ADS HERE
Posts

JAMI'IN DAN SANDA PAGE 4

 👨🏻‍🔧  *JAMI'IN 'DAN SANDA*.  👨🏻‍🔧


*Mallakar*


*Maryam Umar Abdullahi*

(Mmn Yusuf)


*Marubuciyar*

*Minene Asalina*

*Mutum ce kuwa*

*Husna ko Huzna*

 *And now*👇🏻

*Jami'in d'an sanda*



*بسم الله الرحمن الرحيم*

 *____________________________________*


 *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*

*🇦SSOCIATION🤝🏻*

 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*____________________________________*


*_wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin kainuwa writers Ina alfahari da k'unguyar kainuwa da mutanen cikinta Allah yak'ara Mana k'aunar  juna son so fisabilillah_*😍😍





🅿️_4




.............da k'yar ya dafa Baffa ya mik'e tsaye , a zuciye ya juya zai Fara tafiya , wata k'ara ya saki jin wani irin ciyo ya ziyarceshi Babu shiri ya koma ya zauna ya na maida numfashi hade da runtse idanunshi, 

Murmushi Baffa yayi a zuciyarshi Yana cewa too fa Hajar yau kin gamu da gamonki ga Wanda yafiki son d'iya don wannan da alama ko aro bazai iya baki 'yarshi ba,

Afili kuwa cewa yayi "kaga bafa zaka iya taka k'afarnan a yanzu ba , saboda dafin yariga da ya shiga jininka sosai doli zaka zauna anan Koda na sati biyu ne ayi maka magani inba haka ba zaka iya samun matsala da k'afar Nan zuwa gaba , macijin da ya sareka yanada matukar had'ari , daga Haka Baffa ya kamashi ya mayar dashi cikin bukkar Nan,


Tun yanasa ran za'a kawo mashi Muneeba har ya hakura ,saidai a zuciyarshi wani d'aci yakeji yanajin Kamar yaje ya kama wannan yarinyar yayi Mata shegen dukan tsiya,

Tabbas yazama doli yayi nesa da wad'an nan mutanen  don bayason suyi rayuwa da kowa a kusa dasu bai yarda da kowa ba don haka bazai zauna da kowa ba , sannan bayason 'yarshi ta shak'u da kowa inba shi ba , shikadai zai kula da tilon 'yarshi wadda ita kadai ta ragemai a rayuwa ita kadai ce danginshi a halin yanzu ,zai zamo Mata uwa Kuma uba a rayuwa Sam bazatayi kukan maraici ba, Haka yayi ta sake sake har bacci yak'ara awon gaba dashi,



***********************



*GARIN LAGOS*



Motocine guda biyar suke tafiya a jere dukkansu bak'ak'e wulik' , gudu suke Kamar zasu tashi sama , tun suna tafiya cikin gari har suka fara ratsawa cikin dazzuka , a Haka suka rinka gudu sunyi tafiya Mai nisa kamun su yanki wata hanya suka Kara nausawa acikin jejin , 


Abun mamaki sai gasu agaban wani makeken gida Mai kyaun gaske Wanda kallo Daya zaka mashi kasan cewa naira tayi kuka a wajan ,k'aton get din gidan wani basamuden mutum Kuma k'ak'k'arfa ya bude masu , 

Wajan da aka tanadar don ajiye motoci sukayi parking, sannan suka firfito, ba k'aramun firgita nayi ba lokacin da nayi arba da wad'an mutanen , kowace mota mutum biyu ne aciki , gaba dayansu sanye suke cikin bak'ak'en Kaya  suna sanye da tabarau bak'i Wanda yakusa mamaye Rabin fuskarsu maza TAKWAS ne mata biyu , sai dai ba bambanci tsakanin mazan dakuma matan saboda duk shigarsu iri Daya dai dai da hular da suke sanye da ita iri Daya ce wadda ta kasance Ja ,  kallo Daya zaka masu kasan cewa Sam Basu had'a hanya da tausayi  ba , fuskarsu a had'e take Kamar hadari Wanda kana kallonsu zaka hango tsantsar rashin imani a tattare dasu ,tafiya suka farayi a hankali cikin wani irin salo har suka k'arasa babbar k'ofar da zata sadasu da babban falon gidan,. 


Wow shine abunda na fada lokacin da nayi arba da wannan had'ad'd'en falon Mai matuk'ar girma da kyau Babu ce kawai Babu a falon, , Basu tsaya anan ba direc suka nufi wani korido sai gasu a wani Dan k'aramun falo Wanda ya tsaru iya tsaruwa don ya doke na farkon a komai, 


Kujeru ne kusan goma Sha biyu a wajan ,goma suna gefe yayinda aka tsara wajan ko Ina kujera biyu da table a tsakiya , an shak'e table din da kayan ci da Sha kala-kala, sai kujeru biyu  a gefe Wanda mutanen ke fuskantarsu , zama sukayi bisa kujerun wasu suka Fara danne-dannen waya yayinda wasu suka bude computer da suke rike da ita suka Fara bincike a ciki, abun mamaki tunda suka fito daga motocinsu har zuwa wannan lokacin ba Wanda yayiwa wani magana acikinsu ,


Kamar 20mnt sai ga wata makekiyar kofa ta bude ,sai ga wani mutum ya fito Yana sanye da shadda Fara Kal dinkin babbar Riga ya kafa wata bak'ar hula Wanda kana kallo kasan ba k'aramun tsadane da ita ba, mutumin bak'i ne wulik' Yana da manyan ido jajaye yayinda fuskarshi take a had'e Wanda hakan yak'ara fito mashi da ainahin muninshi , Alhaji Saminu Sulaiman kenan Mataimakin gwamna a jahar Lagos , 


Fitowarshi keda wuya duk mutanen Nan suka mik'e tsaye cikin girmamawa, a tare suka furta welcome sir, gyad'a kanshi yayi a hankali kamun ya nemi waje ya zauna Akan daya daga cikin kujerun Nan biyu da sukayi saura, 


Zaman suma sukayi suka nutsu don jin abunda shugaban nasu zaice, 

Gyaran murya yayi a hankali yace , "

Ina jinku ya ake ciki, ? duk da shekaranjiya na tsinci labarin da yafi kowane labari a wajena Wanda hakan ba k'aramun sanyani farinciki yayi ba hakika kunyimun abunda naji dadinshi sosai duk da dama can ban taba saku aiki ya gagara ba , Amma duk da Haka inason ji daga gareku, 


Daya daga cikinsu ne ya Mike Wanda ya kasance shine babbansu gaba Daya Mai suna *big boy* cikin muryarshi Mai kama da injin markad'e yafara magana , yace ,

"Ai oga yadda kabamu umurni haka muka aiwatar ba tareda tausayi ko Imani ba sannan munyi komai cikin taku bamu bar kowace shaida da zata sa a gane cewa ba gobara ce ta tashi a gidan ba , Saida muka masu hukunci Mai tsanani sannan muka sakar masu gas muka toyesu tass inada tabbacin ko tokarsu baza'a samu ba , yakarasa maganar Yana wata irin dariyar jin dadi,


Wata irin dariyar basawa Alhaji Saminu ya fashe da ita wadda kanaji kasan ta mugunta ce yajima Yana babbakata sannan ya shiga yiwa kanshi kirari ,

Duk Wanda yaci tuwo Dani Miya yasha

Saini kurungu mugun dutse

Murucin kan dutse nake banfitoba Saida na shirya

Nine mugu uban miyagu 

Yaro yarone baisan wuta ba sai yataka

Ta'bani kuwa daidai yake da ta'bo ajalinka ..........

Daga Haka Kuma sai yafashe da wani irin kuka Yana fad'in inaaa ban huce ba banajin na huce haushi na sai yaushe ne sai yaushe zanci cewa na huce akan abunda wannan Dan banzar yamun !!!!!!


Duk yaran tsuru sukayi suna kallonshi da tsoro. Abunda zai iya aikatawa , suna ganin to miye ya rage Kuma tunda ya dauki fansar shi mafi munin fansa to mikuma zai dameshi , idan bai hak'ura ba to da waye zaiyi tunda Wanda yakeyi dominshi ko 'tokarshi Babu a doron k'asa!!


A tsawace yabasu umurnin su 'bace mashi da gani kamun ya tashi ya nufi wani daki gaban wani makeken photo ya tsaya ya tsurawa pic din ido bako k'yaftawa ,

Su big boy kuwa tashi sukayi suka fita daga falon suka shiga motocinsu sukabar cikin jejin kamar yadda suka shigo,



************************




Zaune take Akan makeken gadonta kanta yana cikin k'afafunta tana sanye da riga da wando masu matuk'ar laushi da tsantsi yayinda sukabi lafiyayen jikinta suka lafe ,kanta Babu dakwali yayinda dogon gashinta da yake harmutse ya sauko  saman kafadunta har ya rufe Mata fuska baki daya ,


Wata yarinya ce da bazata wuce shekara 16 ba ta shigo tana sanye da uniform na Yan aikin gidan ,hannunta rik'e da k'aton tire Wanda ta shak'owa uwar dakinta kalolin abinci akai ,saboda tun kwanaki  biyu da suka wuce Bata k'ara Sanya wani Abu a cikinta ba da sunan abinci , 


A hankali ta taka har inda take cikin tattausan lafazi tace " ranki ya dad'e ga abinci irin Wanda kikeso na girka maki don allah ki daure kici kinga Momy gaba Daya ta d'aga hankalinta saboda halin da kike ciki sannan..... .........hannu ta d'aga Mata kamun ta d'ago da kanta a zafafe cikin ficewar hayyaci idanunta Kamar gauta saboda tsabar ja Kai kace ba a ta'ba hallitar fari acikinsu ba, cikin wata irin tsawa  tace " Ina Wasa dake ne ? Ina ruwanki Dani ! Na mutu Mana dame zai shafeki ! Oya maza kibar nan Kuma kar nakara ganin shegun kafafunki anan wajan, inba hakaba wallahi sai na karyasu tayi maganar idonta a juye Kamar wata Yar k'waya , 

Azabure wannan Yar aikin tabar dakin jikinta har rawa yakeyi tana rayawa aranta lallai abun na madam kullum Kara gaba yake to Allah ya kyauta , (nace Amin dai)


Ke Haule ya akayi Bata kar'bi abincin ba ?

"Eh hajiya tace karna Kara zuwa inda take inba hakaba zata karyani ,

Shiru hajiya Aisha tayi da alamar damuwa a fuskarta tace "jeki kawai"

Tashi tayi ta tafi dakin yarta *Amna* yadda Haule ta barta Haka Momy ta sameta , zama tayi a gefenta ta dafata tace kinga Amna kiyi hkr ki rungumi kaddara wannan damuwar da kikeyi ba ita zatasa wanda ya mutu ya dawo ba tunda............bige hannun uwar tayi tace "Ni kidaina ta'bani ke ba Momy na bace Sam bakwasona tunda kuka zabi rabani da farincikina , miyasa miyasa Momy ya zakuyi Haka akan son zuciya ???  to inaso kisani daga ke har Dad bazaku sake ganin farincikina ba har abada duk da inaji a jikina Yana raye , tabbas Yana raye...............✍🏼



Tooooo wata sabuwa sukuma wadan nan daga ina🤔🤔🤔🤔🤔🤔



*Karki wuce baki karantaba kila ki amfana*👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻



MAGANIN NANKARWA

Assalamu'alaiki Auntyna barkada war haka Dan Allah ki taimaka min da maganin nankarwa stretch marks Nagode sosai Allah Ya Kara basira Ameen


Da farko dai shi Nankarwa wasu tabbai ne layilayi da suke fitowa mace a jiki musamman wacce ke dauke da ciki zuwa haihuwa Wanda idan anyi maganin sa da wuri wato daga fitowar sa zasu iya bacewa gaba daya amma barin shi ya dade kan hana sa bacewa gaba daye sai dai zai dushe ya zama dan kadan kadan ake iya gani

Suna fitowa ne a wurare kamar haka :-


Cikin mace daga kasa (mara)

Cinya 

Saman mama 

Mazauni 

Saman hannu ta wuraren hammata 

Da sauran su.

ME KE KAWO NANKARWA ?

Akwai abubuwa da dama da suke sa nankarwa kamar:-

1-daukan ciki zuwa haihuwa (wannan shine babban abinda ke kawo nankarwa)

2-ramewa tashi daya (ga mutum mai qiba)

3-yin qiba tashi guda (ga mutum mai rana)

4- gado daga mahaifiya 

5-jinya na tsawon lokaci 

6- damuwa mai yawa da makamantar su


MATAKAN NANKARWA 

Yana da matakai guda uku gasunan kamar haka:-

1) farko fitowar sa zaki gansu sirara yana da pink kala sannan yakan yi kaikayi wannan matakin bashi da wahalar magani

2) zai zama ja ko ruwan bula sannan girman su zai karu yanzun kam babu kaikayi sai lokaci zuwa lokaci zai iya bacewa ki ya ragu ya danganta da yanayin jikin mutum

3) zai zama fari ko ruwan silva wannan kam yana da matukar wahalan magani sai an jure shims din sai dai ya ragu ba wai ya bace baki daya ba.


HANYOYIN MAGANCE NANKARWA


Ruwa

Ruwa da Kuke gani yafi komai mahimmanci a jikin dan Adam. Rashin shan ruwa yana sa jikin mutum ya bushe ya tattare tare da saurin tsufa a yayin da yawan shan ruwa kofi 8-10 kullum yake sanya taushin jiki da kyawun fata kuma da hana wasu cututtuka da dama kama fatar mutum da wuri.

MISALIN YANDA ZAKA SHA KOFI 8 ZUWA GOMA ACIKIN KO WACCE RANA

-Kofi 2 da zaran kin gama wanke baki da safe.

-Kofi daya bayan karin kumallo 

-kofi Daya Kafin azahar kisha 

-kofi Daya kafin abincin rana daya bayan kin gama ci.

-kofi daya da la'asar.

-kofi Daya kafin abincin dare kofidaya bayan kin gama ci.


MAN CIKA-GIDA (CASTOR OIL)

Wannan man yana da Matukar amfani wajen magungunan da suka shafi fata kamar maganin pimples, cin zanzara, tabbai da sauran su.

YANDA AKE AMFANI DASHI 

Ki dibi kadan sai ki sa a wuta yayi dumi sannan ki shafa a duk inda kika san yana da nankarwa ajikin ki da dumi duminsa ba yanda zai kona ki ba. Kiyi hakan har na  tsawo wata guda.

Ko kuma ki shafa man sannan ki dauko yadi mai taushi na cotton ki rufe wurin dashi ki Zuba ruwan dumi a gora ki riqa dorawa a saman yadin.


ALOE VERA

Ki tatse farin ruwan aloe vera kullum ki riqa shafawa a wurin idan ya bushe sosai sai ki wanke da ruwan dumi

Ko kuma ki diba man aloe vera din chokali daya ki hada da vitamin E oil capsule daya ki shafa a wurin.


FARIN KWAI 

K fasa Kwai daya ki cire kwaiduwan kwan ki yar sai kiyi amfani da fork ko whisker kiyi ta kada farin kwan har sai yayi kauri ya yi fari tas kamar cream sannan ki shafa a wurin nankarwan ki barshi ya bushe sannan ki wanke da ruwan sanyi kiyi tayin hakan har na tsawon sati biyu.


RUWAN LEMON TSAMI

ki matse lemun tsami sai ki diba ruwan ki riqa shafawa in circle a inda nankarwan suke har sai kinga ya bushe ki barshi bayan minti goma ki dauraye da ruwan dumi.

Ko kuma ki hada ruwan lemun da ruwan nukakken cucumber sannan ki shafa.


SUGAR 

Ki hada suga da almond oil ko zaitun ko man kwakwa da ruwan lemun tsami ki shafa tsawon minti goma sannan ki shiga wanka.


RUWAN DANKALI 

Ki fere dankali sai ki dauki guda daya ki dan jajjaga ki shafa ruwan a inda nankarwan take idan ya bushe zaki ga yayi fari sai ki wanke da ruwan dumi ki shafa zuma ko zaitun ko man kwakwa.


MAN KADE 

yawan shafa man kade a wurin ma yana rage shi sosai. 

Daga karshe Ina kira ga mata da su daure da zaran sun haihu su fara neman hanyan magance wannan matsalar kuma ku sani cewa wannan hadin gargajiya ce babu kemikal acikin ta dan haka yana daukan lokaci kafin aga canji kamar Sati biyu idan baki ga chanji ba sai ki dauki wani kuma. Allah shine masani. Allah yasa mu dace.


A yayin da ta fito, ta kan zamewa mutane karfen kafa domin ta na da wahalar fita.


Ga hanyoyi guda 5 da za’a iya magance su a saukake ba tare da amfani da mayuka masu illlata fata ba


 


Hanya ta 1: Dankalin hausa


Dankali yana dauke da sinadarin sitaci da yake lausasa fata da kuma sinadarin da yake hana fata lalacewa wato antioxidant. Haka kuma dankali yana dauke da sinadarin vitamin c, potassium, thiamin, riboflavin, iron, zinc da sauran su.


Yanda ake amfani da shi:


A yanka Dankali sannan a shafa a hankali a kan nankarwar. Sai a barshi na tsahon mintuna 15 zuwa 20, sannan a wanke da ruwan dumi. A maimaita haka a kullum


Hanya ta 2: Aloe Vera


Ruwan da ke cikin Aloe vera yana dauke da sinadarin Collagen wanda aka san shi da gyara fatar da ta lalace da kuma kara dankonta, kyanta da kuma yarintar ta.


Yanda ake amfani dashi:


A karya ichen Aloe vera guda sai a shafa ruwan a kan nankarwa. A barshi tsahon awa 2 zuwa uku sai a wanke da ruwa. A maimata hakan a kullum har sai an samu sakamako mai kyau


Hanya ta 3: Man kadanya da Koko butter


Hadin Man kadanya da Koko butter yana dauke da sinadarin vitamin E da kuma sinadaran da ke hana fata lalacewa


Yanda ake amfani da shi


Za’a samu koko butter karamin cokali 2, da man kadanya shima karamin cokali 2, sai sinadarin vitamin E karamin cokali 1. Za’a narka man kadanya da kuma man Koko butter sai a kara vitamin E din a ciki a gauraya. Za’a dura gabadaya a cikin mazubi a ajiye a na shafawa a kan nankarwar kullum.


Hanya ta 4: Lemon tsami


Acid din dake cikin lemon tsami yana taimakawa wajen warkar da ciwo, kurajen fuska da kuma nankarwa.


Yanda ke amfani da shi:


A yanka Lemon tsami gida 2 sai a shafa shi a gurin da nankarwar take. A barshi na tsahon mintuna goma sai a wanke da ruwan dumi. Ko kuma a hada ruwan Lemon tsamin da ruwan kokwamba a shafa a wajen. A yi hakan a kullum idan ana san samun sakamako mai kyau


Hanya ta 5: Man zaitun


Man zaitun yana dauke da sinadaran vitamin A da E wanda suke kara gudun jini zuwa karkashin fata da kuma kara laushin jiki. Suna kuma hana lalacewar fata.


Yanda ake amfani dashi:


A dan dumama Man zaitun a wuta, kar yayi zafi da yawa yanda zai kona fata. Sai a shafa a gurin da nankarwar ta ke. A yi hakan da safe da yamma a kullum.


*Daga taku har kullum mmn Yusuf Mai kayan Mata*😍😍😍😍😍😍


Post a Comment

ADS HERE
ADS HERE