ADS HERE

JAMI'IN DAN SANDA PAGE 1

 👨🏻‍🔧  *JAMI'IN 'DAN SANDA*.  👨🏻‍🔧

                 


               


*بسم الله الرحمن الرحيم*

 *____________________________________*


 *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*

*🇦SSOCIATION🤝🏻*

 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*____________________________________*


*_wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin kainuwa writers Ina alfahari da k'unguyar kainuwa da mutanen cikinta Allah yak'ara Mana k'aunar  juna son so fisabilillah_*😍😍





🅿️ 1





Kuka take sosai har tana shid'ewa ,Yarinya ce 'yar wata ukku kyakykyawar gaske Fara sol Kamar 'yar turawa , kallo Daya zaka Mata kasan cewa ta galabaita tun tana kukan da hawaye har sun daina fitowa ,

Abun mamaki duk wannan kukan da take tana rik'i ne a hannun wani matashin saurayi Wanda bazai wuce shekara 30 zuwa 32 ba , tunda yarinyar ta Fara kuka kanshi yak'e k'asa , fiye da minti talatin ko motsin kirki yakasa Yi duk kuwa da irin yadda kukan yarinyar ke soya mashi zuciya , yanajin kukanta har cikin ruhinshi Amma tsabar tashin hankalin da yake ciki ya Sanya ko motsin kirki yakasa Yi,


A hankali ya d'ago manyan idanunsa Wanda suka rine sukayi jajir yayinda jijiyoyin kansa suka firfito ,kallo Daya namasa Saida na firgita , isashen namiji ne ajin farko Kuma k'ak'k'arfa gaba Daya jikinshi a murd'e yake duk wasu  alamun k'arfi sun bayyana a jikinshi ,


Akan yarinyar ya sauke idanunshi kamun a hankali yafara jijjigata , jakar dake kusa dashi ya bud'e wata 'yar gora ya d'auko ya bude ya kafawa yarinyar a baki , ruwa ne ,takuwa Sha sosai sannan a hankali tayi shiru tana ajiyar zuciya, 

Kamar wata Mai wayo Haka ta kafe shi da ido suna kallon junansu , a hankali wasu hawaye masu zafi suka Fara sauka akan fuskarsa ,


_Bazan yafe ba , bazan ta'bawa yafewa Wanda duk ya jefa rayuwata a wannan had'arin ba ,tabbas sai na dauki fansa Koda Zan rasa Raina sai na dauki fansa wannan alkawari ne_


_Bazan baka *Muneeba* ba har sai kayimun alk'awari biyu, na farko inason kayimun alk'awarin bazaka ta'ba zuwa Neman fansa ba na biyu Kuma inason ka *Ajiye aikinka na d'an sanda* idan ba Haka ba to bazan ta'ba baka 'yata ba *Hisham* gara ta mutu a nana Hisham ta k'arasa maganar cikin tsananin azabar da takeji ga jini na fita ko ta ina a jikinta,_


Magan ganunta suka shiga dawo Masa cikin kunne Kamar yanzu take fad'a Masa ,

Rik'e kansa yayi dayaji Yana juyamasa Kamar zai cire yayinda zuciyarshi ke mashi wani irin zafi Kamar zata fashe, tsabar bakin ciki yasa ya fasa wata irin k'ara wadda Saida dajin ya amsa kuwa , hakan kuwa ba k'aramun razana  *Muneeba* yayi ba nan ta fashe da wani irin kuka a gigice, 


Tashi yayi da ita a hannunsa ya duk'a ya dauki Yar k'aramar Jakarshi ya juya yaci gaba da nausawa a cikin jejin,


Dajine Mai matukar girma da had'arin gaske Haka yarinka ratsawa ta cikinshi Babu alamar tsoro a tare dashi, yayinda Muneeba take goye a bayanshi tana baccin wahala, ................✍🏼


RYAM UMAR ABDULLAHI CE........✍🏼


Post a Comment

ADS HERE
ADS HERE