ADS HERE

ICEFISH SOURCE (SA KISHIYA CIWON ZUCIYA)


 SAUCE DIN ICEFISH

  Abubuwan hadawa

• Kifi ice fish

• Albasa

• Tattasai da attarugu

• Tafarnuwa

• Man gyada

• Maggi

• Kayan kamshi


Yadda ake hadawa


Bayan kin wanke kifinki ya tsane da kyau sai ki ajiye shi a gefe.

Ki yanka albasanki sannan ki yi jajjagen tarugu da tattasai da tafarnuwa.

Ki daura mai kan wuta, da ya yi zafi sai ki sa albasa ki kawo jajjage ki sa ki dan sa ruwa kadan ba mai yawa ba. 

Sai ki sa su maggi da kayan kamshi ki kawo kifinki ki zuba ki rufe ki maida wuta can kasa don ya samu ya dahu a hankali ba tare da ya farfashe ba.

Akalla ki bari na minti biyar sai ki sauke.


Za ki iya ci da farar shinkafa ko taliya ko doya ko dankalin turawa ko ta Hausa ko plantain ko daima biredi da duk dai abinda za ki iya ci dashi.

 


08167151176

_MRS BASAKKWACE_

Post a Comment

ADS HERE
ADS HERE