ADS HERE
Posts

DIJANGALA PAGE 2

Kowa ya zaro ido yana kallanta Dad ya tambayeta dalili, ta ce masa tafi son sai Mustapha ya samu lafiya, Dad baya son takura mata, ya ce to shikenan amma Mum bata ji dadi a zuciyarta ba, haka suka cigaba da tattaunawa Mustapha a harabar gida yana biga kwallo cikin nishadi, Wani motane ya shugo, Haidar ne ya fito daga motar, Mustapha ya tsaya yana kallan Haidar, Haidar ya karaso wurinsa da sauri "Mustapha, kwana da yawa? " Mustapha ya shiga kallan Haidar da alamu bai gane fuskarsa ba "Nine babban abokinka Haidar" Mustapha ya ce ni ban sanka ba Cikin rashin fahimta Haidar ya Kara kallan Mustapha taya za ka ce baka sanni ba ko ka samu matsala ne a kwakwalwarka Mustapha ya tsorata ta yadda Haidar yayi masa magana rugawa yayi da gudu ya koma ciki Haidar ya bishi Dad da Mum da Hamrah da Grandma zaune Mustapha ya shugo da gudu Haidar na biye dashi "Zai kamani" Haidar ya gai da mutanen falon suka amsa gaisuwarsa Dad ya ce Haidar ya kwana biyu? Lafiya lau, "Dad meke faruwa da Muswasan," "Hatsarin da yayi ya dan taba kwakwalwarsa but insha Allah very soon komai zaiyi dai dai" "Subhanallah, amma abu baiyi kyau ba, to Allah ya bashi lafiya" "Amin" Dad ya nunawa Mustapha Haidar "ka ganshi nan abokinka ne, ku dinga wasa tare" Mustapha ya kalli Haidar "ka iya biga kwallo" "Eh na iya" "To muje mu buga" Suka fita harabar gida, suka shiga buga kwallansu, sosai Mustapha yake jin dadin wasan, ranar Haidar a gidan ya wuni sai da daddare yabar gidan Hamrah kwance kan gadon ta tana waya da wani abokinta da suka yi makaranta tare dashi a kasar Russia, Dan Katsina ne, shaida mata yake soyayyarta daya dade yana damunsa a zuciyarsa, ai kuwa ya samu karbuwa hannu bibbiyu, sannan ita Hamrah tana son hirar batsa haka sai suka hadu suka dace Washegari Mustapha ya fito yana buga kwallansa cikin nishadi, bai kula da fitowar Hamrah ba ya jefa kwallo ya sameta, ranta ne ya baci sosai, ta watsa masa mugun kallo "Wannan wane irin hauka ne da shashanci, bana son hauka, wallahi idan haka ya Kara faruwa saina tsinka maka mari" ta ja tsaki ta wuce, jiki a sanyaye ya dauki kwallansa ya shiga ciki Ashe mum tana daga saman bene tana ganin abin dake faruwa, ta kasa jurewa hawaye ya fara bin kumatunta, fadi take yi "yau Mustapha shine ya zama abin wulakantawar Hamrah, lallai rayuwa kenan, na haramtawa Mustapha auren Hamrah koda yau ya samu lafiya, haka ta cigaba da tunani Washegsari Mum ta gama shirin tafiya Hadeja Mustapha ya tada rikici wai sai dai ta tafi dashi, tayi mada duk wani dibara amma yaki ya yarda, babu yadda ta iya haka ta tafi tare dashi Gida ya cika yen uwa da abokan arziki duk sun taru, matan Ya Haruna da Mahmud duk sun zo, Fatima ma tazo daga kano don ita a kano take aure, itama Aishs a Kano ta samu miji, Mum da Mustapha na karasowa gida ya dauki murna "Lale marhaban kawai kake ji" Dije tun data samu labarin zuwan Mustapha taje ta debo ruwa ta shiga bayi tayi wanka sannan ta fito ta zauna tana goge kaujen kafarta, bayan ta gama taje daki tasa kayanta, Dije ta fito tsaf tsaf Dije rike da tayarta ta fito waje zata tafi yawo ta hadu da Mustapha, kallanshi ta tsaya yi, tana ganin kamar shi kamar bashi ba, don tasan Ya Mustapha akwai gashi a kanshi, wannan kuma babu gashi, a zuciyarta ta ce shine fa, shima kallanta ya tsaya yi yana tunani a zuciyarsa kamar ya taba ganinta "Wallahi Yaya nayi wankana, yau banyi wani laifi ba" ta fada cike da tsoro Baibi ta kan maganarta ba ya fara zaiyano mata tambayarsa "Ina ne ake buga kwallo a garin nan?" "A filin kwallo mana" "Rakabi" Babu musu ta ce "to" amma a zuciyarta sam sam bata so ba, Haka suka jera suka tafi Da suka iso filin kwallo babu kowa, kallan Dije yayi "Babu kowa" "Ai sai anjima suke fitowa" "To wani irin wasa kika iya saiki koya min" "Yaya kaima ashe kana wasa?" "Ina son wasa" "Ka iya gara taya? " "A'a" "To bari na koya maka" Nan take Dije ta shiga kada taya a filin makaranta yana kallanta yana nishadi "Nima zanyi, bani nayi" Mika masa tayar tayi ya fara garawa amma bai iya ba, tai masa dariya ta shiga koya masa harya fara iyawa Daga nan filin kwallo ya ce mata suje yawo, nan ta dauke shi yawo har gidan kawarta Rahane, suka je suka sameta da saurayinta da zata aura Rahane ta ce yauwa Dije dama ke nake nema ina son kizo ki ga saurayina Adamu Adamu ya gaisa da Dije, Mustapha bata rai ya yi ya kalli Dije Ni nan wurin bai yi min ba mu wuce Rahane ta ce Dije wannan fa? Yayana ne Adamu ya ce kamar na waye fuskarsa, yana kama da Musty Sule sosai Dije ta ce da sauri "ai to shine" Adamu ya ce haba Dije yada rainin hankali haka "To kenan karya nayi maka" Rahane ta ce Dije jeki gida ina nan zuwa anjima Dije da Mustapha suka yi wucewarsa A hanya suka hadu da me alale, Dije ta tare ta ta ce ta bata Alale, me alele ta ce ba zata bata ba Dije ta duke ta ta amshi alale ta gudu Mustapha ya bita, wani lungu suka je suka boye, suka zauna suna cin alalen suna dariya "Kai amma Dije kina birgeni" "Ai na fada maka kowa a garin nan tsorona yake ji" "Daga yau kece babbar abokiyata, kuma ina sanki sosai" Dije tayi murmushi saboda jin dadin zancen "Amma Yaya meyasa da baka sona kuma kake cin zalina" "Yaushe kenan? Ni dai ina sonki kawai" "To sai muyi aure, mu koma zama tare, mu dinga wasa kullum" "Zan fadawa Mum tare dake zamu tafi, kije ki dinga dukan min Hamrah" "Ai kuwa zan fasa mata kai" "Yaya ai kai mai kudi ne, kana da motoci da kudi da yawa kuma dama Baba ya fada min ni matar manya ce, kuma a waka ma an fada, an ce *Dijangala ta me gari ba auran talaka ba* "Kin iya waka, wakar tayi dadi" "Dagaske Yaya zaka aure ni? " "Yanzu ma zanje na fadawa Mum ayi mana aure sai mu tafi gidanmu mu rika yin wasa" Dije tayi murmushi "to tashi muje mu fada" Suka tashi suka kara gaba Hankalin kowa ya tashi a gida saboda ana ta neman Mustapha ba'a san inda ya je ba, Mum idanta ya cika da ruwa, kamar daga sama sai ga Mustapha da Dije sun zo cikin nishadi, kallan kowa ya koma kansu, Mum ta taso da sauri ta rungume Mustapha "My son ina ka je?" "Mun tafi yawo nida abokiyata" "Wace ce abokiyarka?" Mustapha ya nuna Dije Inna ta kalli Dije "Mustapha karka kara bin Dije yawo kar taje ta janyo fada ko wani abu ya kare a kanka" "A'a, ni zan dinga binta yawo, ta iya wasa kuma ina sonta sosai" Mum tai murmushi ta ce Dijangala ta kenan, na zo ina ta nemanki banganki ba "Inna mun tai yawo ne" Mustapha ya ce Mum zan fada miki wata magana "Ina sauraranka" Ina son Dijangala, kuma ina so muyi aure mu tafi gidanmu mu rinka wasa tare (ya kalli Dije) ko Dijangala?" Ta ce "ehmann" Inna ta kalli Mum, Mum ta kalli Inna sai suka fashe da dariya Inna ta ce kai Mustapha ina kai ina Dije, Dije ai sai bagidaje irin ta Mum ta bata rai "haba Yaya ya zaki ce haka, Dijen ne sai bagidace" Dije ta ce Inna ta birni nifa matar masu kudi ne, Baba me gyaran radio ya fada min kuma a waka ma an fada *Dijangala ta me gari, ba auran talaka ba* Mum ta tintsire da dariya "Allah ya shirya minke Dije" Dije ta cigaba "kinga kuma Yayana yana da kudi da mota masu yawa, kin ga shi mai kudi ne, kuma ina jin dadin wasa dashi "Nima ina jin dadin wasa da ita" Mustapha ya fada sannan ya cigaba, Mum nidai ita kadai nake so, kuma ni zan aure ta mu tafi tare "Nima Yayana ne kadai nake so, ban taba son wani a zuciyata ba sai shi kadai" Inna ta ja karamar tsaki, "kun ga ku fita bakin kofar gida ku yi wasa ni na gaji da jin shirmenku" Mustapha ya bata rai, Dije ta ja hannunsa tana "yi hakuri" suka fita, su Mum suka bisu da kallo Dije da Mustapha suka fito kofar gida, Dije hango jirgi tayi yana tahowa, hankalin ta ya tashi "Mustapha zo ka ga ni" suka jeru suna kallan jirgin sama, Dije ta farawa jirgin waving wato bye bye da hannu, ganin haka yasa shima ya daga hannunsa yana yin abinda take yi har jirgin ya wuce Dije ta kalli Mustapha "ina son jirgin sama" "Dagaske? " "Zan saya miki idan mun koma gida" Dije ta zaro ido cikin murna "Dagaske?" "Dagaske nake fada miki" "Ina sonka Yayana" "Nima haka Dije na" Nan Dije ta ruga a guje tana fadin ka biyo ni, bin bayanta ya yi da gudu basu tsaya ko'ina ba sai wurin Baba me gyaran radio Baba me gyaran radio zaune yana gyaren radio sai yaga Dije da Mustapha sun fado da gudu, Baba ya kalli Dijangala ya kalli Mustapha Dijangala ta nuna Mustapha "baba ka ga yayana, shi zan aura, me kudi ne shi" Baba ya ce ya yi kyau Dije, Allah sanya alkairi, to ya sunan mijin? Sunansa Ya Mustapha, baba kasa masa wannan wakar don Allah ya ji Murmushi Baba ya yi, "Dije kenan" Ya dauki wayarsa ya kamo wakar sannan ya mikawa Dije, Dije da Mustapha suka koma gefe suka zauna suna sauraran wakar suna nishadi Inna da Mum su kadai zaune a daki suna tattaunawa Mum ta ce ina tunanin hada su aure hakan zai fi Inna ta ce Don Allah bar wannan zancen, kina ganin da Mustapha lafiyarsa kalau hanyar da yabi Dije ta isa tabi shi, muna sa ran samun lafiyarsa ba a haka zai dauwama ba "Ina son kafin ya samu lafiyar ne ayi musu aure, ni naji a zuciyata auren alheri ne" "Idan ya samu lafiya ya ga Dije ce matarshi wani mataki kike ganin zai dauka" "Babu abinda zai iya yi har in dai ni ce na haife shi, dole ya zauna da ita, ki yi hakuri na gama yanke hukunci akan Mustapha Dije zai aura" "To shikenan duk yadda kika ce, nasa miki ido" hakadai tattaunawan tasu ya kasance An daura auren Aisha da sahibinta Aliyu, an kaita gidan ta dake Kano, Mum da kanta ta kaita tai mata nasiha sannan ta karasa gida, don suma mazaunan kano ne, T sakanin Mustapha da Dije wani sihirtachcen shakuwa ne ya shiga tsakaninsu da ranar da Mustapha zasu wuce wayau aka musu, an aiki Dije amso fura, shi kuma Mustapha Mum ce masa ta yi ya rakata wani wuri su dawo yanzu yanzu Dije ta dawo da fura ta tambayi Mustapha, Inna ta ce mata ai sun tafi, nan Dije ta watsar da fura ta shiga birgima da ihu wai a dawo mata da Mustaphan ta, Inna bata kula ta ba, ta cigaba da tsabganta, Ta bangaran Mustapha bai san wayo a kayi masa ba sai da ya ganshi a gida, ai kuwa cikin kankanin lokaci ya hana kowa kwanciyar hankali, Fadi yake "Dijangalan shi" mum da Grandma sun rarrashe shi har sun gaji, Dad ya tambayi wace ce wannan Dijangalan "Yer wajen yaya ta mana, Autan ta" "Ban gane ta ba" "Idan ka ganta zaka gane ta" Sai da Mum ta ja Dad suka shiga daki ta fara masa soyayya da kawo masa maganar Dijangala a kan tana so Dad yaje ya samu Mahaifin Dijangala su ajje magana, da farko Dad yaki amincewa saboda Hamrah amma Mum ta yi masa dibara da namiji mijin mace hudu ne, haka dai ta shawo kansa har ya amince Mustapha zaune bakin kofar shiga ciki yayi tagumi yana tunanin Dije har bai ga zuwan Hamrah ba, tsayawa tayi tana kallansa tana harararsa, daka masa tsawa ya yi da sai daya razana, ya mike da sauri "Baka ganni bane kazo ka wani tare min hanya, ka matsa min kona hankade ka na wuce" A tsorace ya matsa gefe, ta galla masa harara ta yi wucewar ta, shima ciki ya shiga ya je ya zauna gefen Grandma Ana shirye shiryen auran Rahane kawar Dije, su Dije ita ce babbar kawa, amma koda haka Dije kwaskwarima ta ke yi, taki yin wanka, cikin hidimar bikin ne ma Dad yazo nemawa Mustapha auran Dije, a take Dad ya biya sadaki kuma suka ajje ranar daurin aure asabar na sama, yaso ya ga Dije amma hakan bai yuhu ba, ranan kwata kwata Dije bata dawo gida ba sai da daddare Ranar auran Rahane su Dije an sha shagali, an yi rawa har an koshi sannan aka kai amarya gidanta kowa ya watse Ta bangaran Mustapha tunaninsa daya a koda yaushe Dije, da Dad ya fada masa za'a kawo masa Dije ran asabar, murna ya rinka yi yana farin ciki, ranar dadi kamar ya kashe shi, Haidar ne yazo, Mustapha ya ja shi gefe yana masa hirar ran asabar zai yi aure, Haidar ya tayashi murna sosai, daga na suka shiga biga kwallo Washegarin tarewar Rahane da sassafe Dije ta je gidan ta shiga kwankwasa musu kofar daki, Adamu ne ya bude ya yi mamaki da ganin Dije "Dije da sassafe haka?" "Nazo fada mata wani magana ne" "To" fita ya yi daga gidan Dije ta shige cikin dakin, ta samu Rahane a kwance lullube da zani sai kuka take yi, Dije tsorata tayi ta tsaya tana kallan ta "Rahane meya faru dake?" Rahane cikin muryar kuka ta shiga yin bayani "Ya ji min ciwo, Jikina zafi yake min" "Ciwo kuma? Duka ya yi miki?" Rahane ta yaye zanin data rufe jikinta dashi, jini ya bata ta Tsigar jikin Dije ya tashi "jar uba, wannan wane irin zalunci ne, ai kuwa saina rama miki, shima saina ji masa ciwo" "A'a kar kiyi masa komai, Innata ta ce min haka ake yi idan anyi aure" "Kenan nima idan nayi aure sai an ji min ciwo" "Dole sai an ji miki ciwo, sai jini ya fito" "Tabdijam ai kuwa ba zan taba yarda ba, babu wanda ya isa ya ji min ciwo" "Ni dai Dije ki taimaka ki hura min wuta ki sa min ruwan wanka, ko zan ji dadi a Jikina" "To, kafin nan dama ina son na fada miki bikina ranar asabar" "Dagaske?" "Dagaske nake fada miki, rannan bana nuna miki shi ba, mai kudi ne fa sosai "Kawata na yi miki farin ciki" "Nagode, bari naje na hura wutan, nasa miki ruwan wankan" Dije ta fita ta shiga hada wuta Hamrah tare da saurayinta mai suna Adnan wanda kullum suke waya dashi, yau yazo kawo mata ziyara, tsaye suke jikin motarsa suna zance, Dad ne ya shugo da motarsa ya yi mamaki da ganin Hamrah na hira da wani, bayan akwai maganar idan Mustapha ya warke za'a yi musu aure, ranshi ya bace amma bai nuna ba, Adnan yaje har kasa ya gai da Dad, Dad ya amsa fuskarsa a sake, ba yabo ba fallasa, itama Hamrah gaishe shi ta yi ya amsa sannan ya wuce Ranar daurin auran Dije da Mustapha, Dad bai je da Mustapha daurin aure ba, ya dauki yen uwa da abokan arziki suka tafi, cikin kankanin lokaci Dije da Mustapha suka zama mata da miji, ta bangaran su Dije anyi shagali, hakama bangaren su Mustapha Dasu Dad suka tashi tafiya, Dije an gama shirya ta, kaita aka yi wurin mahaifinta ya yi mata nasiha, inda dadewar yasa ta ringa jin haushi don ita ta kosa ta je ta ga Mustaphan ta, daga wurin mahaifinta aka dawo da ita wurin Inna, Inna na ganin Dije ta fashe da kuka fadi take "Dije yau ke ce kika yi aure, dama Dije akwai ranar da zan ga auranki" Inna ta cigaba da kuka Dije dariya ta yi ta ce Inna in kuka kike yi ma don na tsaya, wallahi ba zan tsaya ba, wurin yayana zanje Aunty Aisha da Aunty Fatima suka fito da Dije suka rufe mata fuskarta, Dije ta bude, suna rufewa tana budewa, suka gaji suka barta, aka nuna musu motar daukar amarya, suka shigar da Dije suka zauna gefenta, duk wanda zasu kai a amarya sun shiga motocin da aka kawo, bayan an gama aka tayar da motocin aka fara tafiya, Dije fito da kanta ta yi waje ta daga hannunta tana wa Jama'ar Hadeja bye bye, Jama'ar Hadeja kuwa wani ajiyar zuciya suka yi suna wa Allah godiya da Allah ya kawo ranar da Dije zata barsu su numfasa Mustapha kuwa baki yaki rufuwa tsabar farin ciki, shi da Haidar a bakin Gate tsaye suna jiran isowar su Dije, Haidar ya fara gajiya ganin sun fi awa daya suna jita, ya kalli Mustapha "Mu koma ciki, mu dan huta, su Dije ba yanzu ba" "Waya fada maka, ina ji a Jikina ma yanzu zasu karaso" Haka suka cigaba da jira sun kusa shafa awa daya sannan sai ga motoci, nan Mustapha ya shiga tsalle da murna yana fadin "gasu nan sun karaso, dama na fada maka" Dije fito da kanta tayi waje tana kallan gari, ai kuwa suka hada ido da Mustapha, shi murna ita murna, ya karaso da gudu, ta shiga azalzala direban motan da masifa akan ya tsaya ya sauke ta, jin masifar yayi yawa ya sashi tsayawa, Mustapha ya bude mata ta fito, rungumarta Mustapha ya yi yana fadin oyoyo Dijangala ta Kwace kanta ta yi tana fadin kai dan iska ne kana rungume mace Bata rai ya yi, ganin ya bata rai yasa ta ce masa yi hakuri Yayana na kaina, sai ya yi murmushi An bude Gate dukka motoci sun shiga ciki, Haidar ya kasa yarda Dije ita ce matar Mustapha, karasowa ya yi wurinsu saboda ya tabbatar da gaskiya "Mustapha wace ce wannan?" "Ita ce Dijangala ta (ya kalli Dije) yi masa ma wannan wakar da aka yi mikk" Dijangala ta yi gyaran murya *Dijangala ta me gari, ba auran ba* Mustapha ya ce ka ji ko Haidar ya yi mutuwar tsaye yana kallan Dije, da alamun Dije fara ce amma rashin wanka da kazanta yasa tayi baki ta dishe, hatta kumbunanta sun rine, hakoranta sunyi jawur alamun basu taba ganin maclean ba A zuciyar Haidar cewa ya yi "ashe kuwa akwai aiki a duk ranar da Mustapha ya samu lafiya" a zahiri kuwa cewa ya yi ta yi kyau sannan suka gaisa da Dije, Mum ta ga su Aunty Fatima da Aunty Aisha da matansu Yaya Haruna amma bata ga Dije ba "Ina Dijen take?" Aunty Aisha ta ce tana waje tare da Yaya Mustapha Aunty Fatima ta ce Inna Dije sai addu'ar Nan Mum ta fara musu fada akan miye dalilin da zasu bar Dije a waje tana amarya, me mutane zasu ce, ita da kanta ta fita taje dakko Dije Dije da Mustapha da Haidar suna tattaunawa Mum ranta a bace ta fito ta same su "Ke Dije zo mu tafi" Dije babu musu ta je wurin Mum, Mustapha ya bata rai zai bita Haidar ya rike masa hannu "Be a man my Guy, anjima fa kuna tare" Haidar ya lallaba shi, Mum ta wuce da Dije, dakin Mustapha ta kai ta ta zaunar da ita, itama ta zauna gefen ta "Dije ina son na fada miki wani magana, yanzu ke matar aure ce, matar aure tana da daraja da mutunci, ina son ki natsu ki kama kanki ki zauna a dakin ki, idan Mustapha zai fita waje kar ki bi sh, kin jini ko Dije" Mum ta rike kunnan ta daya "Eh naji Inna" Mum ta tashi "karna ganki kin fito waje" ta fita, Dije ta turo baki "Ka ji min wannan Inna ta birnin wai karna fita, Allah saina fita gibe" yen uwa da abokan arziki suka yita shugowa suna ganin matar Mustapha, babu wanda ya shugo ya fita baiyi mamaki ba, Yen uwan Dad kuwa sai da suka tada rigima wai an aura wa Mustapha mahaukaciya saboda anga bai da Lafiya, Nan Mum ta tarkatasu ta ce su fitar mata daga gida ko ta dauki mataki, abu ya zama kamar za'a yi rikici, daga karshe dai suka fita suka bar gidan, Dad kanshi ya kulle yana tunanin ya Dije take da har ake kiranta mahaukaciya, a daren ranar ya nemi ya ga Dije, Mum cikin kwarin gwiwa ta je ta taho da Dije ta kawota falon Dad da yake jiransu Dad na ganin Dije ya mike a fusace ya nuna ta da yatsa "dama wannan abin kika sani na tsayawa dana ya aure ta? Cikin fushi ta dakatar dashi "dakata Dad, don't try to accuse my daughter, idan ba haka ba zan dauke ta yanzu mu bar maka gidanka Wani kallo ya watsa mata "ok, kina amfani da soyayyar da nake miki ne, kina min barazana" "Ba barazana bane, dagaske nake yi" Komawa ya yi ya zauna "Hafsat kawai dauke ta ku tafi Allah ya basu zaman lafiya, amma idan har yaron nan ya samu lafiya kisan yadda zaki yi dashi, ni babu hannuna a ciki "Babu ma abinda zai faru" Ta ja Dije suka bar falon, dakin Mustapha suka kom, Dije tambayar Mum ta yi "Meyasa baban Mustapha baya sona?" Tambayar da Dije tai mata yasa ta ji wani iri a zuciyarta "Ba wai baya sonki ba ne Dije, yana sonki kawai yana fada ne akan wani abu daban" Mum tabar dakin Dije ta bita da kallo, Aunty Aisha da Aunty Zainab da matan su Yaya Haruna suka shugo suka sameta, ransu bai musu dadi ba saboda abubuwan da suka faru a gidan, sun dade a dakin kafin Mum tazo ta kore su akan su wuce makwancinsu, suka tattara suka tafi bada dadewa ba sai ga Mustapha da Haidar sun shugo, Dije na ganinshi ta washe baki tana murna, ya je da sauri ya haye kan gado ya zauna gefenta, Haidar murmushi ya yi "To ni nabar ku lafiya" Mustapha ya ce ba za ka tsaya mu yi wasa ba "A'a ku yi wasanku kawai, sai da safe" Haidar ya fita Mustapha da Dije suka kalli juna suka ce a tare "Washegari kowa ya watse, su Aunty Aisha sun tafi gidajensu, gida ya rage daga Mum sai Dad sai Dije, Mustapha sai Grandma da Hamrah, Auren da Mustapha ya yi Hamrah ko a farcen yatsan ta, cewa tai ma an hada mahaukata biyu Dije zuwa ta yi ta cewa Mustapha ya ta ji shuru ne har yanzu "Kamar ya shuru?" "Abincin safe mana" Mustapha ya yi dariya "mu anan gidan sha daya muke yin breakfast" "Miye kuma breakfast, ni maganar kunu da kosai da burodi nake yi" "Kije ki cewa Mum ta yi miki kunu da kosai" "Nifa gaskiya yunwa nake ji, a bani abinci kawai, ko kuma ni da kaina na girka" "To mu je sai ki girka" Suka jera suka tafi kitchen, Dije kallan kitchen din ta fara yi "To ina murhu da sauran Abubuwa" "Wai an ce miki nan kauye ne, birni ne fa?" Mum ce ta shugo ta samesu ta tsaya tana kallansu "Me kuka shugo yi a kitchen" "Dije ce wai take jin yunwa, shine na kawota ta girka abinci" Ta kalli Dije "daga yau komai kike bukata ki tambaye ni, karki dinga shiga kitchen sannan mu tafi Dining abinci yana can yana jira" Dije ta yi murmushi "yauwa Inna ta birni" Barin kitchen suka yi suka zo Dining duk suka zauna, Mum tasawa Dije da Mustapha breakfast, can sai ga Grandma ta zamsa, tana ganin Dije ta bata rai ta samu wuri ta zauna, Mum tai serving dinta sai ga Dad shima ya karaso bai kalli Dije ba bare ranshi ya baci, Mum ta yi serving dinsa "thanks you" ya fada Hamrah ce ta zo daga karshe ta samu wuri ta zauna sannan ta gaida Mum, Dad da Grandma duk suka amsa, hankalin Hamrah ya koma kan Dije dake cin abinci da hannu kuma da sauri kamar wani zai taya ta, shima Mustapha kallanta ya tsaya yi, shi abin birgeshi yake yi, shima sai ya ajje cokali yasa hannu yana irin cin abincin da Dije take yi, Dad ya daka masa tsawa "Stop it"a Mustapha ya kalleshi a razane, Mum ta kalli Dad "taya zaka dinga razana min yaro" Ran Dad ya bace, barin abincin ya yi ya tashi ya wuce, Hamrah itama cikin bacin rai ta tashi zata wuce Grandma ta dakatar da ita "Zauna kiyi breakfast dinki" Hamrah ta yatsine fuskan ta "I am sorry Grandma ba zan iya cigaba da cin abinci ba ina ganin kayan kazanta" Tana gama fada bata jira ta ji me Grandma zata ce ba tayi tafiyarta, haka suka karasa breakfast din, Dije da Mustapha su dai suna jin dadin cin abincin da suke yi, bayan sun kammala, mai aiki tazo ta tattara kayan da aka bata, ta gyara Dining din tsaf tsaf Dije da Mustapha suka fito harabar gida suna wasa, Mustapha ya ce Dije kin iya biga kwallo? "A'a ka koya min" Nan Mustapha ya dakko kwallansa yana nunawa Dije yadda ake bugawa, ya wurga kwallo dai dai fitowar Hamrah, aiko kwallo yaje ya bigi ruwan cikin ta, sai data durkusa tsabar radadi, tsoro ne ya kama Mustapha ya je ya boye bayan Dije "Dije ki taimake ni karta duke ni" Ai kuwa Hamrah na tashi kan Mustapha ta nufa Dije ta tare, wani kalli ta watsawa Dije "Ina wasa dake ne?" Dije matsawa ta yi ta ce gashi nan, idan kin isa don ubanki ki duke shi, Hamrah ta zaro ido ubana fa kika ce "To don uwarki ki dake shi" Cikin fushi Hamrah ta daga hannu zata saukewa Dije mari, Dije ta yi maza ta rike hannun ta wurgata gefe, Mustapha ya yi tsalle yana murna "Ho Dije ta" Hamrah ta mike cikin fushi ta tsaya tana kallan Dije "banza yer kauye wallahi sai na yi maganinki" ta fada cikin muryar kuka sannan ta barsu a wurin Mustapha ya kalli Dije I love you "Me ka ce' "Ina sonki Dije ta" Dije ta fashe da dariya "Zo muje na baki wani kyauta" Dije tabi bayan Mustapha har dakinshi "To ina kyautar da zaka bani" Bude durowansa ya yi ya ciro Teddy bear ya mika mata amsa ta yi tana yatsine fuska "Ina bala'in son Teddy bear din nan, Grandma ta saya min, na baki kyauta, ina son a duk lokacin da nayi nisa dake ki rike shi a matsayina ku dinga wasa" "Ka rasa abinda zaka bani kyauta sai ginki, bana so" ta jefar dashi "To me kike so?" "Kaza nake so" "To shikenan bari naje nasa house girl ta girka miki, soyayye ko farfesu ko wani kala kike so?" "Ni kawai kaza nake so" "To shikenan bari naje na fada mata" ya fita ta bishi da kallo, bada dadewa ba ya dawo Dije ta ce yauwa ka iya mota "A'a ban iya ba, ina jin tsoro" "Nifa na iya mota, zo muje na koya maka" "Kina da mota ne?" "A'a ba kai kana dashi ba?" "Eh amma makullin yana wurin Grandma" "Muje mu dauka" "To muje" Suka fita, dakin Grandma suka wuce suka same ta tana bachci, zuwa suka yi wurin mukullai, Mustapha ya hango wani "Wannan na Grandma ne banga nawa ba, mu je ki koya min dashi" Suka fita da gudu, motor park suka je "Ga motan Grandma, ya nuna wata Mercedes "To bude motar" Mustapha ya dannan botir din makullin motan ya bude, "na bude" "Kofar bai budu ba" Mustapha ya sa hannu ya bude kofar "au ashe ya bude" "Kasan me zai faru?" "A'a saika fada" "Ka fara tukawa" Mustapha ya zaro ido "Ba zan iya ba, ina jin tsoron mota" "idan har baka tuka ba babu ruwana da kai" Jikinsa a sanyaye ya ce kiyi hakuri, zan tuka "To tuka" Dije ta shiga motan, Mustapha ya shiga bangaren direba, shuru ya yi yana nazari, yana son tuno yadda ake tuka mota, a hankali ya fara ganin kamar bashi ba, yana ganinshi yana tuka mota dishi dishi "Meka tsaya jira, ka tuka mu, mu tafi yawo, kawai sai muyi ta zama a gida kamar yara" Jin muryan Dije ya yi yana masa echo, kunnasa na jiyo masa wasu kararraki na daban, fisgar motar ya yi a guje, Dije ta zaro ido tai ihu, a lokacin Mustapha ya shiga ganin lokacin da jirginsu ya samu matsala, ya ga jirginsu ya fadi ya yi wani ihu, Kicibis motarsu ya yi da Gate din gidan, shuru kawai kake ji Mu hadu a page 3

Post a Comment

ADS HERE
ADS HERE