ADS HERE

Wace Ta Dace Dani? Pg 9-12


*
_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

*WACE TA DACE DANI?*

*story n written by*
*Ummy Ontop*





9-10


Naifa sai kai kawo take cikin harabar Asibitin cen tasamu waje ta zauna ta zabga tagumi tare da tunani kala kala cikin zuciyar ta saka wannan warware wance take tayi lallai Lamis nacikin mawuyacin hali fatan ta Allah ya bawa Aminiyar ta lafiya, cen Saiga Dr mahad ya fito kiran Naifa yayi suka shiga office dinshi bayan yamata izinin zama shima ya zauna a tashi kujerar ya hade hannayenshi biyu tare da sunkuyar da kai kana Yakuma dago dakanshi ya kalli Naifa tare da ajiye siririyar ajiyar zuciya sannan ya soma magana" mene alakarki da Mara lafiyar da kika kawo, Naifa tace Aminiya tace" ina iyayen ta Dr mahad yayi tambayar tare da kurawa Naifa ido danjin Mezata ce,


Iyayen ta basa nan, karatu take anan ,tou ko zaki iya fadamin gaskia tundake aminiyar ta CE nasan kinsan gaskiyar, inshaAllah Dr , Mahad ya sauke numfashi sannan yace" Amma yarinyar nan tana shaye shaye koh , damm gaban Naifa ya yanke ya fadi domin tasan abunda Dr ya fada gaskia ne, karki boyemin , Naifa ta sunkuyar da kai k'asa sannan tayi kokarin furta Tabbas tanayi amma ...
Amma mei? Dr ya tambaya, amma a baya ne yanzu ba sosai takeyi ba,
Dr mahad yace "tou abunda yajanyo mata halin data ke ciki yanzu kenan, wannan shaye shaye yaso ya juyar mata da tunani gaba daya , yazamar mata dole ta daina domin lafiyarta idan har bata daina ba tabbas lafiyarta nacikin matsala babba, a matsayin ki na Aminiyar ta yakamata kitaka muhimmiyar rawa wajen taimakawa lafiyarta, Naifa tayi shiru cen k'asan ranta tana ayyana taya zata shawo kanta bayan itama halinta ne shaye shayen duda ita batakai Lamis din ba.
Ina fatan kin fahimci menake nufi maganar Dr yadawo da ita hayyacin ta, du maganin dazan bata da wani temako matukar bata daina ba a banza zai zama, inshaAllah Dr zanyi du iyakar kokarina zankuma sanar sda iyayen ta dansu sa ido akanta sosai. Shine dai mafita cewan Dr.
Yanzu baxamu sallame ta ba sedai ko zuwa gobe tasake samun hutu. Bakomai Dr Allah yakaimu goben , ameen bari na rubuta miki magungu nan dazaki siyo wa kawar taki, takadda yaja ya rubuta mata sannan yabata tamai sallama tafita a office din.

Dr yayi jugum mamaki du ya isheshi ace yarinya burwa mai karancin shekaru amma cikin wannan hali lallai zamani yazo karshe.



Koda fitan Naifa wajen magani tawuce dan tasiyo tana siyowa tayo dakin da aka kwantar da Lamis kwance take hannunta daure da drip tana bacci bakin gadon taje ta zauna tana kallon ta yacce take bacci a nitse. Allah yabaki lpia kawata



****



A hankali tasoma bude idonta harta gama budesu duka ta saukesu cikin dakin tanabin dakin da kallo ruwan dake daure a hannunta tagani sai lokacin ta fahimci asibiti take, turo kofar akayi a hankali Naifa tashigo dauke da flaks din tea da leda hannunta ajiyewa tayi gefe , Lamis kin farka ya jikin naki, Alhmdlhi naji sauki Naifa, karasawa kusa da Lamis tayi ta tallafota ta zauna muje ki watsa ruwa nakawo miki kayanki, da abun break.. Bari na kira nurse ta cire miki abun nan naga Dr bai karaso ba , Naifa ta juya zataje kiran nurse lamis tayi saurin rik'o hannunta jiyowa Naifa tayi lamis ta sakar mata murmushi sannan tace" nagode aminiyata dabadan ke ba nasan sai yacce hali Yayi nagode , uhm lamis kinjiki dawani Abu ai ke yerUwa tace, nidai ina zuwa bari na
Kira nurse bata tsaya jin mei lamis zata ce ba tasakai tafita daga dakin.

Dameer ne yafado mata a rai wasu zafafan hawaye suka zubo mata , meyasa! Meyasa ne kake wahalar da marainiyar zuciya ta , a ina zan sameka a ina zan ganka yaushe zakazo gareni soyayyar ka tana neman hallakani ka tausayawa jaririyar zuciya ta wacce bata taba sani *SO* ba sedata ganka, najima ina jiran bayyanar ka kuma na ganka saika bacemin...turo kofar da akayi ne yasa tayi saurin goge hawayen dasuka zubo mata, nurse din tacire mata sannu koh ya jikin naki lamis ta amsa da sauki , kamata Naifa tayi takaita toilet ta dawo, bayan ta gama wankan tafito kayanta tasa Naifa ta hada mata tea da bread hadda wainar kwai ta zauna taci sannan tasha magani, Dr mahad ne yashigo ya tadda Lamis nacin abinci lallai kinsamu sauki tunda har ana iyacin abinci Lamis ta sunkuyar dakai kasa tana murmushi, Naifa tace ai saukin kam yasamu Dr tou Allah yakaro sauki Naifa ta amsa da amin bari naje na dawo sai a rubuta muku sallama ko tou Dr cewan Naifa.



Bayan fitan Dr wayarshi tasoma ruri Sunan Dameer yana tsalle saman scream din dauka Yayi tare da kara wayar a kunnenshi, Aboki ya akayi katashi lpia, banji meyace ba kawai Dr yace ok tou seka shigo ina jiranka daga haka ya katse wayar ya wuce office dinshi.




*******




Dina na zaune ta zabga tagumi abun dunia ya isheta tarasa meke mata dadi tunanin wanda tagani a yanar gizo take har yau be karbi request din nata ba kamar ma anjima ba'ahau account din ba gashi tagani dan kano ne garinsu ma daya kodanshi zataso takoma koma kano sedai gaba daya karatun nata saura kadan gara tabari tagama ta taho gaba daya tunda idan tazo kano ma basanin shi tayi ba ba kuma tasan ta ina zata fara ganinshi ba gashi koda hotonshi bata gani sosai sai iyakar suman kai da idanu abunda tasani du inda taga wannan idanun tana kyautata zaton zata ganeshi.

Misha ta jijjigata ta motsa a firgice misha tayi. Dariya ganin yacce ta tsorata kd kuwa ina hankalinki yake sai faman mgn nake kin zubawa window ido bakyajina ,uhm tunanin mexanyi daya wuce project dina. Kai dina shine zesaki irin wannan zurfin tunani kedai akwai wani abun bashi ba Tou ni karki dameni tunda baki yadda ba dina ta fada tana mikewa daga wajen da niyar barin gurin Misha tayi dariya sannan tace idan tayi tsami zamuji ne.




*******



Kofa aka tura bayan anyi nocking anji shiru amma seyaga wayam babu kowa cikin office din kai ina kuma Dr Yayi bayan nacemai ganinan zuwa wayarshi yazaro dan kiran Dr mahad din saikuma yaganoshi cen yashiga wani daki tsuka yaja ya bi bayanshi wata nurse ta karya kwana hannunta rike da files dayawa tana zabga Sauri dawuri kamar zata tashi sama sukasha karo itada Dameer komai ya zube shikuma ya dafe kanshi dan ya bugu saurin kwashewa tayi ta dago tana bashi hakuri bakomai kawai ya iya furta mata sannan yayi gaba   dakin dayaga Dr mahad yashiga nan ya nufa,


Dr mahad yace tou zaku iya tafiya yanzu tunda ansallameku dan Allah Ku kula da kyau kubi du dokokin dana shinfidaku akai shine kawai samun saukin Naifa ta amsa da inshaAllah Dr za"a kiyaye , yawwa Allah ya kara sauwakewa , daidai lokacin da Dameer ya karaso nocking yayi tare da murda kofar ya tura a hankali.....







Maimunatooh




*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

*WACE TA DACE DANI?*

*story n written by*
*Ummy Ontop*



Wattpad @UmmyOntop




11-12




Koda Dameer yabude kofar Kicibus sukayi hadda karo da juna Dameer yayi saurin ja da baya Dr mahad ya karasa fitowa daga dakin yana daria , ganin dariyar dayake ya Kular dashi yadan daga murya yace malam baka ganin yacce ka buge ni ne zakazo kayitamin dariya tou ka kwana kana dariya anan ni kaga nabarma wajen dan takaita dariyar Dr mahad yayi yace" dan tsaya mana kajii" ko sauraranshi ma beyi ba yayi gaba abunshi ya fice waje.

Lamis jin sautin muryar dameer tayi zunbur ta mike ko mayafinta bata dauka ba ta fito tana leke babu kowa kofar dakin cikin asibitin tayi ko takalmi babu kafarta cikin zuciyar ta tana cewa" lallai wannan sautin ruhin raina ne wanda nake nema baxan taba bari ya kubuce min ba yau saina duba, Naifa dai ganin tana mata magana bata saurareta ba yasa ta dauko mata takalmin ta da mayafinta da sauran kayansu tabi bayan ta ,  babu lungu da sako da bata shiga ba cikin asibitin babu office din da bata leka ba ko zata ganshi, tsaya tayi chak baki kofar fita harabar asibitin tana hakki hawaye fall cikin idanunta dan tasoma zaton ko gizau muryar tamata, cigaba tayi da tafiya cikin harabar asibitin tana dubawa amma babu alamunshi jikin wata mota ta dafa tana fashewa da sabon kuka daidai lokacin da Naifa ta karaso ta dafa lamis haba lamis waike meke damunki ne haka lafiyarki kalo kuwa, ina zanyi lafiya bayan abunda nake nema yanamin gizo yana wahalarmin da zuciya dan Allah Naifa ki taimaka min nasamu farinciki na koda ace haduwar daxan sakeyi dashi itace ta karshe inason haka ko baze karbi kokon bara na ba xanji sauki idan na amayarmai da azababban sirrin dake zuciya ta takarasa maganar d asake fashewa da sabon kuka ,ita dai Naifa gaba daya kanta ya kulle , janyo lamis tayi jikinta tana bubbuga bayan ta alamun rarrashi ki kwantar da hankalin ki yanxu muje gida sai muyi maganar kinga ba cikakken lafiya ne dake ba , wani mai adaidai ta ya ajiye wasu Naifa ta tsayar dashi suka shiga ciki koda shigansu ciki yayi daidai da bude motar dasuka jingina jiki ina zuwa I will call u back ya katse wayar dayake yi tare da kokarin tsayar da motar dasu lamis suka shiga dan idanunshi sun nunamai lamis lokacin datake kokarin shiga mota tabbas itace yarinyar dayake nema ido rufe sedai tuni motarsu tayi gaba, be tsaya sanya ba yayi saurin shiga tashi motar ya figeta a dari danbin bayansu , cikin nasara basu b'ace mai ba sedai dadan tazara a tsakaninsu samadiya cinkoson ababan hawa ya hanashi Sauri yasha gabansu haka yasa yayi hakuri babu yacce ya iya yake binsu sannu a hankali , danja ce ta tsayar dasu idan Ransa yayi dubu ya baci burinshi yaga ya tadda motarsu dan yasamu tabbacin shaidar muradinshi ce kokuma I danishi ne basu gane mai daidai ba , ganin dai kamar danja baxata sakesu ba yasa ya fito cikin motarshi dan isa tasu motar jikin shi har tsuma yake sedayazo daf dasu danja tasake su babu b'ata lokaci motarsu taja tayi gaba.



Dameer ji yayi kamar ya kwala ihu dan bakin ciki gashi cen anata dannawa motarshi horn ya janyeta kan hanya, Sauri Yayi ya koma yana bawa mutane hakuri yashiga yaja yayi gaba sedai ya rasa wace hanya sukabi shikenan yanzu yasake yin sake kodai bashi da nasara ne akan yarinyar nan yafada cen k'asan zuciyarshi innalillahi waEnna Elaihi rajiUn kawai yake iya furtawa, idanunshi sunkawo kwalla sunyi ja har wani hucin takaici yake yi besan lokacin daya doki sitiyarin motar ba da karfi yana furzar da iska mai zafi daga bakinshi , kiran Dr mahad ne yashigo wayarshi ya dubi wayar dake gefe ganin Dr ne yasa ya dauki wayar ya kara a kunne tare dafadin yauma na rasa ta Dr, Meka rasa na fito du baka banga motar ka ba na rasa yarinyar nan yasake fada, Dr mahad yace kana ina ne yanzu? Ni natafi sedai muhadu a gida tou shikenan sainazo katse wayar yayi tare da cigaba da tafi yayi gida zuciyarshi na rad'ad'i .



********



Lamis da Naifa na zaune ta zabga ta gumi Naifa tace" ina jinki kinsoma magana kuma kinyi shiru,sauke ajiyar numfashi tayi ta kalli Naifa hawaye har sun sake kokawar barin cikin kwayar idanunta sunason zubowa ta daddage ta maidasu ta fara bawa Naifa labarin Dameer tun daga farko har karshe .

Shiru kamar Naifa batada niyar cewa komai cen kuma tace" gaskiya lamis kin tafka babban kuskure idan nice lokacin nan bazan taba bari ya kubuce min ba Nazo ina ta shan wahar Dakon soyayya, amma hadu dashi idan kina da rabo Allah zekawo mafita sedai bakya fargaba yaki karban soyayyar ki ya zaki a lokacin, lamis tayi murmushi kafin tace" ai Naifa koda baze karbi soyayya ta ba ban damu ba tunda dai nasan nasanar mai da soyayyar danake mai ma rage radadin zuciya ta saikuma na fuskanci ciwon rashin nasara , wallahi koda ace ganinshi ajali nane inaso nasake ganinshi du yanda zan kwatanta miki halin danake ciki bazaki taba ganewa ba Naifa.



Hmmm lallai lamis kina cikin mawuyacin hali iyaka hakama natabba tar kinashan wahala a zuciyarki nasan radadin *so*nasan azaban shi nasan wahalanshi nasan dadinshi, ina mai kyautata zaton baze ki amsar soyayyar ki ba sabida babu makosa tare dake koh ina cike kike 💯 baze taba kin karban ki ba matsayin masoyiya sedai...
Sedai mei lamis ta tambaya idanunta kan Naifa, sedai idan yakiki sabida dabi'armu dan bazance halinki ba ke kadai, kinga dai babu abunda bakyasha na maye kina tunanin akwai namiji mai hankalinki daze karbeki haka barima idan mei tsattsauran ra'ayine, lamis tayi shiru kamar mai nazari kafin tace " tayaya zesan inasha kinga zan iya dainawa wallahi sabida shi Kuma koda ban daina ba bazan bari yasani ba sedai idan ke zaki fadamai.
Allah yasawake idan ban rufa miki asiri ba wa zan rufawa kefa aminiyata ce shakikiya ta wacce kikafi kowa kusanci dani har yen uwana baxasu iya bada labarina ba kamar ke, inshaAllah ma baze sani ba Allah ya doraki akanshi aminiya Allah ya bayyana miki shi lamis ta amsa da ameen.





Maimunatooh

Post a Comment

ADS HERE
ADS HERE