💅💅💅💅💅💅💅💅💅💅💅
⛰️⛰️ *ƘAUYEN MU 2021* ⛰️⛰️
❤️ *(OUR VILLAGE)*❤️
*LABARI DA RUBUTAWA*
*RASHEEDAT USMAN*
*(UMMU NASMAH*
*2/1/2021*
*WACCE TAZO MUKU DA LITTATAFAI KAMAR HAKA*
Sauyin Rayuwa.
Nasmah Ko Nasirah.
Sara Da Sassaqa.
Akan Ƴar Uwata.
Indo A Birni.
So Bai San Jini Ba.
Hatsabibiya Saude.
Ruɗanin Zuciya Biyu.
DOCTOR HASSAN.
*LITTATAFAINA MASU ZUWA*
AMINAINA KO ITA.?
WACECE KARUWAR?
NISAN KIWO.
ƊANYEN HUKUNCI.
RIKICINA DA AMINIYATA.
HUSSAINA.
ƳAR YARINYA.
MAHAUKACI NE KO ALJANI NE?
*SPECIAL GIFT TO*
AUNTY HAUWA ZARIA MAMAN USWAN, son so nake miki fisabilillah, alkairin ki suna da tarin yawa gareni.
*SADAUKARWA GA.*
NANA A'ISHA HAMISU INDON KAINUWA.
ƘAWATA ZARAH ABDUL MOMYN AHLAN.
ABOKINA MU'AZ MU'AZAULLE.
KAKATA AISHA YABO FULANI.
ƘAWAS MAMAN YUSUP.
MOMYN NASMAH UMMI ONTOP.
Na sadaukar da wannan littafin gareku kuna Raina a ko da yaushe.
*____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*____________________________________*
*GARGAƊI*
Ban yadda wani ko wata ya juya min littafi ba, ko ya min editing, ban yadda ba, sannan kar wacce ko wanda ya ɗauki littafin nan ya ɗaura a You Tube ba tare da izinina ba, yin hakan babban kuskure ne, sannan kuma zan ɗauki mummunan hukunci akan haka, idan kunne yaji jiki ya tsira.🤪
Ina roƙon Ubangiji daya tsare hanuna da zuciyata da harshena da tunanina rubuta muku abinda bazai amfani al'umma ba, Allah ya bani ikon rubuta dai-dai.
MASOYANA shin kun tuna 1/1/2020 ranar dana fara sakar muku INDO A BIRNI nasan baku manta ba, to gashi Allah da ikonsa ya dawo damu 1/1/2021 inda na nutsu nayi tunanin ta yaya zan faranta muku rai, to albishir gani nan cikin sabon book ɗina wanda na masa laƙabi da *ƘAUYENMU* nasan zakuji daɗin BOOK ɗin, wanda zai bibiyeni shine zai bada labari.
Idan kinsan kina da INTEREST akan book ɗin nan to ki fara bibiya tun yanzu karki sake ki biyoni pc kice daga farko, dan bazan baki ba, gara ki bibiya tun wuri, karki ce na miki wulaƙanci.
Mu kafta🤾🏼♀️🤾🏼♀️
Na fara da sunan Allah, Allah ka bani ikon rubuta dai-dai.
*Page 1 to 2*
*GOMBE STATE*
*AKKO LOCAL GOVERNMENT*
*ƘAUYEN CILO*
____________✍🏻 "Marka!!! Marka!! Marka!!!"
Marka dake sunkuye gaban murhu sai famar hura wuta take idanunta sunyi jajur, yayin da take ɗiban kashin shanu tana ƙara turawa cikin murhun kasancewar shine iccen nasu da karan dawa, kina kallon yanayin gidan zaki gane suna baƙin ƙauyen da babu wayewar kai ko kaɗan, basu san arabbi ba bare kuma boko, rayuwa kawai suke kara zube mai cike da jahilci, Tabbas rayuwarsu abar tausayi ce, kanta ta ɗago tare da miƙewa tsaye kasancewar ta samu wutar ta kama, tazo daf da wata farar tsohuwa tukuf ta, zauna, tana cewa.
" Iya gani, ina hura wutar murhu sanda kike kirana wutan ne taƙi kamawa, me za'a miki ne iya.?"
" Me kuwa zaki min Marka, wannan YARINYAR ce, *MURJA* ban ganta ba, tun safe, ko motsinta banji ba, ina kika aiketa."?
Cewar Iya, numfashi wacce aka kira da Marka ta sauƙe tace.
" Kin dai manta ne Iya, ɗazun nan fa ta fita, yanzu ma haka kina zaune zakiji ta shigo da abin tsiyar tata da ta saba."
Sandar ta Iya ta hau lalubowa Kasancewar ta makauniya, tana cewa.
" Bari kiga na ɗauko sandar nan tawa na doka miki ita Marka, Uwar mungun baki, ƴar taki ma da kika haifa a cikin ki baki ƙyale ba, kullum cikin aibata ta, kikeyi kina hantararta, to ta Allah ba taki ba, wannan YARINYAR MURJA babu abinda wannan shegen bakin naki zai mata, babu tsiya jikinta sai alkairi."
Rufe bakin Iya keda wuya sai kuwa ga MURJA, ta shigo da gudu, tsalle ɗaya tayi sai gata bayan iya tana sauƙe numfashi, Sai famar zaro ido take tamkar munafuka tana leƙe leƙe, wacce aka kira Marka kallon ta tayi tare da Girgiza kanta tace.
" To Iya gata, ta shigo sai ki tambayeta Maganar mai ta ɗauko yau kuma, ni nayi wajen sanwata, tunda baki ƙaunar laifinta."
Kafin Iya tayi magana MURJA tayi caraf tace.
" Aradun Allah Umma ni ba mágana na ɗauko ba, Sanin gidan Gajeru ne fa, kawai ina cikin tafiyata yace min ke jigar makauniya Iya, shine ni kuma nace masa gara ni ai, makantar Iya daga baya ta sameta, su kuma da suka gaji gurgunta fa, sai nace masa SHEGE guntu ɗan gajeru jikan guntu, shine ya biyoni da gudu."
Ta ƙarisa Maganar tana tura bakinta cikin rashin kunya tana kuma ƙara leƙa hanyar waje.
Girgiza kanta Inna tayi tare da miƙewa tsaye ta koma bakin murhun ta ba tare da ta kuma cewa komai ba, Iya kuwa murmushi tasa tare da cewar.
" Yauwa ƴar albarka, kinyi dai-dai, daga yau abinda zan gaya miki, duk shegen daya takaki a cikin garin nan kema ki takasa karki barsa, ƴar albarka, maza tashi ki shiga bukka ta, akwai Murtala biyar a bakin karamno na, ki ɗauka, ki karɓo min goro wajen Ladi sai ki dawo min da canji maza ƴar albarka."
MURJA tana dariya ta miƙe taje ta ɗauka ta fito, karar ta, ta ɗauka tare da gyara ɗamarar ta, ta fita tana rera waƙa, Inna fatan shiriya ta mata ba tare da ta kuma cewa komai ba.
" MURJA!! MURJA!! MURJA!!"
Cak ta tsaya tana duban Jummai, dake famar ƙwala mata kira harta iso, MURJA cewa tayi.
" Mtss!!! kiran me kike min sai kace wanda kike bina bashi, nifa bana son irin wannan kiran, wai bana nace ki daina kulani ba, banza mayya kawai."
Shuru Jummai tayi kanta yana ƙasa cike da tsoron MURJA tace.
" Haba kiyi hkr mana, tun jiya fa nake baki haƙuri kinƙi ki haƙura, kuma yanzun ma safiya na hango ita da LADO suna hira a gonar Sanda."
Zaro ido MURJA tayi cike da masifa tace.
" Eyye me kikace LADO na shida Safiya suna hira, kuma hirar Soyayya suke dashi."
" Eh wallahi hirar Soyayya suke har suna dariya kizo ma muje ki gani."
Ai Jummai bata rufe baki ba, MURJA ta juya da gudu tamkar barewa, tayi hanyar gonar, hakan ne kuwa suna zaune suna hirarsu cike da nishaɗi, MURJA ɗamarar ta, ta tanke tare da riƙe kunkumi ta lailayo wata ashar.
" Bura Uba, kutu mar Uwa, eh lallai LADO lallai munafuki algungumi ne kai, nine zaka cuta ka haɗa sona da wannan shegiyar mai kama da kurtu, ni LADO zaka haɗa da wannan abar, kalleni fa."
Ta nuna kanta tana jujjuyawa tare da sakin kuka, LADO tsuru tsuru yayi da ido cike da tsoron abinda zai faru domin kuwa shi kansa tsoron masifar MURJA yake ji, wani irin kukan kura tayi ta shaƙo wuyan safiya, ta hau haɗa kanta da kango, ai LADO yana ganin haka ya zille ya bar wajen.
" Sai na kasheki dan UBANKI naga ta yanda zaki ƙara ganin ladon shegiya jikar mayu."
Safiya idanunta jajur yayi, tsabar taji shaƙa duk yanda taso ta ƙwace daga hanun MURJA ta kasa, sanda MURJA ta daketa iya son ranta sannan ta warɓar da ita a ƙasa tana huci, waige waige take ta ina zata ga LADO shima ta dawo kansa , babu shi babu alamarsa, yatsar ta, ta cije cike da jin haushi harara ta jefawa Safiya da ta raɓe gefe sai sheƙar kuka take, barin wajen MURJA tayi da gudu a zuciye bata tsaya ko ina ba sai gidan su LADO ko sallama babu ta faɗa gidan, da Randar ƙasar Inna Harira ta ci karo, da ƙarfi ta daki randar da sandar hanunta ji kike raga-raga randar ta fashe, hakan ma bai mata ba, ta doshi murhun Harira dake ɗaure da sanyawar rana, harta kusa gamawa, ta tuntsirar dashi a ƙasa, take kuwa abincin ya zube, kunkumin ta, ta riƙe tana jijjiga ta hau ƙwaƙwalwa Inna Harira kira.
" Inna Harira!!! Inna Harira!!! Wallahi ki fito yau mai taro ni cikin gidan nan sai Allah, tsiya da rashin mutunci, shine abinda zan shuka yau cikin gidan nan, yau sai nai miki KACA-KACA da GIDAN NAN, LADO yau ya shiga uku ya ɗauko ruwan dafa kansa wallahi."
Ta ƙarisa Maganar tana murguɗa baki tamkar Inna Harira tana gabanta.
Inna Harira dake zaune ita da Lami, suna hira ne, ta tashi suka fito cike da sauri jin muryar wannan masifaffiyar, turus Inna Harira ta tsaya tana ƙarewa randarta kallo dake fashe rugu-rugu, ranta bai gama ɓaci ba, sai da taga, sanwar abincin ta, zuɓe a ƙasa wanda da ƙyar ta samu kuɗin cefenen ta ɗaura ko bata tambaya ba, tasan MURJA ce ta mata, "(innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un wannan wacce irin masifar Soyayya ce, da kullum take jawo min ɓacin rai)" cikin zuciyarta Inna Harira tayi Maganar cike da ɓacin rai kafin tace.
" Ke MURJA, kece kika fasa min randa sanwa ta ma kece kika zubar ko MURJA, kin cuceni wallahi daƙyar na samu kuɗin dana ɗaura wannan sanwar Allah ya Isa tsakanina dake MURJA kin cuceni yau zan wuni da yunwa."
Turo bakinta tayi tare da riƙe kunkumin ta, tana jijjiga tace.
" Ai ba sai kin tambaya ba, tunda kika ganni tsaye ai kinsan nice, ɗanki ne LADO ya jawo miki, kuma wallahi yau koni ko shi a cikin gidan nan, ki ce masa ya fito, kuma Allah ya isanki babu abinda zai min, dama shi Allah ishashene, domin kuwa da bai isa ba, bazai halicce kiba."
Salati Inna Harira ta ɗauka tana tafa hanu.
" La'ilaha'illallah mahammada Rasulullah Sallallahu alaihi Wasallama!!! Cap amma dai MURJA baki da ta ido baki da mutunci, baki da tarbiyya wallahi, yanzu tsiyarki har yanzu bazai bar kaina ba, ko, to Wallahi yau kinyi na ƙarshe zanyi maganin ki, wajen Mai Gari zan kai ƙararki a shiga tsakaninmu dake, wallahi LADO bazai auroki ya kawo min tsiya da masifa cikin gidan nan ba, ƙarya ne, fice min daga cikin gida shasha."
Kanne idanunta MURJA tayi cike da rashin MUTUNCI tace.
" Idan akwai gaba da mai gari ki kaini, mala'ika ne shi mai garin da zai zare min rai, idan kina so kije ki kaini ƙara wajen uban mai gari amma wallahi ina zaune cikin gidan nan, babu inda zanje har sai LADO ya fito."
LADO dake cikin bukkar sa zaune yana jin duk abinda ke faruwa ne, ya sashi saurin fitowa ganin MURJA na neman zagin innar sa, a gaban ta ya tsaya cike da daɗin baki ya tsaya yana ce mata.
" Haba MURJAN Baba masoyiyata Rabin ran LADO, kefa zuciyata tace, bana son naji ranki yana ɓaci, ɗan yimin murmushi muga manga na, eh eh kamota nan, kamota nan.!!!"
MURJA tsuka taja tare da miƙewa tsaye, cikin tsawa tace mishi.
" Rufe min baki dallah munafuki, Allah yasa rannaka ne gaba ɗaya ba rabi ba, algungumi, to Wallahi baka isa ba, ni kaɗai ce, wacce zaka SO cikin garin nan baka isa ka haɗani da wata ba, idan kuma aka kuma cemin an ganka da wata YARINYAR wallahi sai na jaza maka masifa da bala'in da bazaka taɓa iya fita daga cikin sa ba, ka kuma san zan iya munafukin banza munafukin wofi mtsss."
Ta ƙarisa masifar tana ficewa tare da wurga masa mungun kallo, shi dai LADO da Ido ya bita harta fice, Inna Harira ce ta buɗe baki da hanci tana binta da mungun kallo kafin ta sauƙe numfashi cike da mungun ɓacin rai da tsanar MURJA tace.
" LADO!! LADO!! Mahaukaci ne kai ko, wato dai bazaka fita a harkar MURJA ba, ka duba kaga tsiyar da ta shuka min a cikin gidan nan dubi kaga sanwata a zube ƙasa wanda da ƙyar na samu na ɗora, ko sisinka babu ciki amma gashi sanadin ka an zubar min dashi haka kuma zan wuni da yunwa, to Allah ya isa wallahi ban yafe ba, wai idan banda ma kai jaki ne LADO, baka da tunani da sanin mutumcin kanka, yarinyar da kake so ka Aura ta fara zaginka tana ci maka MUTUNCI tun kafin ka aureta, nima da nake uwarka bata ƙyale ba, zagina take neman yi, to WALLAHI muddun ina numfashi a duniya bazaka taɓa Auren MURJA ba, koda kuwa zanyi yawo tsirara sai na shiga na fita na tarwatsa tsakanin ku, wawa kawai."
Inna Harira ta ƙarisa Maganar cike da ɓacin rai ta zari mayafinta, ta fice da sauri cikin huci, Inna Harira bata tsaya ko ina ba sai gidan su MURJA ko sallama babu ta faɗa gidan tana cewa.
" Marka!! Marka!! Kizo kiji ɗiban albarka da ƴarki tamin yau a cikin gidana kuma wallahi zan ɗauki mummunan mataki."
Umma dake zaune ta sawa ɗan autan ta, Sirajo abinci a gaba yana ci ne zuciyarta ta tsinke, cike da fargaba ta ce.
" Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un!!! Na shiga uku yau kuma wace masifar MURJA ta ɗebo min, ki ƙaraso Inna Harira ga kujera ki zauna."
Ƙarasowa Inna Harira tayi tare da cewa.
" Ba zama bane ya kawo ni, nazo ne na baki shawara, ki raba ƴarki da ɗana, idan ba haka ba, wallahi Marka zakiyi danasani marar amfani, domin kuwa zan nakasa rayuwar ƴarki, na illata ta, ta yanda amfanan kanta ma zai gagareta, koda kuwa zan rasa komai nawa ke ko da zanyi yawo tsirara, wallahi sai naga bayan ƴarki muddun bata fita a harkar ɗana LADO ba, akan me, kullum zata ke zuwa gidana tana shuka min tsiya ta fita to Wallahi bazai yiwu ba, harta na neman zagina, Marka kinsanni cikin ƙauyen nan, kinsan halina nasan baki manta nine na haukatar da Jummai ƙanwarki ba, sanda tayi ƙoƙarin shiga tsakanina da MIJINA, karki bari wani abin ya kuma faruwa da ƴarki, idan kunne yaji....."
Ta ƙarisa Maganar tana nuna Umma da yatsa ta, sanan taci gaba da cewa.
" Ta min asarar sanwata ta yau ta kuma fasa min randa dan haka biyani kuɗina."
Ta ƙarisa Maganar tana miƙawa Umma hanu shuru Umma tayi cike da Allah wadarai da halin MURJA da kullum sai ta jawo mata zagi, bakin zaninta Umma ta kunce, wasu tsoffin Naira ɗari ɗari ne guda uku, Umma ta cewa Inna Harira.
" Kiyi hkr, ƴata ta miki laifi, ɗan kuka ne mai jawa uwarsa zagi, kuɗin hanuna kingansu jaka ɗaya da rabi ne, bani da wasu bayan su."
Waftar su Inna Harira tayi, tana cewa.
" Bani na rage asara matsiyatan banza Mtsss."
Umma Shuru tayi tare da rafka uban tagumi, Tabbas bata manta da abinda Inna Harira ta yiwa Jummai ba, sai dai kuma tana fargabar abinda zai samu MURJA tunda ba maganar ta take ji ba, kota hanata bazata hanu ba, Inna Harira zata iya aikata abinda ta faɗa domin ba imani ne da ita ba. " innalillahi!!" wa'inna'ilaihirraji'un!! Hanunta Umma ta ɗaga sama tana roƙon Ubangiji.
" Allah kana ganin halin da nake ciki akan yarinyar nan MURJA ina iya iyawata, domin ganin ta shiryu, amma abin nats kamar gaba yake ƙarawa kullum, Allah ka shirya min MURJA dan girman izzarka."
Ta ƙarisa ADDUAR tana tafka uban tagumi cike da damuwa, MURJA zata kasheta da baƙin ciki idan ba Allah ne ya tausayawa mata ba.
************
*ABUJA*
*UNGUWAR MAI TAMA*
Jingine yake jikin motar ya zuba hannayensa dukka cikin aljihun sa, fuskarsa murtuƙe babu alamun fara'a, yana nan tsaye bakin ma'aikatar Khabeer ya fito fuskarsa ɗauke da murmushi yace
" Muje *SAFWAN* na gama."
Juyawa yayi ya shiga cikin motar Khabeer shine yaja motar suka harba titi sunyi nisa da tafiya Khabeer ya dubi SAFWAN tare da cewa.
" My Man, meke faruwa ne, yau tun safe naga mood ɗinka ya sauya, meke happening."?
Tsuka SAFWAN yaja yana taɓe fuska, cikin cool voice ɗinsa yace.
" Khabeer, na fara gajiya da jiran wannan project ɗin, jiya munji Magana da ABI, nake tambayar sa, sai yake cemin gaggawan me nakeyi, ni kuwa gaskiya na matsu nayi project ɗin nan na kai musu na karɓo result ɗina ina buƙatar aiki a yanzu."
Murmushi Khabeer ya saki tare da cewa.
" Wai meye matsalarka ne, da aiki meka nema ka rasa a rayuwarka da aiki zai ɗaga maka hankali, duk wani jin daɗin duniya ABI ya tara maka shi, to me zai dameka."?
Murmushin gefen baki SAFWAN yayi, kafin yace.
" Kana bani mamaki Khabeer, meyasa kullum kike dangantani da dukiyar Abi, nifa bari gaji kwata-kwata kuɗin Abi basa gabana, burina na tsaya da ƙafofina bada na Abi ba, kuɗin na nake so na tara dan haka babu ruwana da nasa kuma basa gabana."
" SAFWAN dole zan dangantaka da dukiyar Abi domin kuwa kaine magajinsa bashi da wani ɗa a cikin duniyar nan bayan kai, kaga kuwa ai dukiyarsa taka ce, well tunda kana buƙatar neman naka, sai ka ƙara haƙuri muga nan da zuwa wani lokaci mai Abi zaice."
Kafaɗarsa SAFWAN ya ɗaga yana taɓe bakinsa ba tare daya kuma Magana ba, sunyi nisa da tafiya, Khabeer yayi parking a gefen titi cike da mamaki SAFWAN ya bisa da kallo, kansa Khabeer ya leƙa, tare da ƙwalawa wata mata kira wanda ke zaune gefen titi mabaraciya, kayan jikinta cike da ƙazanta, gashi kanta yayi cibbiri cibbiri ya fito daga cikin himar ɗin da tasa, tashi matar tayi ta nufo motar, SAFWAN saurin kawar da kansa gefe yayi yana toshe hanci cike da ƙyamar matar, Khabeer Girgiza kansa kawai yayi, yana ciro kuɗi daga cikin aljihun sa, ya bawa matar sadaka sannan yaja motar suka tafi, SAFWAN cike da masifa yace.
" Khabeer!!! Kana min abinda raina baya so sau nake faɗa maka cewa idan muna tare ka daina gayyato min waɗannan matsiyatan talakawan, ƙazamai wulaƙantattu, amma naga alama sam kunnenka baya ji, this is the last time, da zaka ƙara min irin haka bana so."
" To ubana naji zan daina, to Wallahi SAFWAN ka dawo hankalinka ka gane cewa talaka da mai kuɗi duka Allah ne ya halicce su, baiyi talaka dan baya sonsa ba, haka kuma baiyi mai kuɗi dan shine yafi so ba, wannan tsarin Ubangiji ne haka yaso ya kuma ga dama ya hallici talaka ya kuma hallici mai kuɗi badan fifiko, dan haka talaka shi ba matsiyaci bane, ka san waye matsiyaci kuwa, matsiyaci shine mutumin da zai koma ga mahallicinsa da tarin zunubai bai da abin alkairi ko ɗaya wanda zai kuɓutar dashi zuwa aljanna, sai dai yana ji yana gani zai faɗa wutar jahannama, wannan shi ake kira matsiyaci, dan haka ka gyara kalamanka akan talaka, ka kuma sassauta tsanarka a garesu domin wannan b........"
Da sauri SAFWAN ya ɗagawa Khabeer hanu cike da ɓacin rai kana kallon cikin idanunsa zaka hango tsantsar tsanar talaka a cikin sa.
" Dallah!! Dakata haka wannan wa'azin naka ya isheni, mtsss!!"
Taɓe bakinsa Khabeer yayi kafin ya kuma cewa.
" Bakina bazai taɓa shuru ba, muddun kayi ba dai-dai ba, sai na faɗa maka koda kuwa dukana zakayi, wai ma na maka wata tambaya, ka tsani talakawa, amma meyasa kake cire maƙudan kuɗaɗe, ka bayar kace a rabawa marayu da miskinai, kana sayan kayan abinci kace a rabawa mabuƙata, meyasa kake tallafa talaka bayan baka sonsu, ka amsa min wannan tambayar SAFWAN."
Murmushi SAFWAN yayi, tare da cewa.
" Hmmm!!! Ina yine saboda lahira ta ne, domin tayi kyau, ya kamata ka gane Khabeer inuwa ɗaya ce bana ƙaunar haɗawa da talaka, koda nake tallafa musu ka taɓa ganin naje da kaina cikin su na tsaya, sanin kanka ne, ban taɓa ba, sai dai na aika a basu, dan haka ka daina haɗa min inuwa da tasu, muddun muna tare."
Khabeer cewa yayi.
" Shi mai hali ai baya fasa halinsa, sai dai ya ɗau hutu shiyasa hausawa sukace ko shekara dubu kayi baka tare da mutum idan kun haɗu karka tambayesa halinsa ka tambaye sa kawai ya yake, domin kuwa hali zanen dutse ne baya taɓa gogewa, sai ka faɗa min ina zan sauƙe ka, gida ko Companyn Abi.?"
" Gida zaka sauƙe Ni."
Daga nan Khabeer bai kuma magana ba, har suka shiga unguwar Mai Tama, homm ya danna a bakin wani kantamemen gida na alfarma da sauri mai gadin ya wangale get ɗin hancin motar Khabeer ya danna cikin gidan, wayyo Allah faɗin kyawun gidan ma, ɓata baki ne, ko gidan governor bazai nuna masa tsaruwa ba, fitowa SAFWAN yayi yana cewa Khabeer sai sunyi waya, Khabeer juyawa yayi da motar yayin da SAFWAN ya doshi part ɗin su, ma'aikata sosai cikin gidan, duk inda ya shige sai sun gaishe sa cike da girmamawa, sai dai baya amsa musu sai dai kawai ya ɗaga musu hanu, babban falon ya shiga, AUNTY HAUWA DA ƳAR YARTA SAFNA, suna zaune, kansa ya ɗaga cike da tsanar Safna zai shige Bedroom ɗinsa yaji muryar AUNTY HAUWA tana cewa.
" SAFWAN."
Tsayawa yayi tare da juyowa ya amsa ransa haɗe murmushi AUNTY HAUWA Tayi tace.
" Lafiya kuwa naga ranka a ɓace.?"
A taƙaice ya amsa mata da cewa.
" Ba komai."
Ya bata amsa yana shigewa Bedroom ɗinsa, yana shigewa AUNTY HAUWA taja tsuka, tare da mai da kallon ta, ga Safna tace.
" Kinga wahalallen banza, ɗan wahala sai wani izza da cin magani yake yiwa mutane, wai shi a haka jin kansa yake wani kayan gabar, ke kuma Safna na dawo kanki, naga alamar baki da niyyar dawo da hankalin SAFWAN kanki, to wallahi na kusa na sauya ki da wata, muddun kuwa kika kasa, domin kuwa faɗuwarki nima faɗuwa ta ce, haka kuma nasarar ki nasara ta ce, amma har yanzu bana jiyo ƙamshin Nasara a jikinki, dole fa sai kin Auri SAFWAN kafin mu samu mu kawar dashi daga wannan duniyar, muna buƙatar fara kasheshi kafin mu kashe ubansa, amma naga kamar ke sanyin jiki kike yi, to bazan yadda na faɗi ba, ba tare da na cika burina na mallakar dukiyar ALHAJI NADABO BA, wato Abi, muddun zaki kawo min matsala cikin wannan aikin, zan tsigeki na kawo wacce zata iya ki jawo hankalin NAMIJI kanki abu ya gagara sai kace ba mace ba, ya kamata ki ƙoƙarta."
Numfashi Safna ta sauƙe tare da cewa.
" Ba gagara nayi ba, Aunty kinsanni kin kuma san bazan gagara ba, domin kuwa nima kuɗin nan ina sonsu ina son naga ina zagaye ƙasashen duniya ina business irin su Dubai chaina Ingila India etc, nima na zamo babbar mace wacce take jin ta isa, sai dai Aunty ki sani rashin cikar burinmu ba daga kasawata bace, daga taurin kansa ne, da rashin sakar min fuska da bayayi, Aunty wannan aikin bazamu iya mu kaɗai ba, Dole sai mun haɗa da boka domin karkato mana da hankalin sa, gareni, daga nan ni kuma zan ƙarasa sauran aikin cikin sauƙi.................."
Ruwan comments ɗinku shine zai nuna min kuna tare dani muddun banga Ruwan comments ba, zan ajiye alƙalamina, yawan comments ɗinku yawan typing ɗin da zan dinga muku.
Masu buƙatar LITTATAFAINA na kuɗi Guda Uku complete, su tuntuɓeni akan wannan numbern domin samu cikin sauƙi a farashi ƙalilan 500 kacal zaki samu duka ukun 08147537180, sannan masu buƙatar Complete document ɗin DOCTOR HASSAN shima ku biyo ta wannan numbern domin samun naki, ki hanzarta domin kema a dama dake, anayi dakai yafi ba'ayi da kai, da kuma a baka labari gara ka bayar.
Ina neman alfarmar masoyan Ummu Nasmah da duk wanda ta karanta wannan NOVEL ɗin tayi shares ɗinsa zuwa groups ɗin da take ciki.
*Vote*
*Share*
*Like*
*Comments*
Subscribe my you tube channel, UMMU NASMAH HAUSA NOVEL'S.
*ALƘALAMIN RASHEEDAT USMAN*
*(UMMU NASMAH KUMA MAKAMAR KAINUWA)*
