Posts
WATA KADDARA PAGE 3
❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤
*WATA KADDARA PAGE 3*
❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤
*Na Maryam Muhammad*
❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤
*Hasheem (M jaruma ce)*
❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassoctsan
❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤
*MARUBUCIYAR*
1. Angon mata biyu
2. Dijangala
3. Dogari
4. Izzar Ameera
5. Matar cele and now
6. Wata kaddara
*Ta fannin wasan kwaikwayo (Scrpit) wato film kenan*
1. Gidan Liman
2. Alkalin kauye
3. Dan talaka
4. Dan mace
5. Rayuwar Intisar
6. Auren kaddara
Da sauransu don ba zan iya fadan sauran ba wasu ma na mantasu
*Ga masu bukatar Angon mata biyu audio sai su ziyarci YouTube channel dina mai suna M jaruma novels tv*
https://youtu.be/ShavMDSPnrw
*Zaku iya shiga ta wannan link din dake sama domin sauraran audion*
*GODIYA TA TABBATA GA ALLAH UBANGIJIN TALIKAI DAYA BANI DAMAR FARA RUBUTA WANNAN LITTAFI DANA MISHI SUNA DA WATA KADDARA, ALLAH YASA NA GAMA LAFIYA KUMA YASA MU AMFANU DA SAKON DA YAKE DAUKE DASHI*
*ALLAH KA YI SALATI GA SHUGABANMU ANNABI MUHAMMAD SAW DA IYALAN GIDANSA DA SAHABBANSA*
*ADDU'AR KU A KULLUM SHI KE TASIRI A KAINA, ALLAH YA BAR MIN KU IYAYENA DA YAN UWANA*
*JINJINA A GAREKU MASOYANA, BANI DA BURIN DAYA WUCE NISHADANTAR DAKU A KOWANI LOKACI, INA ALFAHARI DAKU, ALLAH YA BARMU TARE*
*NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA KAINUWA WRITER'S ASSOCIATION, INA YINKI OVER AUNTY FAUZY, MAMAN NOOR DA HARUNA BIRNIWA*
*Wannan littafin kage ne, labarin ya fito daga kasar zuciyata ce, mallakina ne kuma ban yarda wani ko wata ta sauya min labari ba ta kowata hanya*
❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤
Hafeez ya katse ta cikin tsawa "Baiwar Allah miye kuma ma kuka, saboda bokatin roba ne kike wannan kukan?"
Haleema ya sauke masa idanunta day suka sauya zuwa ja, cikin muryar kuka ta ce fashewar wannan Roban tamkar karewar rayuwana ne, wallahi idan yau Inna ya barni da raina, ba karamin sa'a na yi ba
Hafeez ya ce OK, to shikenan, yanzu bari na baki wasu kudi, sai ki kai ma Innar taki, kudin zai isheta siyan irin wannan bokatin guda dari
Haleema ta katse shi cikin muryar kuka "idan ka bani kudi na kai mata, ka Kara min wani laifine akan laifin fasa robar man, Inna sai ta yanka ni, sai ta yi min kazafin sato kudin na yi ko kuma bin maza na yi"
"To ke kina bin maza ne?"
Haleema jin zancen tai kamar saukar aradu, da sauri ta girgiza kai alamun a'a tana fadin ni bana bin maza, KO saurayima ban taba yi ba
Hafeez tsura mata ido yai sai ya Kawar da kanshi daga kallanta, yana toshe hancinsa "to ke yarinyarnan narasa gane lamarinki, dazu kin ce rabonki da wanka tun mahaifiyarki na da rai, yanzu kuma ta kan roba Innanki zata kashe ki, na kawo solution kin ce ba mafita bane, yanzu sai ki fada min mafita don sauri nake yi, na kosa nabar garin nan
Haleema ta zuba gwiwowinta a kasa cikin kuka "don girman Allah ka yi min rai, ka fitar dani daga cikin ukubar Innata, wallahi yau kasheni zata yi"
Tsayawa yai cikin mamaki yana kallanta yana nazari, can ya ce to tashi mu je gidan tare sai na yi ma Innar taki bayanin abin daya faru
Haleema ta mike tana kallan Hafeez, nuna mata motansa ya yi "mu shiga mu wuce"
Haleema ta zaro ido cikin tsoro "a garin nan mata basa shiga motar samari, idan wani ya ganni na shiga motarka akwai matsala
Hafeez ya ja karamin tsaki sannan ya ce har yanzu ku yan kauye jahilai ne, babu wayewa a tare daku, miye idan kin shiga mota ta, nifa ba zan tsaya 'bata lokaci ba, idan zaki shiga mota ki shiga, babu mai ganinki, motar bakin gilashi yake dauke dashi, sai dai ke ki ga wanda yake waje, amma har mu kai gidanku babu wanda zai iya ganinki
ya kai karshen maganar ya je ya bude mota, kofar baya "zo ki shiga nan" shuru Haleema ta tsaya kamar ba za ta je ba sai kuma ta tako a hankali ta karasa, ta shiga ciki, ya kulle sannan yazo ya bude gidan gaba ya shiga, ya saka face mask dinshi don ba zai iya juren shakar tsamin daudan da Haleema take yi ba, Hafeez ya ja motar Haleema na kwatanta masa hanyar gidansu
❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤
Rabi na aikin goge gogen katafaran falo mai dauke da kayan alatu, ta kawo kan wani zanen hoton Hafeez da ya yi matukar kyau kamar a kirashi ya amsa, Uwani ta shigo ta sameta, zaro ido Uwani tai cikin tsoro "ke Rabi me kike yi da hoton Little master?" Rabi tai smile sannan ta ce kawai hoton ya birgeni ne, Little master ya yi matukar kyau a cikin hoton, Madam ta yi sa'an miji
Maganganun Rabi ya fadi a kunnan Hanan da ta shigo cikin falon cikin isa da tsananin izza, kallan Rabi ta tsaya yi cikin tsananin fushi, tana huci kamar macijiya, Rabi na hada ido da Hanan ta aje hoton da sauri jikinta na 'bari, Hanan ta karaso ta tsaya gaban Rabi, Rabi za tai magana, Hanan ta dakatar da ita da wani mari, zata kara magana ta kara tsinka mata mari, ta nunata da yatsa "ke 'yar matsiyata, mijina ne zaki yaba, how dear you, wacece ke da zaki yaba mijina" ta sa kafa ta tureta, Rabi ta fadi kasa, dukawa tai ta shiga rokwanta "Don Allah madam ki yi hakuri, na yi kuskure, ki gafarce ni" Uwani tana gefe ta yi tsuru tana kallansu
Hanan ta ce ni bana yafiya duk kankantar laifi sai na yi hukunci, bare wannan laifin da kika aikata ya yi girma da yawa, bana wasa da mijina, mijina shine rayuwata, bana son wata ta rabe shi, bana son ya birge wata, ni kadai nake so ya birge, dani kadai zai yi rayuwa
Rabi ta ce Hajiyata ke ta dabance cikin matan duniya, masu irin halittanki basu da yawa a duniya, ke ta dabance mai dauke da baiwa na musamman, takunki da adonki ko dawisu ba za tai sa'a dake ba, ballantana azo kan muryarki mai zaki daya zarce na sarewa, har kina tunanin akwai wata 'ya mace a duniya da mijinki zai kalla ta birgeshi, ke kadai ce kike birge mijinki, dake kadai zai kasance har banyan ransa, ki gafarce ni Hajiyata uwar daki ta, ni mai kishinki ce
Hanan murmushi tai tana dan girgiza kai, ta kalli Rabi ta kara kallanta "hakika kin gano laggo na, kin tsallaka rijiya da baya, na yi miki afwa" Hanan ta cire hoton Hafeez daga falo ta juya tai wucewarta cikin tsananin farin ciki
Rabi ta kalli Uwani sai ta yi wani ajiyar zuciya "oh ni Rabi, Allah ya taimake ni"
Uwani ta ce sai gaba ki yi taka tsantsan, yakamata ki sani madam bata wasa da mijinta
Rabi ta ce ai yanzu na kara tabbatarwa, zan kula sosai
Hajjaju ce ta shigo ta samesu, Hajjaju fara ce, bata wani tsufa can ba, sanye take da farin gilashi don idonta ba kwari ne dashi ba, ta karaso a natse cikin dattako ta zauna kan kujera ta kalli Uwani, "dakko min kilishina, ki hada min da lemu na abarba mai sanyi, sannan ki soya min kwai shida"
Uwani ta ce to sannan ta fice, Rabi ta cigaba da goge gogen ta
Hanan tana shiga bedroom dinta, ta rungume hoton Hafeez tana murmushi tana kara tuno kalaman Rabi, daukar wayarta tai ta shiga neman numban Hafeez amma baya tafiya, karamin tsaki ta ja sannan ta ce kawai ya tafi garin da babu service, Ina ta so na ji muryarsa amma babu dama, to ai nemo min magani ya je yi, na tabbata yanzu yana hanyar dawowa yanzu, Allah ka dawo min dashi lafiya
❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤
Hafeez ya karaso kofar gidansu Haleema yai parking, fitowa yai sannan ya je ta gidan baya ya budwwa Haleema kofa, dai dai da shawo kwanan Mal Adamu da amininshi Mal Tanimu, Haleema na fitowa suka yi ido hudu da mahaifinta Mal Adamu, Mal Adamu ya tsaya cak yana kallan ikon Allah, Mal Tanimu ya kalli Mal Adamu sannan ya ce wa nake gani kamar 'yar wurinka ta fito daga mota
Haleema fashewa tai da kuka ta kalli Hafeez "shikenan yau tawa tazo karshe, dama na fada maka"
Hafeez ya kalleta yana fadin wai ke miye matsalarki, meke faruwa, idan Ina tare dake komai mai sauki ne
Cikin tsananin fushi Mal Adamu da Mal Tanimu suka karaso wurinsu Hafeez suka tsaya, Mal Adamu ya nuna Hafeez sannan ya ce yanzu saboda iskanci da lalacewa 'yar tawa zaka saka a cikin mota? Gaskiya ka gama cuta ta a duniya
Cikin rainin wayau Hafeez ya ce malam ban fahimceka ba, dama 'yarka ce, to ni banma sani ba kawai daga ka ganta a cikin mota ta sai ka yi tunanin wani Abu
Mal Tanimu ya nuna Hafeez cikin fushi "kai dan marasa mutunci, karka kawo mana rainin hankali, a tunaninka zamu barka ne, dole sai mun hukuntaka
Hafeez yai karamar dariya sannan ya ce gaskiya kuna da abin dariya, har ni little master zaku hukunta, kun san waye ni kuma kun san waye ubana, idan mafarki kuke yi to ku farka, ni zan tafi banda lokacin da zan tsaya 'batawa tare dak.... Mal Adamu ya dakatar dashi "bala isa ka wuce ba wallahi, idan kana takama da rashin kunya muna da wanda suka damaka suka shanyeka, idan kuma arziki kake takama dashi mu muna takama da sihiri, daga kai har uban naka sai mu batar daku a doran kasar, idan kuma ka musa, sai mu zuba mu gani
Shuru Hafeez yai yana tunani a zuciyarsa, fadi yake "kawai na rabu da mutanan nan lafiya, Ina ga zai fi zama alkairi, ba zan iya komai ba, babu service bare na kira jami'ai" Haleema ta koma bayan Hafeez ta cigaba da yin kuka kasa kasa, Mal Tanimu ciro 'kaho ya yi daga cikin aljuhunsa, nan take ya shiga hurawa, ko'ina ya dauka
Hafeez ya shiga rarraba ido "me kake yi haka?" Kamin ka ce miye kauraye suka karaso da karnukansu da makamansu, wasu da adda, wasu da gora, wasu da baushe, sun taru sun kai su talatin, yaron Mal Tanimu wato Damisa, ya kalli mahaifinsa ya ce Baba meke faruwa ne? Barayi ne suka shigo garin? Mal Tanimu ya ce A'a (ya nuna Hafeez) wannan mara kunyar ne yasa 'yar wurin aminina a cikin mota, muna masa magana yake neman ya yi mana rashin kunya, shine nake so ku nuna masa irin naku rashin kunyar
Damisa ya kalli Hafeez cikin tsananin fushi ya ce ai kuwa sai dai yau babarka ta haifi wani
Cikin fushi Hafeez ya nuna shi da yatsa karka kara Koran babata, don babata tafi karfinka, Damisa ya yunkuro zai yi kan Hafeez Haleema tai sauri ta tare gabanshi tana kuka sosai tana fadin karku cutar dashi, wallahi bai da laifi ko daya, taimakona zai yi
Mal Tanimu ya kalli Mal Adamu sannan ya ce ka gani ko, alamar ya gama hure mata kunne
Hafeez ya kalli Mal Adamu ya ce please, zan baku hakuri, tsautsayi ya riga ya faru, ku fadi ko nawa kuke so zan baku, ni dai ku barni na tafi safely, mata ta tana jirana
Mal Tanimu ya ce au an ce maka mu mutanan banzane, baka isa ka rude mu da kudi ba, munfi karfinka kuma matarka sai dai ta ga gawarka yau
Kaurayen nan suka hayayyako, suka yi kan Hafeez, Mal Adamu ya dakatar dasu "ku dakatar" Mal Tanimu ya ce meyasa zaka dakatar dasu, ka barsu su kashe banza mara amfani
Mal Adamu ya je ya tsaya gaban Hafeez yana kallan shi shima Hafeez kallanshi yake yi, "ka ce matarka na can tana jiranka, ka adana matarka a gida ni kuma 'yata ce a wulakance, yanzu ka shigar da 'yata cikin mota wanene a garin nan zai zo ya nemi auranta? Samari gudunta zasu dinga yi, kafin ta sami mijin aure sai an wahala, to baka isa ba wallahi babu hukuncin daya dace da kai irin auranta"
Mal Tanimu ya ce wannan shawara ya yi Mal Adamu, yanzu za'a daura auren nan ko yana so ko baya so
Hafeez jin zancen yai tamkar saukar aradu, ya zaro ido cikin tsoro ya maimaita kalmar "aure....."
*Please ku tayani sharing zuwa sauran groups 🙏🙏🙏*
Wa'inda basu turo katin data ba, suyi hanzarin turowa ta wannan numban 09049493054
Mu hadu a page 4