ADS HERE
Posts

WATA KADDARA PAGE 2


 ❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤


*WATA KADDARA PAGE 2*


❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤


*Na Maryam Muhammad*


❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤


*Hasheem (M jaruma ce)*


❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*

*🇦SSOCIATION🤝🏻*

 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassoctsan


❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤


*MARUBUCIYAR*


 1. Angon mata biyu

 2. Dijangala

 3. Dogari

 4. Izzar Ameera

 5. Matar cele and now

 6. Wata kaddara


*Ta fannin wasan kwaikwayo (Scrpit) wato film kenan*


 1. Gidan Liman

 2. Alkalin kauye

 3. Dan talaka

 4. Dan mace

 5. Rayuwar Intisar

 6. Auren kaddara

 Da sauransu don ba zan iya fadan sauran ba wasu ma na mantasu


*Ga masu bukatar Angon mata biyu audio sai su ziyarci YouTube channel dina mai suna M jaruma novels tv*


https://youtu.be/ShavMDSPnrw


*Zaku iya shiga ta wannan link din dake sama domin sauraran audion*




*GODIYA TA TABBATA GA ALLAH UBANGIJIN TALIKAI DAYA BANI DAMAR FARA RUBUTA WANNAN LITTAFI DANA MISHI SUNA DA WATA KADDARA, ALLAH YASA NA GAMA LAFIYA KUMA YASA MU AMFANU DA SAKON DA YAKE DAUKE DASHI*


*ALLAH KA YI SALATI GA SHUGABANMU ANNABI MUHAMMAD SAW DA IYALAN GIDANSA DA SAHABBANSA*


*ADDU'AR KU A KULLUM SHI KE TASIRI A KAINA, ALLAH YA BAR MIN KU IYAYENA DA YAN UWANA*



*JINJINA A GAREKU MASOYANA, BANI DA BURIN DAYA WUCE NISHADANTAR DAKU A KOWANI LOKACI, INA ALFAHARI DAKU, ALLAH YA BARMU TARE*


*NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA KAINUWA WRITER'S ASSOCIATION, INA YINKI OVER AUNTY FAUZY, MAMAN NOOR DA HARUNA BIRNIWA*



*Wannan littafin kage ne, labarin ya fito daga kasar zuciyata ce, mallakina ne kuma ban yarda wani ko wata ta sauya min labari ba ta kowata hanya*





❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤

 

Halima ta kai tsawon awa daya tana zaune a waje kamin Zeenai ta fito rike da bokatin roba ta sameta, galla mata harara ta fara yi sannan ta wurga mata bokatin "jeki dabo min ruwa, saura kuma ki 'bata min lokaci" Zeenai ta juya ta koma cikin gida, Haleema kallan bokatin tai a dai dai wasu hawaye na fita daga idanunta, ta dauki bokatin ta shiga gida, ta shigo ta sami Inna Larai da Zeenai zaune suna tattaunawa, Zeenai ta watsa mata harara "don uwarki debo ruwan dana saka ki kenan, meya shigo dake?" Cikin natsuwa Haleema ta ce nazo daukan hijabina ne "to yi sauri ki dauka ki  fita" Haleema ta shiga kitchen ta dauki kodaddan hijabinta daya yi datti sosai, ta saka hijabin sannan ta fita, Inna Larai ta bita da harara "maiya kawai, ai baki gama ganin azabana ba"



Tafiya Haleema take yi a tsanake, kafarta babu takalmi, sake sake cike a zuciyarta, wata zuciyar na fada mata ta gudu, ta shiga duniya domin ta huta daga ukubar Inna Larai da 'yarta Zeenai, tana wannan tunanin ne wani mota ya tsaya ta gefenta yana mata magana amma tunaninta baya jikinta "baiwar Allah tambaya fa nake ko ke kuma ce" a firgice Haleema ta dawo duniyar tunani ta kafe idanunta a kan Hafeez daya rage ba'kin gilashin motarsa yana kallanta, wani kamshi ya daki hancinta


Yatsine fuska Hafeez ya yi ya dan ja gilashin motarsa yai sama kadan da alamu hancinsa yana jiyo masa wani wari, lokaci guda ya 'bata rai yana kallan Haleema, tambayar ta ya yi ina ne gidan Mal Sambo?


Bude baki Haleema tai ta shiga magana "idan ka mike sambal, layi na farko, zaka ga wani gida mai bishiyar mangwaro nan ne gidan" da sauri ya dauki face mask ya manna a fuskarsa ya rufe hancinsa da bakinsa don ba zai iya jure warin dake fita daga jikin Haleema ba, cikin mamaki ya kara kallanta sannan ya ce ke baiwar Allah meyasa kike wari, bakya wanka ne?


Haleema ta ce rabona da wanka tun kafin mahaifiyata ta rasu


Hafeez ya ce ya za'ai mutum ya yi rayuwa batare da wanka ba, jikinki baya miki kaikayi, to miye ma ya hada rasuwar mahaifiyarki da rashin wankanki?


Haleema ta dukar da kai sai wasu hawaye suka fara fitowa daga idanunta, bata jira ta ji me zai ce ba ta yi wucewarta, tabe baki yai sannan ya ja motarsa, yabi kwatancen da Haleema tai masa, sai gashi a dai dai bishiyar mangwaro na gidan Mal Sambo, samun wani karamin yaro ya yi yasa ya aikashi cikin gidan ya ce ana sallama da Mal Sambo, yaron ya shiga cikin gidan bada dadewa ba sai gashi ya dawo "wai ka shiga ciki" ciro dari biyar yai ya bawa yaron kyauta, yaron ya amsa yana murna, Hafeez ya shiga cikin gidan Mal Sambo ya sameshi zaune kan sallaya yana jan carbi, sallama yai ya karasa gaban Mal Sambo ya duka, Mal Sambo ya amsa sallamar


Mal Sambo makaho ne kuma tsoho ne sosai don zai iya kaiwa shekara dari a duniya


Hafeez ya ce sannu Baba, dafatan na sameka lafiya


Mallam Sambo ya ce lafiya lau yaro, kasha hanya

Hafeez ya kalleshi sosai kamin ya ce ya akayi kasan na sha hanya, bayan baka sanni ba baka san da zuwana ba kuma ba gani kake ba bare ka ga alamun na sha hanya


Mal Sambo ya yi karamin murmushi sannan ya ce yaro kenan, ba iya hanya nasan kasha ba, nasan sunanka Hafeez, sunan matarka Hannatu ana kiranta da Hanan, kana matukar sonta kamar rayuwarka itama haka take matukar sonka, shekaranku biyar da aure baku haihu ba, yanzu neman haihuwa kuke yi ido rufe


Hafeez ya zaro ido cike da tsoro yana kallan Mal Sambo "A gaskiya Malam kana da abin mamaki, wallahi duk abin daka fada gaskiya ne, yanzu ya za'a yi a taimaka mana, zan iya baka duk wani abin dana mallaka don Allah ka taimaka mana ta haihu"


Mal Sambo ya ce ka yi hakuri Hafeezu akan abinda zan fada maka, matarka Hannatu ba za ta taba haihuwa ba har tabar duniya


Hafeez ya rike kai da hannayensa bibbiyu "inna lillahi wa inna ilaihir raji un, yanzu Baba kana nufin ba zan haihu ba har nabar duniya"


Mallam Sambo ya ce ban ce kai ba zaka haihu ba, cewa nai matarka Hannatu ba za ta taba daukar ciki ba har tabar duniya, amma kai zaka haihu, zaka haifi 'yaya masu albarka da duniya zasu yi alfahari dasu

Cikin sanyin murya Hafeez ya ce taya zan haihu bayan matata ba za ta iya daukar ciki ba


"Kai mijin mata hudu ne Hafeez, amma na gani kai mata biyu zaka yi rayuwa dasu"


A rikice Hafeez ya tsaya yana kallan Mal Sambo sannan ya ce taya zan yi rayuwa da mata biyu, ni mijin mace daya ne, mata ta ita ce rayuwata, da ita zanyi rayuwa a kowani hali, ko ba za ta haihu ba na zabi na yi rayuwa da ita a haka, ba zan taba yi mata kishiya ba


Mal Sambo ya ce yaro kaddaranka ne yazo a haka, abin dana gani nake fada maka, duk wayaunka  da dibaranka sai ka kara aure, kuma auren zai zo maka a wani fuska ta daban, auren za'a daurashi kamar ka rufe idonka ka bude


Hafeez cikin rainin wayau ya ce to tunda ka iya gane mata biyu zan aura, sai ka yi min cikakken bayani akan dayar matan da zan aura, idan kuma 'yarka ce zaka aura min to bismillah


Mal Sambo yai yar karamar dariya sannan ya ce duka yarana mata sun yi aure, sannan ita matar da zaka aura sunanta HALEEMATUS SA'ADIYYA, sau daya kuka taba haduwa da ita, a haduwarku da ita na gaba zata zama matarka, ita ce wacca zata haifa maka kyawawan yaranka da zaka yi alfahari dasu, zaka sota fiye da kowata mace a duniya kuma zaka........ Hafeez ya mike gami da dakatar dashi cikin fushi da tsawa "Stop! Tsohon banza kawai, ko kunyar yi min karya baka ji ba, to wallahi nafi karfinka, hauka kake yi ka ce zan yiwa matata kishiya, taya zai faru, da hankalina da tunani na, to bari na fada maka matata ita ce rayuwata, zan kasance da ita ko tana haihuwa ko bata haihuwa" Hafeez ya ja dogon tsaki sannan ya fita cikin fushi, Mallam Sambo yai yar dariya yana fadin Hafeez nasan zaka dawo, dole zaka dawo


Aliyu yana fitowa ya shiga motarsa, ya ja motar cikin fushi ya yi wucewarsa, tuki yake yi amma tunaninsa baya jikinsa, sake sake fal a cikin zuciyarsa "da nasan zan zo kauyen nan mutumin nan ya bata min rai wallahi da ban zo ba, Matsiyacin tsoho kawai, ni zai damfara, bai san nafi shi bariki ba"


Bai ankaraba ya ji ya bige mutum, jan birki ya yi da sauri ya bude kofar motar ya fito ya tsaya yana kallan Haleema


mikewa tai dakyar ta kai kallanta kan bokatin roban data debo ruwa ya 'bare, daukar bokatin ta yi ta shiga dubawa, ganin ya fashe yasa ta kalli Hafeez sai ta fashe da kuka....  Tana fadin shikenan na mutu, yau tawa ta kare, nasan Inna kashe ni zata yi



*Please ku tayani sharing zuwa sauran groups 🙏🙏🙏*


Wa'inda basu turo katin data ba, suyi hanzarin turowa ta wannan numban 09049493054



Mu hadu a page 3

Post a Comment

ADS HERE
ADS HERE