SIRRIN MU 1-2
*🍇🍇SIRRIN MU🍇🍇* ✍🏻 By NIMCYLUV *A KULLUM INA SON GANIN NA DAI-DAI TA AL'ƘALAMI NA✍🏻 WAJAN GANIN NA BAKU DARASI WANDA AKE FAMA DASHI A WANNAN SOCIETY NAMU,BAN SANI BA KO WANNAN KARAN LABARIN NAWA ZAI SAMU DAI-DAI TO A CIKIN ZUCIYOYINKU?? KUYI HAQURI NASAN ZA KUCI KARO DA SABBIN LAMARI A CIKIN LITTAFIN WANDA BAN TAƁA IRINSA BA,DAN ALLAH KUYI HAQURI YANAYIN LABARIN NE, HAKA ZANYI KOMAI A BAI YANE WANNAN KARAN😂🤕 NO MORE SURUTU* _Wannan littafin na kuɗi ne,haƙƙin mallakata ne Na'ima sulaiman NIMCYLUV, kada kai tunanin juya min labari tako wacce siga kada kuma kasai book ɗina domin ka fitar,kowa ya sani bana faɗa ko Allah ya isa a book ɗina ƴan *UNCLE NE* zasu shaida hakan, idan Free book kake so akwai ka tambaya ga *MOON* nan, yanzu zan bada free pages ne kuma only 10 free pages so a kakkaɓe zani Mutane na ƴan vip, so you can share and share and share_ EPISODE1️⃣-2️⃣ MAIDUGURI/ BARNO My first word on my story is SAMBISA Forest, The Sambisa Forest is a forest in Borno State, northeast Nigeria. It is in the southwestern part of Chad Basin National Park, about 60 kilometres (37 mi) southeast of Maiduguri, the capital of Borno State. Baƙin daji ne mai girma da tsayin gaske, anyi noticing babu wani daji daya kaisa girma da both faɗi tsayi,ga wasu manyan bishiyoyi da kwazazzabe, duhun dake cikin dajin yafi gaban kwatance, kai tsaye bazan iya siffanta muku duhun sa ba, but yaya kake imagine ace ka rufe idanunka wanne kalan duhu zaka gani? To zan iya haɗa hudun cikin idanun mutum da kuma duhun dake ciki dajin SAMBISA, mugwayen dabbobi babu kalan da babu har wacce ba kayi tunanin ganinta a wajan ba zaka sameta, lokuta da dama ko da bamu da masaniya a kan dajin Sambisa but muna jin labarinsa a cikin kafar yaɗa labarai, irin su Redio,T.v, media, uwa uba idan ka je BBC Hausa news, ko kuma ka kunna tashar aljazira, wasu da dama basu san dajin Sambisa ba, amma faruwar annoba ta farko wata BOKO HARAM, wanda kowa yasan cewa BOKO HARAM ya fara a 2002 zuwa 2009. (BOKO HARAM Home Politics, Law & Government Law, Crime & Punishment Crime, Terrorism & Counterterrorism Boko Haram Nigerian Islamic group BY The Editors of Encyclopaedia Britannica View Edit History FULL ARTICLE Boko Haram, (Hausa: “Westernization Is Sacrilege”) byname of Jamāʿat Ahl al-Sunnah li-l-Daʿawah wa al-Jihād (Arabic: “People Committed to the Prophet’s Teachings for Propagation and Jihad”), from 2015 also called Islamic State in West Africa (ISWA) or Islamic State’s West African Province (ISWAP), Islamic sectarian movement, founded in 2002 by Muhammed Yusuf in northeastern Nigeria, that since 2009 has carried out assassinations and large-scale acts of violence in that country. The group’s initial proclaimed intent was to uproot the corruption and injustice in Nigeria, which it blamed on Western influences, and to impose Sharīʿah, or Islamic law. Later the group vowed to avenge the deaths of Yusuf and other group members, who were killed by security forces in 2009. In 2015 the group pledged allegiance to the Islamic State in Iraq and the Levant (ISIL) and took the name Islamic State (or State’s) West African Province (ISWAP; also known as Islamic State in West Africa, or ISWA). The next year the group split, with one faction retaining that name and the other reverting back to the original appellation). Wata tafkekiyar bishiya ce,wacce take ɗauke da manyan koguna wajan goma a jikinta , ko wane kogu idan ka shiga zaka samu hanyar ɓullewa a cikin sa, banda kukan dabbobi kala daban-daban babu abinda yake tashi a cikin kogunan, can cikin baccinsa ya ji kamar ana ƙwalla kiran sunansa, kasancewarsa ba mai nauyin bacci ba, yasa ya buɗe dara daran fararen idanunsa wanda suka janye tare da yin jaa sbd zallar baccin da yake cikin sa, har wani ciwo-ciwo ya ji kansa nayi masa, shiru yay domin yana son ya ƙara tabbatar da abinda kunnuwansa suka jiyo masa a cikin baccinsa, jin shirun yay yawa yasa yay baya kaɗan tare da sauke wata wahalalliyar ajjiyar zuciya,/kana ya juya zuwa ɓangaren hagunsa, sannan ya karanta addu'ar neman tsari, yana lumshe idanunsa ya ji an ƙara kiran sunansa, tamkar mai kiran yana cikin ɗakin nasa, da sauri ya ƙara buɗe idanunsa ya shige dube-dube amma babu abinda ya gani, lubalun dake saƙale jikin ƙofar bedroom ɗinsa ne ya kaɗawa sannu a hankali, harya gama kaɗawa idanunsa na kan labulan, waro manyan idanunsa yay waje saboda baƙar matashiyar buduwar mai masifar kyau da ta bayyana a gabansa, ko kaɗan bai ji tsoron ganin wannan halittar ba,sai dai yanayin baƙin fatar ta da kuma dugun baƙin gashinta wanda yake jan ƙasa kaɗai ya isa ya sanya zuciyar mutum rabewa gida biyu, abinda ya bashi mamaki yadda idanunta ya kasance baƙi sosai kamar yadda farar jikinta take, sai dai eyes balls ɗinta blue ne sosai, ga eyes lashes ɗinta zara-zara, har taɓa girarta yake, abu faɗi ɗaukar hankali a jikinta shine jajayen laɓɓanta masu kauri sosai wanda suka kasance ƙarama ya marasa faɗi, tana sanye da fararen kaya har ƙasa wanda suka rufe kofaton dake jikin ƙafarta, tattausan murmushi ta sakar masa, wanda yasa ya ƙara ware manyan idanunsa a kanta, da ace yana mugayen mafarkai kai tsaye zai iya cewa mafarkin yake, but isn't dream is real, a zahiri yake ganin komai a cikin ɗakinsa kuma a gabansa, ƙara sakar masa Murmushi tayi kafin a hankali ta miƙa masa hannunta, cikin wata murya very cool and slowly tace "zo mu je", juya mata ƙwayar idanunsa yay kana yay mata nuni da shanyayyun ƙafafuwansa, kallon ƙafar tayi sai kuma ta marairaice fuska, kafin a hankali ta taka zuwa gare sa, tana zuwa ta zanƙalelen hannunta ta dafa ƙafaɗarsa, nan take wata guguwa mai ƙarfin gaske ta lulluɓe su, bai tashi ganinsa ba sai a cikin wannan kogun dake cikin bishiya na dajin Sambisa. A gigice yake juya idanunshi yana ƙarewa cikin kogun kallo, shigarsu cikin kogan kuma yasa yay haske sosai, kai tsaye wajan wata haɗaɗiyar kujera mai kyau da kuma tsarin gaske ta zaunar da shi, sai a lokacin ya fahimci ashe a hannunta yake riƙe, ba tare kuma da tayi masa magana ba ta juya ta shige cikin wata ƙaramar hanyar, har 5mins yana zauna yana ƙarewa wajan kallo, a iya tarihin rayuwarsa zai iya cewa bai taɓa ganin waje mai haɗarin gaske irin cikin kogun nan ba, ko a Indian series film dake yake kallo anytime bai taɓa ganin haka ba, ko da a cikin horo Film ne, sai gashi yanzu a zahirance yake ganin komai a idanunsa, bawai a bashi labari ko ya gani a Film ba, a'a all this yana faruwa dashi ne a karan kansa, tambayar da yakewa kansa why bai ji tsoran ta ko kuma ya shiga firgici da ganin ta ba??, Ko dai yana cikin replaction ko nightmare ne?? Fresh skin ɗinsa ya kalla a hankali kuma ya miƙa hannunsa tare da mintsinar saman fatar sa, zafin da yaji yasa yay saurin faɗin "Auchhhhhi!!" Daga can masan kansa yaji ance "what happened to you Bil'adama??" Fararan idanunsa ya ware cikin ransa yace ashe suna iya English? Ita kam tana barin wajan cikin wani makaken kogo ta shige a nan ta samu dandazon Jinnu ƴan uwanta kala daban-daban, wata tsuhuwa ce wacce ta fito a siffar mutane ta kalli buduwar tace "Duk kin tashi hankalinki! Muma kin tashi namu,wai kekei faruwa dake ne Airah??" Wasu hot hawaye ne suka kawo cikin idanun Airah, sai kuma ta zube a ƙasa tace "Kiyi min afuwa Kakata, nasan kaf cikin zuri'arki nice na fara karya dokar ki ta shiga jikin Bil'adam, amma babu yadda na iya dole tasa nai haka, kince zamu iya taimakawa mutum a lokacin da mu kaga yana buƙatar taimako, kin hanemu da shiga jikin Bil'adam bisa raddin kanmu" shiru tayi sbd tsawar da Tijama tayi mata, wannan shine karan farko da kakarta ta tayi mata tsawa, cikin ɓacin rai da kuma tashin hankali TIJAMA tace "you're mad Airah,Yajjju da baihakkk Airah ,Bisaka wadayikiii bil Adam Arjun?" Cikin kuka Arjun tace "Laa Kaka,but ina son taimaka masa ne,am going to help him Tijama" cikin tsawa Tijama tace "me ne?? Ki rasa wa zaki taimakawa sai shi?? Kin san wanene shi kuwa Airah? Mu kanmu muna buƙatar taimakonsa bare mu mutaimakesa, you're so selfish Airah" Wani Saurayi ne ya kalli Tijama yace "Amma Tijama yana da kyau mu ji dalilin daya sa take son taimku Bil'adam kamar wanann mutumin wanda idan yaso a lokaci ɗaya zai iya kaimu lahira gaba ɗayan mu kuma...," Shiru yay saboda hannu da Tijama ta ɗaga masa tace "stop interrupt Tuɓe ,babu abinda Airah zata faɗa wanda ban san da shi ba,komai ana barwa lokaci ne, domin shi ke sawa a bayyana komai , Airah tayi mana gaggawa ta ɓata mana komai, ko da za muyi nasara akan taimakon nasa amma yanzu bamu da damar yi, saboda Airah ta ɓata komai tayi abinda sai nan da shekaru wajan biyar ya dace ace munyi shi, babu wanda baya son mutumin nan,hadda mu Jinnu muna ƙaunarsa, mu musulmai ne kuma Turawa ne, haka kuma ALLAH! Yayo mu a cikin halittun da ba kowa yake ganin su ba, sai dai mu kalli abinda mu kai niyya, Airah kina da girman kai sosai, baki jin magana, baki san girman kai yasa Ubangiji ya sakko da Iblis daga Sama ba zuwa duniya ba?? Ko so kike ki zama ƴar uwarsa Airah ??" Da sauri Airah ta girgiza kanta tace "Auzubillahi! bana fatan hakan Kakata, ni dai alfarma nake nema wajanki Kakata ki daure kiyi min ita dan Allah!", murmushin baƙin ciki Tijama tayi, domin tasan jikar tata abu ne mai wahalar gaske ta fahimci abinda take son fahimtar da ita, kuma bata son gaya mata muhimman abubuwan da suke tare da wannan bawan Allan,tana son ta bari lokacin komai yazo ya wuce, da zarar lokaci yazo komai zai bayyana kansa ba tare da sun bayyana shi ba, shiru ne ya biyo baya kowa da abinda yake saƙawa a cikin ransa, ita Airah tana son faɗawa Kakar tata wani abu amma tana tsoro, kamar daga sama taji muryar Tijama tana faɗin "me kike ɓoyewa a ranki Airah ! Feel free to ask" girgiza kai Airah tayi tace "No! Tijama idan lokacin yayi zaki sani amma wannan *SIRRIN MU* ne", Murmushi kawai Tijama tayi kafin tace "me kike so yanzu ai masa?" Da sauri Airah tace "Ina son na bashi muƙami" kafin Tijama tayi magana Juɓe yace "Muƙami a cikin Jinnu Airah? How can that be possible?" Kallon Yayan nata Airah tayi kafin tace "Is very simple ai, shi kansa bazai san an bashi muƙamin ba, but every night zanna dauƙo sa zuwa zaman fada, zan mantar da shi komai", Dariya Tijama tayi tace "Shirme dai sai yaro, Bil'adam zai zama jagoran Jinnu kenan Wow!" kamar Airah zatai kuka tace "please Tijama" jinjina kai Tijama tayi kana tace "je ki bashi Allah ya ba shi ikon Mulkan rundunar Jinnu bisa gaskiya da Amana", tana faɗin hakan tai girgiza ta ɓace daga wajan, shi Juɓe bayan ta yabi ya ɓace. Yana zaune yana lumshe idanunsa time to time ya kan buɗe su,wani sanyi yaji a saman ƙafaɗarsa ga wani abu mai tsayin gaske daya fara yawo a saman wuyansa , da sauri ya ɗaga kansa nan idanunsa ya sauka saman ƙatuwar mesar dake bin jikinsa tana naɗesa, kasa motsi yay, kuma har zuwa lokacin babu wani tsoro daya shige sa, shi ji yake ma ina ma ya dauwama a wajan har ƙarshen rayuwarsa, domin da rayuwar da yake a cikin mutane gwamma wannan sau dubu da waccan, sai da Mesar ta kama naɗesa tsaf sannan ta ɗaga fuskarta zuwa dai-dai fuskarsa ta shiga ƙare masa kallo, can kuma tai girgiza sai gashi ta rikiɗe ta dawo Airah ,tai kwance jikin sa, motsi yay kaɗan da idanunsa ta kalli bakinsa sai kuma ta kalli idanunsa, shi ma kallonta yake ko ƙiftawa babu, a hankali Airah ta miƙe daga jikinsa kafin cikin ɗaga murya tace "Congratulations! Now you're the king of Jinnu, yanzu kai sarkin ALJANU ne SHEIKH IMAM HAMDAN!!....✍🏻