ADS HERE
Posts

UMURNIN SAURAYINA


 *°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°*

*1441H/2020M.*




®☄

*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍️*

_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata,Burinmu mu faɗakar da Al'umma Domin Ribantar Duniya Da Kuma Lahira.}_


'''🎐G•W•A🎐'''

*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*



*NA MARUBUCIYA:-*

*SUMY M NA'IGGE✍🏼•*


*SADAUKARWA GA:-*

*GASKIYA WRITER'S ASSCIATION.*



~Wattpad @GaskiyaWritersAsso.~




*SHAFI NA 1📑*


*__________📖* Wayar tace ke rura, tana son ta tashi ta ɗauka amma ta kasa, saboda irin yadda ya manne ta a jikinsa.


Sosai wayar ke rura aƙalla anfi yin miss call goma amma tana ji ta kasa tashi ta ɗauka.


Ba dan komai ta kasa tashi ba sai dan kada ta ɗan mutsa ta ta da shi,abinda bata so ita kuma.



Wayar ce taƙi dai na ƙara,kuma gashi bata son ƙarar data ke, dan bata son ƙarar ta dame shi yana baccin sa,dan haka ta fara tafiyar da hannuta slow-slow har ya kai kan wayar.



Ɗauko wayar tayi lokacin kuma wayar ta sanya wata ƙara.



Da sauri ta sanya ta silent, duba miss call ɗin tayi taga wake kiran ta.



Fara dubawa tayi aikuwa gaban ta ne ya yi munmunar faɗuwa da taga wanda ya kira ta.



Tana cikin wannan fargabar sai ya fara mutsi alamun zai tashi,jikinsa ya ƙara jawuta kana ya ɓuɗe idonsa waɗan da bacci basu gama sakin shi ba.



Ahankali ya fara mata magana akunne yace, "My Sweet nah, ki tashi ki haɗemun abunda zan karya saboda yanzu na ke son tafita office dan jirana akeyi".



Ba musu tace, "yanzu kuwa Hayateena".



Kumatunta ya shafa haɗe da kai ma kiss kana yace, "shiyasa nake ƙara sonki".



Murmushi tayi mai ɗan sauti kana ta tashi taje kitchen ta haɗa masa abunda yake buk'ata.



Har takusa kammalawa wayar ta tasake ƙara,da sauri ta ɗauku waya tana mai duba sunan dake yawo saman screen ɗin wayar.



Gabanta ne yaba da dummm hannuta na karkarwa ta kara akunninta.



Kafin tayi wata magana har anfara magana cikin faɗa-faɗa.



"Hafsa ina kikaje?ina kika kwana?miyasa kikeso kijamin abun magana da mahaifinki, ehh!".


Muryar ta narawa tace, "Mama wallahi karutune yayimin yawa kuma kinsan munkusa Fara exams kuma wannan karun mai zafice zamuyi shiyasa nayi bacci na a hostel,amma ki bashi hak'uri anjima kaɗan zan dawo".



Sai Mama tace, "to naji amma kirinƙa faɗamin idan zaki kwana saboda nasamu natsowa kinji ɗiya ta".



Tace, "tau Mama sai nazu anjima".


Bayan sunyi sallama da Mamar ta,tashi tayi ta haɗe masa komai na breakfast,bayan ta kammala taje toilet ta haɗa masa ruwan wanka,bayan ta gama haɗe masa taje ta faɗa masa yazo yayi wanka.



Bayan yayi wanka ya fito,da kanta ta shirya sa ta fesheshi da turare mai ƙamshi kana ta kaishi dining Yayi bearkfast.


Bayan ya kammala ya tashi zai fita office,jikin sa ya jawota kana ya kai mata kiss a baki,ido cikin ido ta dubeshi ciki da shagwaɓa tace,"Hayatee nah, anjima zanje gida dan Mama takirani tana faɗa dan ma nace mata ina hostel ne ta ƙyaleni".


Tunda ta fara Magana ya heɗi fuska har ta kai karshe.



Yace,"bawani Mama ta kiraki kina dai son kitafi dan yanzu naga alamun kin daina sona".



Kamar tayi kuka tace, "kadaina faɗin haka wallahi inasonka sosai,amma tunda bakaso naji na fasa zan san me nace mata.



Aikuwa tana faɗin haka wani murmushi ya bayyana afuskar sa,lokaci ɗaya ya fara kiss ɗinta.


Abun ne yaga zaifi ƙarfinshi kuma anajiran sa a office dan haka yasake ta ya ɗau jikar sa ya fice batari da ya saki waiwayo wa ya dube taba......






_*Idan kunji daɗi mucigaba idan ko bakujiba na aje na huta*😁_ 






*#Vote*

*Comment*

*Shere*

Post a Comment

ADS HERE
ADS HERE