ADS HERE
Posts

WATA KADDARA PAGE 1


 ❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤


   *WATA KADDARA*


❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤


*Na Maryam Muhammad*


❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤


*Hasheem (M jaruma ce)*


❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*

*🇦SSOCIATION🤝🏻*

 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassoctsan


❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤


*MARUBUCIYAR*


 1. Angon mata biyu

 2. Dijangala

 3. Dogari

 4. Izzar Ameera

 5. Matar cele and now

 6. Wata kaddara


*Ta fannin wasan kwaikwayo (Scrpit) wato film kenan*


 1. Gidan Liman

 2. Alkalin kauye

 3. Dan talaka

 4. Dan mace

 5. Rayuwar Intisar

 6. Auren kaddara

 Da sauransu don ba zan iya fadan sauran ba wasu ma na mantasu


*Ga masu bukatar Angon mata biyu audio sai su ziyarci YouTube channel dina mai suna M jaruma novels tv*


https://youtu.be/ShavMDSPnrw


*Zaku iya shiga ta wannan link din dake sama domin sauraran audion*




*GODIYA TA TABBATA GA ALLAH UBANGIJIN TALIKAI DAYA BANI DAMAR FARA RUBUTA WANNAN LITTAFI DANA MISHI SUNA DA WATA KADDARA, ALLAH YASA NA GAMA LAFIYA KUMA YASA MU AMFANU DA SAKON DA YAKE DAUKE DASHI*


*ALLAH KA YI SALATI GA SHUGABANMU ANNABI MUHAMMAD SAW DA IYALAN GIDANSA DA SAHABBANSA*


*ADDU'AR KU A KULLUM SHI KE TASIRI A KAINA, ALLAH YA BAR MIN KU IYAYENA DA YAN UWANA*



*JINJINA A GAREKU MASOYANA, BANI DA BURIN DAYA WUCE NISHADANTAR DAKU A KOWANI LOKACI, INA ALFAHARI DAKU, ALLAH YA BARMU TARE*


*NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA KAINUWA WRITER'S ASSOCIATION, INA YINKI OVER AUNTY FAUZY, MAMAN NOOR DA HARUNA BIRNIWA*



*Wannan littafin kage ne, labarin ya fito daga kasar zuciyata ce, mallakina ne kuma ban yarda wani ko wata ta sauya min labari ba ta kowata hanya*




❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤


Hanan da Hafeez zaune a tsakiyar gado, Hafeez rungume da Hanan da take kuka yana ta faman rarrashinta "Hanan ki yi hakuri, ki mikawa Allah komai, shi zai kawo mana maganin damuwar" Hanan ta shiga magana cikin muryar kuka "na yaudari kaina, nina cuci kaina da kaina, na biyewa rudin zuciya gashi yanzu abinda ya kai ya kawo" Hafeez ya kara jawota jikinshi yana shafa kanta "Ki yi hakuri Baby, ina tare dake" Hanan ta banbare jikinta daga nashi ta ce ka fada min ya kuka yi da likita? Shuru yai yana tunani da alamu yana fargaban fada mata yadda suka yi da likita, rike hannunshi tai "please karka damu ka fada min ya kuka yi da likita, rashin fada min shi zai sa na kara shiga damuwa" ajiyar zuciya ya yi sannan ya ce a gaskiya ya ce ba za ki taba haihuwa ba, alluran da kika yi ya kashe mahaifarki gabadaya


Nan take Hanan ta shiga rera wani sabon kuka kamar ranta zai fita daga jikinta, fadi take yanzu shikenan haka rayuwata zata kare, janyota yai jikinshi ya toshe bakinta da wani hot kiss, ya kai tsawon lokaci yana shan bakinta sannan ya daina, ya kai bakinshi saitin kunnanta ya shiga yi mata magana cikin sanyin murya "ki kwantar da hankalinki, akwai wani mai magani da aka hadani dashi a wani karamin kauye, yana bayar da taimako sosai, ina da tabbacin zai bani maganin da zan baki, da ikon Allah zaki samu ciki, gobe zan je wurinsa"


Sai yanzu murmushi ya baiyana a fuskar Hanan ta kalli Hafeez "kenan idan ka je wurinsa ka dawo da magani zan samu ciki"


"Insha Allah" cikin farin ciki ta rungumeshi tana fadin to idan kuna na yi amfani da maganin ban samu ciki ba me zai faru?" Hafeez ya ce babu abinda zai faru, Hanan ko kin haihu ko baki haihu ba zan kasance tare dake har abada kuma batare da na yi miki kishiya ba


"Ka yi alkawarin ba za ka min kishiya ba?"


"Na yi alkawarin ba zan taba yi miki kishiya ba matata, ke kadai zuciyata take so, ba zan raba soyayyar da nake miki ba dana wata 'ya a duniya ba"


Sosai Hanan ta kara rungume Hafeez tana jin wani tsananin kaunarsa na ratsa ilahirin jikinta


Hafeez kallan kirjinta ya shiga yi, sanye take da wani rigar bacci mai tsantsi, sai nonuwanta su kai dai dai a ciki, lokaci daya idanunsa suka sauya, ya kai hannunsa ya shiga shafa su, sai kuma ya hade bakinshi da nata ya fara tsotsa


Janye jikinta tai a marairaice "i am not in the mood"


Hafeez dakyar ya bude baki ya ce Baby ina cikin mood din, ina so na yi


Lokaci guda Hanan ta hada rai, ta kwanta gami da rufe jikinta da bargo tana fadin ni karka tabani gaskiya fa, bana jin yin wani abu yanzu, ta kai maganarta ta rufe idanunta, Hafeez ya tashi cikin bacin rai ya fita ya bar dakin, dakinshi ya wuce direct ya fada kan gado cike da takaici, rungume filo ya yi sosai yana dan juye juye, zuciyarsa na raya masa ya fita ya je ya nemi matan banza, wata zuciyar kuma na fada masa kar ka ci amanar farin cikin ka Hanan, haka dai ya kasance dakyar ya samu bacci ya dauke shi


❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤


*KAUYE*


Gidan Mal Adamu dakuna guda biyu ne, daya na Mal Adamu da Inna Larai, dayan dakin kuma na Zeenai ne, bangare guda kuma dakin girkin abincine wato kitchen, duk bangon kitchen din ya yi baki, Haleema ce kwance ciki tana bacci, ta kudundune wuri daya da alamu sanyi take ji


Can Inna Larai ta fito daga daki tana mika batare da salati ba, hankalinta ne ya kai kitchen ta hango Halima, lokaci guda ta bata rai tana fadin lallai ma, har kin samu damar da zaki kai wannan lokacin kina bacci, ai kuwa saina hukuntaki, daukar bokatin ruwan tai ta yi hanyar kitchen, tana isa ta kwarawa Haleema ruwan


A firgice Haleema ta mike cikin tsananin tsoro tana salati


Haleema yarinya ce yar shekara goma sha hudu, kallo daya zaka yi mata kasan kyakkyawar gaske ce amma kyawunta ya disashe saboda bakar wahala, farin fatarta har wani dauda dauda ya yi tsabar rashin wanka, kitson kanta kuwa duk tsaga sun boye tsabar tsufa, amma jelar kitson sun kwanta a kafadunta


A rikice Haleema ta durkusa a gaban Inna Larai "Inna ki gafarce ni" Inna ta watsa mata harara "don uwarki har kin sami damar da zaki kai wannan lokacin kina bacci, uban wa zai yi miki aikin gida?"


"Inna ki yi hakuri ba zan kara ba"


Inna Larai ta rike kunnanta daya "daga yau da asuba zaki dinga tashi, ki fara ayyuka, idan kika kara kaiwa wannan lokacin sai jikinki ya fada miki, yanzu sai ki tashi ki je ki hada wuta, ki daura ruwan koko"


Haleema ta mike tana fadin to Inna


Inna Larai ta watsa mata harara sannan ta wuce daki, Haleema ta shiga hada wuta


❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤


Hafeez tun daya tashi bai hadu da Hanan ba, bathroom ya shiga ya yi wanka sannan ya fito ya shirya cikin wata farar gyazner mai matukar kyalli, ya feshe jikinsa da turaruka masu matukar kamshi, Hanan ce ta budo kofar dakin ta shigo cikin shiga ta alfarma, sanye take da leshi mai matukar tsada, sai tashin kyau da kamshi take yi, Hafeez dake gaban madubi yana kafa wularsa ya juyo yana kallanta "tunda ba za ki gaisheni ba, ni bari na gaisheki ina kwana"


Hanan ta ce au na manta Good morning darling


Smile yai sannan ya karaso gabanta ya tsaya "love you my madam"


"Harka shirya tafiya wurin mai maganin kenan?"


Ya shafa kumatunta "eh na shirya"


Hanan ta marairaice sannan ta ce nifa ba don dole ba bana son ka da hanyar kauye


"To ai kamawa yake yi, kuma dai kin san muna san Baby dole mu je mu nemi magani"


Hanan ta ce hakane, waya ganni da ciki, ranar babu bacci tsabar farin ciki


"Karki damu burin mu zai cika, zaki haifa min yara su cika gidan nan, batare da wata ta tayaki ba"


Hanan ta bata rai "nifa ba da yawa zan haifa ba biyu sun ishe ni"


Hafeez ya ce ni ban amince ba gaskiya, ya kamata ki sani ina son yara


"ni kuma biyu kawai zan haifa, dole ra'ayina zaka ba"


Hafeez ya tsaya kallanta cikin mamaki batare da ya ce komai ba, zuciyarsa na kawo masa tunani daban daban, komawa ya yi gaban mirrow ya dauki agogo ya makala a hannunsa sannan ya kalleta "ni zan tafi sai na dawo"


Ta gefenta ya bi ya wuce har ya kai bakin kofa ta dakatar dashi "Baby ka dauki securitys ku tafi tare, ina tsoron hanya"


"Karki damu babu abinda zai faru" bai jira ya ji me zata ce ba ya yi wucewarsa tabi bayanshi da kallo


❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤


Haleema ta riga data hura wuta, ta dora ruwan koko, tai tagumi gaban murhu tana tunanin Ummanta, hankalinta ya dawo kan Zeenai da ta shigo dauke da kayan wanki a hannunta, fuskarta babu rahama, ta watsa mata kayan wanki a fuskar "gashi ki wanke min" Haleema ta kalli kayan wankin sannan ta kalli Zeenai "jiya fa na wanke miki su"


Zeenai ta ce cikin tsawa to basu fita ba, sai yasa na dawo miki dasu, idan kinga dama yauma karki wanke da kyau ki ga abinda zai faru, Shashasha mara amfani kawai


Zeenai ta wuce Haleema ta bita da kallo hawaye na bin kumatunta, fadi take a zuciyarta "Allah sarki Ummana, kin tafi kin barni a cikin kangin rayuwa, azaba zai kashe ni"


Hankalinta ya koma kan ruwan kokon dake tausa, dakko kullin koko tai ta dama sannan ta sauke ruwan dake tausa ta dama koko, bayan ta gama ta juye a wani roba mai murfi ta rufe sannan kamar kullum ta je ta dakko taburma ta shimfida a gefen kofar dakin Inna Larai, ta dawo ta dauki robar kokon da kofina ta je ta aje kan taburmar sannan ta tsaya bakin kofar tana sallama

Inna Larai bata amsa ba cikin tsawa ta ce kin gama ne?


Haleema ta ce eh Inna na gama


"To sai ki je ki kama wasu ayyukan"


Tsintsiya Halema ta dauka ta shiga yin share share, can Inna Larai da Mal Adamu suka fito daga daki, Inna Larai rike da katon biredi, Haleema tai saurin dukawa kasa kanta a sunkuye "Baba ina kwana" batare daya kalleta ba ya amsa kasa kasa, suka zauna kan taburma


Inna Larai ta shiga kwalawa Zeenai Kira "'yar mama, yar mama fito ki ci abinci"


Zeenai ta fito daga daki tana fadin haba Inna, kina ta kwalamin Kira da karfi har gabana ya fadi


Inna ta yi murmushi cikin sanyin murya ta ce yi hakuri yar mama, taho ki ci abinci


A shagwabe Zeenai ta karaso ta zauna gefen Inna Larai, Inna Larai ta zuba mata koko a kofi sannan ta diba mata biredi mai girma, Zeenai ta amsa cikin farin ciki


Haleema ta dakata da sharan da take yi ta tsaya tana kallan yadda suke shan koko suna cin biredi, sai faman hadiye miyau take yi, suka hada ido da Zeenai, Zeenai ta kalli Inna Larai "ji yadda waccan maiyar ke kallonmu kamar zata cinye mu"


Inna larai ta ce ai maiyar ce, kin taba ganin yadda barewa tai gudu danta yai rarrafe


Inna larai ta kalli Haleema "fita waje ki tsaya idan mun gama saiki shigo ki cigaba da aikin"


Muryar Haleema na rawa ta ce Inna yunwa nake ji, ku taimaka min


Mal Adamu ya kalleta sai dauki kofin ya zuba koko zai mika mata Inna Larai ta dakatar dashi "karka kuskura, indai ba fushina kake son gani ba" Mal Adamu ya aje kofin kokon yana bawa Inna Larai hakuri


Inna larai ta ce ke yar mara mutunci fita waje ki zauna idan mun gama sai ki shigo


Haleema ta aje tsintsiyar ta fita da sauri, kofar gida ta wuce ta zauna, ta saka kanta a tsakankanin gwiwowinta tana kuka mai taba zuciya "oh Allah Ummana kin tafi kin barni, Baba baya sona, Umma idan baki dawo ba mutuwa zan yi" haka Haleema ta cigaba da kuka babu mai rarrashinta


*Please ku tayani sharing zuwa sauran groups 🙏🙏🙏*


Wa'inda basu turo katin data ba, suyi hanzarin turowa ta wannan numban 09049493054



Mu hadu a page 2

Post a Comment

ADS HERE
ADS HERE