RANAR DAUKAR FANSA PAGE 1
*MARYAM M HASEEM*
*M JARUMA*
09049493054
Page 1
*_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassoctsan
*_____________________________________*
*MARUBUCIYAR*
1. Angon mata biyu
2. Dijangala
3. Dogari
4. Izzar Ameera
5. Matar cele and now
6. Ranar daukar fansa
*Ta fannin wasan kwaikwayo (Scrpit) wato film kenan*
1. Gidan Liman
2. Alkalin kauye
3. Dan talaka
4. Dan mace
5. Rayuwar Intisar
6. Auren kaddara
Da sauransu don ba zan iya fadan sauran ba wasu ma na mantasu
*Ga masu bukatar Angon mata biyu audio sai su ziyarci YouTube channel dina mai suna M jaruma novels tv*
*Zaku iya shiga ta wannan link din dake sama domin sauraran audion*
*GODIYA TA TABBATA GA ALLAH UBANGIJIN TALIKAI DAYA BANI DAMAR FARA RUBUTA WANNAN LITTAFI DANA MISHI SUNA DA RANAR DAUKAR FANSA, ALLAH YASA NA GAMA LAFIYA KUMA YASA MU AMFANU DA SAKON DA YAKE DAUKE DASHI*
*ALLAH KA YI SALATI GA SHUGABANMU ANNABI MUHAMMAD SAW DA IYALAN GIDANSA DA SAHABBANSA*
*ADDU'AR KU A KULLUM SHI KE TASIRI A KAINA, ALLAH YA BAR MIN KU IYAYENA DA YAN UWANA*
*JINJINA A GAREKU MASOYANA, BANI DA BURIN DAYA WUCE NISHADANTAR DAKU A KOWANI LOKACI, INA ALFAHARI DAKU, ALLAH YA BARMU TARE*
*NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA KAINUWA WRITER'S ASSOCIATION, INA YINKI OVER AUNTY FAUZY, MAMAN NOOR DA HARUNA BIRNIWA*
*Wannan littafin kage ne, labarin ya fito daga kasar zuciyata ce, mallakina ne kuma ban yarda wani ko wata ta sauya min labari ba ta kowata hanya*
🌹💞🌹💞🌹💞🌹💞🌹💞
Alh Usman bafulatanin Agadas ne dake kasar Niger, tun yana dan matashi ya dawo Nigeria da zama yana kasuwancinshi, cikin kankanin lokaci kasuwancinshi ya bunkasa ya fara bude kamfanin sarrafa fulawa ta nau'i daban daban, kamarsu biredi, Cake, bounce da sauransu, daga Niger ya auro matarsa Hajara, Hajara ta kasance yar uwarsa amma ta nesa, haka rayuwa ya cigaba da tafiya kasuwancin Alh Usman na habaka, a yanzu ya zama mashahurin dan kasuwa, baya sati biyu bai fita kasar waje ba, duk da dukiyar da Allah ya bawa Alh Usman yanzu shekara goma kenan babu haihuwa, babu inda basu je sun nemi maganin haihuwa ba amma abu ya gagara, A kasar India suka sami likitan daya yi bincike akan matsalarsu sosai, ya gano matsalar daga wurin Alh Usman yake amma ya tabbatar masa da akwai hanya guda daya da zai iya samun haihuwa, wannan hanyar kuwa shine a cire kwan matarsa Hajara sai a debi maniyinsa a hada
Haka kuwa ya kasance, Doctor ya debi sperm din Alh Usman sannan ya dabo kwayayen Haj Hajara, ya yi inject din sperm cikin kwayayenta, bayan kwanaki kwai daya ya zama embryo, inda Doctor ya dasa embryo a cikin mahaifan Haj Hajara, cikin nasara embryo ya yi attach da cell membrane, a can kasan India suka zauna suna rainon cikin har Allah ya sauke ta lafiya, ta haifi dansu mai matukar kyau da kama dasu, Haj Hajara ta yi matukar farin ciki amma farin cikinta ya kasance ragagge don ita 'ya mace taso ta samu, Allah ya sani tana matukar son ya mace, gashi an tabbatar musu da ba za su samu wani dan ba, haka dai tai hakuri
Yaro ya ci suna Adam, an dawo Nigeria an yi shagalin biki, yan uwa daga Niger duk sun zo taya su murna
Haka rayuwa ya kasance har tsawon Shekara takwas
Haj Hajara mace ce mai matukar taimako da son al'umma, akai akai tana ziyartan gidan marayu har yaran gidan sun saba da ita
Wani ranar litinin Haj Hajara ta shirya ta zo gidan marayu, da zuwanta ta tarar da wata kyakkawar yarinya da aka kawo gidan, ba zata wuce shekara hudu ba, kuma abin mamaki yarinyar cikin shiga ta alfarma take, babu wahala sam sam a tattare da ita, sai kuka take ta faman yi, lokaci daya Haj Hajara ta ji tausayi da soyayyar yarinyar ya dabaibaye mata zuciya
Ta karasa ta amshi yarinyar a hannun mai kula dasu tana tambayar yau bakuwa kuka yi a gidan?
"Ai kullum cikin yin baki muke in dai gidan nan ne, gaskiya akwai matsala a rayuwan nan in dai ba'a dauki mataki ba"
Yarinyar tunda ta shiga hannu Haj Hajara ta yi shuru ta kwanta a kafadarta, sai bacci ya dauke ta
Haj Hajara ta nemi da a bata yarinyar, shugabar gidan ta ce Hajiya ai nan gidankine, babu abinda zamu ce miki sai dai Allah ya biyaki, sannan wannan yarinyar an baki ita halak malak, Allah ya tayaki riko
"Ameen"
Haj Hajara ta dawo gida da yarta cikin farin ciki, Adam na ganinta ya shiga yin murna wai Mamanshi ta yi masa kanwa, ta kira likita ya duba lafiyar jikin yarinyar sannan tasa aka yi mata odan kaya masu matukar kyau da tsada
A lokacin da yarinyar ta farka daga bacci tana kallan Adam tai murmurshi ta ce Amad
Haj Hajara ta kalleta, koda bata fadi sunan dai dai ba tasan Ahmad take nufi
"Ya sunanki?"
Yarinyar cikin yaranta na gwaranci ta ce jeenat
Haj Hajara ta yi shuru tana tunani "kina nufin Zeenat"
Yarinyar ta maimaita "Jeenat"
Haj Hajara ta shafa mata kumatu "Allah sarki Zeenat dina, Allah ya raya min ke"
Koda Alh Usman ya zo ya ga Zeenat farin ciki ya yi sosai kuma ya amsheta hannu bibbiyu akan zai zame mata uba nagari
Haka rayuwa ya cigaba da tafiya, a lokacin da Zeenat ta kai shekara goma sha takwas Haj Hajara ta tabbatar mata da ba ita ce ta haifeta ba, hasalima daga gidan marayu ta dakko ta, Zeenat ta yi kuka sosai har ta fara jin ta mutu tabar duniya yafi ta cigaba da rayuwa a duniya, daga baya Haj Hajara tazo ta fara nadama akan fada mata gaskiya da ta yi ganin yadda Zeenat ta shiga damuwa sosai, haka rayuwa ta cigaba da tafiya
Tsakanin Adam da Zeenat akwai shakuwa mai tsananin, sun tashi cikin matukar son junansu, daga baya al'amarinsu ya juya ya koma soyayya, tunda su Alh Usman suka kula da haka sai suka yanke shawaran su hada su aure, cikin kankanin lokaci aka yi musu aure
Adam da Zeenat suna rayuwarsu cikin farin ciki, tashin farko Allah ya yi musu kyautar diya mace da taci suna Ummu rumana, Ummu rumana nada shekara biyar aka yi mata kanwa da taci suna Hajara
Zeenat nada wani tsohon ciki, Allah ya yiwa Alh Usman da Haj Hajara rasuwa sanadiyyar hatsarin jirgin sama akan hanyarsu ta dawowa daga Turkey, Adam da Zeenat sun ga tashin hankalin da tun da suka zo duniya basu taba gani ba, sun yi matukar girgiza amma ya zasu yi, wanda ya fisu sonsu shi ya amshi abinshi, bada dadewa ba Zeenat ta haifi danta namiji daya ci sunan Alh Usman amma ana kiranshi da Affan
Komai na Alh Usman ya dawo hannun Adam, shi ya cigaba da juya kamfanoninsa, cikin ikon Allah abubuwa suka bunkasa fiye dana baya, Adam ya zama mashahurin dan kasuwa mai fada a ji
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, tsakanin Adam da Zeenat da yaransu guda uku Ummu Ruman, Hajara da Affan, rayuwar farin ciki suke yi sosai, zuri'arsu ita ake yi wa take da Happy family
*Bayan shekara goma sha uku*
💞🌹💞🌹💞🌹💞🌹💞🌹
Wani ajiyar zuciya Rumana ta yi gami da yin tsiririyar murmushi sanadiyar jirginsu da ya yi landing, a natse jama'an ciki suka shiga fitowa, har ya kawo kan ta, ta fito ta tsaya ta dauki akwatunanta sannan ta mike inda jama'a suke tsayuwa domin daukan yan uwansu da abokansu da masoyansu harma da iyayen gidansu
Alh Adamu ta fara hangowa dake tsaye shi da Affan, da sauri ta karaso tai hugging dinsu cikin farin ciki "oh my Dad and my little na yi missing dinku"
Alh Adamu ya banbare ta daga jikinshi yana fadin Ummu Ruman yakamata kisan kin girma fa
Ummu Ruman tai smile tana fadin haba Dad I am just 20, shekara ashirin fa nake
Alh Adamu ya ce a haka kuma zan aurar dake
"A'a Dad sai na yi masters zan yi aure"
Ta rage tsawonta tana kallan Affan "Little ya kake?"
"Lafiya lau Aunty"
"Na kawo maka tsarabarka na musamman"
"Good Aunty"
Suka wuce inda motoci suke jere suna jiransu, Suka shiga motar tsakiya, Security na motar baya da gaba, suna tafiya a jere
Ummu Ruman ta kalli Alh Adamu tana fadin Dad abin mamaki, ban taba tunanin Mum ba za ta zo tarbana ba, ko akwai wani damuwa ne?
Alh Adamu ya ya ce tana ta fushi, tun jiya taki yin magana dani
Ummu Ruman ta ce amma Dad meyasa take fushi, kodai ka yi mata wani laifi ne? Kuma hakan na ga bai taba faruwa ba
Alh Adamu yai smile yana fadin ni babu abinda na yi mata kawai kawai zan karo aure ne, shine kawai abinda take yiwa fushi
A take fuskar Ummu Ruman ya canza ta kalli mahaifinta cikin mamaki "Dad har akwai ranar da zaka yiwa Mum kishiya? I can't believe it, please Dad kar ka yi wa Mum haka"
Alh Adamu ya kalli Ummu Ruman na wani lokaci kamin ya ce ki naso Dad dinki ya je ya dinga bin matan banza ne ko kuma so kike Dad dinki ya rufawa kanshi asiri ya karo aure ya tsare mutuncinsa dana iyalinsa?
Shuru Rumana tai bata ce komai ba, ta fahimci mahaifinta sarai, ta gane dalilin da yasa yake so ya kara aure, tabbas da yau ace ga mahaifinta yana aikata zina gwara ace ya yiwa Mum dinta kishiya
Ta kalleshi ta ce to Dad Allah yasa hakan shi yafi zama alkairi
"Yauwa ameen dota"
Haka suka cigaba da tattaunawa sama sama har suka karaso gida
💞🌹💞🌹💞🌹💞🌹💞🌹
Falmata Bukar yar asalin Kannuri ce ta garin Borno, ita ce kadai 'ya a wurin mahaifinta Mal Bukar, Mal Bukar ya kasance shahararran kasurdumin Malami, da ake yiwa aikinsa lakabi da yankan wuka, ya shahara sosai a garin Borno, duk wasu manyan yan kasuwa da yan siyasa wurinsa suke zuwa neman taimako
Falmata neman duniya take ido rufe, bata da wani burin daya wuce hanyar da zata sami duniya, ta mallaki dukiya masu dumbin yawa, ta kasance daya daga cikin masu arziki da za'a kirasu su amsa
Ta fara tunanin manyan masu kudin Nigeria, babu wanda ya fara fado mata a rai sai Alh Adamu Usman, mahaifinta ya bata maganin da tai amfani dashi ta sami aiki a babbar masana'antan Alh Adamu, bayan ta sami aiki a masana'antar, ta fara zuwa, sai Mal Bukar ya turo mata da magungunar da zata dinga amfani dasu domin shiga zuciyar Alh Adamu, ai kuwa haka ya kasance da farko Alh Adamu bai yarda yana son wata 'ya mace ba bayan matarsa, ya canza matsayin Falmata zuwa PA dinsa, daga baya kuma ya zo ya shaida mata yana sonta kuma a shirye yake ya aure ta, cikin kankanin lokaci aka fara maganar aure, an yanke masa kudin da zai biya na aurenta, ya ninka kudin biyu ya biya, ansa ranar bikin nan da wata daya, gashi yanzu kwana goma kacal ya rage a daura auren, tunda Alh Adamu ya shaidawa matarsa Haj Zeenat zai kara aure, shikenan ta shiga damuwa, bata taba tunanin akwai ranar da wannan labarin zai risketa ba, tai kuka har ta ji babu dadi, sai kuma ta mikawa Allah komai akan idan kara auren da zai yi shine alkairi Allah ya tabbatar
💞🌹💞🌹💞🌹💞🌹💞🌹
Haj Zeenatu zaune a falo tai tagumi tana tunani, Ummu Ruman ta bude kofa ta shigo, da sauri ta karasa wurin Mum dinta, ta rungume ta cikin farin ciki "ina missing dinki mum"
Haj Zeenatu ta kalleta tana murmurshi "Rumana mutanan turai, an kammala karatu lafiya?"
"Lafiya lau Mummy"
Alh Adamu da Affan suka shigo, Alh Adamu ya yi sallama, Ummu Ruman ta amsa sallamar, Haj Zeenatu ta amsa kasa kasa, Ummu Ruman ta kalli mahaifiyarta cike da tausayi sannan ta ce Mummy kina fushi da Daddy saboda zai kara aure? Don Allah ki daina fushi, ki barshi kawai ya kara auren, yau ba za muso a ce ga mahaifinmu yana aikata abin da bai kamata ba, mu masu taimaka masa ne da bashi goyon baya wajen kare mutuncinsa
Haj Zeenatu ta kalli Ummu Ruman tai smile tana yaba hankalinta da kaifin tunaninta, tana matukar alfahari da ita
Affan ya je ya zauna gefen Haj Zeenatu Alh Adamu kuwa samun wuri yai ya zauna da kiran sunan Allah
Haj Zeenatu ta ce Rumana, na riga dana hakura, kawai Allah ya kawota lafiya, ni kawai bana son tazo ta rabamu da farin cikinmu ne
Ummu Ruman ta ce insha Allahu da alkairi zata zo kuma zamu cigaba da rayuwarmu kamar yadda muka saba
Hajara ta shigo falon tana fadin muryar wa nake ji kamar na Auntynmu
Ummu Ruman ta mike tana smile "ita din ce ma ba kama bane" ai kuwa Hajara tazo da sauri ta rungumeta tana tambayar tsaraba
"Tsarabarki ke da Little yana nan na musamman"
"Dakyau Auntynmu"
Umma Ruman ta mike tana fadin bari na je na watsa ruwa na canza cikin kaya marasa nauyi
Ta fice tabar falon, Alh Adamu ya kalli Haj Zeenatu sannan ya ce nagode da goyon bayan da kika bani matata, Allah ya barni tare dake
"Ameen" kawai ta ce sannan ta tashi tabar falon ya bita da kallo, har a zuciyarsa yasan har yanzu tana fushi dashi, tashi yai yabi bayanta, falon ya rage daga Hajara sai Affan
Haj Zeenatu tana shiga dakinta ta zauna bakin gado ta fashe da kuka mai matukar taba zuciya Alh Adamu ya shigo ya sameta, zama ya yi gefenta ya jawota jikinshi yana rarrashi "zan iya fasa auran nan saboda ke, idan hankalinki bai kwanta ba kawai gwara na fasa"
Haj Zeenatu ta bangaren jikinta daga nashi, ta shiga share hawayenta tana fadin karka fasa, ka yi auranka, bana son na shiga hakkinka, bana burin na haramta maka abinda ya zamana halas, Allah yasa hakan shi yafi zama alkairi
Ya tsura mata ido yana kallanta "to meyasa kike kuka?"
"Kawai ina yi ne idan na tuna tsintata aka yi, bani da kowa a duniya, wanda suka maye gurbin iyayena sun bar duniya, daga kai sai 'yayenmu kadai suka rage min, ya zan yi idan na rasaku?"
Rungume ta ya yi sosai "ba za ki rasamu ba, kuma bana son na kara jin kina wannan maganar, bana so"
Ta cigaba da kuka, ya cigaba da rarrashinta har ya samu ta daina kuka
Ta bangaren Ummu Ruman tai wankanta tsaf, ta canza kaya sannan ta feshe jikinta da turaruka, wayarta ne ya shiga ringing, ta dauka gami da duba allon wayar *Besty* ta gani a rubuce, cikin smile ta amsa tana fadin Allah sarki kawata Ramlat har na fara kewarki
Ramlat ta ce nima nan kewarki nake ta yi wallahi, yanzu jirginmu ya sauka, yanzu haka muna hanyar zuwa masarauta
Ummu Ruman ta ce ku dai yan masarauta kun ji dadi, ni dai ina sha'awar sarauta, har ina fatan ina ma ace ni jinin sarauta ce
"to kawai na hadaki da Yayana ki aureshi, kin ga kin zama gimbiya" Ramlat tai maganar tana yar dariya
Ummu Ruman ta ce ai ni nafi karfin a hadani da wani ya aure ni sai dai shi da kanshi ya ganni ya kyasa
Ramlat ta ce waya fada miki yayana irin samarin nan ne masu saukin sha'ani, da farko shi yarima ne mai jiran gado, shi jarumi ne, duk inda kike tunanin namijin gaske ya kai, mata rushing suke yi a kanshi
Ummu Ruman tai yar karamar dariya sannan ta ce Ramlat mu bar zancen nan, let talk about something else
Nan take suka canza wani hirar
🌹💞🌹💞🌹💞🌹💞🌹
A kwana a tashi babu wuya a wurin ubangiji, yau aka daura auren Alh Adamu da Falmata, kawayen Haj Zeenatu duk sun hallaro
A wannan ranar aka kawo Falmata katafaran gidan Alh Adamu, ta tare a bangaren da Alh Adamu ya ware mata, tare da kawayenta ta kwana inda washegari Alh Adamu ya sallamesu da ma'udan kudi
Da karfe shida na yamma Falmata ta shiga kitchen dinta ta girka farfesun kifin ruwa, ta dakko wani kullin magani da mahaifinta ya bata ta zuba a ciki, bayan nan ta dakko gawayin bature ta kunna, bayan ya yi rushi ta shiga barbada wani garin magani mara dadi tana kiran sunan Adamu, ta cigaba da zagaye duk wani sako na bangarenta tana kiran sunan Adamu, bayan ta gama ta shiga wani store ta bude wani kwando dake dauke da bakar kaza, sa hannu tai ta dauki kazar sannan ta wuce kitchen ta dau wuka tasa a wuyar kazar ta yanka tana fadin "ga jini na baku domin biyar bukata ta, karku kunya tani" sai data tabbata jinin kazar ya gama tsiyayewa sannan ta aje gefe ta fice
Bedroom dinta ta wuce ta shiga bayi tai wanka sannan ta fito ta saka kaya ta shafe jikinta da wasu turaruka na tashin hankali
Bayan sallahn isha'i jikin Alh Adamu na rawa ya shigo gida bangaren Haj Zeenatu ya wuce ya sami Ummu Ruman da Hajara da Affan zaune a falo suna hira cikin nishadi da annashuwa
Duk suka yi masa sannu da zuwa, ya amsa cikin farin ciki yana mai alfahari dasu, ya tambayi mahaifiyarsu Ummu Ruman ta ce tun dazu tana badroom dinta
Alh Adamu bedroom din Haj Zeenatu ya wuce ya sameta zaune kan kujerar mirrow tai shuru tana tunan, karasawa ya yi gefenta ya tsaya yana yar dariya yana fadin uwargidata bakya laifi
kallanshi tai ta ce wane ni, ai wannan taken sai amarya, hmmm su Ango kenan mijin Amarya
"mijin Uwargida dai, ina sonki matata, uwargida sarautar mata, ko dubu ne suka shigo sai sun tafi sun barni dake"
Haj Zeenatu ta mike tana fadin zuwa kai na raka ka wurin Amaryarka
Ya dan sosa keya yana fadin a'a kawai na zo ganinki ne da 'yayenmu
Haj Zeenatu ta ce koda haka dai ya kamata na raka ka wurin amarya daga nan sai ka yi mana nasiha Ina ga hakan ai zai fi
Alh Adamu ya ce eh to hakane muje
Alh Adamu rike da hannun Haj Zeenatu har bangaren Falmata, suna shigowa falonta suka sameta zaune kan kujera, ta yi zama irin na mulki
Alh Adamu cire hannunsa ya yi daga na Haj Zeenatu, ya tsaya cak, a take ya ji kamar wasu abubuwa na shigan jikinshi, ya rike kai gami da rufe idanunsa
Haj Zeenatu a rikice ta ce Alhaji lafiya, ko baka da lafiya ne?
Murmurshi Falmata tai ta taso daga inda take zaune ta karaso gaban Haj Zeenatu ta tsaya tana kallanta sannan ta ce ki gaggauta yin bankwana da mijinki sannan ki je ki fara tattara kayanki domin a daren nan zaki bar gidan nan
Cikin tsoro da rashin fahimta Haj Zeenatu ta ce ban fahimceki ba, me kike nufi?
Dariya Falmata ta shiga yi sosai bayan ta tsagaita ta kalli Alh Adamu da a yanzu ya koma dai dai, kallanta yake yi, ta ce ina son ka sake ta yanzu batare da bata lokaci ba
Alh Adamu ya ce yadda kika ce haka zai kasance
A rikice Haj Zeenatu ta ce karya kike yi, mijina ba zai taba saki na ba, baki isa ki rabani da mijina ba
Alh Adamu ya kalli Haj Zeenatu sannan ya ce na sake ki, ki tattara kayanki ki fitar min daga gidana, bana son ganinki
Cak Haj Zeenatu ta tsaya tana kallan Alh Adamu cikin mamaki, bakinta na rawa, hawaye na fita
*Please ku tayani sharing zuwa sauran groups 🙏🙏🙏*
Wa'inda basu turo katin data ba, suyi hanzarin turowa ta wannan numban 09049493054
Mu hadu a page 2
