ADS HERE
Posts

DIJANGALA PAGE 4

Hamrah dakin Grandma ta wuce ta fada jikinta tana kuka "Hamrah meya faru, ko yer kauyen nan ta dake ki ne?" "Grandma ina son Yaya Mustapha sosai, na ga alamun kamar Mum tana son ta rabani dashi" "Haba Hamrah daina kuka mana, taya zata rabaki da masoyinki, yana sonki kina sonshi, ai kawai kisa min ido auranku ke dashi nan da sati daya, babu wanda zai dakatar dani" Hamrah ta rungume Grandma cikin farin ciki "I love you Grandma" "Love you too my dear" Mum tuwan semo da miyan kuka ta shiga girkawa Mustapha, ya na son tuwo da miyan kuka, kuma yafi son Wanda mum ta girka Dije zaune a falo ta yi tagumi, Hamrah ta shugo tana murmushin mugunta "Bagidajiyar yer kauye" Dije ta juyo ta kalli Hamrah "Yanzu kika fara tunani kuma yanzu kika fara kuka, Mustapha nawa ne, kuma sai ya rabu dake" "Karya kike yi, Yayana baya sonki, ni yake so kuma ba zan yi kuka ba, ke zan saka kuka" "Kanki ake ji, ni kinga tafiya ta" Hamrah ta kara gaba Dije ta kara yin wani tagumi tana tunani "make faruwa ne, yayana ya koma ba yayana ba" hawaye ya fara bin kumatunta Mum bayan ta kammala tuwan ta kai wa Mustapha a daki, ta zauna gefenshi tana bashi a baki yana amsa, soyayya na kara shiga tsakaninsu, bayan ta gama bashi tuwan sai ta bashi ruwa ya sha "Mum thank you" "You are welcome" Tai murmushi ta tashi ta kwashe kwanukan ta fita Har yanzu Dije na falo, da ta ji bachci na son daukarta dakin mum ta je ta kwanta, bata tashi ba sai da magriba Mum ta shugo ta tashe ta domin ta yi sallah, babu musu ta tashi taje tayo alwala sannan ta dawo, da ta ga Mum ta fita bata yi sallar ba komawa ta yi ta kwana, can sai ga Mum dauke da abinci ta kawowa Dije "Kin yi sallar?" "Eh" "To ga abinci, sakko ki ci" Dije ta sakko daga kan gado ta zauna kan kafet din tsakiyar dakin ta ci abincin da Mum ta kawo mata, bayan ta gama, ta kara komawa ta kwanta Wurin karfe tara Mum ta shugo ta tashe ta "tashi ki tafi dakinku" Dije ta marairaice "ni anan zan kwana, ina jin tsoron Yayana" "Babu abinda zai yi miki, koma mai ya yi miki ki zo ki fada min" "To Inna" Dije ta tashi ta fita Mustapha kwance kan gado yana kallan sama yana tunani, ya ji an budo kofa, kallan kofar ya yi Dije ce ta shugo, kawar da kanshi ya yi daga kallanta, yadda ta ganshi tsoro ya kamata, karasowa ta yi dakyar ta zauna gefe ta Jingina da bango "Dije" Mustapha ya kira sunanta "naam" "Je ki yi wanka" "Na yi ai" "Koma ki sake yi" Babu musu ta shiga bayi ta yi wanka ta fito, tashi ya yi zaune "koma ki sake yi" ta zaro ido "na yi fa" "Ina wasa dake ina magana kina kawo min wani magana" Dije ta koma bayi ta yi wanka ta fito "Jeki canza kaya" Zuwa ta yi ta bude durowa ta dauki sabbin kaya ta shiga bayi ta saka sannan ta fito, ya nuna mata kan gado "zo ki kwanta" Cikin tsoro ta je ta kwanta kan gado, Mustapha jera filo ya yi a tsakanin su saboda kada cikin dare ya taba jikinta bai sani ba, shi yana kallan kudu ita tana kallan arewa, sun dade suna tunani a zuciyoyinsu, bachci ya gagaresu sai wurin karfe daya sannan bachci ya sace su Da asuba Mustapha ya farka, jin kafar Dije ya yi a jikinsa, da sauri ya tashi ya sa mata tafi a baya ta farka a razane "Wayyo Inna ta" "Wannan wani irin wawan bachci kike yi, har zaki dora min kafarki a Jikina" Tayi dai dai da ido "to da sanina ne, ba bachci nake yi ba" Watsa mata harara ya yi sannan ya tashi ya shiga bayi ta bishi da kallo "Ai komai ka yi min zan fadawa Inna" ta koma ta kwanta Ya fito ya sameta ta kwanta, ya daka mata tsawa "Dije" ta mike zaune a rikice "Ki tashi kije kiyi alwala ki yi sallah" Ta turo baki "ni sai da safe zanyi" "Idan baki shiga bayi kinyi alwala kin fito kinyi sallah ba sai nayi miki tsinannan duka, ina wasa dake?" Dije ta tashi tana turo baki tana kananun maganganu, bayi ta shiga ya ja tsaki ya fita ya wuce masallaci Dije ganin ya fita yasa ta fito daga bayi ta hau kan gado ta kwanta Mustapha bayan sun idar da sallah a masallaci ya dawo yana ganin Dije a kwance jikinsa ya bashi bata yi sallah ba, wani dundu ya yi mata a baya ta tashi da sauri a razane "Me kuma na yi?" "Je ki yi sallah" "Nifa na yi" Ya daka mata tsawan da bata san lokacin data Sauka daga kan gado ba ta shiga bayi, cikin takaici ya zauna bakin gado yana tunani Dije ta fito bayi, ta dakko hijabi ta saka ta shiga yin sallah, hankalin Mustapha tashi ya yi yadda ya ga Dije bata iya sallah ba, ya ce a zuciyarsa "wai wannan ne mata ta, ko sallah bata iya ba, gaskiya nidai an cuce ni, tashi ya yi ya fita don baima son ganin fuskar Dije Falo ya dawo ya yi kwanciyarsa, Hamrah ta fito ta sameshi "Baby ya zaka zo ka kwanta a falo" Ya tashi zaune, ta zauna gefenshi "Love ina cikin matsala, ba zan iya rayuwa da Dije ba" "Nima nasan ba za ka iya rayuwa da ita ba, nama yi mamakin yadda kuka kwanta daki daya da ita" "Love ki taimake ni, ni ke ce nake so, ya zanyi na mallake ki, ga Mum tana son rabamu" "Kwantar da hankalina, akwai wani abu dake shirin faruwa" "Mene ne kenan?" "Grandma tana shirya aure na da kai amma a cikin sirri, karka bari Mum ta sani" Ya zaro ido "dagaske kike" "Kasan dai ba zan maka karya ba" "Amma wallahi na yi farin ciki sosai" "Amma nan da yaushe ne?" "Ka je wurin Grandma zaka ji komai a wurinta" Ya mike "ai kuwa ba zan tsaya bata lokaci ba" Ya wuce dakin Grandma, Hamrah ta bishi da kallo tana murmushi Dije tsakiyar gado zaune tana tunani, "wannan ba yayana bane, yayana ba mutu bane, yana wasa dani, a take ta shiga tuna yadda suke wasa da da Mustapha a lokacin da bai da lafiya, tsintar kanta ta yi cikin nishadi, sai murmushi take yi ita kadai Grandma zaune kan sallaya tana wuridi Mustapha ya shugo ya zauna gefenta, ta juyo ta kalleshi "Grandson ykk?" "Ina kwana Grandma" "Lafiya lau" "Dama nazo ne akan wani magana da Hamrah ta fara fada min, wai kina shirya aure na da ita" "Eh gaskiya ne, kuma nasan ba za ka bani kunya ba" "Ni Grandma ma farin ciki na yi wallahi, yaushe ne bikin?" "Jumma'an nan me zuwa, ana idar da sallahn jumma'a" "Wow Grandma so much love" "Kai kasan ai ina yinkA sosai" "Amma fa ina tsoron matakin da Mum zata dauka" "Karka damu, babu yadda zata yi dole ta yi hakuri ta barni da miradina" Suka cigaba da tattaunawa daga karshe ya bar dakin, dakinsa yaje ya sami Dije zaune kan gado ya galla mata harara Ta kawar da kanta, zuwa ya yi zai shiga bayi sai ya tsaya ya juyo yana kallanta "Ke na tambayeki mana?" Ta tsura masa ido "Wani abu ya taba shiga tsakanin mu" Murmushi Dije ta yi ta ce Yaya abubuwan da yawa sun faru mana Ya zaro ido "kamar me da me?" Ta karayin murmushi tana shiga cikin shauki, kamar wasanninmu, ina son tuno wasannin da muka yi Rikicewa ya yi ya karaso wurinta "wani irin wasa kenan?" "ka koya min buga kwallo, muna kada taya tare, muna cin abinci tare" "Amma na taba taba jikinki?" "Eh" Ya kalleta a rikirkice "kana rungume ni kamar yer yarinya" Mustapha ji ya yi zufa ya fara keto masa "na shiga uku" ya fada a hankali ya daure ya kara tambayarta "amma na taba taba miki nan wurin" ya nuna kirjinta, kunyane ya kamata, ta rufe fuska tana yer dariya, wani haushi ya tsaya mishi a wuya "Ke tambayarki nake yi, ba shirme na ce ki yi min ba" "Baka taba tabawa ba" Wani ajiyar zuciya ya yi, ya ce "Allah nagode maka" Komawa ya yi zai shiga bayi ya kara tsayawa ya juyo ya ga tana kallanshi, bata rai ya yi "Na tambaye ki?" "Ina jinka Yaya" "Da Mustapha me wasa dake, da wannan Mustaphan dake tsaye gabanki wanne kika fi so?" Shuru ta yi tana tuna Mustaphan ta tana yer murmushi, tana kara tuna yadda suke wasa "Nafi son Yayana me wasa dani" "Yauwa yafi miki alheri, haka nake son ji, kisa a ranki wannan Mustaphan da kike wasa dashi ya mutu, wannan wani ne daban" Ta tsura masa ido "amma Yaya kamanninku daya, yanzu haka daka tsaya ina jin yadda nake ji a raina a duk lokacin da muke tare dashi, sannan tare dakai muka hau mota muka yi hatsari, kai ka ce kana sona kai ka ce baka da Babbar kawar data wuce ni" "Kamanninmu daya ne dashi, hatsarin nan da kuka yi dashi ya mutu, kisa haka a ranki" Ya bude bayi ya shiga ta bishi da kallo, idanunta sun ciko da ruwa sosai, fadi take "dama Yayana ya mutu ya barni" Tashi tayi da sauri ta fita bata tsaya ko ina ba sai dakin Mum, ta fada jikinta tana kuka, gaban Mum ya fadi "Dije meya faru, me ya yi miki?" "Inna ashe Yayana ya mutu" Cikin rashin fahimta Mum ta ce bangane ya rasu ba "Ashe da muka yi hatsarin mota Yayana da muke wasa ya mutu, wannan Yaya Mustaphan baya sona shine mai duka na" "Shine ya fada miki Yayanki da kuke wasa ya mutu?" "Eh" Ta rungumota jikinta "karki damu da maganarsa wasa yake miki, shine yayanki da kuke wasa dashi" "Inna dagaske shine yayana da muke wasa" "Tabbas shine" "To meyasa yanzu baya sona?" "Ki kwantar da hankalinki, yayanki yana sonki sosai, bai da lafiya ne, ki yi masa uziri, duk abinda zai dinga miki ki dinga masa kallan mara lafiya" "Kenan bai da lafiya ne?" "Eh" Mum dai ta cigaba da kwantarwa da Dije da hankali, Har Dije ta samu natsuwa Mustapha bayan ya fito wanka ya shirya tsab cikin riga da wando kananun kaya ya yi kyau sosai, falon Dad ya wuce direct, ya zauna kujeran dake fuskantar na Dad, Dad ya nuna wasu file a kan center table "Takardun kamfanoni ne guda biyu, jiya na saye su, daya naka daya na mahaifiyarka" "Wow Dad, na yi farin ciki sosai sannan idan Mum ta samu labarin nan nasan zata yi farin ciki" "Kuma fa toshiyar baki na yi mata akan maganar auranka da Hamrah" "Dad ashe kaima kasan shirin Grandma" "Na sani mana, dole za'a yi bikin a sirri saboda kasan kafiyan Mum dinka" "Hakane Dad" Dad ya dauki file daya, "amsa naka" Mustapha ya amsa ciki farin ciki, "sannan Dad ina neman alfarma ba zan iya barin kwallan kafa ba" "Babu damuwa, ina maka fatan alkairi, jeka bude durowata ka dauki laptop da wayoyinka da mukullan motanka" "To Dad" Mustapha ya je ya bude durowan Dad ya dauki kayayyakinsa sannan ya yiwa Dad sallama ya wuce Da shugowarsa falon Mum ya tarar da Dije tana fitowa daga dakin Mum, karasowa ta yi wurinshi da sauri, ta tsaya gabanshi "Ke ina wasa dake?" "Ashe karya kake yi, kaine wanda muke wasa da kai, Inna ta ce baka da lafiya" Wani bakin ciki da bacin rai ya tsaya masa a wuya, ya daga hannu ya koda mata mari, sannan ya nunata da yatsa "Har yaushe kika samu damar da zaki karyatani, kuma har kice min banda lafiya, idan kika kara makamancin wannan wasan dani, saina miki rashin mutunci" Ya ja karamin tsaki ya wuce, Dije kuwa ta duka a wurin ta fara kuka Dije rarrashin kanta ta yi sannan ta tashi ta wuce daki, bata tarar da Mustapha ba, ta kwanta kan gado a wahalce, sai bachci ya dauke ta Mustapha zuwa ya yi ya hadu da Haidar, Haidar ya yi farin ciki da ganin Mustapha ya samu lafiya, zaune suke a Garden suna tattaunawa "Abokina na tayaka murna, ban taba tunanin zaka samu lafiya nan kusa ba" "To abu na Allah, shike daurawa bawa cuta kuma ya warkar dashi" "Amma nasan hankalinka ya tashi da ka ga matarka?" "Haidar bari kawai, wallahi duniyarnan na rasa meke yi min dadi" "Amma kasan miye kuwa?" "A'a saika fada" "A lokacin da kake cikin nalura, ka so Dije kamar rayuwarka" "Karka bata min rai mana" "Gaskiya nake fada maka, kaima yakamata ka tuna soyayyar da kuka nunawa junanku" Mustapha ya mike "na ga alamun kana nema ka bata min rai, ni zan wuce" "A'a koma ka zauna saimu canza topic" Mustapha ya koma ya zauna "da yafi dai" Nan Mustapha ya fara yiwa Haidar magana akan kamfanin da Dad ya saya mishi, suka fara shawarar yadda zasu tafiyar da kamfanin Mum ta ji Dije shuru yasa tazo ta dubata ta sameta tana bachci, bata tashe ta ba ta fita abinta, falon Dad ta wuce ta je ta sameshi yana karanta jarida, zama ta yi a gefenshi "Sannu da hutawa Dad" Ya kalleta "yauwa Madam" "Ba ka yi breakfast ba har yanzu" "Eh yanzu zan zo na yi, kafin nan ga takardan kamfaninki dana saya miki, ina son ki fara business" Farin ciki ya baiyana a fuskarta "wow aiko godiya nake Dad, Allah ya kara arziki ya kuma barni tare dakai" "Amin mata ta" "Yanzu dai ka tashi mu je ka karya" "Bari na gama karanta nan shafin' Ta matsa wurinsa tana kallan cikin jaridar Dije ta jima tana bachci kamin ta farka sannan ta fita ta je kitchen ta zuba abinci sannan ta dawo daki ta zauna tana ci amma bata tantance dadin abincin, kawai tana danne ciki ne Haka ranar Dije ta wuni a daki babu abinda take tunani sai Yaya Mustaphanta, har yau ta rasa gane gaskiyar al'amari, ya mutu ne ko yana raye, don ta tabbata Yayanta Mustapha ba zai taba koda mata mari ba, hango Teddy bear ta yi a gefe guda, ta shiga tunanin lokacin da Yayanta ya bata kyautarsa, yana fada mata "a duk lokacin da ya yi nisa da ita, ta rike shi a matsayin sa" Ta kalli Teddy bear din tana hawaye "Yayana Mustaphana mai sona ya mutu, yanzu kaine yaya Mustaphana" ta rungumesa tana hawaye, tana kankame da Teddy wbachci ya dauke ta Wajen karfe tara na dare Mustapha ya dawo ya tarar da Dije kwance tana bachci ta kankame Teddy bear, hawaye duk sun bushe a fuskarta, fuskarta ya yi fayau, tsaki ya ja gami da galla mata hara Bayi ya shiga ya yi wanka sannan ya fito ya saka jallabiya, ya tsaya yana kallan Dije dake kwance a tsakiyar gadon cikin tsananin bacin rai Kiran sunanta ya fara yi cikin tsawa, ta tashi a firgice cikin tsoro tana kallansa "Koma gefe ki kwanta" Dije ta ja ta koma gefe, sai ya je dayan bagaran gadon ya kwanta, ya jera filuka a tsakiyarsu Dije kara kankame teddy bear ta yi fadi take a hankali "ina sonka yayana, ka dawo mu cigaba da wasa" Dakyar bachci ya dauke ta, bata tashi ba sai da asuba da Mustapha ya tashe ta da dundu akan ta je ta yi sallah, ta tashi ta shiga bayi shi kuma ya wuce masallaci Da Dije ta fito daga bayi kwanciya ta yi akan sallaya, da ta ji motsin shugowar Mustapha ta tashi zaune ta yi kamar tana zikir Tsayawa ya yi yana kallanta sannan ya yi mata kallan banza ya wuce ya kwanta kan gado, Dije bata iya komawa kan gadon ba, anan kan sallayar ta koma bachci Da sassafe Dije ta tashi ta dauki Teddy bear dinta ta rungume "yayana dafatan ka tashi lafiya" Farkawa Mustapha ya yi daga bachci, hankalinsa ya kai kan Dije "Yau zamu yi wasa da kai, zamu biga kwallo kuma zamu yi sauran wasannin da muka saba" Karamar tsaki Mustapha ya yi ya sauka daga kan gado "Ke bana bukatar hauka" Ta kalleshi "bafa da kai nake yi ba, da yayana Mustapha nake yi" "Ina yake?" Ta nuna Teddy bear "Au shine yayan naki?" "Eh shine, Yayana kafin ya mutu shine ya bani yer bebin nan, ya ce min a duk lokacin da ya yi nisa dani, na rike shi a matsayinsa" "Da kyau mahaukaciya" Mustapha ya fada sannan ya shiga bayi Haka rayuwa ya kasance tsakanin Dije da Mustapha har ranar jumma'a Dije rungume da Teddy bear tana zaune tare da Mum a falo "Inna yaushe zan koma Hadeja?" Mum ta tsura mata ido "me kuma zai komar dake Hadeja?" "To Yayana ya mutu, mai kama dashi kuma azzalumi ne, baya wasa dani" Grandma da Hamrah suka fito falo, Grandma na guda tana fadin Alhamdulillah, Allah ya tabbatar, aure ya dauru, Hamrah kuwa farin ciki yaki daukewa daga fuskarta Mum ta ce mama auren wa kuma aka daura banda masaniya Grandma da Hamrah suka samu wuri suka zauna, "jikana ya Mustapha yau ya angwance" Mum ta mike gami da zaro ido "ban fahimci me kike fada ba" "Hausa na yi miki ai, an daura auran Mustapha da Hamrah yau a masallaci"

Post a Comment

ADS HERE
ADS HERE