π¨π»π§ *JAMI'IN 'DAN SANDA*. π¨π»π§
*Mallakar*
*Maryam Umar Abdullahi*
(Mmn Yusuf)
*Marubuciyar*
*Minene Asalina*
*Mutum ce kuwa*
*Husna ko Huzna*
*And now*ππ»
*Jami'in d'an sanda*
*Ψ¨Ψ³Ω Ψ§ΩΩΩ Ψ§ΩΨ±ΨΩ Ω Ψ§ΩΨ±ΨΩΩ *
*____________________________________*
*ππ°AINUWA πΌRITER'S✍πΌ*
*π¦SSOCIATIONπ€π»*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
*_wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin kainuwa writers Ina alfahari da k'unguyar kainuwa da mutanen cikinta Allah yak'ara Mana k'aunar juna son so fisabilillah_*ππ
π Ώ️_2
..............Yayi tafiya Mai nisan gaske kamun yasamu gidin wata babbar bishiyar mangoro ya zauna Yana maida numfashi , zuwa wannan lokacin ita kanta Muneeba ta gaji da baccin hawalar da ya sureta ta tashi , saboda yanayin yadda ya goyata din ma ya Isa ya wahalar da ita,
Wannan karon batayi kuka ba sai sauke numfashi da takeyi a hankalai hannunta Yana cikin bakinta tana tsotsa yayinda take kallonshi tana wutsil-wutsil da kafafu irin na yara,
Shima idon ya tsuramata cikin matuk'ar damuwa da tausayin tilon 'yarshi hawaye ne suka Fara fita daga idonshi suna sauka akan fuskarta , hawayen da bayajin akwai Ranar da zasu daina zuba,
Jin saukar danshi akan fuskarta yasa ta bingile da dariya a hankali ya sakar Mata murmushi ganin yadda take dariyar ,sun shagala sosai Kamar daga sama yafarajin wata irin suwa kadan kadan , juyawa yayi yafara dube_dube , aikuwa sai ganin k'aton maciji yayi ya laulaye waje Daya ya fasa kanshi Yana fitar da harshenshi irin yadda maciji keyi in yaso mugunta ,
A firgice ya mik'e tsaye Yana maimata innalillahi wa Inna ilaihin raji'un Sam ba kanshi yakeji ba Muneeba yake ji da don ta shine da baik'i macijin Nan yayi ajalinshi ko ya huta da wannan bak'incikin,
Take wata zuciyar tace mashi _kana nufin zaka iya mutuwa ba tare da ka dauki fansa akan mak'iyanka ba ? Yana da matukar muhimmanci ka rayu yazama doli karama abunda aka maka_ duk acikin Yan second yayi wannan tunanin ,
Macijin kuwa ya tare hanya ba inda zai ra'ba ya wuce , gashi kiris yake jira ya motsa ya kawo mashi Sara , ganin Babu yadda zaiyi Haka yafara motsa kafarshi a hankali , aikuwa Kamar jira macijin keyi yayi kanshi gadan-gadan da sauri Hisham ya d'aga k'afa da niyar guduwa Amma kamun kyaftawar ido macijin ya kawo mashi Sara a k'afa , wata k'ara ya saki saboda azabar da yaji taga-taga yayi zai fad'i Amma Yak'i yarda ya Kai k'asa hannunsa na rik'e da Muneeba k'am kamar zai maidata ciki,
Yink'urawa maciji yayi yak'a Kai mashi wani Sara a k'afa take yak'ara sakin wata azababbiyar k'ara Wanda baisan sanda ya saki Muneeba ba ya fad'i k'asa , take duniyar tafara juyamashi idanunshi suka Fara gani dishi-dishi hannunshi ya d'aga yanata son yakai ga Muneeba Amma yakasa a hankali idunshi suka Fara rufewa ,yayinda yakejin wani irin zafi a k'asan zuciyarshi , tausayin Muneeba dakuma rashin daukar fansarsa , inaaaa yakamata na rayu, yakamata na rayu wannan itace kalmar da yayi ta nanatawa har idonshi suka rufe ruf,
Muneeba kuwa tana gefe tana rusa kuka kamar zata tashi wajan don taji ciyo a kanta sanadin fadowar da tayi daga hannunsa , a hankali macijin Nan yafara kusantar ta har yaje inda itake , kuka takeyi sosai yayinda macijin ya fasa Kai da nufin saranta,
Kai *Hajar* kamar kukan yaro nakeji ko, ?
" Eh Nima naji saratu na dauka ko kunne na ne yaji ,
"to amma mi zai kawo yaro cikin wannan k'asurgumin dajin Mai had'arin gaske ,? Wanda mu kanmu da muke da tsarin jikinmu ba k'aramun fama mukeyi da miyagun abubuwan dake cikin dajin Nan ba,
"Kinga saratu ba wannan ba zo muje muga Mike faruwa Haka suka mik'e da azama suka nufi inda sukejin kukan yaron,
Kamar daga sama suka hango yaro kwance Yana tsala kuka ga Kuma maciji yana Shirin saranshi, cikin matuk'ar zafin nama da k'warewa Hajar ta fito da bakar ta ta saita macijin , cikin matuk'ar k'warewa ta sake mashi kibiyar suttt sai a tsakkiyar kanshi , take yayi wata irin gumza.yafara birgina a k'asa ,kamun kace mi ya mutu a wajan , da sauri Hajar ta k'arasa ta dauki Muneeba tafara jijjigata cikin harshen fillanci take cewa da Muneeba tayi shiru,
Itama saratun cikin fillancin take cewa ke Hajar Taya Zaki dauki yaro daga ganinshi bazaki tsaya har ki tantance ko mutum ne ba , inba hakaba Taya za'ace an samu yaro anan shi kad'ai" ?..............maganarta ta katse ne lokacin da sukayi ido hudu da Hisham kwance ba alamar Yana numfashi ,
Aguje sukayi kanshi suna dubashi , ganin saran maciji a k'afanshi yasa suka zaro ido waje cike da tashin hankali , Nan Hajar ta dubi saratu tace "Saratu Yi sauri kije ki kiramana Baffah yazo ya dubashi ,
Hajar inaga fa ya mutu kawai kizo mu koma gida inyaso sai mu tafi da wannan yaron daga baya su Baffah suzo su tafi da gawar,
"Aa Sarah Bata tunanin ya mutu kawai kije ki Kira Baffah Ni Zan tsaya anan ................... *daga alkalamin Yar mutan sokoto maman Yusuf*
Karki wuce baki karantaba kila ki amfanaππ»ππ»ππ»ππ»ππ»
ππ
ππ
*MAGUNGUNAN CIWON SANYI (TOILET INFECTION)*ππ»
ππ
*KARIN NI'IMA DA GAMSAR DA MAIGIDA*ππ»
*CUTA DA MAGANI*π π
ππ
*_Mu na rokon da Allah ya bamu lafiya ingantatta kuma yasa kaffarane_* .
_A gwada daya daga cikin wadannan_ :ππ»
1- A samu Saiwar Garafuni da Sassaken Magarya, sai a tafasa, idan ya dan huce sai mace ta dinga kama ruwa da shi. Kullum sau daya. Yana maganin budewa da kaikayi.
ππ
2- A samu Garafuni da Sassaken Sanya sai a tafasa,
mace ta dinga shan rabin kofi da safe, rabi da yamma.
Ya na fitar da dattin mara da maganin farin ruwa mai wari.
ππ
3- A samu Furen Tumfafiya, sai a shanya ya bushe, a
daka a dinga zubawa a cikin Nono a na sha. Ya na magance matsalar ruwan infection.
ππ
4- A samu Lalle da Ganyen Magarya da Kanumfari, a
hada waje daya a daka sannan a tafasa a zuba farin
miski a ciki. Idan ya dan huce sai ta shiga ciki ta zauna
tsawon kamar minti goma. Yin haka yana maganin
kaikayi da kuraje da budewa da dadewar gaba.
ππ
5- A samu Kabewa a dafa ta, bayan an dafa sai a tsame
daga ruwa a jajjagata ko a birga, a zuba Madara ko
Nono sannan a sa Zuma a sha. Wannan yana mganin rashin sha’awa da bushe wa da rashin gamsuwa.
ππ
6- A dafa Zogale, idan ya dahu sai a murje shi ko a
dama, a tace, a yi lemon juice da shi. Yana maganin fitar
farin ruwa mai wari da cushewar mara kuma ya na kara ni’ima.
ππ
7- A samu Dan-Tamburawa da Albabunaj a tafasa a zuba Man Hulba a ciki. Sai ta dan tsuguna tururin ya dinga shigarta. Idan ya dan huce kuma sai ta shiga ciki ta
zauna. Zai magance mata kaikayi da kuraje kuma ya na sa matsewa.
ππ
8- A samu Farar Albasa da Kanumfari da Citta da Malmo da Barko no da Raihatul Hubbi, sai ta da ke su ta yi yaji tadinga cin abinci da shi. Ya na saukar da ni’ima damagance duk matasalolin sanyi.
ππ
9- A samu Sabulun Zaitun da Sabulun Habba sai a daka
su. A samu ganyen Magarya da Garin Bagaruwa a daka a
tankade. Sai a zuba akan sabulan da aka daka sannan a
kwaba da Ma’ul Khal, a zuba Man Tafarnuwa da Farin
Almiski. Sai mace ta dinga kama ruwa da shi kullum sau
daya. Da ruwan dumi amma ake tsarki da shi. Wannan Sabulu ya na maganin kuraje da kaikayi da fitar ruwa mai wari.
ππ
10- A samu Man Zaitun da Man Habba da Man
Tafarnuwa da Man Kanumfari sai a hade su waje daya.
Mace ta dinga shan cokali daya kullum kafin ta karya. Ya
na wanke dattin mara kuma ya na samar da ni’ima.
ππ
11- A samu Ciyawar Kashe-Zaki da Farin Magani sai tahada waje daya ta dinga jika rabin karamin cokali ta nasha. Sannan ta dinga shan Man Zaitun Cokali dayakullum kafin ta karya.
Wannan ya na maganin dattin mara da wanke daudar mahaifa.
ππ
12- A bare tafarnuwa, idan za ki kwanta bacci sai ki daukisala daya ki yi matsi dashi, ana son idan mace za ta yi wannan hadin to miji ya daga mata kafa wato kada ya
kusance ta, Da safe sai ta tafasa garin hulba ta zauna a
ciki zata yi hakan har tsawon kwana uku.
ππ
13- Ki hada hulba da bagaruwa guri daya, ki dafa idan ruwan ya sha iska sai ki zauna a ciki, kuma ki samu man
habbatussauda ki yi matsi da shi.Ni’ima Ba Sassauci
Da farko daki samu kaza budurwa wadda ba ta fara kwai ba.Sai ki cirere hanjinta ta cikin dunbutu tunda ba a bukatar ayi mata gunduwa-gunduwa. Sai ki gyara ridinki (kantu) kishanya ya bushe sai ki daka shi. Kina iya tafasa kazar sannan sai ki zuba ridin ta cikin zunbutun kazar. Sai kisamu abu ki daure zumbutun; sannan ki hada kayan
miya kadan sai ki kara zuba nonon rakumi a cikin kayan miyar ki hada ki dafa har sai sun dahu sai ki sauke.
Ki cinye ki shanye romon π
Sannan a ranar ki jika kanumfari ya jiku sosai. Ya zama
ruwan shanki.
Muna sayarda ingantattun kayan mata zafafa masu kyau da inganci don neman Karin bayani sai a tuntubeni ta wannan number 09035027743
. •-------••∆ππ§‘π•-------