*🥙BASAKKWACE'Z KITCHEN🥙*
07092021
*FATAN DAN KALIN TURAWA*
INGREDIENTS
Dankali
Attarugu
Albasa
Maggi
Cittah
Kifi (ice fish).
Alayyahu
Kori
Man gyada
*METHOD*
Da farko uwar gida zaki fere dankalinki, ki yanka daidai misali.
Sai ki wanke kifinki, ki cire dattin, ki yanka gunduwa-gunduwa, ki zuba albasa da maggi da cittah a kai, sa'annan ki dora a wuta.
Bayan haka sai ki jajjaga attarugu da albasa da cittah ki ajiye.
Sai ki duba kifinki, idan ya tafasa ki sauke ki barshi ya dan huce, in ya huce sai ki bare shi ki ajiye.
Anan sai ki dauko tukunya, ki zuba manki ki yanka albasa a ciki, ki barshi ya soyu kadan.
Kisa jajageggen attarugu da kika jajjaga, sai ki zuba ruwa daidai misali, ki rufe yayi mintina ya tafasa.
Idan yayi sai ki zuba dankalinki, ki sa maggi da gishiri kadan da kori da cittah, ki rufe ya nuna.
In yayi sai ki zuba kifinki da alayyahu da albasa, ki juya, ki taba ki ji, idan komai yayi sai ki rufe, ki barshi yayi minti biyar.
08167151176
_MRS BASAKKWACE_