Posts
JANNAT (tsugunno bata kare ba) page 2
*⚖️👩🎓🎓 JANNAT (tsugunno bata kare ba)🎓👩🎓⚖️* LABARI DA RUBUTAWA (MRS ABDULL CE✍️)_ *Hakkin mallaka na mrs Abdull ne kawai ban yarda wani ko wata ya juya min labari na ta kowacce siga ba hakan laifi ne mai girma kuma tabbas zan dau mataki, idan suna ko halayya yazo daya akasi ne, labari na kirkirarren labari ne banyi shi dan cin zarafi ko tozarci ga wani ko wata ba, kuma insha Allah zan ringa posting sau hudu ne a sati* _Littafin SADAUKARWA ne ga mamana *Khadijah sulaiman Gombe* alkairan Allah su tadda ki har gadon bacci_ https://chat.whatsapp.com/JWinbPSk9h5FGL7KmFbWg1 *_________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_________________________________* *Kasan addinin ka* ```LOKUTA HUDU NA AMSA ADDU'A``` Da Sunan Allah Mai Rahma Mai Jin ƙai 2.YAYIN SAUKAN RUWAN SAMA: Haka Kuma Lokacin Saukan Ruwan Sama Lokaci ne Na Amsa Addu'oin Bayi. Hadisi Ya Tabbata Manzon Allah (ﷺ) Yana Cewa: عن ﺳﻬﻞ ﺑﻦ ﺳﻌﺪ رضي الله عنه قال: ﺃﻥ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻗﺎﻝ: ”ﺛﻨﺘﺎﻥ ﻣﺎ ﺗﺮﺩﺍﻥ : ﺍﻟﺪﻋﺎﺀ ﻋﻨﺪ ﺍﻟﻨﺪﺍﺀ ، ﻭﺗﺤﺖ ﺍﻟﻤﻄﺮ “. {ﺍﻟﺤﺎﻛﻢ: ٢٥٣٤} An Kar6o Daga Sahli bn Sa'ad (ra), Lallai Manzon Allah (ﷺ) Yace: “Addu'oi Biyu Ba'a Mayar Dasu: Addu'a Yayin Kiran Sallah da Kuma Addu'a Lokacin Saukar Ruwan Sama”. {Abu-Daud: 3078} ______________________________📲 ~SHAFI NA BIYU~ Sai da ta gama aikin ta tsaf sannan ta fito daga kicin, ana ta salla a masallaci dan haka kai tsaye daki ta wuce don mika farali, katon bedroom ne mai dauke da gado da durowa sai madubi da wani showglass mai dauke da turaren wuta, a cike yake da turaren wuta da humra kala_kala, Babu wani tarkace a dakin,gadon yasha gyara da rantsattsen zanin gado mai daukar hankali, kai tsaye bandakin ta wuce ,bayan ta gama bukatun ta ta yi alwala ta fito, kai tsaye ta tada salla bayan ta gama ta zauna tana azkar na maraice, horn taji kafin daga bisani aka bude gate, cikin ranta ta raya ''Alhamdulillah sun dawo.'' miƙewa tayi bayan ta kammala ta fito parloun ,dayday lokacin suka shigo parloun dauke da jakankunan su duk zube su suka yi a kan tattausan kafet din dake tsakiyar parloun, nasmah ce ta matso kusa da ammin su ta daura kan ta a kan cikin ta ta zagaye hannunta zuwa bayan ta tayi luf a jikin uwar, a hankali JANNAT ta ɗago kan ta tana fadin ''ya ya day nasmah ? Jkin ne.'' kasancewar yarinyar ba mai koshin lafiya ba kullum tana cikin ciwo shiyasa komai nata ya tafi daban a yaran bata da irin kiciniya na yara masu lafiya haka nan take. ''Tun a makaranta kanta ke ciwo amma munje an bata magani da sauki ma yanzu kam dazu jikin ta ya danyi zafi ba kamar yanzu ba, ya sake.'' cewar juniour yana kallon ammin nasu. ''Allah ya kara sauki ya yaye.'' JANNAT ta fada tana kama nasmah zuwa kan kujera ta kwantar da ita. Kallo yaran JANNAT tayi sannan tace ''A tashi a yi wanka ayi salla maza a ci abinci idan kuma anyi a makaranta to sai a yi wanka a fito a ci abinci.'' ''To'' suka amsa sannan suka wuce juniour yayi dakinsa itama nasreen ta wuce nasu dakin. Cikin kulawa JANNAT ta kalli nasmah tace ''Ina ke miki ciwo?'' A hankali nasmah tace ''Kai na ne kawai kuma shima ya kusa ya daina.'' ''Ok Zaki iya yin wanka ko?'' ''Zan iya ammi.'' nasmah ta fada tana mikewa dakin su ta wuce,inda JANNAT ta bita da kallon tausayi, bata da isasshen lafiya ko kadan yarinyar. ****** Bayan sun gama cin abinci a al'adar su kullum zasu dauko abin karatu zuwa magriba kamar kullum, dan haka duk suka fito da takaddun su domin yin karatu, yau kam nasmah bata jin dadi dan haka juniour da kanshi ya fara koyawa nasreen homework. Suna tsaka da karatu HUDAY ya dawo kamar kullum kafin magriba. Bayan sun mishi Barka da zuwa ya wuce dakin shi JANNAT na biye dashi, ''sannu da zuwa my love'' ''Yawwa sannu angel ina mamana kuwa ban ganta a parlou ba?" ''Nasmah bata da lafiya jikin ta yayi zafi way an bata magani a skull yanzu tana kwance bacci ma ya dauke ta,.'' ''Subhanallah yanzu ya jikin nata day?'' HUDAY ya tambaya yana zaro mayan idanunshi. ''Kwantar da hankalin ka jikin da sauki har tayi bacci ma go and bath, ka fito an kusa kiran salla.'' Ajiyar zuciya ya sauke yana faɗin ''masha Allah, Allah ya tsayar haka, wallahi ciwon NASMAH yana bani tsoro!. ''Insha Allah babu komai kayi wanka an kusa kiran salla. ta sake maimaita masa , da 'To' ya amsa sannan ya fara cire kayan sa, taimaka masa tayi ya cire sannan ya nufi banɗaki , sai da yaje bakin banɗaki yace ''haka ne abin kuma?'' yayi maganar yana tura baki, cikin dariyar ta da take kunshe wa tace ''me kuma nayi dan Allah?'' ''Azo a tayani wankan'' ya faɗa kamar karamin yaro, ''pls ya HUDAY kayi wankan ka an kusa kiran salla fa dan Allah kaji?'' bai ce komai ba ya wuce toilet yana dariya. ***** Bayan sallar isha suka shigo gida daga masallaci, suna shigowa HUDAY yace su shirya zasu je gidan uncle Hakeem,tsalle nasreen ta kamayi tana fadin zanje wajen leemat zan ga leemat,dariya duka suka yi nasmah ma da bata jin dadi sai da tayi dariya kuma tayi farin ciki sosia sabida zuwa gidan uncle Hakeem yana dauke mata kewa ba dan kadan ba sabida akwai yara Sa'annin ta su samha da samiha, shi kuma juniour dama ba'a magana , idan za'a je gidan uncle Hakeem yafi kowa murna a cewar sa gidan shi za'a je Kasancewar uncle Hakeem mai sunan shi ne sannan kuma ga mai sunan HUDAY (imamu)dan gidan uncle Hakeem din haka suka shirya tsaf suka wuce gidan uncle Hakeem, ƙatuwar jeep ce Wanda idan zasu je anguwa Dukansu driver ke kai su, Ishaq(direba) da HUDAY suna gaba sai JANNAT ita da yara a baya, suna yan taɗi jefi jefi har suka isa gidan uncle Hakeem, a katon gate din ishaq yayi horn, mai gadi ya bude gate din suka kutsa kai ciki, inda ya dace ta parking anan ya faka su kuma suka fito daga motar ,idan ka gansu gwanin ban sha'awa. Cikin gidan suka nufa, kofar da zata sada su da babban falo na gidan. Tun kafin su shiga hayaniyar yaran ya riske su. Nasmah da nasreen da gudu suka riga ciki, su HUDAY suka bi bayan su suna dariya. Katon falo ne mai dauke da tarkace na wasan yara su keke ne su mota ne babu abinda babu kadangare roba raƙumi sune a zuzzube, Dattijo ne da a ƙalla zaiyyi 60 Yes a zaune kan kujera yana kallon yaran suna ta wasan su idan zasuyi fada ya tsawatar musu fuskar shi dauke da murmushi, shigowar su nasmah da gudu ne ya saka falon kaure wa da ihun murna nasmah ta rungume samha, suna tsalle nasreen kuwa ita da Abubakar ne suke nasu tsallen, uncle Hakeem ya Mike yana faɗin ''Barka da zuwa son! Kune a tafe?'' Cikin murmushi HUDAY yace "wallahi uncle kawai nace bari mu yi ziyara" ''ahhh masha Allah hakan yayi daidai Bismillah zauna'' ya fada yana komawa kujerar da ya taso ya zauna. JANNAT har ƙasa ta tsugunna ta gaida uncle Hakeem, cikin fara'a ya amsa yana tanbayar ta yara. ''lpya kalau uncle gasunan'' ta amsa tana miƙewa domin shiga ciki. 'masha Allah'' ya faɗa yana murmushi shima. Kai tsaye dakin anty Hafsah ta wuce matar uncle Hakeem ta idar da sallan isha bata ko tashi daga sallayar ba , zama JANNAT tayi tana faɗin ''antyn mu.' ''Yar gari kune a tafe dare dare?'' ''wallahi kuwa anty ya gida?muka ce bari muyi ziyara sai mu wuce.'' ''Ay kuwa kun kyuata wallahi'' cewar anty Hafsah tana nade sallayar da tayi salla. Uncle Hakeem ƙanin mahaifin HUDAY ne da baban HUDAY da uncle Hakeem uwa daya uba daya suke ya'yan uncle Hakeem biyar, na farkon yan biyu ne wanda kusan rana daya aka haife su da juniour imamu da batool, sai na biyun ma yan biyu su kuma duka mata samiha da samha, sai na biyar din Abubakar mai sunan baban HUDAY, a hankali zaku fahimci wannan ahalin idan muka shiga cikin labarin gadan gadan. Anan suka yi hira har goma da rabi sannan suka koma gida kamar a barsu nasmah acan haka suka ringa ji basa gajiya da gidan uncle Hakeem. Suna komawa gida aka fara shirin bacci dan kowa ya gaji kasancewar asabar ce washe gari shiyasa babu wata damuwar tashi da wuri ko wani abu sai day sallar asuba kawai a cigaba da bacci. Sai da ta fito wanka ta shirya tsaf tana shirin hawa gado ta tuna bata kashe waya ba, dan haka ta dauki wayar tana kokarin kashe wa,rabonta da waya tun da safe a kotu sai yanzu, sakon ne ya hana ta kashe wa, tana ta wasiwasi ta duba ko kuma ta kashe kawai, a hankali ta bude sakon, HUDAY da ke kan gado yana kallon ta har ya mike ya iso wajen ta bata sani ba sai zare ido take kamar taci kudin ayka. ''Menene angel?'' ya tanbaya da neman karin bayani Bata ce masa komai ba sai mika masa wayar da yayi ta koma bakin gado ta zauna ta haɗa kai da gwiwa. A hankali yake karanta sakon har ya gama sannan yace ''Number Nigeria ne, haka yana nufin ta shigo kasar ko ma ta iso gomben baki daya ne? Indai kuwa haka ne , nuwairah ta shiga hannuna bazata ji dadi ba zata fuskanci hukunci mai tsanani wallahi, taa kawo kanta. Ya faɗa idon shi na canza kala lokaci guda. Cikin damuwa JANNAT tace ''Ba damuwa ta Ni ba,damuwa ta ya'yana, damuwa ta anty da abuu da kuma kai, idan ta cutar min da wani daga cikin ku zuciya ta bazata dauka ba, zan iya jure komai amma banda cutar da daya daga cikin ku! ''Babu abinda zai faru JANNAT ki kwantar da hankalin ki, a baya nuwairah tana ihu ne daga nesa, amma zuwa yanzu nasan ta shirya tsaf domin tunkarar abinda ta saka gaba, amma nasan cewa matata ta rigata shiri, ke mai dakakkiyar zuciya ce kada ki bari zuciyar ki tayi sanyi wajen taran abokan gaba, ki shirya karɓar nuwairah a duk yanayin da tazo miki, kada ki daga mata kafa, kuma kada ki saurara mata, na miki alkawarin samun goyon baya daga gareni da duk wani taimako da zan iya.'' HUDAY ya faɗa alamun kara bata karfin gwiwa. ''INSHA ALLAH yaya HUDAY nayi alkawarin kawo bayan karshen rashin mutumci irin na nuwairah,da duk wani mai hali irin nata domin ya zama izina ga wasu masu shirin aykata laifi irin nata.'' JANNAT ta faɗa tana dora kanta kan kafadar HUDAY. ******* _Nuwairah_ Kai tsaye gida usama(use boy) ya kaita, gidan da ya kasance nata mallakin kanta tun bayan da karayar arziki ya samu mahaifin ta, gida ne madaidaici mai dauke da abubuwan more rayuwa wanda wani minister ya mallaka mata shi, dan haka ta dauko iyayen ta ta saka su a ciki. Suna isa use boy ya fita ya bude gate yazo ya shiga dasu, Kasancewar har yau bata saka mai gadi ba a cewar ta sai ta dawo zama daram cikin gidan tukunna yanda zai ringa bude mata gate Yana rufewa idan ta tashi shigowa da mota. Bayan yayi parcking ya zagayo ya bude mata kofar ta fito, karamar jakar kawai ta dauka usama ya dauki trolleyn. Kai tsaye cikin gidan suka nufa, madaidaicin parloun mai dauke da kayan alatu da more rayuwa, tv ne madaidaici na bango akan abin dora tv irin na zamani yana ta ɓaɓatu a tashar mbc, babban mutum da a ƙalla zai kai shekaru 67 ko da 8 zaune kan kujera cikin shadda ruwan goro da sandar guragu a gefen sa cikin tsafta yake tass dashi babu wani datti da alama kafar sa guda ɗaya ce kawai. Cikin siririyar Muryar ta ta shigo tana fadin ''Hi guys'' da murmushi akan fuskar shi ya ɗago kamar zai tashi ya rungume ta sabida murnar ganinta ,da alama dama yana begen ganin nata. Itama cikin dariya ta zo har kujerar da yake zaune ta zauna ta dora kanta akan kafadar shi ''dady na! Ta faɗa kamar ta saki kuka. ''My daughter how are you? How is everything? I missed you so much my dear'' ya faɗa da alamar damuwa a kwance a fuskar sa ''Am fine dady ya jiki? Duk da nasan day usama yana kula da kai babu wata matsala ko ina mom? ta fada tana waige waige. ''Mom dinki ta fita Amma zata dawo ba da dade wa ba, nayi missing dinki nuwairah.'' ''nima haka daddy Amma ka kwantar da hankalin ka zuciyar ka tayi maka sanyi ka saka a ranka matsalar mu ta gama zuwa karshe, na shirya tsaf na daura damarar tunkarar duk wani wanda yake son ganin bayan mu,Ni ce zan ga bayan su dad, kudi na nemo kudi dady! Kuma ina kan neman su ina da tabbacin zan cigaba da samu har lokacin da bukata ta zata biya, bazan taba bacci da ido na guda biyu ba har sai na tabbatar rayuwar ahalin commissioner Abubakar ta shiga cikin tagayyara, Hajiya sadiya ita ce mutum ta farko a rayuwa da ta fara kawo maka nakasu a cikin lamuran ka wanda har zuwa yau kake cigaba da samun nakasuun, sannan HUDAY shine mutum na farko da ya fara kawo min cikas cikin rayuwa ta daga karshe matakin da ya dauka na sauya min halitta daga mai kunne zuwa akasin haka na dawo mai kunne guda daya, matar sa kuwa ita ce halitta ta farko da na tsana cikin wannan duniyar sannan ya'yan da ya haifa suka biyo baya, tabbas zan dau fansa a kansu, Allah ya ajiye ka dad amma Ni ya daga Ni, zan bi kowacce hanya domin ganin na rama duka wadanda abubuwan, basu san Ni ba dad Basu san sun kwaso ruwan dafa kansu ba, zanje Abuja da na dawo akan su zan fara ayki ,sai na nemo hanyar tozarta su ko da kuwa zan rasa raina ne, suna daukar abin wasa basu san cewa _*tsugunno bata kare ba*_ .'' tayi maganar tana kallon mahaifin ta. ''Ina alfahari dake daughter ke din mace ce mai kamar maza duk hanyar da zaki saka sadiya kuka na baki damar ki nemo ta, duk hanyar da zata kamu da ciwon zuciya na miki umarni ki lalubo domin ki cusa mata ƙunci da bakin ciki.'' Nayi maka wannan alkawarim dad kaji?'' ta fada tana miƙewa Dakin da ya kasance nata ta shiga da trolleyn ta da use ya shigo mata dashi, a gyare komai yake sai dan ƙurar da baza'a rasa ba ,bata bi ta kan komai ba ta shiga wanka, tana fitowa ta shiga goge jikin ta, kira ne ya shigo wayar ta ko ta kai bata bi ba ta cigaba da abinda take yi, kusan minti biyar aka sake kira dan haka ta dauka sai taga Hajiya hari a kan screen yana yawo, a hankali ta dauka ta saka a kunne tana bata fuska, "Hello nuwairah ykk ya gida? Yanzu usama yake gaya min kin shigo gari , wallahi muna cikin tadi dashi sai ga kiran uwar gidan deputy ta ƙira way tana da appointment da wasu damusoshi shine take son a Bata wata mai zafi, kece kawai zaki iya da uwargidan deputy da ahalin ta,kuma kinsan ayki dasu ba karamin harka bane a da ma balle yanzu da suke kan ganiyar su,shiyasa nace barin miki magana sai inji ko zaki shiga dan idan kin samu ay Nima kin ga na samu! ido nuwairah ta lumshe tana sauraran Hajiya hari, duk da ta gaji tana bukatar hutu amma dole zata yi wannan aykin sabida tana bukatar kudin cigaba da aiwatar da abubuwan ta, bata son kudi su yanke mata, ''sai tayi din bazai zo da matsala ba'' ta raya a zuciyar ta. Maganar da aka yi ta wayar ne ya katse mata tunani... ''kina jina kuwa nuwairah hello?'' " Ina jinki hajjaju! Kwana nawa ne sannan nawa ne kudin aiki?'' ''Kamar ta gaya min kwana uku ne, kuma kudin zasu kai kamar 1.5 million, Amma kin San zasu iya wuce haka ɗin ma tunda 3 days ay da yawa watakila a hadu da wasu Lion's din a can.'' ''A ina ne kuma yaushe zamu wuce? Gaskiya ina da appointment da wani Minister on Tuesday a abuja Kuma kince 3 days ne kinga yau Friday Kar mu wuce kuma ya kira Ni inda nake dashi kuma da nisa, appointment ya wargaje ina tsammanin wajen 2.5 million a wajen shi kinga kar nayi asarar! Nuwairah ta fada tana duban kanta a madubi. Daga wayar aka ce ''Shikenan ma faduwa tazo dai-dai da zama dama jirgin dare zaku bi zuwa Abuja kinga idan kin gama da nasu sai ki fara naki kun gama on Monday shi kuma sai ki fara nashi on Tuesday din hakan yayi ko?'' ''Is ok Hajiya, use ya zo ya sauke Ni a airport din zuwa dare sai mu haɗe dasu acan kawai kafin nan na gama shirya wa.'' ''To babu damuwa hakan ma yayi sai na jiki.'' Ta fada tana tsinke wayar.✍️ (To niday nace ''wannan kuma wanne Irin ayki ne haka mai ɗauke da makudan kuɗaɗen🤔to Allah masani.'') *Mai bukatar JANNAT na farko zai iya Tuntuba ta don na bashi complete ya karanta domin gane inda aka dosa ta cikin wannan littafin na (tsugunno bata kare ba)* Kana bukatar farin ciki?😁 Yawaita istigfari 📿 *_Kafcen ba a haka zai tsaya ba kamar yanda kuka gani a sama zaku ga wani note basai na gaya maku na menene ba wacce ta karanta ta sani, to haka littafin zai cigaba da zuwa muku da abubuwa irin na gyaran jiki da kuma gyara aure da gyara sanwa da kuma gyara muhalli gyaran Addini yanda mutum zai kyautata tsarkin sa da kuma kyautata ibadar sa duk a cikin wannan littafi na JANNAT (tsugunno bata kare ba)_* *_Littafin JANNAT littafin kudi ne game buƙatar karanta wannan littafin daga farko har karshe zata biya kudin ta Naira dari biyu cas ta wannan account din 0009243783 Nafisa Rabiu Umar jaiz bank, sai a turo shaidar biya ma'ana Screenshot KENAN ta wannan lambar 07059305867 ko katin waya na MTN ta wannan lambar 07059305867 hoton katin za'a turo, free PAGES zasu kare ne da nayi page ashirin cif insha Allah. Na fada JANNAT (tsugunno bata kare ba) na kudi ne kar wata ta gaya min maganar wofi idan na gama free PAGES Dan bazan dauka ba a kiyaye. Mai bukatar biya zai iya biya tun daga yanzu domin wanda suka shirya har na fara jin alert, idan na gama free PAGES bazan tsaya ba zan cigaba ne da posting kawai._* #share #comment #Vote Pls Dan girman Allah duk wacce ta karanta tayi share sabida Allah _07059305867_ *MRS ABDULL ce*✍️
