*_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
*WACE TA DACE DANI?*
*story n written by*
*Ummy Ontop*
*Alhmdlhi!!! Fan nasake dawowa bayan tsawon lokaci ina fatan zaku bani hadin kai domin da zafinta na dawo , kubiyoni cikin wannan labari mai cike da sarkakiya danjin yacce zaka kaya*
Page 1-2
Lamis!lamis!!lamis!!! kallonshi budurwa da ake kira da limis batayi ba bare tasamu damar bashi amsa, ran yasir idan yayi dubu ya b'aci a fusace ya k'araso gurin da lamis ke zaune cikin zafin nama ya daga hannunshi yasauke a fuskar lamis, yakuma yunkurowa ze kuma kaimata wani Marin a karo na biyu akayi saurin damke hannunshi kull karka soma maimaita danyen aikin nan, haba! Kai dan saurayi yazaka mari mace har kana kokarin kara mata wani kuma a bainar jama'a wannan ba girman ka bane Sam baikamaceka ba gaka da siffar mutumin kirki , mata abun atausaya musu ne , akuma girmamasu , mata sunada daraja babba, yasir banda muzurai da huci ba abun da yake yi , warce hannunshi yayi daga rukon da saurayin yamishi ya nuna lamis da tsaya wacce tun ganin saurayin nan bata iya motsin kirki ba hankalinta yabar jikinta zuciyarta gaba daya bata tare da ita, yasir yace" wallahi lamis saikinyi mugun nadama matukar baki bani kudina ba na baki nan da zuwa la'asar karfe hudu daidai naga kudi na idan ba haka ba zakiyi gagarumin nadamar amsar kudin nan, nawa ne kudin? saurayin ya tambaya ,yana faman muzurai yace" dubu talatin ne, yasa hannu a aljihu yaciro dubu hamsin yace ga kudin ka, nan kidan ya chanja salo yasir ya dagaje baki cewa yake" hamsin fa ka bani yahaura talatin din, eh ka rike duka kasha ruwa nan gaba ka rike girmama mata aduk inda ka gansu please, daga haka yasa kai yayi gaba .
Lamis data lulu wani kagin da batasan sanda tajeba ta Ankara da ya tafi ta tashi da Sauri tabi bayanshi ta taddashi yana kokarin barin harabar makarantar tayi saurin tare gaban motarshi ba shiri yayi saurin taka burki , yayi k'asa da gilas din motarshi ta karaso yazaka tafi ,ya tsyaa kallon ta dan be fahimci metake nufi ba, yazaka tafi banyima godiya ba ta fada cikin yanayin marairaicewa , murmushi yayi da yakara bayyanar da asalin kyanshi , murmushin nan yakuma tasiri a zuciyar lamis , wani kallo take mai mai cike da ma'ana tace" na gode sosai da karemun mutunci na dakayi agurin yasir, da za'a samu mutanen kirki irinka za'amu cigaba a rayuwa, murmushin yasake yimata sannan yace" babu komai yen mata amma kema ki rikà kame mutuncin ki da kanki basai wani ya kare miki ba kuma ki rika hakuri da yacce kika samu kanki karkice dole saikin nema wajen da za'a wulakantako shi abun dunia ba komai bane idan kayi hakuri zaka samu wataran Allah yana sane da komai ki kame kanki yerUwa , inshaAllah nagode da tunatarwar ka , daga haka bai tsaya kunajin mezatace ba yaja motarshi yayi gaba , shikuma wannan haka yake ya tafi bangama magana ba koh sunanshi da number shi be bani ba.
******
K'aton gida ne na alfarma daga waje gate din Gidan seka daga kai sama zakaga karshen shi, daga wajen gidanma abun kallo ne hakan ze shedama ciki kuma aljanna ce ta dunia.
Horn yake dannawa ajere cen saiga megadi ya fallo a guje ya wangale tafkeken gate din gidan, a miliyan ya danna hancin motar cikin fakeken gidan , wata runface da akayita ta alfarma dan Adana motoci ciki yashige ya faka tangamemiyar motar tashi yaziro kafafuwanshi waje adaidai lokacin da wayar shi tahau ruri sunan Dr mahad na yawo saman screen dinshyi, dauka yayi tare da kara wayar a kunne kana yafito daga motar yayi cikin gidan wanda tafia ce medan nisa daga wajan da aka ware dan adana motoci, ya akayi Dr cewar Dameer
" wallahi mutumina baka da kirki ka shanyani kasan kuma kai nake jira"
Dameer yace" kazo ka sameni a gida semu wuce mana"
Mahad yaja dan k'aramin tsaki yace ok senaxo, daga haka Dameer ya katse wayar ya k'arasa shiga cikin makeken falon da ya hadu da kayan alatu, falon anyi barin kudi acikinshi ya hadu iya haduwa sai wanda ya gani.
Upstairs ya haye sanadin be tadda kowa a falon ba direct dakinshi yawuce , ashe bamuga komai ba se anshiga dakin Dameer xa'asan gidan yaci kudi iya son ranshi , dakin babu tarkace dayawa ciki da falo ne amma yayi kyau komai kwallian blue ne acikin falon yayin da cikin dakin maroon ne yasha kyau Bango guda hotonshi ne a manne yayi masifar kyau cikin hoton.
Kayan jikinshi yacire yashige toilet ya watso Sabon wanka ya fito yashirya cikin kaya coffee colour shadda ya gyara sumar kanshi yasha turare da agogo da takalmi yadau phone nashi yayi waje , part din amminshi yayi yayi mata sallama tabashi izinin shigowa yashiga da sallama , cikin girmamawa ya tsuguna ya gaishe da mahaifiyarshi ta amsa tanamai samai albarka da farincikin samun da maiadabi da girma ma mutane.
Tun yaushe ka dawo baka sanarmin ba shine sai yanxu , Sosa qeya yayi yana murmushi yace" sori ammi nazaci ko bacci kikeyi kuma mahad na jirana xamu fita shiyasa na wuce naje na shirya , tou yaron kirki yanzu ka wuce kaci abinci karka sake Ka fita bakaci komai ba kaji ko, yadan gyada kai yana murmushi cen k'asan zuciaya shi yana cewa" naga ranar dazan girma abincin ma kullum sai an sakani naci Allah ya barmin ammina" sallama yamata sannan ya wuce dining room dan cin abinci already suna zaman jiranshi dama , xamanshi keda wuya saiga sallaman Dr Mahad , k'arasowa ciki Dr yayi yaja kujera dayacikin kujerun dinin din ya xauna bayan sun gama gaisawa Dr yace ina ammi ne tana ciki Dameer ya bashi amsa a takaice
Tou kayi ka gama ni nayi ciki wajen ammi zanje mugaisa.
Ku cigaba da bina cikin labarin nan mai ratsa xucia ina alfahari daku ma fans
Maimunatooh
*_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
*WACE TA DACE DANI?*
*story n written by*
*Ummy Ontop*
Page 3-4
Lamis kwance tana juyi ita kadai kan madaidaicin gadon ta gaba daya ta tsumduma kogin tunanin Dameer daya taimaka mata a makaranta , tunani take be Santa ba betaba ganinta ba amma ya taimaka mata gaskia mutumin kirki ne, a iya rayuwarta bataga namiji daya dace da ita ba sai Dameer , shine irin mijin da take mafarkin ta aura shine wanda take zana siffarshi cikin mafarkin ta ashe dagaske akwaishi ckin duniyar acewa wani sashi na zuciyar ta , dole tashiga cikin rayuwar shi dole ta nemo a inda yake , zuciyar ta baxata barta ta nutsu ba idan bata nemo mata mamallakin ta ba, kamar wacce aka mintsina tayi zunbur ta mike zaune batare da tasani ba tafurta a fili nayi sake dana bari yatafi ban San indah yake ba ko sunanshi ban sani ba dole na nemoshi nasani xaki iya lamis bantaba son Abu na rasa ba kuma bazan fara rasawa ba akan Kyakkyawan saurayin nan ba.
******
Bayan Dameer yagama cin abincin yatashi yayi wajen ammin tare yagansu sai hiransu suke ita da Dr mahad anashan daria, yacce Dr mahad ya baje yake zuba shine yabawa dameer mamaki kamar ya manta da fitan dazasuyi du ya azalzaleshi amma yanxu yazo nan ya baje yanata zuba, gyaran murya Dameer yayi sannan yace" wai Hiran mei kukeyi ne haka ammi tun dagacen nake jiyo dariyar Ku , ammi tace sirri ne biya kasha labari Mahad yace ahto kai baka xauna cen ba kai kadai anyi bakai, harara Dameer ya sakarwa Mahad yace tou seka tashi mutafi ka azalzaleni kuma kaxo nan kayi zamanka ammi mu zamu fita, tou saikun dawo Ku kula da kanku Allah ya taaremin Ku suka amsa da ameen sannan sukasa kai suka fice a gidan,
Kayansu dasuka iso daga itali yaje dubawa kaya sunyi sun gama komai sai bayan magariba sukabar wajan , a hanyarsu ta dawowa Dameer yake fadawa Dr Mahad labarin Lamis, Dameer yace " yarinyar tayi sedai abunda zai baka takaici da ita batada class , wannan idan kanwata ce saina zaneta muka koma gida, itama abunda yasa na taimaka mata kasan banason ganin ana wulakanta mace du lalacin ta gayen nan ya batamun rai da banxo wajen ba cin mutuncin daze mata saiyafi haka, Mahad yace ai kadan ka gane matan zamanin nan fa sun wuce tunanin ka danma ba mu'amala kake da matan ba sosai shiyasa amma sunzama abunda suka zama , tou Allah ya shiryamu baki daya Dameer ga fada yana sauke ajiyar zuciya har gida Dr mahad yakai Dameer sedai yaki shiga ciki kasancewa yana Sauri ze wuce asibiti kuma dare yayi, saukeni bakin gate ma tunda kaga jiranka ake a asibiti basai ka kaini ciki ba Dameer ya fada yana jawo wayarshidake ajiye gefe , tou Aboki Allah bamu alkhairi sai munyi waya anan sukai sallama Dr ya wuce Dameer yakarasa shigewa gida.
Yana shiga ya Tatar da ammi a falo tana kallo lami na zaune tana matsa mata k'afa har andawo ina Dr mahad din , ya wuce hospital Dameer ya fada a takaice, Ga abincin ka a dining yana jiranka , a koshe nake ammi kuma na gaji ne xanje masallaci idan na dawo zandan kwanta ne zandai sha tea ne kawai shikuma sai bayan na dawo, tou shikenan adawo lafiya .
*****
12:00am dare ya soma nisa Dameer ya fito daga toile dauke da towel daure a qugunsa da daya yana goge ruwan dake sumar kanshi, seda yagama tsane ruwan yajawo farar jalla biyarshi ya zira yasa turarenshi mai sanyin kamshi ya haye kan sallayar shi domin gabtar da salla daya saba gabatarwa nafila kafin yakwanta bacci kullum ne saiyayi wanna salla tazamemai kamar wani sashi na rayuwarshi koda bacci yadaukeshi beyi ba saiya tashi yayi, Dameer ma'abocin ibada ne baya wasa da ibada ko kadan, salla yayi raka'a biyu yazauna yayi addua sosai bayan ya kammala ya nade dadduma ya nufi makeken gadonshi wanda yake bango guda ne ya haye yayi addua bacci , sedai bacci yaqi samuwa fuskar Lamis ta giftamai ta cikin idanunshi kawar da tunanin yayi Amma Sam fuskarta yaki dainamai gizo , zancen ta ke fadomai *Yazaka tafi banyima godiya ba* yarinyar tanada zakin murya muryarta ya burgeni da yanayin yacce take magana yafada yana smiling ahaka bacci yayi awun gaba dashi.
******
Wanene Dameer?
Muhammad Yusuf Muhammad shine asalin sunanshi ana kiranshi da Dameer Yusuf dashi kowa yasanshi d'ane ga Ambassador Yusuf Muhammad Raji, babanshi babban dan kasuwa ne kuma dan siyaya mutumin kirki ne maison taimakon al'umma da gajiyayyu mai gaskia da amana ne mahaifinshi mutum ne na mutane, alokacin dayayi tafiya U.S hanyar dawowa jirginsu yayi hatsari, a lokacin da labarin mutuwarshi ta baza koh ina mutane sunyi kukan rashinshi sosai har suka dangana , sai danshi yazamar wa jamaA jigo kamar mahaifinshi.
Mahaifiyarshi shi matar kirki ce kamar mahaifinshi sedai ita tanada zafi bata daukar raini koh wulakanci amma mutuninyar kirki ce
Suna zaune a kano.
Dameer mutumin kirki ne kamar mahaifinshi, yanada hakuri da biyayya ga iyaye da duk wanda ya fushi yana bawa kowa girman shi baya raina mutane koh ya suke , yanada gudun zuciya tausayi saukin kai sedai baya daukar raini ba'a shiryawa dashi anan bashida surutu sosai.
Fari ne dogo mei dan jiki yana da sumar kai wacce ta karamai kyau da gemunshi luf gwanin burgewa,
yayi karatunshi mai zurfi har zuwa matakin MSC a business administration, yazama babban dan kasuwa Dan baya aikin gwamnati dorawa yayi daga inda babanshi ya tsaya, sabida shi kadaine mahaifinshi ya haifa a duniya , Hajia zainab ita kadai ce matarshi
Tunda aka haifi dameer Allah bekuma basu haihuwa ba sedai hajiya zainab tayi bari da dama .
******
Wacece Lamis
Y'ace ga Alhaji Nasir Aminu, da hajiya Binta garba, mahaifinta yanada rufin asiri daidi gwargwa do ma'aikacin gwamnati ne a gidan nepa tun tana k'arama sukayi hatsarin mota ita kadai ce ta tsira mahaifin ta da kanin mahaifinta Ya'au Aminu da mahaifiyarta babu wanda yayi rai duka suka mutu , a hannun k'anwar mahaifinta ta taso Yasira, alokacin da ana tunanin wane zai dauki lamis ya rike ta dage ita zata rike lamis harta aurar da ita bakomai yasa tayi wannan yunkuri ba saidan kadarorin lamis da mahaifanta suka mutu suka barmata zaidawo hannunta, haka kowa ya hakura ya sallama mata aka barmata lamis a wajen ta tun tana shekara daya a dunia ta raine ta har ta girma
Baba yasira ita da mijinta tanko mai turare yana sayar da turare dan duri a kifar gidanshi suka haye kan dukiyar marainiya suke watayawa San ransu , ita kuwa lamis basu damu da ita ba baba yasira tanada yah guda biyu duka mata maryam da habiba su kana kallonsu kasan sunajin dadi ita kuma lamis sai yacce hali yayi , babu wata cikakkiyar kulawa datake samu bare har ayi maganar tarbiya.
Lamis asalin sunanta Aisha ake kiranta da lamis ,
tunda ta taso babu cikakkiyar kulawa babu ishasshiyar tarbiya a tare da ita asalima dama itadin mai rawar kai ce cike take da yarinta a tare da ita, sedai du abun nan sun kula da karatun ta sabida gudun maganar dangi, ahakanma wataran sai ankai ruwa rana kafin a kukuta a biya mata kudin makaranta.
Shiyasa lamis ta taso ba kintsi ba kamin kai itace cin bashi itace kula kawayen banza sedai duda haka batayi watsi da martabar ta ba.
Wannan kenan
******
Maimunatooh
*_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
*WACE TA DACE DANI?*
*story n written by*
*Ummy Ontop*
5-6
* INDIA*
A nutse take takunta da wasu takaddu a hannunta ga k'aramar jakar ta a rataye, Dina! Dina!! batare data juya ba ta tsaya dan tasan mai kiranta, misha ta k'araso da sassarfa , ke haka akeyi daga cewa kijirani saikiyi tafiyar ki, cigaba sukayi da tafiya suna hira , dina ta yamutsa fuksa sannan tace ina zan tsaya jiranki da wannan shegen nawan naki , indai Abu na saurari ne karma a nemeki wallahi yacce kikasan baki da laka haka kike, kuma kinsan Sauri nake supervisor na yana ajirana yace fita zeyi daga skul din zuwa 12:pm kuma kinsan dakyar nasame lokacinshi yau koh ,kinga ta ina zan tsaya jiranki, hmmm ai dina naki da sauki nifa ina ganin mutuncin spvsor ki wallahi akan nawa bashida mutunci yaki barina nayi gaba kullum cikin gyara nake har ynxu fa a chapter 2 nake banje ko ina ba ga lokaci na tafiya. Allah ya doramu a Kansu dina ta fada misha ta amsa da amin, suna zuwa bakin office din malamin nasu Dina tayiwa misha sallama tashiga ita kuma misha ta wuce wajen nata malamin.
Nocking Dina tayi aka bata izinin shiga, cikin girmamawa ta gaishe ya amsa tare da bata izin zama , bayan ta zauna ta mikamai aikin nata ya karba yana dubawa , yayi mata iya gyran da zemata tare da tambayar dayayi niya du ta bashi amsa sannan ta karbi gyaranta ta bar office din
A bangaran misha ma hakane sedai yau tayi nasarar wuce wa batare da supervisor din ya wahalar da ita ba , cike da farinciki tabaro office din tare da karfin gwiwa. Cen kasan zuciyar ta tana cewa" da ace haka kake kullum ae danayi nisa a wannan project din amma ka tsaya kana iyayin jaraba dason nuna kai kasan mekakeyi mtwws.
Kamar wanda suka hada baki tare suka fito inda suka rabu nan suka hade , dariya misha tayi tace kin fito kenan eh wallahi cewar dina mtsww kiji dan iskanci kinga uban gyaran dayayim kuwa , misha ta tillike da dariya tace" inaga yau chanje akayi naki yadawo nawa , nawa kuma yadawo naki ,sakeke Dina tayi tana kalon misha tare dacewa me kike nufi , yau Allah ya dorani kan nawa supervisor din yanxu nagama mitar wulakancinsh kinga kamar wanda aka fadamai yau bai tsaya wannan shegen kakalan nashi ba koh gyara beyimun ba , uhm tou Allah ya doramu a Kansu muje cafeteria musamu wani Abu muci yunwa nakeji Dina ta fada tana yatsuna fuska.
Malt Dina tasa aka kawo mata da snacks haka itama misha da ruwa mei sanyi suka zauna sukaci suka koshi , bayan sun gama suna zaune basu bar wajen ba Dina tadauko wayar ta tadan kunne data rabon data hau social media da sunan chat harta manta kawai taji tana sha'awar tashiga shafinta na Facebook ,
Tana shiga tana scrolling harta wuce ta dawo baya ganin wani hadadden gaye datayi ya dauki hankalinta cikin lokaci kadan duda fuskarshi ba abuse take ba duka iyaka idanunshi kadai kake iya gani amma ahakama ya burgeta , smiling tayi kawai ta danna mai frnd rqst ,
Muryar misha ce ta dakartar da ita daga abunda take , kitashi muje musan abunyi ki ajiye wayar nan sonake naje na Dora daga inda na tsaya a project dina na k'agu na gama Nasan inda dare yamun wallahi . Dina tayi smiling tace " muje".
********
Wacece Dina?
Fatima Ibrahim Muhammad shine asalin sunant, da Dina kowa ke kiranta du wanda yasanta da sunan ya santa, Yace ga Ibrahim Muhammad da Rahama Abdul, mahaifinta dan kasuwa ne babba kowa yasan shi sabida yayi suna a kasuwanci acikin k'asar Nigeria da ketare, Fatima twns ce sedai tun a wajen haihuwansu aka rasa dayan dan uwan nata itun wanna lokacin mahaifiyarta bata sake haihuwa ba sabida matsalar data samu na fibroid wanda yajanyo da aka mata tiyata likita ya shaida mata sedai a hada da mahaifar a cire idan ma ba'a cire ba zaisake dawo wa ne haka ba yanda sukaso aka cire wannan dalilin yasa mahaifiyar Dina bata sake haihuwa ba , Dina ce kadai yah daya tilo a wajen su, sun dauki soyayyar duniya sun Dora mata , mahaifinta zai kashe ko nawa ne dan farincikin ta hka zalika mahaifiyar ta basason damuwar ta ,Tunda tagama primary skul tabar k'asar a India tayi karatun ta secondary da jami'a sabida tsananin son indiya datakeyi tana yarinya yasa iyayenta suka kaita cen karatu a gidan abokinshi take tare da yaran gidan suke zuwa makaranta kafin daga bisani sukoma gida Nigeria alokacin kuma Dina tazama budurwa tagama secondary school tashiga university saita kama gida itada abokiyar karatun ta Misha.
Dina tanada hanki , nutsuwa tsantsar addini a zuciyar ta lokacin tana k'arama gidan abokin baban ta sunsamu horo mai tsanani bangaran addini da ilimin islamiyaa wanda abun yashiga zuciyarta sosai,
Yarinya ce ma nutsuwa da kamun kai wanda a makarantar tasuma kowa yashedeta da haka, tana final year nata a makaranta na Bsc medicine
Dina batada saurayi ko daya ita karatun ta tasa agaba har ilokacin nan bata samu wanda yashiga koh yakwanta mata a zuciya ba .
Wannan kenan
*******
Kwanaki sunataja anshafe sati biyu, indah soyayyar Damir nakuma nisa a zuciyar lamis ta dukufa nemanshi a kullum saitaje wajen dasuka hadu tayi xaman jira ko Allah zaisa yadawo ko zasu hadu amma babu alamunshi babu labarin shi, haka zalika shima Bangaran Damir yakasa gane kanshi akan lamis yarasa mai zuciyarshi take nufi akan lamis da tsananin tunanin ta ya addabi zuciyarshi saita samu mahad yake shedamai halin da ake ciki , mahad yayi dariya yace" mutumina ka harbu kenanda soyayyar yarinyar nan kuma kana cin xalin zuciyar ka tunda ka hanata zuwa ta bayyana abunda ke damunta, hmm Dr kenan banda abunka tayaya zan bayyana bayan na tafka kuskure a farko ban tsaya na saurareta yacce ya kamata ba ban tsaya na tambaye ta koda sunan ta ba, ta ina zan hadu da ita bare harna zayyana mata sirrin zuciya ta yanzu, ai abune Mai sauki wannan saidai idan bakaso ba , Damir yayi shiru ya tsurawa mahad ido cike da alamun tambaya a fuskarshi, nunfashi ya sauke kafin yace" mai kake nufi tayaya kenan hakan zai faru Dr?" Yayi tambayar yana tsurawa Dr ido da zakuwar jin abunda Dr mahad zecemai.
Dr mahad ya nisa yace" ba a Makaranta kuka hadu da ita ba? Kwarai kuwa Cewar Damir, touh ai nan zaka koma inda kuka hadu ko za'a dace saiku sake haduwa a karo na biyu, Gaskiya abokina ka kawo shawara kuma fa kasan Allah tunanin nan Sam baizomin ba , wani hanzari ba gudu ba idan ba a makarantar take ba fah , bazeyiwu ace ba amakaran tar take ba daga yanayin yacce kabani labarin yana nuna a skul din take kaidai ka jarra ba, Damir yace" badan yanzu magrib yakusa ba da yanzu ba abunda zai hanani zuwa, Dr mahad yasa dariya sannan yadora da " lallai abokina ka harbu dayawa idan kayi hakuri yauda gobe du daya ne idan bani da aiki dayawa gibon saina rakaka , bakomai nagode da shawara ka mutumina sukasa dariya a tare sannan sukai sallama kowa yayi hanyar gida.
Maimunatooh
*_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
*WACE TA DACE DANI?*
*story n written by*
*Ummy Ontop*
7-8
Ranar Monday tunda sassafe Damir ya kira Dr Mahad wayar tagama ruri be dauka ba , saukowa yayi daga tangameman gadonshi ya fada toilet ya sheko wanka ya fito a gaggauce yayi shirin sa cikin Sauri duda gaggawa yake amma yayi kyau milk colour shadda daya sa tahau jikinsa sosai, gashin kanshi ya kwanta luff gwanin burgewa sai kamshi yake turarawa kowani sashi na jikinshi na fidda sanyanyan kamshi mai dadi zuqa.
a gogon shi ya Zara ya daura a hannu yadau car key da wayarshi yasanya hula ya karewa kanshi kallo gaban dressing mirror shi kanshi yasan yes yayi kyau 💯, smiling yayi yana tunano gashi ga lamis yau sun hadu , sedai koh me zefara cemata, ganin dai yanata b'ata lokaci yasashi ya fita a dakin koda ya sakko k'asa bega kowa ba alamu sun nuna mutan gidan basu fito ba gani yayi kamar ze bata lokaci idan yace sai ya jira an hada breakfast yaci kuma yasan koda yaje site din Ammi ba lallai yanzu ta tashi ba yasan ta koma bacci idan tayi salla asuba tayi azkar nata tagama tanadan komawa bacci 10am take tashi ta kintsa a hadu a breakfast. Kuma yanzu 8:30 agogon dake makale a hannun shi ya nunamai.
Zefita yayi kicibis da inna balaraba mai aikinsu ta gaidashi a gaggauce ya amsa yayi waje zuciyarshi cike da farinciki, inna balaraba ta juya tana kallanshi ganin yacce yau yake zambada Sauri gaisuwarma ta gagara yacce aka saba cen qasan zuciyar ta tace yaukuma ko farincikin me akeyi da gaggawan nan ganindai bamai bata amsa yasa tayi ciki dan fara aikinta.
Wajen da aka tanada dan ajiye motoci yaje yayi parking nashi motar sannan yafito cike da zumudin yaga lamis inda suka hadu nan ya nufa sedai babu kowa a wajen beyi k'asa a gwiwa ba yasamu waje yazauna a wajen yana jiran tsammani.
Tun makaranta bata cika ba har dalibai suka cikata anata kai kawo shiru har aka shafe sama da awa biyu babu giftawar lamis amma hakan baisa Damir ya karaya ba yasawa zuciyarshi tabbas zega lamis yau
Wayarshi ce tahau ruri ya duba sunan Dr mahad yake yawo kan screen din dan murmusawa yayi sannan yadauki kiran , Dr mahad yace barka Aboki ka kirani nashiga wanka lokacin kuma dana fito banbi takan wayar ba nayi asibiti sai yanxu nasamu kaina, bakomai Aboki ni yanzuma haka ina makarantar su lamis, mutumi na baka da dama kace harka shiga, touh meza'a jira Dr ,Dr Mahad yasa dariya kafin yace" ince dai andace, inafa tun shigowa ta banga Mai kama da ita ba bare nasa ran zan ganta, zuciya ta tafaramin zafi Dr Nasoma karaya burina naga yarinyar nan yau nasamu na zayyana mata halin da zuciya ta ke ciki ko zansamu sassauci daga radadin da takemin, ka kwantar da hankalin ka Aboki inshaAllah xa'a dace kasake jira kadan nadan lokaci nima ina hanya zanzo na taddaka, tou shikenan saika karaso daga haka sukai sallama Dr mahad ya kashe wayar yana jijjiga kai da tunano Dameer lallai Wannan karon so beyiwa Dameer da wasa ba dama ka ki yayi Wanda so baitaba ritsawa ba ranar daya ritsaka baxakaji da dadi ba da wannan zancen zucin yakarasa abunda zeyi yafita dan zuwa wajen Dameer.
Karfe daya saura minti goma agogen dake hannun Dameer ya nuna tashi yayi jiki sanyaye ya nufi wajen alwala yayi yashiga masallacin cikin makarantar dan gabatar da salla azhar.
Bayan sun idar fitowa yayi Yakumawa wajan daya baro ya zauna , sam ya rasa mekemai dadi kuma ga dukkan alamun bashi da sa'a ne amma tabbas idan ya rasa samun yarinyar nan zeshiga wani hali yana wannan tunanin ne kiran Dr Mahad yashigo wayarshi jiki du yayi la'asar haka yadauka ya kara wayar a kunne , kwatancen indah yake yamai saiga Dr ya karaso zama yayi kusa da Dameer wanda kana kallonshi kasan cikin wani yanayi yake , kafadanshi Dr mahad yayi sannan yace" Haba Jarumin maza karka bari so yasauyama yanayi mana har yanxu ba'a dace ba kenan, Ajiyar zuciya Dameer yasauke kafin yayi karfin halin furta, baxaka gaane halin da zuciya ta take ciki ba yanxu Dr kuma ni nasoma karaya ga dukkan alamun yarinyar nan ba karatu take cikin makarantar nan ba kuma da ace nasan koda sunanta ne sainaje nayita cigiya har adace da wanda yasan ta a makarantar.
Karka cire rai Dameer bafa aje koh ina ba kake kokarin karaya shiga SO bayason rago a tafiyarshi idan ka karaya yazakayi da zuciyar ka kenan, saikace ba namiji ba karka bani kunya dan Allah inshaAllah ina tare dakai zanbaka du gudumuwar daya dace.
******
Tun wancen lokaci Dameer yana faman neman Lamis kullum saiya shiga makarantar ko za'a dace amma shiru har aka shafe sati guda inda alokacin yasoma fitar da rai da ganin Lamis ya barwa Allah komai yasan idan yana da rabon sake haduwa da ita Allah zenufa, sedai tabbas zuciyarshi nacikin sarkakiya tana azabtuwa da tunanin Lamis kullum cikin nadamar rashin tsayawa sauraranta yake inama akoma baya daya gyara kuskureb dayayi.
******
Sautin nishi ke tashi daga cikin karamun dakin koda na leqa Lamis ce ke kwance inda fuskarta tayi kacha kaca da hawaye tana fitar da kuka Mara Sauri idanunta sunyi jawur wanda dakyar take iya dagasu gefen ta kuwa wasu kwalabe ne birjik a zube wasu babu komai anshanye abun da ke cikinsu,sallama ake bakin kofar amma takasa koda motsawa bare tasamu damar magana, kutso kai akayi aka shigo Kawarta Naifa ce , saurin yasar da jakar ta tayi ta k'araso kusa da lamis , lamis afiya kuwa kike meya sameki tamata tambayar a Jere , lamis wacce dakyar take iya bude idanunta bata samu nasarar bata amsaba sabida yacce gurin ke juya mata tana ganin komai goma goma,dogon ajiyar zuciya lamis tasauke wanda dagashi bata sake motsawa ba , Innalillahi waEnna Elaihi rajiUn Naifa ta furta da karfi Lamis ! Lamis!! take kiranta tana jijjigata cike da tsoro karara tatattare da ita.
*****
