAI TAB'A ZUCIYA*😔

_ya k'unshi soyayya, tausayi, cin amana, hassada, munafirci_



*Dedicated to LEEMAHT pinky*💞



®🏝

 *ZAFAFA WRITTERS FORUM* ✍🏻


             

  *_Z• W• F•🏝_*



    *Gyara da kanki*


_Zaki iyayin kwaɗon zogale yaji ƙuli da tomato da cucumber ga ƙarin jini ga ƙarin Nm riba biyu kenan._


🆓page


No. 14


   Ita kanta Sadiya gaba ɗaya ta shiga damuwa na Hanata fita da Mumyn nasu tayi gashi ta Amshe wayarta, har fakon idon mumyn nasu takeyi in ta shiga Toilet ta shiga ɗakin, saidai duk binkicenta bata ganin wayar, Haka ta dinga tura ƙaramin ƙaninsu ya ɗauko mata wayar inya ganta saidai shima bai taɓa gano wayar ba.


   Kullum da tinanin Abin take kwana take tashi gaba ɗata Hankalinta na gun su Mama da Leemaht dake tsare, saidai bata da yadda zatayi ta taimakesu. Itama Addu'a ta dage dayi akan ubangiji ya kawo musu mafita cikin Lamarin.


.....

Yau Leemaht ɗin zaune take a cikin gurin da take tsare, gaba ɗaya tayi laushi kana ganinta zakasan tana shan wuya, duk da babu wani abu da ake yi mata amman zaman gurin ya isheta dan kwata kwata bata bacci kirki saboda ƙaiƙayin da jikinta ke yi mata na rashin wanka, ga kuma Abinci da baya zama cikinta dan ko taci sai ya dawo. Wata irin rama ta zabga kamar wacce ta shekara tana jinya, tana zaune shiru a gurin wani ɗan sanda yazo ya buɗeta yace ta fito, tashi tayi ta biyo bayanshi suka fito. Wanda ke zaune ya nuna mata a matsayin mai son magana da ita sannan yai gaba ya basu guri.


   Gurin ta kallah, wani matashi ne zaune cikin kyakykyawar shiga, binta yake da kallo tinda ta fito hannunshi riƙe da wani file da alama Takaddu ne ciki. Ganin ta tsaya ne ya sanya yace.


   "Bissimillah zauna mana." ba musu ta zauna ɗin kuwa kanta a ƙasa.

   "Sannu baiwar Allah."

Kai ta gyaɗa alamar Amsawa. Nan ya cigaba da cewa.


   "Nasan baki gane niba, to da farko dai ni Sunana *BARRISTER LEERWAN* kuma nine lawyer ɗin da aka ɗauka wanda  zai tsaya miki a kotu a matsayin mai kareki, dan haka inason ki saki jikin ki ki faɗamin gaskiyar abinda ya faru a wannan rana". Kai ta kuma gyaɗawa tanajin ƙarfin gwiwa na samunta Nan tace. "Insha Allah zan faɗa maka gaskiya akan komai ka tambayeni."


   "Good!.zanso fara jin sunanki da kuma taƙaitaccen labarinki tukunnah."


   "Sunana Ikleemah B. Abubakar.Amman yawanci mutane kan kirani da LEEMART. Ni kaɗai iyaye na suka haifa, yanzu haka mahaifi na ya jima da Rasuwa daga ni sai mahaifiya ta muke zaune a gidan da muka gada daga mahaifina. Mahaifiya tace ta jajirce gurin sanyani makarantar islamiyya da Boko, yanzu haka munyi  candy, a Islamiyya kuma mun kusa kammala saukewa."


    "Masha Allah. A wannan Rana da abin ya faru me zakice akan yadda lamarin ya kasance."


   Wani yawu ta haɗiye mai ɗaci tanajin wani iri a ranta sannan tace. "A ranar Juma'a da yamma mun taso daga makaranta kasancewar bamayin hutu yanzu munason kammala saukewa da wuri shiyasa muke zuwa har Alhamis da juma'a amman  bamu kai lokacin tashi ba. A lokacin da na shigo lungun namu ne........!"


   Nan ta kwashe duk abinda ya faru a wannan rana ta sanar dashi. Saida ta kai ƙarshe sannan tayi shiru tanajin zafin zargin da ake yi mata da kuma kallon da jama'a keyi mata.


   Shiru yayi shima yana saurarenta yana rubuta abinda zai ɗauka a maganganunta, saida yaji tayi shiru sannan ya nisa yace. "Zaki iya gane Number ɗin motar da kikace ta fita a lungun a daidai wannan lokaci.?"


   Girgiza kai tayi sannan tace. "Gaskiya bazan iya tina Number motar ba dan na tsorata sosai a lokacin."


    Rubutun ya kuma yi, sai can ya kuma ɗagowa yace. "Naji duk abinda kika faɗa kuma na gamsu, ki kwantar da Hankalinki insha Allah zaki kuɓuta, Saboda kawai dan kinga mutum da wuƙa ajikinshi kin cire mai bashi ke nuna ke kika kashe shiba, saida abu ɗaya yasa kika shiga cikin zargi tsundun saboda bakiyi abin da shaida ba, sannan Hannunki kika sanya kika ciremai wuƙar, amman Insha Allah zanyi iya bakin ƙoƙari na akan wannan cest ɗin dan ganin ba a yi miki hukunci kan abinda ba laifinki ba, kici gaba da Addua insha Allah zaki kuɓuta."


    "Nagode sosai." ta faɗa tana share Hawayen idonta. Daidai nan Ɗan sandan ya dawo yace ta tashi su koma ciki. Tashi tayi ta shige ciki. Shima Lawyern godiya yayi musu ya tattara abinda yazo dashi ya tashi dan tafiya. 


..... 

Ana gobe za a shiga kotu Mama ta kuma dawowa Division ɗin saidai yauma ba a barta ganin Leemaht ɗin ba, haka ta bayar da Abincin data kawo mata aka kai mata, har yanzu kuma Sadiya ƴar fillo bata zo ba, a dangin Mahaifin Leemaht ɗin ma ba wanda yazo, dole a ƴan kwanakin suka kuma dagewa da Addu'a dan ubangiji ne kawai zai taimaka musu,  a daren ranar ko baccin kirki Mama batayi ba tanata kaiwa Allah kukanta.


.......

A Ranar da akayi Adduar bakwai ɗin ne Zulaihat ke ƙara tinatar dasu Mamy Shari'ar da za a shiga washe gari, da Mamyn cewa tayi ba inda zataje tinda ba dawo mata da Ammar ɗin za a yi ba, saida Daddyn ya ɗan tattausheta sannan ta yarda zataje.


   Itakam Zulaihat har ta matsu gobe tayi dan tini Lawyer ɗin data ɗauka ya gama duk binkicen da zaiyi kan cest ɗin, ya riga ya gama Hango Nasarar da zaiyi dan Bai taɓa tsayawa shari'a ya faɗi ba, ita kanta Zulaihat yarda dashi da tayi wajen gwanan cewa a aikinshi yasa ta ɗaukeshi.



      *WASHE GARI*

         *KOTUUU*✍🏻





_Comment and share pls_

*SUBSCRIBE*

_DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV_


https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ


*بسم الله الرحمن الرحيم*

 


        *😭BANI NA KASHE SHIBA*😭


           *Story and wrtten*

                      

                  *By*


       *FATIMA UMAR KAS*

                 *_(MUMMYN MIHAL_ )*


_Marubuciyar_👇🏼

*BAK'IN CIKIN KISHIYATA*

     *RAYUWAR MIHAL*

*ABINDA ALLAH YA NUFA*

    *SILAR ABAYA*

*'YA'YAN MIJINA NE*

     _AND NOW_

*BANI NA KASHE SHIBA*



*PAID BOOK*

 _(Littafin kud'i_) 



*LABARI MAI TAB'A ZUCIYA*😔

_ya k'unshi soyayya, tausayi, cin amana, hassada, munafirci_



*Dedicated to LEEMAHT pinky*💞



®🏝

 *ZAFAFA WRITTERS FORUM* ✍🏻


             

  *_Z• W• F•🏝_*



    *Gyara da kanki*


_Zaki sami kashin awakai bushashe da kanunfari, ƙaro, lallen hausa, sai ki riƙa zubawa a garwashi kina tsugunnawa sau uku a rana, sai ki saka farin miski inkin gama, wannan haɗin yana da kyau wacce tayi ɓari ma zata iyayi._



🆓Page.

   

No.18


    "Ya mai girma mai shari'a inason a gabatar min da Excort ɗin marigayin dukkansu a gaban kotu akwai tambayoyin da zanyi musu."


   "Kotu tana neman waɗannan mutane yanzu a gabanta." Alƙali ya faɗa, take kuwa aka shigo dasu, zuwa sukai suka tsaya inda aka Nuna musu. Matsawa Barrister yayi gabansu, na farkon ya kalla da Alama shine babbansu sannan yace. "Ka bamu tarihin Kanka a taƙaice." tsaiwa ya gyara shima sannan ya soma da.


    "Nidai sunana Abubakar. Kuma ni ɗan Asalin maiduguri ne neman Aiki ne ya kawoni Kano, na jima ina nema ban samu ba har Allah ya haɗani da Alhaji ya tambaye ni zan iya zama mai tsaron yaronshi a duk inda zaije? Nan na tabbatar mai zan iya dan ni daman cen Allah ya Halicce ni da Rashin tsoro da kuma ɗaukar Raini, yana min tayin naji zan iya nan take na Amince, Alhaji bai bani damar kasancewa da Yaronshi ba saida yasa akaje har can inda iyaye na suke akai binkice a kaina sannan ya ya Amincemin. Yau kimanin Wata takwas kenan da fara wannan Aikin dan a gabana duk aka kawo su suma."


   Ya ƙarasa faɗa yana nuna wadanda ke kusa dashi. Kai Barrister ya jinjina sannan ya  kuma cewa. "A ranar da Aka kashe mai gidanku ku kuna ina.?"


    "A ranar bayan ya fito cikin shirin tafiya masallaci har Mun buɗe murafin motocin da muke binshi munzo mun buɗe mai sai ya dakatar damu da Faɗin mun manta Ranar juma'a bamu binshi masallaci? Hakan ne ya sanya jiki a sanyaye muka bar gurin gami da maida motocin muka rufe. Muna kallo har ya tashi motar ya fice. Haka muma mukai Alwala muka nufi masallacin dukkanmu cike da damuwa dan Ɓamason fitar da yake shi kaɗai ga kuma bamu da damar sanar da Alhaji dan ya gargaɗemu akan kar mu bari kowa yasan Hakan a gidan in muka bari kuma akaji to a bakin Aikinmu. Hakan ne ya sanya ba Wanda muka sanarwa."


    "Tsawon wanne Lokaci ya soma fita shi kaɗai."


   "Tsawon sati Huɗu kenan, shima duk juma'a ne yake fita shi kaɗai har Juma'ar da maƙiya sukai galaba akanshi ta zama biyar. Allah sarki Allah ya jiƙanka mai gida."


   Ya faɗa yana Matsar kwallah. Jikin kowa ƙara yin sanyi yayi. Girgiza kai Barrister yayi sannan ya kuma jefo mai tambayar.


    "Lokacin da kuka tafi Sallahr juma'ar ƙarfe nawa Kuka dawo sannan kun biya wani guri ne.?"


   Girgiza kai yayi sannan yace. "Bayan munje sallahr juma'a mun dawo babu inda muka kuma fita Ana idarwa muka taho babu inda muka tsaya. Akwai mutane da yawa da muka dawo tare dasu a ranar, muna cikin gidan tare da sauran yaran gidan ko su ka tambaya zasu tabbatar maka da Hakan."


   matsawa yayi gurin na gaba ya maida Tambayar kanshi. Shima Amsa ya bayar daidai da tambayar da akayi mai. Haka ya dinga binsu ɗaya bayan ɗaya yana yi musu tambayoyi duka Amsa ɗaya suke bashi na basu san komai game da Kashe mai gidan nasu ba.


    "Kun tabbatar da Abinda kuka faɗa Gaskiyane.?" 


   "Mun tabbatar." suka faɗa. "In Aka baku Alƙur'ani zaku Dafa ku rantse dashi akan duk abinda kuka faɗa babu ƙarya ciki?."


    "Eh wallahi zamu Rantse." suka faɗa har suna haɗa baki. "Shikenan bari a kawo ɗin." Kai suka gyaɗa dukkansu, ɗan Nazarin Yanayinsu yayi saidai baiga wata Alama ta Rashin gaskiya tattare da suba. Shafa goshinshi yayi dan ya fara Hango Rashin Nasarar da suke shirin yi, Amman duk da Haka saida yai ƙarfin Halin furta.


   "Shikenan kuje." ya sallamesu, kallonshi ya maida kan Alƙali sannan yace. "Ya mai girma mai Shari'a inason kotu ta ƙara ɗage wannan zama har a gano Ainihin mai laifin dan na tabbatar ba ita tayi kisan nan ba. A binkicen da Nayi na gano Leemaht ko Abokin faɗa bata dashi dan ko cacar baki bata taɓayi da wata ba mutane da yawa sun shaideta gurin sauƙin hali da kuma kyawawan ɗabi'u uwa uba Tausayi dan a yanzu ma tausayin wannan bawan Allah ne yasa ta Taimakeshi inda ta taka sawun ɓarawo.


   Kuma Kotu ta duba Rauni na wannan yarinya kasancewar ta Marainiya da take ƙarƙashin kulawar mahaifiyarta dan Abincin da zasu cima sai mahaifiyarta tayi wankau suke samun na siya dan haka nake roƙon wannan kotu mai Adalci ta ƙara mana lokaci dan gano Ainishin wanda yai wannan kisan na rashin Imani. Nagode ya mai Shari'a." 


   Ya faɗa yana komawa ya zauna. Rubuce Rubuce Alƙalin yayi sannan ya ɗago yace. "Iya Shaidar da kake da ita kenan yanzu ko akwai wata?".


   "Babu ya mai Shari'a saidai munason a ƙara mana Lokaci zamu gabatar da wata nan gaba."


   "Ko Lauyan masu ƙara yana  da Shaidar da zai gabatar yanzu a gaban kotu." Alƙalin ya faɗa.


   "Eh akwai ya mai girma mai Shari'a." Barrister Yusif ya faɗa yana miƙewa. Wata takadda ya ɗauka gami da miƙawa Alƙalin yace. 


    "Wannan Shine sakamakon gwajin yatsu da akayi na jikin wuƙar da aka kashe marigayi da kuma Yatsun ita wannan Yarinya." miƙo Hannu Alƙali yayi ya karɓa gami da Warwarewa ya soma dubawa.......✍🏻






_Comment and Share pls_

*SUBSCRIBE*

_DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV_


https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ


*بسم الله الرحمن الرحيم*

 


        *😭BANI NA KASHE SHIBA*😭


           *Story and wrtten*

                      

                  *By*


       *FATIMA UMAR KAS*

                 *_(MUMMYN MIHAL_ )*


_Marubuciyar_👇🏼

*BAK'IN CIKIN KISHIYATA*

     *RAYUWAR MIHAL*

*ABINDA ALLAH YA NUFA*

    *SILAR ABAYA*

*'YA'YAN MIJINA NE*

     _AND NOW_

*BANI NA KASHE SHIBA*



*PAID BOOK*

 _(Littafin kud'i_) 



*LABARI MAI TAB'A ZUCIYA*😔

_ya k'unshi soyayya, tausayi, cin amana, hassada, munafirci_



*Dedicated to LEEMAHT pinky*💞



®🏝

 *ZAFAFA WRITTERS FORUM* ✍🏻


             

  *_Z• W• F•🏝_*



    *Gyara da kanki* 


_Ki samu kankana ki haɗa da kwakwa ki markaɗa, amman kada ki tace sai ki zuba kaɗan ki riƙashan wannan haɗin._



   _Last free page_


      No. 19_20


Bayan ya bawa Alƙali takaddar ne yaci gaba da faɗin. "Wannan Result ɗin ya tabbatar shatin yatsun jikin wuƙar yai daidai da Shatin yatsun wannan yarinya, Hakan ya Nuna tabbas ita tai kisan, maganar a ɗage shari'a ma bai taso ba tinda gashi nan Komai ya bayyana. Abokin Aikina yana kawo mana misalai ne da basa cikin Abinda muke yi a yanzu na cewar wai tana da sauƙin hali batada faɗa. Shifa ɗan Adam yana da wuyar gane Hali kuma Mugu bashi da kama mutum mugun ice ne. Sannan mutum nawa ne Allah a bakinsu yayinda in ka bincika Zuciyarsu ba komai a ciki face Abubuwan ƙi. Kasancewar Wannan yarinya a wajen mutane ta gari ce bashi ke nuna ba ita tai laifin ba.


   A kwanakin baya munji inda Ƙawa ta lumawa Ƙawarta wuƙa a ciki akan ta kai ƙararta gidansu tana tsokanarta, ita kuma Bataso hakan ba yarinyar na tahowa tazo ta bayanta ta luma mata Wuƙar har saida ta ɓullo ta gaba sannan ta ƙara mata a wuyanta._(Ya faru a gaske😭_) irin Hakan na faruwa sosai a wannan lokacin dan Haka nake kira da Kotu da ta dubi shaidun da aka gabatar ta yankewa wannan yarinya Hukunci daidai da Laifin data Aikata dan  Hakan ya zama Izina ga ƴan baya masu wannan ta'ada ta kashe mutum ba tare da wani ƙwaƙwƙwaran dalili ba. Nagode."


   Ya faɗa yana komawa ya zauna. Tsit! Kotun tayi kowa yayi shiru yana jiran yaji me Alƙali zai yanke. Sai can tukunna Alƙali ya ɗago sannan yace.


    "Kotu ta Saurari bayanan da aka gabatar a gabanta da kuma Shaidun da aka gabatar, ta kuma yi Duba da Nazari akan Lamarin inda ya tabbata Ikleemaht B. Abubakar ita ta Aikata wannan kisan dan mutane da dama sun gani sun shaida. saidai taƙi Amsa Laifinta balle musan dalilin da ya sanya tayin Hakan. 


   Dan Hakan kamar yadda Lauyanta ya nema mata Sassauci kotu ta yanke mata Hukuncin *ƊAURIN RAI DA RAI* a gidan kurkuku. Ma'ana acan zata ƙare Rayuwarta,😭 saidai Ikleemaht nada damar ɗaukaka ƙara nan da Wata guda."


    "Innalillahi wa inna ilaihirrajiun!. Suka faɗa kusan Lokaci ɗaya, Mama, Sadiya ƴar fillo, sai  Mamy data dafe kanta tanajin ba daɗi a ranta, shi kanshi Alhaji Bilyamin kanshi kawai yake girgizawa.


   Buga Gudumar gabanshi Alƙalin yayi gami da miƙewa ya soma tattara takaddu. Suma mutane miƙewa sukai suka soma ficewa, Shi kuwa Barrister Leerwan tinda ya sunkuyar dakai bai kuma ɗagowa ba. A ranshi ya Ayyana Shikenan ta faru ta ƙare.


    Wani irin kukane ya kufce wa Leemaht jin Hukuncin da aka yanke mata. Kukan takeyi da dukkan zuciyarta na tausayin Rayuwar ta data Mahaifiyarta, Kuka takeyi sosai mai taɓa Zuciyar duk wani mai saurarenta dan tinda take bata taɓa irin kukan da takeyi yanzun ba.😭

Nan ta durƙushe jikin abin tana buga kanta jikin Katakon tana wani irin kuka mai cin rai. Ji take gwara mutuwarta da ganin wannan baƙar Rana a gareta.


   Gaba ɗaya kotun yawancin mutane tausayinta ne ya sanya su zubda ƙwalla mama da Sadiya ma kukan sukeyi sosai. Fuskar mutum ɗaya ce ke bayyanar da farin ciki wato Barrister Yusif, cike yake da murnar Nasarar da sukai har ya matsu ya fita ya kirawo wacce ta ɗaukeshi yai mata Albishir.


    A hankali duk aka fice a kotun aka tsatstsaya a waje, A lokacin wasu ƴan sanda suka fito da Leemaht ɗin suna biye da ita. Tana Ganin su Mama tsaye tazo ta faɗa jikin Mama gami da ƙara fashewa da kuka, cikin kuka take faɗin.


    "Wallahi Mama *BANI NA KASHE SHIBA* taimaka mai kawai nayi ko da sauran Ranshi amman bani na caka mai wuƙar ba." sosai Mama ta kuma Riƙeta ƙaƙam jikinta tana bubbuga bayanta Alamar Rarrashi, sosai kuka yaci ƙarfinta itama, da ƙyar ta iya furta.


   "Ikleemaht kiyi Haƙuri ke taki Ƙaddarar ce tazo a haka. Kiyi Haƙuri kiyi ƙoƙari ki cinye wannan jarrabawar taki nasan Abin da wuya kuma da zafi, Amman ki sani akwai waɗanda Ubangiji ya jarraba fiye da yadda ya jarrabeki kuma da sukayi Haƙuri suka fawwalawa Allah Lamuransu sai sukaga Sakamakon Haƙurin a gaba, ki sani a cikin Rukunan Musulunci akwai yarda da Ƙaddara mai kyau ko mara kyau, dan Haka Nake Roƙonki kiyi Haƙuri ki karɓi wannan ƙaddarar data faɗo cikin Rayuwarki."


    "Muje to." Wani ɗan sanda ya faɗa. Ƙara Ruƙunƙume Maman tayi wannan karan Harda Sadiya Ƴar fillo ta haɗa suka cigaba da kukan. "Ki wuce mu tafi akace."


  Ya kuma faɗa. A hankali ta janye jikinta daga garesu ta juya dan tafiya tana waigensu gami da ɗaga musu Hannu. Motar aka buɗe mata inda aka kare ta shiga, duk da Haka ta kasa shiga ciki tana kallonsu idonta na tsiyayar Hawaye. "Shiga ciki mana a tafi." ya faɗa Ɗan sandan. Kama ƙofar tayi tana cigaba da yi musu Bye Bye kuka ne ya kuma kufce mata da ƙarfi ta  furta.


    "Mamana!Wayyo Allah Mama!Mamaaaaaaaaa!!!!".😭 Ta ƙwalla da ƙarfi sannan tai mata Bye Bye ta duƙa ta shige ciki. Mama Sandarewa tayi a gurin kukan Leemaht ne kawai ke Amsa kuwwa a kunnenta musamman sunanta da take ta kira. "Wayyo Allah Mamanaaaaaaa!!!" Tana kallo aka tashi  motar ta tafi. "Shikenan Nida ƴata har Abada saidai inje in ganta in dawo?Ashe bazan ga Auren Ƴata ba dana mallaka ita ɗaya?". Jitai Zuciyarta na kuma karyewa, ƙafafuwanta ne suka fara rawa ji tai sun fara gaza ɗaukarta, wani duhu ne ya mamaye idonta  sai gashi ta yanke jiki ta faɗi. Da gudu Sadiya Ƴar fillo ta durƙusa tana jijjiga Maman gami da kiran sunanta da ƙarfi amman maman bata motsaba.


    "Wayƴo Allah! Jama'a ku kawo mana ɗauki dan Allah." ta faɗa tana cigaba da girgiza  maman da ƙarfi tana gunjin kuka😔.........!✍🏻



    *Hmmmmmmmmmmm!!!*

       *WASA FARIN GIRKI*


*Yanzu zamu shiga cikin gundarin  Labarin namu* 


_Ga dai mama ta yanke jiki ta faɗi shin me yake samunta.???_


_Ya Rayuwar Leemaht zata kasance a kurkuku???_


_Shin ina Labarin Amir ina ya shige tsawon wannan lokaci???_


_Shin su waye suka kashe Ammar???_


_Shin Ana ganosu masu kisan kuwa? to tayaya????_


   ~Dukkan Waɗannan Amsoshin suna cikin wannan littafi mai suna *Bani Na kashe shiba.* Littafi mai taɓa zuciya. Ya ƙunshi Soyayya, tausayi, cin Amana, yaudara, Hassada.~


```Kudai ku biyoni cikin wannan littafi dan jin yadda zata kaya, Masoyana masoyan littattafai na ku nuna min soyayya ta Hanyar siyan littafina akan Naira 200 kacal, sai na jiku🤗```




   *Ga Number na👇🏼*

       *09036257038*

*SUBSCRIBE*

_DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV_


https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ


*بسم الله الرحمن الرحيم*

 


        *😭BANI NA KASHE SHIBA*😭


           *Story and wrtten*

                      

                  *By*


       *FATIMA UMAR KAS*

                 *_(MUMMYN MIHAL_ )*


_Marubuciyar_👇🏼

*BAK'IN CIKIN KISHIYATA*

     *RAYUWAR MIHAL*

*ABINDA ALLAH YA NUFA*

    *SILAR ABAYA*

*'YA'YAN MIJINA NE*

     _AND NOW_

*BANI NA KASHE SHIBA*



*PAID BOOK*

 _(Littafin kud'i_) 



*LABARI MAI TAB'A ZUCIYA*😔

_ya k'unshi soyayya, tausayi, cin amana, hassada, munafirci_



*Dedicated to LEEMAHT pinky*💞



®🏝

 *ZAFAFA WRITTERS FORUM* ✍🏻


             

  *_Z• W• F•🏝_*



    *Gyara da kanki*


_Ki samu garin Riɗi ki haɗa da minannas kisa zuma cokali ɗaya sai kisa nono ki riƙa sha, ga wanda basu son nono zaki iya saka yoghourt._



🆓page


   No.17


"Ni kaina bazan ce miki ga inda ya shige ba, saidai tabbas nasan ba ƙaramin uzuri bane zai sanya ya kasa zama gurin zaman makoki ba kuma yaƙi Halartar kotu. Duk inda Amir yake to nasan Hankalinshi yana nan. Amman bari mu koma gida zan kirawoshi naji ko yana ina."?


    "Gaskiya kam ka kirawo shi muji ko yana Lafiya dan shirun yayi yawa." mamyn ta faɗa A raunane." Haka dai suka cigaba da tattauna maganar har suka isa gida. Saida Suka fara leƙa Zulaihat sannan suka wuce ciki, cike da Tausayinta ganin yadda ta Birkice gaba ɗaya tin rasuwar mijin nata bata dawo daidai ba. Yanzu ko magana ba sosai takeyi ba.

 kasancewar Tana takaba babu ita a zaman kotun, saidai duk abinda ake ciki Barrister Yusif yana  sanar mata ta Waya.


    A ranar kuma bayan su Mamy sun dawo wasu ƴan sanda su biyu sukazo akan zasu tafi da Excort ɗin, ba musu suka Amince tinda a gabansu Alƙali yai Umarnin Hakan, Haka aka tisa ƙeyarsu duka su biyar ɗin aka wuce dasu caji office. 

 A daren kuma Alhaji Bilyamin ya dinga gwada kiran Number Amir Amman a kashe, a gaban Mamy yake ta kiran nashi bai sameshi ba. Shiru sukayi dukkansu kowa da Abinda yake Ayyanawa. Ita kuwa Mamy ta sakawa Amir ayar tambaya tini zuciyarta ta fara Raya mata wani Abu.


......

A can kuwa sanda mama ta isa gida zubewa tayi a tabarma tana sauke gajiya dan gaba ɗaya da ƙyar ta iya kawo kanta gida. Zamanta kenan wani yaro yai sallama ya shigo, ta ganeshi maƙotanta sune.


  "Wai Momyn  mu tace zakiyi Wankau a kawo miki?." shiru tayi tana tinanin ta karɓa ko kar ta karɓa? Tasan dai in ta karɓa zata samu ƴan canjin da zatai girki har tai sauran kuɗi a hannunta. Saidai jikinta ba ƙwari tanajin kamar bazata iya wanki ba amman ya zatayi???.


   "Eh a kawo." tai ƙarfin halin faɗa, dan ganinta gwara tayi ɗin ko ta samu na komawa Kotun. Dan bazata ƙara irin tafiyar da tayi yanzun ba a ƙasa. Juyawa yayi ya fita.


    Bai jima ba ya dawo da tilin kayan wankin ya ajiye sai Sabulu da Omo daya ajiye akan kayan sannan ya juya dan fita. "Kace ta baka ko Rabin kuɗin wankin ne ka kawo min." kai ya gyaɗa sannan ya fice. Can sai gashi ya dawo. Yana zuwa ya miƙa mata Ɗari uku ya kuma ficewa.


  Sosai mama taji daɗin samun kuɗin, a take kuwa ta tashi ta kuma ficewa, kai tsaye kanti taje tasai taliya guda ɗaya, canjin da aka bata bashi da yawa amman haka ta juyo dan tafiya, saidai maganar da taji ita ta dakatar da ita. can ta tsinkayo muryar wasu samari dake zaune ƙofar Shagon mai kantin suna magana ɗaya ne yace.


   "mubarak wannan ba Mahaifiyar Yarinyar nan bace datai kisan kai."?


    "Itace mana Nima na ganeta ai tin ranar da ƴar tata tai Aika Aikar, kai Allah ka rabamu da son zuciya irin na wasu mutanen talauci yasa ka kauce Hanya?."


    "Ai talauci bai yiba wallahi, Allah wadaran naka ya lalace, wayasan iya kuɗin da aka bata akan ta kawar dashi, kasan ɗan babban mutum ne a garin nan, kuma irinsu basu rasa Mahassada, yanzu haka wani ne ya biyata akan ta kashe mai shi kuma ta Aiwatar."


   "Aikuwa bataci banza ba tinda gashinan itama ta shiga Hannu kaga dole a kasheta kamar yadda ta ƙashesh.....!"


   Da wani mugun sauri Mama tabar gurin jin Zuciyarta na zillo musamman da sukace Za a kashe mata Leemaht ɗinta, sauri takeyi ta isa gida  tana toshe bakinta jin kuka na shirin kufce mata. Ji take inama bata fito ba da bata ji abinda Ya kuma ɗaga mata Hankali ba. Ashe Zargin da Mutane keyi musu kenan?.


     Tana isa gida ta fashe da kukan daya ke tason kufce mata. Saida tayi mai isarta sannan ta rarrashi zuciyarta Idanunta kuwa duk sun jeme saboda kuka. "Allah gamu gareka a gurinka muke neman taimako."


   Ta faɗa tana komawa inda take zaune ɗazu, Tagumi ta zuba tana tinanin Yadda Rayuwa tayi dasu. Jitai Girkin ma ya fita a ranta dan tinda ta ajiye Taliyar bata waiwaiyeta ba.


   Tananan Zaune Abinda duniya duk ya isheta, tinawa tayi da Wankau ɗin data karɓa, kuma tasan a yau komai dare zasu turo karɓa gashi ta riga ta kashe kuɗin dan baifi 50 tai Ragowa a kuɗin ba. Miƙewa tayi da ƙyar ta shiga banɗaki ta ɗebo botikai,  Rijiya ta buɗe sannan ta fara ɗebo ruwan tana yi tana Nishi. Saida ta ɗebo wanda zata iya sannan ta janyo kujera ta zauna gami da janyo tilin  kayan wankin ta fara wankewa zuciyarta a cunkushe.


__________________________________


Haka Lokacin ya cigaba da gangarawa har gashi yau an dawo Katu Zama na biyu kuma na ƙarshe, yau Har Anfi zaman farko cika dan kowa so yake yaga yadda Zata kaya da kuma Hukuncin da Alƙali zai yanke bayan gama Shariar.  Dukkansu lauyoyin kowa yazo da ƙwaƙwƙwarar shaidar da yake fatan yai Nasara a Kotun. 


    Shigowar Alƙali ba jimawa aka shigo da ita, wannan karan Jemewar da tayi har yafi zaman farko dan tsawon satin nan tana gidan kaso a tsare, sai taji har gwara Cell da aka kaita akan Kurkukun.


  Saida Alƙali ya zauna sannan aka fara Gabatar da Bayanai nan Alƙali ya Nemi da Lauyan wacce ake zargi ya gabatar da shaida ta gaba. Tashi Barrister Leerwan yayi gami da faɗin........✍🏻






_Comment and Share pls_

Post a Comment

ADS HERE
ADS HERE