ADS HERE

GAJEN HAƘURI PAGE 1


 [8/29, 8:41 PM] Mai Zafafa: *GAJEN HAK'URI*

 



BY

    *SADIYA ABDUL(Mai zafafa)*



*☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️*



SADAUKARWA GA K'UNGIYATA 🥰




*MATAN AURE,ZAWARAWA,Y'AN MATA,YA NA DA KYAU KU KARANTA,DOMIN ZAI TA'BO DUK WATA MATSALA TA GIDAN AURE WADDA TA KE 'BULLOWA DAGA WURINKU*

  


Page 1



    "Wai don Allah Musa ka fi kowa talauci a duniya!?"


Wata matashiya ce, da ba za ta wuce shekara goma sha takwas ba ta ke maganar cikin masifa,da hayaniya,har wani kashe ido d'aya ta ke saboda tsabar bala'i.


 Wanda ta kira da Musa ya tashi daga kwancen da ya ke,cikin takaici ya fara magana

"Haba Zubaida,ni fa mijinki ne bai kamata a ce duk maganar da ta fito daga bakin ki za ki dinga fad'a min ba,babu tunani"


"Au!ni ce ma mara tunanin ba kai ba ko?to wallahi na gaji,haba jiya jiyan nan maman Sadik ta ke fad'a min mijinta dubu talatin ya bata kud'in kayan sallah,amma ni ka yi shiru har yanzu ko zancen ban ji ka yi min ba?"


Zubaida ta yi maganar cike da rashin kunya


Musa ya ce"ai kin ji!a kullum ina fad'a miki ita rayuwa na k'asan ka za ka kalla ba na saman ka ba,sai ka zauna lafiya kuma kullum ka kasance cikin godiya ga mahaliccin ka,amma muddin ki ka ce za ki kalli na saman ki to kuwa tabbas za ki kasance cikin k'unci,da rashin godewa ubangiji"


  Zubaida ta mik'e tsaye ta rik'e k'ugu kamar mai shirin dambe ta fara magana"bakin ka ya sari d'anyen kashi,in sha Allah ba zan yi rayuwar k'unci ba,sai dai kai ka yi ,da kuma matar da za ka aura a nan gaba!"


"Me ki ke nufi?" Cewar Musa ya na tashi tsaye had'i da kad'e rigarsa.


 Cikin tsiwa ta ce"au ba ka fahimta ba?za ka gane nan ba da jimawa ba,don wallahi da kyau na da komai ban ga dalilin da zai sa na zauna wahala ta nakasa ni ba".


 Ta na gama maganar ta shige d'aki.


Musa ya girgiza kai ya fita daga gidan,ya na ta tunanin irin halin Zubaida na rashin yarda da k'addara.


Bai dawo gidan ba sai da ya yi sallar isha'i,kwance ya same ta,ta na kallo a y'ar k'aramar wayarta mai madannai,kallo d'aya ta yi masa bayan ta amsa masa sallama,ta ci gaba da kallon ta.


  "Zubaida yau kuma abincin ma sai na rok'a?"

Cewar Musa ya na cire rigarsa.


 Guntun tsaki ta ja,ta tashi ta shiga d'an k'aramin kitchen d'in nasu ta d'akko masa sauran abinci a gefen kula.


"Ga shi nan,ina saukewa Umma(mahaifiyar sa) ta zo shi ne na zuba mata a kason ka"


Ta yi maganar ta na ajiye masa guntun abincin da bai fi d'an shekara uku ya ci ba.


  Shi dai bai ce komai ba,ya janyo kular ya fara ci,ganin ko nuna alamun damuwa bai yi ba ya sa ta fad'in


"To abinci ne a ke yin shi kai da kai,dole ka hak'ura ka ci saura tun da ita ma Umman ta sani y'ar taliyar dai ba za ta d'ara leda d'aya ba,amma duk da haka ta zauna ta ci,wataran ma ba za ka samu sauran ba,in dai y'an uwanka su na zuwa a lokac..."


"Ke Zubaida! ya isa haka dan Allah, ko kin ji na yi k'orafi ne?ke me yasa ba kya raina abin fad'e ne?"


Musa ya fad'a da alamun 'bacin rai.


Zubaida ta ce"to ai gaskiya ce na fad'a, yanzu in da da yawa ka ke ajiye kayan abinci don y'an uwanka sun zo sun cinye,ai ka ga zan tashi na kuma d'ora wani abun,to taliya ce leda d'aya kamar rai!"


 Bai kuma ce mata komai ba,har ya gama ya d'auki tabarma ya fito tsakar gida ya shimfid'a,saboda yanayin zafi da a ke ciki.



  Musa da Zubaida dai masoya ne,tun tana yarinya ya ke k'aunar ta,kasancewar a unguwa d'aya su ke,kuma Zubaida ta na son shi sosai.Duk da ita ma iyayen ta ba masu k'arfi bane amma sun fi iyayen Musan rufin asiri,ya yi karatu har ya kammala diflomarsa amma bai samu aiki ba.


Ganin ya na da hankali sai wani mak'obcin su ya siya masa adaidaita sahu,ya ke kai masa balans duk sati,da taimakon adaidaita sahun ya samu ya tara kud'in auren Zubaida,a ka yi auren su ke zaune lafiya cikin rufin asiri.



  Wata d'aya da auren Allah ya yi wa alhaji Ummaru rasuwa,wanda shi ne mai adaidaita sahun da Musa ya ke ja,don dole ya mayar wa da iyalansa mashin d'in.



Ganin zama haka ba zai yi wu ba yasa ya samu wani shagon nik'a ya fara zuwa,ya na aiki a can,tun daga nan abubuwa su ka canza don d'an abin da ya ke samu ba mai yawa bane.


Zubaida ta canza,ta fara aro wasu bak'in halayen da a da bai santa da su ba,da ya ke Allah ya ba shi hak'uri, kuma ya na k'aunar ta,ya sa ya ke hak'urin zama da ita duk da cin mutunci da rashin kunyar da ta ke yi masa.



  A 'bangaren Zubaida kuwa ladama sosai ta ke yi na auren Musa,sai yanzu ta ke ta tuno hud'ubar k'awarta Asiya,da kullum ta ke jaddada mata ita kyakkyawa ce,kar ta sake ta auri talakan da zai kashe ta da ranta,don a cewar ta auren talaka mutuwar tsaye ce


Ita ma sai yanzu ta ke kuma ganin kyaun ta,ta kuma tabbata lallai ta yi *gajen hak'uri* na saurin yin aure ba tare da ta jira mai kud'i ba.


A yanzu tunanin mafita kawai ta ke yi,na yanda za ta 'ban'bare Musan daga rayuwar ta.


 

  Yau da bak'in shayi(ruwan bunu)su ka karya, sai tsaki ta ke ja ita kad'ai,shi kuwa sai dai ya kalleta ya kau da kai


 Ya lula duniyar tunani ya ji muryar ta kamar daga sama ta ce"zan je gidan k'awata"


"Ba za ki je ba" Musan ya fad'a kai tsaye.


"Wallahi sai na je!" Ta yi maganar ta na fita daga d'akin


Musa ya bi bayan ta da kallo ya na tunanin yanda a ka yi ya yi sake har matarsa ta raina sa haka,kafin ta fito daga wanka ya bar gidan,don haka ta fara shirin fitar ta cikin nutsuwa.


  Su na zaune a k'ofar shagon nik'an su,ya ji abokan aikin sa su na fira


"Kai!wannan wace irin rayuwa ce?yanzu mata sun zama abin da su ka zama?" 


'Dayan ya ce"kai Hamza me matan su ka yi?"


Wanda a ka kira da Hamza ya ce"wai a ce mace idan ba ka da kud'i,kai da d'an iska duk d'aya ta ke kallon ku?har wani raini ne zai shiga tsakanin ku, ta dinga yi maka rashin kunya kamar ba mijinta ba?duka dai saboda talaucin da ba kai ne ka d'orawa kanka ba?"


"Hmm!wallahi ka ta'bo min inda ya ke min k'aik'ayi,ashe dai ba ni kad'ai matsalar ta ke shafa ba,wallahi idan ina da kud'i kar ka so ka ga yanda ta ke washe min baki,ta na nan-nan da ni,har fa suna ta ke canza min,irin na soyayya,amma idan ba ni da shi ko kallon arzik'i ba ta yi min".



  'Dif!Musa ya daina sauraron firar su,sakamon ganin Zubaida tsaye a gefen titi,ta ci kwalliya kamar budurwa ta na tsaida d'an sahu

[8/29, 8:41 PM] Mai Zafafa: *GAJEN HAK'URI*

 



BY

    *SADIYA ABDUL(Mai zafafa)*



*☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️*



SADAUKARWA GA K'UNGIYATA😘



PAGE   2



  

    Sosai Musa ya yi mamakin ganin Zubaidar,don a iya zaman su bai ta'ba hana ta fita ta k'i hanuwa ba sai yau, ya jinjina kai ya na kuma sarewa lamarin ta,don ya lura lallai da gaske ta ke,ya na kallo ta shiga adaidaita sahun su ka bar wurin.



  A wani gida mai kyau da girma a ka sauke ta,ta d'an jima ta na kallon gidan kafin ta k'wank'wasa jiki a sanyaye


Babu jimawa Hafsa ta zo ta bud'e mata,da farinciki sosai ta tare ta,ta na yi mata sannu da zuwa,Zubaida ta bi bayan ta su ka shiga ciki



  Bayan sun gaisa Hafsa ta cika mata gaban ta da kayan k'walam da mak'olashe,ta kalli Hafsa ta ganta fes da ita babu alamun wata damuwa,daga gani ta na jin dad'in rayuwar auren ta,sa'banin ita da kullum ta ke cikin k'unci da takaici


Tare su ka yi karatu da Hafsa tun daga k'aramar makaranta har babba,amma sai ta ke ganin yanzu kamar Hafsan ta girme mata sosai,ta wuce ajinta,duba da ganin yanda ta k'ara girma da kyau



Ta yi nisa a duniyar tunani ta ji muryar Hafsa"hajiya Zubaida,ki ci mana kafin na d'ora girkin rana,amma dai wuni za ki yi ko?"



  Zubaida ta sauke ajiyar zuciya ta ce"eh,wuni zan yi"


"Ke!wai ya na ga duk kin zama shiru-shiru?ko laulayi ki ke yi?hahaha Zubaida Aminu ta ji maza!"


Hafsa ta yi maganar ta na kwashewa da dariya.


Zubaida ta yi y'ar dariya ta ce"dallacen,ke ba na son iskanci,wane irin laulayi kuma a na zaune k'alau?"


Hafsa ta shek'e da dariya ta ce"ina fa a ke zaune k'alau?kullum ki na manne da miji ki ce min wane irin laulayi?za ma ki fad'i gaskiya"


 Zubaida ta ce"ni wallahi Hafsa ba na fatan na samu ciki"


Hafsa ta zaro ido ta na fad'in"subhanallah!abin da kullum na ke fatan samu?ke Zubaida ki na da hankali kuwa?ciki kuwa ga wanda ya yi auren fari ai abin nema ne".


 Zubaida ta ce"tabbas!ni ma ban ce ba na son haihuwa ba,amma ba na fatan had'a zuri'a da Musa"


"Ban fahimce ki ba?" 


Hafsa ta fad'a ta na gyara zama.


Zubaida ta kwashe duk irin rayuwar da gidan mijinta ta ke ciki ta fad'a wa Hafsa,sannan ta d'ora da fad'a mata k'udurin ta a yanzu.


 Nan take fara'ar fuskar Hafsa ta d'auke,ta 'bata rai kamar wadda za ta daki Zubaidan ta fara magana, cikin fushi


"Amma wallahi Zubaida kin ba ni mamaki, yanzu dama a kwai wadda za ta zauna ba ta morewa kyaun da Allah ya bata ba? ke wallahi da ni ce da irin kyaun ki,ko gwamna ya zo sai na ja masa aji!"


 Zubaida ta ji kanta ya fashe,ta cire mayafi ta ajiye a gefe kafin ta ce"to ya zan yi Hafsa?k'addara ta riga fata"


"Tabb!ai wallahi k'addara ba ta riga fata ba,amma idan kin so,idan kin k'i kuma sai ki ci gaba da zama har wahala ta kashe ki"



Hafsa ta fad'a ta na turo d'aurin d'ankwalin ta gaba,had'i da ta'be baki.


Zubaida ta ce"to ya zan yi Hafsa?shi fa ko me za ki yi masa, kamar ba ya jin haushi,na rasa irin zuciyarsa"


Hafsa ta gyara zama ta ce"ai fito masa za ki yi a mutum!ki zage ki yi ta surfa masa rashin mutunci,na safe da ban, na dare da ban"


 Zubaida ba ta ce komai ba ta fa tsiyayi lemo ta fara sha a hankali


Hafsa ta ce"saurara da kyau ki ji abin da zan fad'a miki!"


Zubaida ta ajiye kofin ta tattara duk nutsuwarta gurin Hafsa ta ce"ina jinki"


 "Kin ga wannan shawarar da na baki?to fa ba za ta ta'ba yin tasiri ga Musa ba sai da taimakon abu d'aya,don kin san talaka da shegen nacin tsiya,bare ya na tunanin idan ya sake ki,ta ina zai samu kud'in auren wata?ko ba haka bane?"


  Hafsa ta yi maganar ta na rik'e k'ugu daga zaunen da ta ke.


Zubaida ta ce"haka ne"


Hafsa ta ce"to mafita dai d'aya ce,wanda shi ne abu mai girman da zai raba ku da Musa,kin san dai ki ka samu ciki a halin yanzu kin shiga garari?"


Zubaida ta ce"na sani,ai shi yasa ba na son samu"


   Hafsa ta gyara zama ta ce"ai ko kin sani zan kuma tuna miki,idan ki ka sake ki ka samu ciki abu ne mai wahala Musa ya sakeki,idan kuwa a ka yi sa'a ya sake ki,to an kashe miciji ne ba a sare kansa ba"



   Zubaida ta ce"ban fahimta ba?"


 "Eh ai ba za ki gane ba, tunda na ga tunanin ki kad'an ne,to duk wadda ta auri talaka ai ta na da rangwamen tunani!"


   Zubaida dai ba ta ce komai ba ta ci gaba da sauraron ta.


   "Bari dai mu yi magana mai muhimmanci,ba kwana-kwana ba,yanzu da Musa ya sake ki da ciki,ya maza dole ki zauna har ki haihu,sannan ki yaye d'an da ki ka haifa,kafin ki fara tunanin wani auren!wannan shekara nawa zai d'auke ki?"


   Zubaida ta jinjina kai,ta na gamsuwa da zancen k'awarta


  Hafsa ta d'ora da fad'in"to ba a nan gizo ya ke sak'ar ba,kin ga da zarar an ce mace ta haihu?to wani namijin ya gama da babin ta,wallahi ina me tabbatar miki da wuya ki samu irin namijin da ki ke so idan har ki ka haihu kuma ki ka shayar da d'an,duk ya zuk'e miki nono!"


   Zubaida ta ce"hakane wallahi,amma ya zan yi?kenan yanzu planing (tsarin hauihuwa)zan yi ko?"


   Hafsa ta shek'e da dariya ta ce"dad'i na da ke tun mu na makaranta ba kya kwashewa"



   Zubaida ta yi y'ar dariya ta ce"ba na son wulak'anci"


  Hafsa ta ce"to ai ke d'in ce,wataran sai na rasa ina k'wak'walwar ki ta dosa,wane mahaukaci ne zai yi planing kafin ya yi haihuwar farko?ba planing za ki yi ba,hana shi kanki za ki yi,duk runtsi duk wuya kar ki sake ki kuma had'a shimfid'a da shi,ta hakane zai fahimci lallai kin gaji da shi,kuma shi ba dutse ba ne,idan takaici ya ishe sa dole ya gaji ya sawwak'e miki"



   Zubaida ta fara wani had'ad'd'en murmushi ta ce"tabbas!na ji dad'in zuwa na gidan ki,dama wallahi na tsani yanda ya ke yin yanda ya so da ni,shi ba wani abun arzik'i ya ke ta'buka min ba"



  Hafsa ta ce"ai talakan mutum babu wanda ya kai shi nacin masifa,su had'a maka zafi biyu,kai kenan kullum cikin k'unci"


  "Wallahi kamar kin sani kuwa,nacin masifa ne da shi"


  Zubaida ta fad'a ta na janyo plate d'in snacks d'in da Hafsa ta kawo mata,jin ta ta ke yi fess babu wata damuwa,don har ta fara hango ta na zubawa Musa rashin mutunci.



   Sai bayan la'asar ta bar gidan,bayan ta ci abinci mai rai da lafiya,Hafsa ta na kuma bata wasu nau'ika na rashin mutunci da tunzura namiji,ita kuma ta na ta godiya farinciki har zuciyarta.


  Ta na dab da fita mijin Hafsa ya dawo,cikin shigar k'ananan kaya,sai zuba k'amshi ya ke,su ka gaisa sai kallon sa ta ke ta k'asan ido,ta yi mamakin ganin ashe ma yaro ne,ga shi d'an gayu kuma ga shi da kud'i, su na zaune lafiya da matarsa,da fara'ar sa ya k'irgo dubu biyar ya bawa Hafsan ya ce ta bata,Zubaida ta yi ta godiya kamar za ta tsugunna,ita Hafsa abin ma kunya ta bata.



```ALLAH KA HA'DA MU DA K'AWAYE NA GARI```🤦🏻‍♀️



  Bayan ta bar gidan Hafsa kai tsaye gidan su ta nufa,su kai ta fira da mahaifiyar ta,ko kad'an ba ta fad'a mata da tsakanin ta da Musa ba,sai da ta yi sallar magriba ta baro gida


 Sai ta taho a k'afa,duk da cewa da y'ar tazara tsakanin gidan su da gidan mijin nata,dab da za ta shiga gida ta hango mak'obciyar ta Samira ta na k'wankwasa gidan maman Sadik,sai ta k'arasa da fara'a su ka gaisa kafin ta ce"Samira me za ki yi wa maman Sadik da daren nan?"


Samira ta ce"ke dai ba ki na k'unshe a gida ba?ai mu kullum nan na ke zuwa ina kallo don na rage dare,yau gidan Badamasi za a yi"


  Kafin Zubaida ta yi magana maman Sadik ta bud'e, ta na murmushi ta ce"ke ba za ki shigo ba?"


  Zubaida ta shige ta na ta washe baki.


 Sai bayan sun shiga ta ke cewa maman Sadik"wai mai gidan ba ya nan ne?"


Maman Sadik ta na ta'be baki ta ce"yana nan mana,to ya zai yi da ni?ai dole ya hak'ura sai kun gama kallon ku,ni gwara ma na yi ta yin bak'in,na huta da shegiyar jarabar sa!"


  Samira da ta kasance amarya ta ce"wallahi kuwa,wannan azabar a yi ta takura maka"


  Su ka shige falon su ka hau kallo,sai da a ka d'auke wuta sannan Zubaida ta ciro wayar ta da ta jona a caji,zaro ido ta yi ganin har k'arfe goma da kwata


  "Kai!ashe haka dare ya yi?na tafi sai da safe"


 Ta yi maganar ta na tashi,jikinta duk ya yi sanyi,don ba ta ta'ba kai wa dare haka ba,ga shi ba ma da izinin shi ta fito ba


   Tare su ka fito da Samira,ta shige gidanta,ita ma ta doshi na ta gidan,da y'ar fargaba,zaune ta tadda Musa a k'ofar gidan ya wani had'e rai,da alama ta kai shi bango yau,wani farin yadi ne a jikinsa ya wani k'wama hula kamar malami,dogon tsaki ta ja tunowa da yanda ta ga mijin Hafsa d'an gayu,sai zuba k'amshi ya ke



  Ba ta ko kula shi ba,ta bud'e gidan ta shiga,shi kuma ya tashi ya na kad'e jikin sa,saboda zaman da ya yi a k'asa,ya bi bayan ta.

[8/29, 8:41 PM] Mai Zafafa: *GAJEN HAK'URI*

 



BY

    *SADIYA ABDUL(Mai zafafa)*



*☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️*



SADAUKARWA GA K'UNGIYATA😘



PAGE   3



   

     Ya na tsaye ta bud'e d'akin ta shiga,ba ta dad'e ba ta fito ta d'aura alwala,ta gabatar da sallar isha'i,sai da ta idar sannan Musa ya shigo ya kalle ta da kyau ya ce


  "Zubaida daga ina ki ke?"


 "Mak'obta" Ta ba shi amsa a tak'aice.


 Ya ce"ba na son rainin hankali,ko ba ki san na ga lokacin da ki ka tari d'an sahu ki ka shiga ba?"


Zubaida ta ta'be baki ta ce"eh,wannan gidan k'awata na je daga nan na wuce gidan mu,kuma idan kai ba kurma bane ina tunanin ka ji lokacin da na tambaye ka ko?"


Musa ya ransa idan ya yi dubu ya 'baci,cikin harzuk'a ya ce"da ki ka tambaye ni na ba ki izinin fita?"


Zubaida cikin ko in kula da fushin nasa ta fara k'ok'arin hayewa kan gado.


  Musa ya finciko ta,ya dawo da ita har sai da ta kusa fad'uwa


   "Ni sa'an wasan ki ne?ina yi miki magana ki na hayewa gado?"


  Ya yi maganar da mugun 'bacin rai


Zubaida cikin d'aga murya ta ce"na haye d'in!saboda ba ni da lokacin sauraron shirmen ka!kalle ka don Allah ko kunya ba..."


Sai maganar da za ta yi ta mak'ale,ganin yanda ya d'aga hannu ya na shirin marin ta,sai kuma ya fasa ya cije le'be,bakin sa ya shiga rawa,ya na nuna ta da yatsa irin ransa ya yi mugun 'bacin nan har ma ya rasa me zai ce,kuma ba ya so ya fara dukan ta,sai kawai ya yarfar da hannun sa zai fice



  Zubaida da tsoro ya gama cika ta,don ganin yanda Musan ya fusata ainun,ta danne tsoron ta d'aga murya ta ce"da ka dake ni yau wallahi da ka daki auren ka!"



  Musa ya yi mamaki sosai,a nan tsakar gidan ya kwana saboda gudun zuciya,kar Zubaidan ta kuma tunzura shi a yi babu dad'i.


  Washegari haka ya tashi babu walwala,gefe guda kuma ya na ta tunanin halin da Zubaida ke k'ok'arin shigowa da shi,cikin zaman su


  Ko gaisuwar da ta saba yi masa da safe yau ba ta yi ba,don haka ya kuma tabbatarwa abin na gaske ne


  Ko fitowa ba ta yi ba daga d'aki,bare ya sa ran za ta d'ora tukunyar shayi


  Sai da ta ji ta fara jin yunwa,sannan ta d'auki jakarta ta ciro dubu d'aya a kud'in jiya da mijin Hafsa ya bata,ta zira hijjabi ta fito


  Ganin sa ta yi ya na zuba ruwa cikin bokiti,da alama wanka zai shiga,kallo d'aya ta yi masa ta saka takalmi ta fice daga gidan


  Tsananin mamaki ya sa Musa ya kasa magana,zama ya yi a wurin ya na jiran dawowar ta


  Ba ta jima ba ta dawo hannun ta rik'e da leda,ta wani had'e rai wai kar ma ya kawo mata raini


Kai tsaye kitchen ta shiga ta d'akko kwano ta zo ta gaban shi ta shige d'aki.


   Sai da ya yi wankan ya shiga d'akin,zaune ya tadda ta ta na cin wainar shinkafa da miya,nama zuk'u-zuk'u a ciki



  Cikin fad'a ya fara magana"Zubaida daga ina ki ke!?"


  "Waina na je na siyo"  


Ta yi maganar ba tare da ta kalle sa ba.


  Ran shi ya kuma 'baci,tunowa da yanda maza su ke cika wurin Delo me waina,amma wai matar sa ta je siyan waina da kanta,cikin wannan mazan


  "Da izinin uban wa ki ka fita?"


Ya yi maganar da matsanancin 'bacin rai


  Abin da ya kuma tunzura shi,kamar da dutse ya ke maganar,don Zubaida ko kallon sa ba ta yi ba,waina kawai ta ke aunawa birnin timbin ta.


  "Ke!Zubaida,kada fa ki ga ina raga miki ki yi zaton tsoron ki na ke ji,gaskiya na fara gajiya da abin da ki ke yi min daga jiya zuwa yau,yanzu saboda ba ki da hankali duk mazan wurin Delo me waina, ki ka iya zuwa ki ka tsaya da auren ki?kar ki bari ki kai ni bango wallahi za ki sha mamaki na!"


  Ya yi maganar ya na jin kamar ya kifa mata mari.



  Har ya gama ba ta kalle sa ba,sai da ta gama tsotse k'ashin ta a nutse sannan ta ce"dad'i na da talaka ya iya zuciya da fushi daga fatar baki,idan na kai ka bango me za ka yi min Musa?"


 Sai kuma ta fara dariya ta ce"ni yau ka cewa mahaukaciya ko?to in dai wannan hauka ne,ka sa a ranka yanzu na yanki tikiti,sai ka shirya zama da mahaukaciya,kuma ka san ko a kotu ba a shari'a da mahaukaci ko?"


Ta na gama maganar ta tura masa sauran wainar ta ce"ga waina ko za ka ci"



  Wannan karon Musa kasa daidaita kansa ya yi,sai da ya wanke ta da lafiyayyun maruka har guda biyu,don ya ma kasa magana


  Zubaida ta dafe kuncin ta,saboda azaba tuni hawaye su ka fara sauka,amma duk da haka ta daure ta kuma fad'in


  "Ni ka mara?Allah ya isa tsakani na da kai,kuma wallahi ka mari auren ka!"


   Bai kuma magana ba,ya canja kaya ya fice daga gidan cikin k'unar rai



  Ya na fita ita ma ta saka hijjabi ta fice,ba ta zarce ko ina ba sai gidan su


Kuka ta fashe da shi bayan ta zauna kusa da mahaifiyar ta


Umma cikin tashin hankali ta ce"Zubaida lafiya?me ya faru?"


  Zubaida ta na ci gaba da kukan ta ce"Musa ne ya kama ni ya yi ta duka na,kawai saboda na tambaye shi kud'in cefane"


  Lokaci d'aya Umma ta had'e girar sama da ta k'asa ta soma surfa masifa"amma lallai wannan yaron ya bani mamaki,dama ya na dukan ki shi ne ba ki ta'ba fad'a ba,Zubaida ki ka zauna zai kashe ki a banza!?"


  Wani farinciki ya lullu'be Zubaida, don ba ta ta'ba zaton Umman za ta yi saurin yarda ba,duba da ganin yanda duk y'an gidan na su,su ke k'aunar shi


Haka Umma ta yi ta zabga masifa da zagin Musa,har mahaifin Zubaida ya fito tafiya kasuwa.


  Bayan Zubaida ta gaishe shi,ya amsa ya ce"ke kuma me ya fito da ke da sassafe haka?"


  Kafin ta yi magana Umma ta yi karaf ta amshe zancen"to ba dole ta fito ba,dukan ta fa ya yi da sassafen nan,daga ta tambaye sa kud'in cefane,shi ne ya hau dukan ta babu ji,babu gani,sai kace talauci hauka ne?"



  Mahaifin Zubaida ya yi guntun tsaki ya na girgiza kai,kafin ya nemi wuri ya zauna,ya fara magana


"To ni dai ba ke na tambaya ba,kuma wannan abin da ki ke k'ok'arin yi,bai yi ba sam!ba haka a ke hukunci ba,saboda ta zo ta fad'a miki magana, sai ki yarda kai tsaye babu bincike?"


Sai ya maida duban sa kan Zubaida ya ce"ke!me ya had'a ki da mijinki?"


Zubaida ta gabanta ya fara fad'uwa,amma ta dake ta ce"kullum haka ya ke fita ba ya bani kud'in cefane,idan na tambaye shi sai ya yi ta fad'a, shi ne yau har da duka na"


  "Kin tabbata?kin sanni,idan na kira shi na ji a kasin haka sai ranki ya 'baci ko?"


 Baban ya fad'a ya na tsare ta da ido.


  "Eh" Ta fad'a ta na k'ok'arin kauda tsoron ta.

[8/29, 8:41 PM] Mai Zafafa: *GAJEN HAK'URI*

 



BY

    *SADIYA ABDUL(Mai zafafa)*



*☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️*



SADAUKARWA GA K'UNGIYATA😘



PAGE   4





       Tsugunne ya ke a gaban surukan nashi,ya na jira ya ji dalilin kiransa,duk da ya san kiran ba zai rasa nasaba da marin da ya yi wa Zubaida da safe ba


  Mahaifin Zubaida ya ce"Musa da gaske yau da safe ka daki matarka?"


   Cikin tsananin jin kunya da kuma nadamar saurin hannun da ya yi,yace"eh Baba, wallahi tsautsayi ne in sha Allah hakan ba zai sake faruwa ba"


  Baba ya jinjina kai ya ce"to Allah ya yarda,kowa hak'uri ya ke yi da halin mata,kuma Zubaida yarinya ce,dole sai ka na yi mata uzuri ka ji ko?"


"In sha Allah" Ya fad'a ya na tashi,ya yi waje.


Ba dan ta so ba ta bi bayan shi,su ka koma gida,a hanya babu wanda ya yi wa wani magana, har su ka isa gidan.


  

   Yau d'in ma a waje ya yi kwanciyar shi,don kuwa bai gama hucewa da abin da ta yi masa ba,can cikin dare kuwa idonsa ya ce bai san bacci ba,saboda shi d'in mutum ne me yawan buk'atuwa,kuma cikin kwana biyun da su ka fara sa'insan nan bai neme ta ba


  Can cikin baccin ta ta ji a na lalubata,ai kuwa tai wuf ta tashi zaune dama can ba ta da nauyin bacci


"To meye hakan kuma?" Ta yi maganar da fad'a, kamar ba wadda ta tashi daga bacci ba



Musa ya kuma janyo ta,ba tare da ya yi magana,don ya lura idan har ya biye ta tunzura shi za ta yi,ya hak'ura,kuma ya san kan shi zai cuta



  Wata hankad'a da ta yi masa ne ya dawo da shi cikin hayyacin sa,da d'unbin mamaki ya ke kallon ta,ta cikin duhun d'akin kafin ya ce


"Wai ke meye hakan ki ke yi?"


  Zubaida ta ja tsaki ta ce"au ba ma ka san abin da na ke yi ba? Za ka sani nan ba da jimawa ba".


Ta na fad'ar haka,ta koma k'arshen gado ta juya masa baya.Musa ya cika da mamakin wannan sabon lamarin,haka ya koma waje ya kwanta da tunani barkatai bacci ya d'auke sa.


   

    Haka a ka cigaba da zaman doya da manja tsakanin Musa da Zubaida,kullum sai ta takale sa da fad'a, tun ya na share ta har ta kai yanzu hak'urin sa ya k'are,shi ma ya fara biye ta don kullum sai mak'ota sun jiyo kansu


  Kuma duk masifar sa haka ya yi ya hak'ura,don Zubaidar ba ta kuma yarda sun had'a shimfid'a ba.Sosai abin ya ke damun sa,don ya na cutuwa ba kad'an ba,don haka yau ya k'udure duk wadda za a yi,sai dai a yi amma dole ne ya kar'bi hak'k'in sa.


  

  A na sallar isha'i ya dawo gidan,a d'aki ya tadda ta ta na ninkin kayan da ta wanke da rana,ya zauna gefen gado ya had'e rai kafin ya ce"Zubaida a matsayi na na mijinki,ina so yau ki fad'a min dalilin ki na hanani hak'k'i na,har tsawon sati biyu"


  Zubaida ta wane ta'be baki ta fara magana"tabb! Su miji manya,wai hak'k'i,kai don Allah ko kunyar tunkara ta da maganar ba ka ji ba? To in dai hak'k'in ka ne, na cinye,kuma kar ka saka ran zan bayar  har abada!"


 

  "To meye dalilin ki?" Ya fad'a da d'an d'aga murya


"Ni ma yanzu na san daraja ta,ina da ajin da ba ko wane gaja ne zai yi yanda ya so da ni ba,wanda ya faru a baya ma tsautsayi ne"


Ta k'arashe maganar da yi masa kallon banza


Bai ce komai ba ya tashi ya fita daga gidan,ya na jin k'unci a zuciyarsa



Ranar sai cikin dare ya dawo,lokacin har ta yi bacci,dama hakan ya ke so,ruwa ya zuba ya yi wanka kai tsaye ya shiga d'akin


  A baje ya tadda ta,ta na sharar bacci kai tsaye ya haye gadon, ya kai hannunsa jikinta da nufin kar'bar hak'k'in sa


Ai kuwa ta fara neman k'wacewa,don a yau d'in ta yi wankan tsarki,bayan d'aukewar al'adar ta,wanda ta ke ganin wata babbar k'addara ce za ta sa ta yarda da shi a yau d'in


  Ganin da gaske nema ya ke ya fi k'arfin ta,sai ta yi saurin wawurar kaskon turaren wutar da ta gama turarawa d'azu,wanda na k'arfe ne,ba ta yi wata-wata ba ta k'wala masa a kansa


Azabar da ya ji ce ta saka shi d'aga kansa sama,tare da k'ank'ame hannun ta,ko zai ji sauk'i,abin ka da duhu ita sam ba ta san halin da ya ke ciki ba,jin yanda ya kuma rik'e hannun ta ne,ya sa ta yi zaton bai hak'ura ba ne,ai kuwa ta had'a duka k'arfin ta ta kuma k'wala  masa,cikin rashin sanin inda ta sauke


  K'arar da ya k'walla ce ta sa ta yi saurin tashi,ta ta sakko daga gadon,fitila ta kunna ta kai duban ta garesa,sai ta yi saurin ja da baya ta na zare ido tare da dafe k'irji,kwance ta ganshi daga kansa zuwa fuskarsa,duka jini ya wake don kuwa tun bugun farko da ta yi masa ta fasa masa kai,na biyun kuma a fuska ta buga masa,daidai gefen idonsa



  Cikin rashin sani abun yi ta fara kuka,don ta kasa k'arasawa inda ya ke


  Da kyar ya tashi don dishi-dishi ya ke gani,saboda jinin da ya wanke fuskarsa, dafe da kansa,ya tafi falo ya d'akko wayarsa,k'aninsa ya kira ya ce masa ya zo ya raka shi kemis.


  Zubaida dai ta na raku'be a gefe ta na sharar k'walla ta ji k'wank'wasa k'ofa


"Yaya zo ka bud'e min mana"

 

Ta ji muryar Ashiru k'anin Musan,hijjabi ta saka ta je ta bud'e masa ya shigo ya na tambayar ta ya me jikin?


  Zubaida ba ta ce komai ba ta yi gefe ta tsaya


Fitowar Musan daga d'aki ne ya sa Ashirun saurin kwallon ta,cikin kid'ima ya ce"me ya same shi!"


  "Mu je Ashiru,a fara bani taimako tukunna" Musan ya fad'a ya na yin gaba


Ashiru ya bi bayansa,ya na waiwayen Zubaida wadda rashin gaskiya ya bayyana k'arara a fuskarta.


 Dama a mashin ya zo,ya tada shi ya na fad'in"hau mu je,wannan ai ya fi k'arfin kemis,sai dai asibiti

[8/29, 8:41 PM] Mai Zafafa: *GAJEN HAK'URI*

 



BY

    *SADIYA ABDUL(Mai zafafa)*



*☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️*



SADAUKARWA GA K'UNGIYATA😘


 

PAGE   5





     Zubaida ta na zaune ta na zulumi,har asuba ta kusa ba ta ji dawowar su ba,saboda haka ta kwanta ta fara sharara baccin ta,wanda ya sa ta makara,don ko kiran sallar asubar ba ta ji ba


 Cikin baccin ta ta ji a na ta jijjiga k'ofar gidan kamar za a karya ta,ta yi firgigit ta tashi ta saka hijjabi ta fito


Ta na bud'ewa Fauziyya yayar Musa ta wanke ta da mari.Ta dafe kuncinta ta na yi mata kallon mamaki


  "Bak'ar munafuka,y'ar daba wallahi yau da idon d'an uwa na ya tsiyaye kema sai na je na tsiyaye na ubanki!"


Fauziyya ta yi maganar ta na k'ok'arin k'ara mata wani marin


 "Ke! Ba na son shashanci" Su ka ji muryar Umma mahaifiyar Musan


  Daga adaidata sahu su ka fito har da shi,sai dai bai k'araso ba ya tsaya daga gefe,ya na kallon Zubaidar,don gani ya ke abin kamar a mafarki ya faru,wai shi yau matarsa ta sunna ta yi wa wannan ta'ddancin kawai saboda ya nemi hak'k'in sa


  Cikin gidan su ka d'unguma su ka shiga,a nan tsakar gidan kowa ya yi wa kansa matsuguni


 Umma ta kalli Zubaida ta ce"Zubaida da gaske ke ce ki ka yi wa Musa wannan aikin?"


 Zubaida ta sunkuyar da kai a hankali ta ce"eh"


 "Meye dalilin ki" Umman ta tambaya


"Saboda na gaji da zama da shi" Ta fad'a kai tsaye.


 Umma ta ce"to kai ka ji dalili,don haka yanzu a nan kafin na k'ifta ido ka saki yarinyar nan,don mu ba mu gaji da kai ba,tun da ta fara fitar maka da jini nan gaba ba mu san me za ta yi maka ba"



 Babu musu kuwa ya ce"na sake ki,saki d'aya kuma na yafe miki abin da ki ka yi min"


  Zubaida ta ji gabanta ya fad'i,sai ta ji duk babu dad'i duk da ta dad'e ta na son jin wannan furucin daga bakinsa



 "Na gode" Ta fad'a da sanyin murya.


  Fauziyya da har yanzu huci ta ke yi,ta na jin kamar ta rufe Zubaida da duka ta ce"munafuka kamar ta Allah..."


"Ke! Shige mu tafi" Umma ta katse ta


  Su ka fice daga gidan,har da Musan,Zubaida ta shiga d'aki ta zuba kayan ta kala uku cikin jaka, ta saka hijjabi ta fito ta kulle d'akin


A k'ofar gida ta tadda shi,ya na zaune fuskarsa da alamun damuwa sosai,har d'inki a ka yi masa a gefen idonsa,ba ta ce komai ba ta mik'a masa mukullin ta wuce sa.



   Ta dad'e a zaure ta na tunani kafin ta kutsa kai cikin gidan da sallama.Umma da ke soya wainar fulawa ta amsa ta na k'are mata kallo,ganin ta da jakar kaya


  Kai tsaye d'aki ta shige,ta ajiye jakar sannan ta fito ta yi alwala ta koma d'akin ta yi sallah, wurin da Umma ta ke ta je ta zauna


"Ina kwana?" Ta yi maganar da sanyin murya


  Umma ta k'are mata kallo kafin ta ce"ke daga ina ki ke da safe haka? Na ga sai wani sissine kai ki ke yi,kamar mara gaskiya"


Zubaida ta ce"Umma Musa ya sake ni"


Ta yi maganar ta na yin k'asa da kai,ga mamakin ta sai ta ji Umma ta ce"da gaske? To alhamdulillah"


  Zubaida ta yi saurin d'agowa ta kalli Umma,sai ta ga murmushi shimfid'e a fuskarta


  Kafin ta yi magana Umma ta ce"ai ni dad'in wannan lamari na ji wallahi,ta ya za a ce da k'uruciyar ki,ki na zaman hak'uri ko haihuwar fari ba ki yi ba? Ki kwantar da hankalin ki in sha Allah wannan rabuwar ta alkhairi ce"


  Jin haka ne ya sa Zubaida sakin jikinta,har ta kar'bawa Umma suyar wainar,bayan sun gama Umma ta zuba mata wainar da kunun gyad'a,ta shige d'aki ta fara ci hankali kwance



  Bayan ta gama ta shiga nazarin yanda za ta gidanar da rayuwar zawarcin da za ta shiga


  Hayaniyar da ta ji ne ya dawo da ita daga tunanin,muryar Baba ta ji ya na fad'in"ina ta ke? Ke babu jin ba'asin sakin kawai sai ki hau fad'ar dama yaro ba d'an mutunci ba ne? Ke Zubaida!"


  Zubaida gabanta ya fad'i,don Baba ba shi da wasa ko kad'an,kuma ya tsani rashin gaskiya,fitowa ta yi ta tadda su zaune a tsakar gida,har da yayyun ta maza guda biyu da su kai shirin tafiya aiki


Ta durk'usa d'an nesa da shi,ta na gaida shi


Bai amsa ba ya ce"a kan wane dalili Musa ya sakeki?"


   Ta ji gabanta ya fad'i,amma ta yi k'arfin halin cewa "babu komai Baba"


  "Dama ina wasa da ke ne Zubaida? Yanzu ni zan tambaye ki,ki tsaya yi min gargada?"


Baban ya fad'a ya na kafe ta da ido.



"Haba! Malam ka san dai halin mazan yanzu,har sai mace ta yi mu su laifi za su wulak'anta....."



Umma ba ta k'arasa ba Baba ya tari numfashin ta da fad'in



"Ba fa da ke na ke ba,ki saurara haka tunda ita ba kurma bace"



  Zubaida fa cikinta ya d'uri ruwa,kamar za ta yi kuka ta ce"duka na ya ke yi,shi ne da na ga abin ya yi yawa na yi k'ok'arin k'watar kaina"


  Baba ya ce"ki ka k'waci kanki ta ya ya?"


  Ta yi shiru,ta na auna maganar da za ta fad'a, ganin yanda duk su ka tsare ta da ido ya sa ta sunkuyar da kai ta yi shiru.


  Nasiru da ya yo halin Baban ya daka mata tsawa ya ce"ke! Wai waye sa'an wasan ki a nan? Ba tambayar ki a ka yi ba?"


  

  "Umm...kasko na k'wala masa" Ta fad'a kamar za ta yi kuka.


  Yayyun na ta su ka d'au salati,Baba ya kalli Umma ya ce"to kin ji dai ko?"


  Sannan ya kai duban sa ga Zubaida da ta ke ta muzurai ya ce"to mu na jinki,da ki ka k'wala masa sai a ka yi me kuma?"


  Sai ta fara share hawayen da su ke zubo mata,kafin ta ce"kaskon na k'arfe ne,shi ne ya ji ciwo,yau da safe kuma kawai ya ce ya sake ni"


   Nan yayyun ta su ka bulbule ta da masifa kamar za su dake ta,Baba ma ya yi tasa tijarar ya gama ya bar gidan


 Ita dai Zubaida kuka kawai ta ke yi,sai da su ka bar gidan sannan Umma ta dube ta ta ce"gaskiya Zubaida ba ki kyauta ba! Yanzu da abin ya zo da tsautsayi fa?"


   "Ba zan sake ba" Ta fad'a ta na goge hawaye


 Umma ta ce"ai dama ba komawa za ki yi ba,bare ki sake namiji me duka bai yi ba sam! Ga talauci ga cin zarafi,abu goma da ashirin?"


 

  Zubaida dai d'aki ta koma ta kwanta ta na kiran wayar Hafsa k'awar shawarar ta.

[8/29, 8:41 PM] Mai Zafafa: *GAJEN HAK'URI*

 



BY

    *SADIYA ABDUL(Mai zafafa)*



*☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️*



SADAUKARWA GA K'UNGIYATA😘



PAGE   6




      Murna sosai Hafsa ta taya Zubaida na mutuwar auren ta,kai ka ce abin arzik'i ne ya samu Zubaidar


    A yanzu fes ta ke jin ranta,damuwar ta d'aya yanda zaman gidan ya fara gundurar ta,kullum ta na zaune a gida, tunda idda ta ke yi


   Sai dai zaman ta wurin d'aya ya k'arawa fatar ta kyau,har wata k'iba ta yi,duk lokacin da ta kalli mudubi shaid'an kuma yi mata hud'uba ya ke,ta na jin farashin ta na kuma hauhawa,wanda har ta ke jin lallai auren ta sai mai rabo.



   Kamar yau ne auren ya mutu,sai gashi har ta kammala iddar ta tsaf,ranar da ta fara fita gidan Hafsa ta nufa,don su tattauna ta ji maganar da kullum Hafsan ta ke fad'a mata cewar sai ta zo za ta ji.



   A bud'e ta tadda k'ofar gidan,don haka ta shiga kai tsaye,Hafsa ta tare ta da murna


Bayan ta sha ruwan da ta kawo mata ta kalle ta ta ce"ki fara ba ni bayani Hafsa kin tsaya ki na k'are min kallo?"



  Hafsa ta yi murmushi ta na wani lumshe ido ta ce"wallahi Zubaida hango ki kawai na fara yi a gidan alhaji Sunusi"


   Zubaidar ta d'an zaro ido ta ce"waye kuma alhaji Sunusi?"


 Hafsa ta ce"hmm! Kedai fara tsalle kawai,kukan ki ya zo k'arshe ai dama sai da na fad'a miki kefa matar manya ce,ke ba dan ma k'addara ta sa wannan Musan ya maida ke bazawara ba ai da sai kin fi samun matsayi wallahi,amma yanzun ma kin samu"



 "Ni fa ba na son kwana-kwana,ki fad'a min kai tsaye,don Allah me ya faru?"


Zubaida ta fad'a ta na cire mayafin ta


  Hafsa ta fara mata bayani"ai tun wata d'aya da mutuwar auren ki,mijina ya zo ya ke min firar me gidan sa,da ya ke son yin aure,babban mutum ne amma bai ta'ba yin aure ba,shi ba ya son rayuwar takura shi ya sa ya ke zaune shi kad'ai a gidan sa,to mahaifiyar sa ta matsa masa ya yi aure,shi ne ya ke fad'a wa mijina ya nemo masa wata,ya na fad'a kuwa na ce ga k'awata,a ka tura masa hoton ki a ka ce amma bazawara ce,cikin sa'a kuwa ya ce kin yi masa babu matsala".



  Zubaida ta sauke ajiyar azuciya,ta na jin mad'aukakin farinciki ta ce"Hafsa don Allah da gaske ki ke? Me kud'i ne sosai?"


 

  Hafsa ta harare ta kafin ta ce"a a,k'arya na ke yi,y'ar rainin hankali har na ce miki ogan mijina ne,amma ki ke tambaya ta wai me kud'i ne?"



  Zubaida ta yi dariya ta ce"Allah ya huci zuciyar ki,k'awata na gode sosai"



"Haba! Zubaida wannan ai yi wa kai ne,ke dai idan an yi auren ki ajiye duk wani duhun kai,ki zage kawai ki dinga faranta masa rai,na san duk wani jin dad'in duniyar nan za ki samu a gidan alhaji Sunusi".



  "To yanzu ina ya ke?" Zubaida ta tambaya cike da farinciki.


  Hafsa ta ce"me ki ke ci,na baka na zuba? Ai zai zo da kan shi,jiya a ka fad'a masa kin kammala idda,ba d'an garin nan ba ne shi ya sa,a Kaduna ya ke amma ya ce cikin satin nan zai zo,ki gan shi"




   "Allah ya kawo shi,ke ni ko ban gan shi ba ya yi min wallahi" Ta yi maganar ta na jin kamar duniya babu wanda ya kai ta sa'a.


 

   "Wato har ma ya yi tun kafin ki gan shi? To me k'aton ciki ne"


 Hafsa ta fad'a ta na dariya.


  Zubaida ta ce"Hafsa kenan,ke a na zancen kud'i ina a ke tuna wani k'aton ciki? Ai babu matsala ya zo kawai"



     Haka su ka sha firar su,kafin Zubaida ta tafi.A ranar kuwa alhaji Sunusi ya kira ta a waya,sai dai ba wata fira su ka yi ba,ya ce zai zo cikin satin.


  

    Washegari ta yi tsammanin zai kuma kira,sai ta ji shiru,ta kira Hafsa ta ke fad'a mata jiya ya kira amma yau ta ji shiru,Hafsa ta rufe ta da fad'a ta na cewa za ta yi wa kanta,wai ai irin su alhaji mace ce ta ke bin su,ba su ne su ke bin ta ba,don haka ita za ta dinga kiran shi a waya,kamar sau biyu a rana,sannan kullum ta tura masa sak'on soyayya guda uku a rana


  Haka Zubaida ta gamsu da shawarar Hafsa, ta na mamakin ashe haka masu kud'i su ke?


  

    Yau ne su ka yi da alhaji Sunusi zai zo,saboda haka tun safe ta fad'a wa Umma,kuma ta ce mata ranar da ta je gidan Hafsa ne su ka had'u,nan Umma ta hau shiri girki kala-kala a ka yi masa,Zubaida kuwa ta d'au wanka sai zuba k'amshi ta ke,ta gyara d'akin yayan ta Nasiru don a nan zai sauka.


   

    K'arfe biyar na yamma ya k'araso gidan, da kwatancen da ta yi masa,Zubaida ta fito ta na ta yauk'i da wani karya kai,wai ita fa a dole sai ta tafi da imanin alhajin nata


  

   A tsaye ta ganshi jikin mota ya na amsa waya,sai ta tsaya ta d'an nesa da shi ta na jira ya gama,ta k'asan ido ta k'are masa kallo tas.Ba shi da tsayi sosai,bak'i ne me y'ar k'iba kad'an,ba wani kyakkyawa bane,sai wasu manyan idanuwa kamar k'wai,kuma ashe da gaske Hafsa ta ke ya na da k'aton cikin.


 

   "Assalamu alaikum"

 

  Ta ji muryarsa,don ita ta tafi guntun tunani,ba ta san ya gama wayar ba.


  Zubaida ta na murmushin d'aukar hankali ta amsa,ta na d'an rusunawa ta gaida shi


  Ya amsa ya na k'are mata kallo da manyan idanun sa,har sai da ta ji ta tsargu.


Ya sauke ajiyar zuciya ya ce"ya ma sunan naki,Suwaiba ko?"


   Ta d'ago ta yi masa kallon mamaki,tunowa da shawarwarin Hafsa ya sa ta sakin murmushi ta ce"a a,Zubaida ne"


"To to to,na sha'afa ne,da ya ke abunuwan da yawa". Ya fad'a ya na k'ok'arin ciro wata wayar daga alhajihu saboda neman agajin da ta fara.


  Zubaida ta yi shiru har ya gama,ta na ji duk firar a kan aikin sa ne.


  

  "Alhaji mu shiga daga ciki ko?" Ta fad'a da murmushi


   Ya d'an shafa kai ya ce"to ai fa ba dad'ewa zan yi ba,don jirana a ke yi yanzu haka,bari na shiga mu gaisa da babar ta ki"


   Ta shige gaba ya na bin ta a baya da k'aton ciki, su ka shiga cikin gidan,sai da ya d'an duk'a sannan ya gaida Umma,ta amsa ta na ta washe baki,sannan ya shiga d'akin da ya ga Zubaida ta shiga,nan ta shiga gabato masa da girke-girki,ya ci kad'an ya ce a k'oshe ya ke.


  "To Zubaida, da fatan dai na yi miki?"


Ya tambaye ta kai tsaye.


  "Ai alhaji babu macen da za ta gan ka,ba ta yi fatan samun ka a amatsayin miji ba,ka yi sosai wallahi, ni ce ma na ke tsoron ko ban yi maka ba?"


Ta fad'a ta na wasa da yatsun hannun ta,da ya sha jan lalle.


  Alhaji ya ce"a a,kar ki damu kin yi min sosai"


  "Yawwa! Har na ji dad'i,tun da na ji muryar ka na ji son ka ya mamaye zuciyata,yanzu kuma da na ganka sai na ji idan na yi sake na rasa ka,kamar rayuwata ta zo k'arshe ne" Ta fad'a ta na murmushi.


  

 Alhaji ya yi y'ar dariya ya ce"a a a,to madallah! Yanzu dai kin ga ni ba yaro bane,don haka ba zan tsaya wani jan magana ba,tunda Allah ya sa na yi miki kawai sai a yi zancen aure,idan yanda na ke so ne ma,nan da sati biyu a d'aura kawai,ya yi miki?"



  Zubaida ta ji sati biyu ya yi kad'an,amma ta yi yak'e ta ce"a ya yi alhaji,a she dai ba ni kad'ai na matsu na ganni a gidanka ba?"


  "Ni ma na matsu da auren sosai,Zubaida kin ga ni ba yaro bane,kuma a da ba na sha'awar yin auren,saboda ba wani zama na ke yi a gida ba,ni aiki na ya fi min komai, to ganin mahaifiya ta ta matsu na yi auren ne ya sa na ce zan yi,shi ne ta samo min wata yarinya wai na aure ta,to a gaskiya yarinyar ba ta yi min ba,don siririya ce gaba d'aya a tsaye ta tafi,kamar ai(i) ni kuma na fi son y'ar duma-duma,kamar dai ke d'in nan".


  

Ya k'arashe maganar ya na washe baki, tare da kuma k'are mata kallo.


Zubaida ta ji wani dad'i ya mamaye ta,ta ce" to kuma yanzu Maman ta hak'ura da zancen yarinyar?"


  "A,kar ki damu babu matsala". Ya fad'a ya na amsa wayar da ta shigo yanzu.

[8/29, 8:42 PM] Mai Zafafa: *GAJEN HAK'URI*

 



BY

    *SADIYA ABDUL(Mai zafafa)*



*☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️*



SADAUKARWA GA K'UNGIYATA😘



PAGE   7





     Alhaji Sunusi bai bar gidan ba sai da su ka gaisa da mahaifin Zubaida, ya fad'a masa gobe zai turo magabatan shi,Baba ya yarje masa bayan ya tambaye sa adreshin gidan su na can Kaduna



  Kud'i masu nauyi ya bawa Zubaida, ta yi ta godiya ta na kuma bin sa da kalamai


    Bayan tafiyar sa Baba ya kira Zubaida ya tambaye ta inda su ka had'u,ta fad'a masa a gidan k'awar ta ne,sannan ya tambaye ta ta na son shi? Ta ce ta na son shi.



   Kamar yanda alhaji ya fad'a kuwa haka a ka yi,washegari ya turo manyan sa,da kayan aure duka,lefe akwati takwas ya yi mata, cike da kaya na nutsuwa masu tsadar gaske,a ka saka rana sati biyu


  A ranar ya turowa Zubaida kud'i masu kauri ya ce ta yi shirye-shirye,sanda ta tambaye shi yanda tsarin gidan ya ke,don a san abubuwan da za a siya,sai ya ce ko tsinke kada su siya,ita d'in kawai ya ke so don ya riga ya zuba komai da za ta buk'ata a cikin gidan.


  Hafsa ta bawa kud'i ta had'o mata duk wasu kayan gyara,ta gyaru sosai kuwa ta yanda har sai da ta k'agauta a yi auren


  Lokacin da ta tambaye sa fatin da za a yi,sai ya ce shi fa ba yaro bane,ba zai tsaya wannan shiriritar ba,duk abin da za ta yi ta tambaye shi kud'in zai turo mata ko nawa ne,ita ma sai ta hak'ura da fatin kawai ta ce tunda ba ya so a bar shi.


   Hausawa su ka ce "rana ba ta k'arya..."


   Yau ne a ka d'aura auren Zubaida Aminu,da alhaji Sunusi Ibarahim a kan sadaki dubu d'ari lakadan ba ajalan ba,d'aurin auren da ya yi suna,a ke ta zancen sa a gari,don manyan mutane masu fad'a a ji duk sun halarta



   Kowa ya yi zaton ba a ranar za a tafi da amarya ba,amma sai su ka ji alhajin ya na zancen Zubaida ta fito su tafi,kuma ya ja mahaifin Zubaidan gefe ya shaida masa mutum biyu sun isa rakiyar amarya,Baba ya yarda da hakan,don shi ba wani me son bidi'a bane.



  Zubaida ce rik'e da waya ta 'bata rai kamar za ta yi kuka,ta na jira a d'aga kiran da ta ke,ya na d'agawa ta fara magana kamar za ta yi kuka"haba alhaji,ya za a yi haka? Ga k'awaye na duk su na jiran kai amarya kuma ka ce da mutum biyu za a je?"


  "E! Hakan na tsara" Ya fad'a ya na katse kiran.


   Hafsa da ta fahimci a kwai matsala ta ja ta ge ta ke tambayar ta,nan ta fad'a mata halin da a ke ciki,Hafsa ta ce"ke yanzu a kan wannan ki ke damuwa? Ba komai bane,shi alhaji ba ya son hayaniya shi ya sa,daga baya duk za mu zo"


  Zubaida ta ce"gaskiya ban ji dad'i ba Hafsa,ko dai ba ya son hayaniya ina laifin mutum biyar?"


  "Ki yi hak'uri,babu matsala" Hafsa ta fad'a ta na k'arfafa mata guiwa.


   

  Yayar babar ta da k'anwar baban ta ne su ka raka ta Kaduna,tun daga bakin get d'in gidan Zubaida ta shiga zazzare ido,wani irin tamfatsetsen gini ta gani,na gani na fad'a duk cikin unguwar gidan ya fi girma


  Mai gadi ya wangale musu get su ka shiga,ita kanta farfajiyar gidan abar kallo ce,an k'awata ko ina da ado ga shuke-shuke ma su kyau da fitilu gidan gwanin ban sha'awa


Hamdala ta dinga jerowa cikin ranta sanda su ka shiga falon,su kuwa y'an rakiyar sai gyad'a kai kawai su ke,babu bakin magana saboda mamakin irin dukiyar alhajin


   Komai na buk'ata ya zuba a gidan,ba ta gama mamaki ba sai da ta bud'e sif,ta ga uban d'inkakkun kaya a jere,kala-kala,ba zanin gado ba hatta labulaye sai ta yi shekaru kafin ta buk'aci wasu,haka ma kitchen komai na buk'ata ya zuba, kayan amfani kuwa harda na'urorin da ba ta ta'ba gani ba,kayan abinci ma babu kalar da bai ajiye ba



 Zubaida ta yi ta murmushi,ta na kuma shiga lungu da sak'o na gidan



Bayan sun yi sallah wani ya zo ya kawo musu had'ad'd'an abinci,in ji alhaji,sai da su ka ci su ka yi nak sannan k'anwar mahaifin ta ta ce"ma sha Allah,komai ya yi Zubaida kin yi dace,sai fatan zaman lafiya"


  Yayar mahaifiyar ta ta ce"k'warai kuwa,sai dai wani hanzari ba gudu ba,na ga babu wanda ya zo cikin y'an uwan sa mata,tun da a ka fara zancen auren nan,ga shi yanzu ma mun zo ba mu ga kowa na shi ba"


   K'anwar Baba ta ce"gaskiya kam! Ya kamata a ce sun zo,mun damk'a ta a hannun su"


  Zubaida dai,ta na jin su ba ta ce komai ba,ita dai gani ta ke tun da ta samu irin gidan da ta ke so an gama komai.


   

   Da Zubaida ta ga dare ya yi sai ta yi tura masa sak'o,ta na tambayar sa ko ya dawo ne ta zo? Ya ce mata ba a gidan zai kwana ba.Su ka yi kwanciyar su tare da bacci me dad'i.



     Washegari tun da sassafe ya zo gidan,ya gaisa da y'an rakiya kuma ya ajiye musu kud'i mai yawa,ya ce idan sun shirya motar da za ta mai da su ta na jiran su


  Nasiha sosai su ka kuma yi mata kafin su tafi.


  Bayan tafiyar su da kamar awa d'aya ya dawo gidan,ta ci kwalliyar ta cikin wani tsadadden leshi,d'inkin riga da sket,ta tare shi da fara'ar ta ta na jin wata k'aunar sa na ratsa ta


  Ya kafe ta da manyan idanun sa,sai da ya kalle ta sosai sannan ya yi murmushi ya na sosa kai,nan ya shiga nuna mata ko ina na gidan, ta na bin sa a baya da farinciki sosai.


 

   A falo su ka zauna ta na yi masa hira,har kiran sallar azhar sannan ya yi waya ya sa a kawo mata abinci ya fita.


  Ta yi mamaki ganin ba ya irin zumud'in nan na angwaye,don ta ga dai har yanzu ko hannun ta bai rik'e ba,sai dai ta sa a ranta su masu kud'i haka su ke.



   Bayan ta idar da sallah ta ci abincin ta shiga kiran y'anuwa ta na yi musu ban gajiya.ta na nan kwance a falon har a ka kira la'asar,ta tashi ta yi sannan ta yi masa waya


  Bayan ya d'aga ta ce"na ji shiru,ba ka dawo ba?"


  "E! Na tafi wata sabgar ne,a kwai abin da ki ke buk'ata ne?"  Ya tambaye ta.


  Ta ce "a a,dama cewa zan yi da dare ba sai an siyo wani abun ba,zan yi girkin kawai"


  "To,shi ke nan babu matsala" Ya fad'a ya na katse kiran.


  

   Girki ta ja me rai da lafiya,ta jere a dining, magriba ta yi lokacin,sai ta yi wanka ta yi sallah,sannan ta yi kwalliya me haske ta shiga y'an gyare-gyare a d'akin gado



  Har a ka kira sallar isha'i bai dawo ba,saboda haka ta d'auki waya ta kira shi


"Hello! Alhajina na ji shiru" Ta fad'a bayan ya d'aga wayar



  Ga mamakin ta,sai ta ji ya yi guntun tsaki ya ce"to ya a ka yi?"


 Ta ji babu dad'i a ranta,amma ta daure ta ce"amm...dama abinci na ke jira ka zo mu ci"



"Kar ki damu,ki ci,ki yi kwanciyar ki ina wani aikin ne"


Ya fad'a, ya na kashe wayar ba tare da ya jira amsar ta ba.



  Jiki a sanyaye ta ci abincin,ba ta kwanta ba kamar yanda ya ce,sai ta kunna kallo don rage kewa,ta na nan zaune ta na kallon ta na duba wayar ta,ta ji an k'wank'wasa k'ofar falon,ta yi zaton ma shi ne,sai ta ga wani saurayi ne,ya yi mata murmushi ya na mik'o mata leda wai inji alhaji,ta kar'ba ta koma ta zauna


  Kaji ne masu rai da lafiya,sun sha gashi sai k'amshi su ke zubawa,ta juye a faranti,ta ci kad'an ta kai sauran dining, ta koma falo ta zauna jiran tsammani



 Sai k'arfe goma da minti hamsin ya dawo gidan,da mukulli ya bud'e k'ofar falon ya shigo



 "Ke! Ba ki yi bacci ba?" Ya fad'a ya na ajiye laftop d'in hannun sa.


  Zubaida ta wani narke ta ce"ta ya zan iya yin  bacci,ban ga dawowar mijina ba?"


  "E! Lallai ki shirya kwana a nan wata rana" 


 Ya yi maganar ya na mik'a mata hannu.


  Hannun ta ta mik'a masa, don a zaton ta nufin sa kenan.


  Sai ta ga bai kar'bi hannun nata ba ya zauna a kujera rigija! Kafin ya ce"ke wayar ki za ki mik'o min"


  Ta mik'o masa,ta dawo kusa da shi ta zauna,sai ta tsaya kallon sa ganin ya na k'ok'arin bud'e murfin wayar


  Ya cire batirin,sannan ya cire layukan ya karya su ta na kallo,ya watsar ya ajiye wayar a gefe.

[8/29, 8:42 PM] Mai Zafafa: *GAJEN HAK'URI*

 



BY

    *SADIYA ABDUL(Mai zafafa)*



*☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️*



SADAUKARWA GA K'UNGIYATA😘



PAGE   8





    Zubaida ta ji wani irin 'bacin ran da ba ta ta'ba ji ba,amma ta danne saboda gudun 'bacin ran shi,ta ce"alhaji ya haka kuma?"



 "Ba ni da ra'ayin matata ta rik'e waya ko da k'arama ce,bare kuma babba"


Ya fad'a ya na d'aukar wayar da laptop d'in sa ya wuce ta,Zubaida ta daskare a wurin ta ma kasa furta masa komai,ta ya ma zai ce ba za ta rik'e waya ba,alhalin ya sani y'an uwan ta ba a garin su ke ba? To yanzu da ya za su dinga gaisawa kenan?


  Ba ta gama tunanin ba,ta ji muryarsa "idan kin gama ina jiran ki a d'akina".


  Ta tashi ta bi bayan sa,ta na k'ok'arin 'boye damuwar ta,ba ta same shi a falo ba,saboda haka ta shiga d'akin gadon kai tsaye,nan ma dai ba ta ganshi ba,sai dai ta ji k'arar ruwa daga inda ta ke kyautata zaton band'aki ne,zama ta yi a bakin gadon ta shiga tunanin mafita,don gaskiya ba ta jin za ta iya hak'ura da wayar


  K'arar bud'e k'ofar band'akin ta ji,ta na d'agowa sai ta gan shi ya fito d'aure da towel iya k'ugunsa,k'aton cikinsa ya bayyana,kuma ta ga ashe kaya rage masa k'iba su ke


  Ya yi mata murmushi ya ce" na bar ki da zaman jira ko?"


 "Babu komai" Ta fad'a ta na k'ok'arin aro murmushi ta d'orawa fuskar ta.



  Sunkuyar da kai ta yi ganin ya na k'ok'arin kunce towel d'in a gaban ta,ko kunya ba ya ji wani rusheshe da shi,ba ta san lokacin da ya gama ya hayo gadon ba, sai jin muryarsa ta yi"kashe hasken d'akin ko?"



   Ta tashi ta kashe,ta dawo gadon ta kwanta,janyo ta ya yi jikinsa,ya fara magana a hankali


"Na ga ranki ya 'baci don na kar'bi wayar ki ko? Ba na son haka,ina da ikon hana ki rik'e waya,tunda ba ibada bane"


"Ka yi hak'uri" Ta fad'a da sanyin murya.


 "Na hak'ura,amma idan ina yanke hukunci ki na nuna min bai yi miki dad'i ba za mu dinga samun matsala,ni ne na ke da iko da ke"


  

Ya fad'a ya na juya ta,ya haye ruwan cikinta.



  Washegari ta riga shi tashi,sai da ta yi alwala sannan ta tashe sa,ya bud'e jajayen idanun sa masu cike da bacci,ya had'e gira kafin ya ce"ke! Ba a tashi na daga bacci,ko me za a fad'a min tsayawa a ke har sai na tashi tukunna"


  Zubaida ta ce"yi hak'uri, kiran sallah ne a ke yi,na ga wai kar a shiga sallar ba ka tashi ba"


  Bai ce komai ba,sai juyi da ya yi,ya na wani sakin nishi irin na maza masu k'iba


  Sai ta shimfid'a sallaya ta yi raka'atanil fijr,kafin ta yi sallar asuba,ta na nan zaune ta na sak'a da warwara har gari ya fara haske


Ta kai duban ta gadon,sai ta ga ya na ta sharara baccin sa hankali kwance,tashi ta yi ta fito falo ta shiga goge-goge,duk da babu wani datti,bayan ta gama had'a abin da za su ci,ta tafi d'akinta,ta yi wanka ta shirya cikin wata atamfa d'inkin doguwar riga,ta dawo falo ta zauna ta na jiran fitowar sa


 Jin shirun ya yi yawa,ya sa ta komawa d'akin nasa,sai ta same shi a yanda ta bar shi ya na ta kwasar bacci,ta juyo ba tare da ta kuma tashin sa ba,dining d'in ta nufa ta ci abinci ta k'oshi,ta dawo falo ta dasa sabon zama.


  Ta na zaune ta na kallon agogo,sai k'arfe goma da rabi ya fito,cikin wata dakakkiyar shadda,ya na ta zuba k'amshi.


 

 Ta saki murmushi ta na tasowa ta ce"barka da fitowa alhaji"


  "Yawwa" Ya fad'a ya na wani mazewa kamar ba shi bane ya yi ta zuba mata sambatu ba daren jiya



"Ina kwana,fatan ka tashi lafiya?"



"Lafiya lau,ya ki ka tashi?". Ya fad'a ya na yi mata guntun murmushi


  "Lafiya k'alau" Ta amsa.


  Zama ya yi a d'aya daga cikin kujerun falon ya na k'ure ta da kallo ya ce"ban fiya son shigar manyan kaya ba,ki dinga saka k'ananu kin ji ko?"


  "To" Ta fad'a ta na d'an kallon kayan jikinta.


 Ya ce"a kwai abin da ki ke buk'ata?"


  "A a,ai na ga a kwai komai" Ta fad'a ta na murmushi.



  Tashi ta ga ya yi,ya na k'ok'arin fita,ta yi saurin fad'in"ga abinci fa a dining".


  Ya d'an yamutse fuska ya ce"kar ki damu,ni ba na cin komai da safe,na tafi"


Bin bayan sa ta yi da nufin rakiyar nan,sai ta ji ya ce"a a,koma ki yi zaman ki ba sai kin wani fito raka ni ba"


  "Haba,ka san fa zan yi kewar ka shi ya sa zan raka ka ko wurin mota ne,ka ga dai na d'an k'ara kallon ka ko?" 


Ta yi maganar ta na wani shagwa'bewa.


    Ya yi guntun murmushi ya ce"kar ki damu,sai na dawo"


 "To a dawo lafiya,Allah ya tsare min kai,ya..."


Ba ta k'arasa ba ya amsa da"amin"  Ya yi ficewar sa.


  Ta koma ta zauna a kujera ta na tunanin irin halin nasa


  K'arfe goma sha biyu ta tashi za ta d'ora girki,sai a lokacin ta tuna da abinci safe a dining, ta saka hijjabin ta ta kwashi abincin,har da sauran kazar jiya ta fito farfajiyar gidan,ta na hangen ta inda za ta ga me gadi



 Wani tsoho ta gani zaune a kan wata kujera ya na jin radiyo,sai ta k'arasa ta yi masa sallama,ya amsa ya na gaishe ta


  Ta ce"Baba ina wuni?"


Ya ce"lafiya lau hajiya,barka da fitowa"



Ta mik'a masa abincin ta ce"ga shi Baba,anjima zan zo na kar'bi kwanukan".


 "Madallah! An gode Allah ya saka" Ya shiga jero godiya kamar zai duk'a.


 

  Kai tsaye ta shiga kitchen, ta zauna ta nutsu sosai ta zabga girki mai dad'i,ita kanta ta ji dad'in abincin,bayan ta gama ci ta yi wanka,ta yi sallah,ta saka wata riga iya guiwa,ta yi fakin d'in gashin ta da ribom kalar rigar,ta na nan zaune a falo ta ji a na danna k'ararrawa a lamun a kwai bak'o a waje,sai ta saka k'aramin hijjabi ta bud'e k'ofar,wasu mata ta gani su uku su na tsaye,sai harare-harare su ke yi,da alama dai ba abin arzik'i ne ya kawo su ba



"Za ki iya bamu hanya mu shige?" 'Daya daga cikin su ta tambaya


  'Dayar ta yi farat ta ce"ai dole ta bamu,tunda ba gidan ubanta bane!"


  Zubaida ta ji gaban ta ya fad'i,sai ta yi saurin matsawa ganin babbar ta na shirin ture ta


"Bayin Allah daga ina ku ke? Kuma me ku ke nema?"


Zubaida ta fad'a ta bin bayan su,ganin sun shige falon.


  Zama su ka yi a kujeru su na bin gidan da kallo,d'aya daga cikin su ta ce"lallai yarinya wuyanki ya isa yanka,yanzu dama saboda ke yaya Sunusi ya k'i auren y'ar uwar mu? To kuwa ki sa a ranki kema ba zama ne ya kawo ki ba,don wallahi sai kin yi waje,shegiya y'ar matsiyata!"


   Zubaida kamar za ta yi kuka ta ce"Allah ya baku hak'uri, shi aure k'addara ne,Allah ya yi ni d'in ce matarsa"


  Sai kuwa y'ar k'aramar cikin su ta yi tsalli ta damk'i wuyan ta,ta shak'e za ta fara dukan ta kenan,sai ga alhaji ya shigo falon kamar daga sama.


  Wata irin tsawa ya daka mata,nan da nan jikin su ya shiga rawa,har na zaunen,babbar cike ce murya na rawa ta ce"don Allah ka yi hak'uri "


  "Daga yau,duk shegiyar da na kuma gani a cikin gidan nan sai na karya ta!"


Ya fad'a, ya na zaro manyan idanun sa.


  "Ku fice min!" Ya daka musu tsawa.


 Kafin ka ce kwabo sun fice har da gudu-gudun su.


Ajiyar zuciya Zubaida ta sauke,ta na dafe k'irji ta ce"alhaji su waye?"


  "K'anne na ne" Ya fad'a ya na zama a kan kujera Zubaida ta cire hijjabin ta na zama a gefen sa ta ce"wallahi na ji tsoro sosai"


 Ya ce"kar ki damu,ba za su dawo ba".



  Wanka ya yi,ya ci abinci ya kuma fita,ita dai Zubaida har yanzu a tsorace ta ke.

[8/29, 8:42 PM] Mai Zafafa: *GAJEN HAK'URI*

 



BY

    *SADIYA ABDUL(Mai zafafa)*



*☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️*



SADAUKARWA GA K'UNGIYATA😘



WANNAN SHAFIN NAKI NE MY ZEE BABY😉


PAGE   9



  

    

    Yau satin Zubaida d'aya a gidan alhaji,amma har zaman gidan ya fara gundurar ta,kullum idan ya fita da safe sai dare ya ke dawowa,kuma ba ya wani zama su yi fira,yanda ta fahimce sa dai ba shi da surutu,ga wani abu da ya ke k'ona mata rai,yanda ya ke da saurin bacci,da ya dawo idan ya yi wanka ya kwanta minti uku ya yi yawa,zai fara jan rago(munshari),abin ya na bata haushi,ta wuni ita kad'ai a gida babu d'an fira babu waya,amma idan ya dawo a ce ba zai zauna su yi fira ba? 


Shi dai abin da ya sani kawai idan gari ya waye ya tambaye ta ko da abin da ta ke buk'ata.Sau uku ya na kira mata Baba a waya,duk ta gaisa da y'an gidan,kuma ko irin ya matsa gefen nan ko za ta yi sirri da iyayen ta baya yi,sai dai ya tsare ta da manyan idanunsa ma su abin tsoro.




  Kamar kullum yau ma ta na zaune a falo ta na jiran fitowar sa,ta na kallon k'ofar d'akin da ya ke ciki ta na kuma auna yanda za ta tunkare sa da maganar


  Kamar kullum k'amshin turaren sa ne,ya fara ankarar da ita fitowar shi,don alhaji Sunusi a kwai shi da son k'amshi



"Barka da fitowa alhaji" Ta fad'a ta na mik'ewa tsaye


  Ya na gyara zaman hular sa ya ce"yawwa,a kwai matsala ne?"


 Wannan tambayar ta shi ta na mugun bata haushi,amma ta maze ta ce"e to! Alhaji dama ina son rok'on alfarma ne,don Allah ka bar ni na rik'e wayata,zaman ni kad'ai ba ya min dad'i"


  Alhaji ya mik'e tsaye rai 'bace ya fara magana


"Ke! Ba ki san babu abin da na tsana kamar raini ba ko? Ki na k'ark'ashi na har na yanke miki hukunci ki kasa yarda da shi? To idan kin ganki da waya wallahi kin bar gidan nan! Kuma idan ki ka sake yi min zancen waya sai kin gane ba ki da wayo,shashasha kawai!"


  Tuni k'walla ta cika idanunta,ta bishi da kallo ta ma rasa bakin magana,ya fice ya na cigaba da maganganun sa.


  

   Ranar ko abincin rana ba ta ci ba,haka ta wuni da bak'inciki,ta na buk'atar ganawa da aminiyar ta Hafsa ko da ta waya ne,domin ta bata shawara a kan wannan zaman nasu da alhaji,amma ta rasa ta yanda za ta ji ta har su yi maganar.


  Tsaki ta ja,da ta tuna babu number kowa a kanta sai ta Musa,gashi yanzu babu amfanin da za ta yi mata,da ta haddace wata number sai ta je wurin Baba me gadi,ta san ba zai rasa k'aramar waya ba,sai ya dinga ara mata.



  Yau da wuri ta yi girkin dare saboda yunwar da ta ke ji,don ba ta ci komai ba da rana,zubawa Baba me gadi ta yi a cikin kwanon da ta ware masa,ta saka hajjabi ta fito kai masa



Zaune ta tadda shi ya na jin rediyo,ta k'araso da fara'arta ta gaishe shi ta na ajiye masa kwanon.


Baba ya washe baki ya ce"sannu y'ata,Allah ya saka da alkhairi"


Zubaida ta amsa da amin,ta na tsugunnawa nesa da shi ta ce"Baba ashe a na karanta littafi a rediyon garin nan?"


  Baba ya k'aro sautin rediyon kafin ya ce"wallahi kuwa,kullum ina ji saboda littafin a kwai abin tausayi da k'addara ga kuma fad'akarwa,da soyayya me ban tausayi duka a ciki".


  Zubaida ta ce"Baba ya sunan littafin?Allah ya sa ba a yi nisa ba"


"Sunan shi BA NI ZUCIYARKI,a cikin satin nan dai na ji sun fara".

 

  Zubaida ta janyo kujera ta zauna ta bada nutsuwar ta,wurin sauraron karatun littafin,wanda ta ji an ce Princess Ayshatou ce ta rubuta shi


  Sai dab da magriba a ka gama,ta sauke ajiyar zuciya don ba ta so a ka gama ba,ta ce" kai! Amma dai littafin nan zai yi dad'i Baba"


  Baba ya ce "kuma kinga kullum a ke yin shirin"


 Zubaida ta ce"ai kuwa in sha Allah ba zan manta ba, zan dinga zuwa ina saurara,ya rage min wata kewar"



Baba ya ce"gaskiya kam,zaman wuri d'aya ba shi da dad'i,amma sai ki yi ta hak'uri tun da ibada ne"


 Ta yi wa Baba godiya ta kuma d'aki,ta na ta tunanin irin son da IRSHAD ya ke yi wa IRAM a cikin littafin.



   To tun daga ranar Zubaida ta samu abin yi,da wuri ta ke gama girkin dare, ta tafi wurin me gadi jin rediyo,shi kuma Baba sai ya k'arawa zaman jin rediyon armashi ta hanyar siyo gyad'a marau-marau su na ji su na ci,cikin kwanciyar hankali.



  Yau alhaji bai fita aiki ba,tun safe ya na zaune a falo ya na ta aiki a system, sai dai lokaci zuwa lokaci ya dinga amsa kira,ya na kur'bar lemon da ta ajiye masa.


   Zubaida ta fara kallon agogo ganin lokacin fara shirin ta ya kusa,gashi yau alhaji ya kafa ya tsare,ta rasa yanda za ta yi wani k'ululun abu ya zo wuyan ta ya tsaya,kamar za ta yi kuka



  Ba ta jin za ta bari shirin yau ya wuce ta,don kuwa jiya sai da ya d'akko wani shegen dad'i sannan a ka gama,burin ta kawai ta ji shin da gaske IRAM za ta iya fad'awa IRSHAD ta na son shi? 


"Kai ba zai yi wu shirin nan ya wuce ni ba" Ta fad'a a zuciyarta.



  Mayafi ta saka ta fita,kai tsaye ta je ta shimfid'a salayyar ta kamar yanda ta saba,nan Baba ya gabato mata da gyad'a ta na ci su na jin rediyon su


  

  Alhaji Sunusi ya cika da mamaki,ganin ta yafa mayafi ta fita,kuma shiru ba ta dawo ba,nan ya fara tunanin ko dama ta na fita waje idan ba ya gidan? Hakane ya sa shi rufe system d'in ya fito farfajiyar gidan



 Can ya gango ta,zaune a sallaya,dab da me gadi ta mik'e k'afa ta na ta 'barar gyad'a



   Zubaida da ta yi nisa wurin sauraron shiri,sam ba ta san da fitowar alhaji ba,bare k'arasowar sa,sai jin muryarsa  ta yi cikin daka tsawa ya ce"wannan wane hauka ne haka?!"



   Ba Zubaidar ba har Baba sai da ya mik'e tsaye,saboda tsorata da jin irin muryar alhajin,sim-sim ta ra'be gefen sa ta shige cikin gidan



  Zama ta yi a falo gaban ta na tsanan ta fad'uwa,ya d'an dad'e kafin ya shigo falon


  Zubaida ta yi tsumu ta na jiran duka,ko kuma ruwan bala'i,ga mamakin ta sai ta ga ko kallon inda ta ke bai yi ba ya shige d'akinsa,kuma har a ka yi sallar isha'i bai fito ba,hakane ya sa ta saki jikinta,har ta ci abinci kafin ta shige d'akinta,da fargabar hukuncin da zai yanke bacci ya kwashe ta.



  

  Washegari da ta gaida shi ko kallon inda ta ke bai yi ba ya yi ficewar sa,hakan ne ya tabbatar mata da lallai ya yi fushi da ita.


  

Bayan ta gama karin safe,sai ta kwashi sauran kamar yanda ta saba za ta kai wa Baba.


  Dab da za ta k'arasa bakin get d'in ta ci wani wawan burki had'i da sakin farantin hannun ta,sakamakon ganin wani k'aron namiji me murd'ad'den jiki,ya zuba mata jajayen idanun sa,fuskar nan babu alamun rahama


  

  Tiger sabon me gadi kuwa tasowa ya yi,ganin ta yi 'bari zai kwashe mata,ai kuwa Zubaida ta k'walla k'ara had'i da zundumawa a guje ta shige d'aki har da murd'a key.

[8/29, 8:42 PM] Mai Zafafa: *GAJEN HAK'URI*

 



BY

    *SADIYA ABDUL(Mai zafafa)*



*☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️*



SADAUKARWA GA K'UNGIYATA😘



PAGE   10





     Jingina ta yi da k'ofar ta dafe k'irji ta na sauke numfashi da sauri da sauri,ta d'an jima a haka kafin ta samu nutsuwa,sai ta lek'a ta windon falon,amma ta ga wannan k'aton har yanzu ya na nan,ita dai a zaton ta d'anfashi ne ya shigo gidan ya ke jiran dawowar Alhaji


 Zaro ido ta yi da ta tuna watak'il ya kashe Baba me gadi,wani tsoro ya shigeta,ta kuma kwasa a guje ta shige d'akin gado ta kulle da mukulli,ta zauna ta fashe da kuka.Sai yau ta kuma jin takaicin Alhajin na hana ta rik'e waya,gashi yanzu za a kashe ta a banza ya na can bai sani ba,kukanta ya tsananta ta kwanta ta na ta yi,har da shasshek'a.


  Ganin har azhar shiru ba ta ji an zo an buga k'ofar ba,ya sa ta daina kukan,kanta har ya fara ciwo ta tashi ta yi alwala ta yi sallar azhar,ta shiga addu'o'in neman tsari.Ta na nan zaune da jan ido har la'asar ta yi,nan ma ta tashi ta yi sallar,ta koma ta kwanta kan sallayar ga yunwa ta na sakad'ar ta,amma babu halin fitowa ta ci wani abun.



  Sai bayan sallar isha'i Alhaji ya shigo gidan,ya saba dama da mukullin shi ya ke bud'ewa,ta na jin bud'ewar shi ta zabura ta mik'e tsaye daga gyangyad'in da ta fara,lek'owa ta yi ta windon d'akin amma ba ta hango kowa ba,saboda d'akin ya d'an shiga lungu,hakan ya sa ta bud'e k'ofar kad'an ta lek'o,sai ta sauke ajiyar zuciya jin k'amshin turaren Alhajin.



  Fitowa ta yi cikin jigata,ta k'araso inda ya ke a zaune ya na amsa kira


"Alhaji d'anfashi ya shigo gidan nan fa!" Ta fad'a ta na sauke numfashi



    Ko kallon ta bai yi ba,sai da ya gama wayarsa tsaf sannan ya kalleta,ganin duk ta yi wujiga-wujiga ya ce"ke me ya ke damun ki?"


  "Alhaji wani shirgegen k'ato na gani a bakin get,kuma ban ga me gadi ba,ina kyautata zaton 'barawo ne".


  Alhaji ya ja tsaki ya ce" ke! Matsa ki bani wuri kafin na mazge ki"


  Jiki a sanyaye Zubaida ta ce"wallahi da gaske na ke"


  Cikin k'osawa Alhaji ya ce"sabon me gadi ne,idan kin so shi ma sai ki dinga zuwa ki na zama a wurinsa,banza ballagaza!"


 Bai jira cewarta ba ya wuce ya bar ta tsaye,da tsoron da ya bayyana a fuskarta.



Zama ta yi ta fara share hawaye,wai yau ita namiji ke fad'awa kalmar ballagaza a gabanta? Gefe guda kuma ta na fargabar yanda za ta zauna da wannan k'aton a cikin gida,daga ganin shi ma ba musulmi bane.




 Haka ta yi ta tunani kafin ta tashi ta shiga kitchen, ta d'ebo d'an abin da za ta iya ci,ta ci ta kwanta.



     Washegari ya na fitowa ta taresa da y'ar fara'arta ta neman alfarma ta gaida shi


Ya amsa ya na nazarin ta,ya zauna kamar yanda ya saba,idan zai tambaye ta abin da ta ke buk'ata.



Zubaida ta karyar da kai ta fara magana"Alhaji dama na ga tun da a ka yi auren nan ban je na gaida mahaifan ka ba,shi ne na ga dacewar hakan"


  Ya zuba mata manyan idonsa kafin ya ce"ke za ki fad'a min abin da ya dace? To ba za ki je ba,ke bari na fad'a miki gaskiya kar ki saka ran za ki lek'a waje ba tare da kin yi shekara d'aya a cikin gidan nan ba. E! Ni haka tsarina ya ke,duk shekara zan dinga kai ki gidan ku,ki ga y'an uwanki,amma babu ruwan ki da nawa y'an uwan,tun da zama na ki ke ba nasu ba".



  Wani tashin hankali ya dirar wa Zubaida,cikin firgita da jawaban sa ta ce"E...um...Alhaji ban gane manufar ka ba?"



  "Za ki gane a hankali,tun da dai mu na tare" 


Ya yi maganar ya na ficewa daga gidan.



  Zubaida ta dafe k'irjinta da ya ke mugun bugu,tabbas ta tsorata da zancen Alhaji, idan har da gaske ya ke yi,sai shekara za ta fita to kuwa tabbas gwara ta za'bi rabuwa da shi,don shi ne mafita a gareta.

[8/29, 8:42 PM] Mai Zafafa: *GAJEN HAK'URI*

 



BY

    *SADIYA ABDUL(Mai zafafa)*



*☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️*



SADAUKARWA GA K'UNGIYATA😘



PAGE   11





      Haka ta yi wunin ranar, ba ta da maraba da me jinya,ta buga nan ta buga can ta rasa mafita,ta san Hafsa ce kawai za ta taimake ta a halin  da ta ke ciki yanzu,to ga shi kuma ba ta da damar ganin ta.



   Haka ta cigaba da zaman matsi da takura,kamar wadda ba ta da dangi,babban abin da ya ke ci mata tuwo a k'warya yanda idan Alhaji ya kira mata iyayen ta su gaisa,sai su ce ta yi ta yi wa mijinta godiyar abin alkhairin da ya ke yi musu,ga shi duk sanda ya bata wayar ba ya matsawa sai ya ji komai,ita kuma wannan godiyar da su ke kwararowa ita ta ke hana ta bayyana musu halin da ta ke ciki.



  A haka Zubaida ta samu wata uku cir,ta na rayuwa ita kad'ai,don yanzu abin nasa ya ci tura,tun da wataran ma ba kwana ya ke a gidan ba.'Dakinsa kuwa sai ya yi sati be gayyace ta ba.



  Yau dai hak'urin ta ya zo k'arshe,saboda haka sai da ta daidaici lokacin dawowar shi,sannan ta zo falo ta kwanta a k'asa ta baje,kamar gawa.



  Ta na jin shigowar sa ta dafe k'irjinta daga kwancen da ta ke,ta fara sakin numfarfashi da sauri da sauri,sai juya kai ta ke yi irin na wanda ciwo ya ke cinsa,kallo d'aya za ka yi mata ka san ta na cikin mawuyacin halin da ta ke buk'atar taimakon gaggawa



  Da sauri Alhaji ya k'araso, ya tsugunna a inda ta ke ya fara kiran sunan ta.


  Zubaida ta yi banza da shi,ba ta fasa abin da ta ke yi ba


 Saurin ciro wayarsa ya yi daga aljihu,ya dannawa likitansa kira


  "Doctor! Ka zo gidana yanzu don Allah, za ka duba matata ta na cikin mawuyacin hali"



  Cak! Zubaida ta dakata ta na sauraron shi,cikin zuciyarta ta fara magana


"Lallai wannan mutumin! Wato ma ba zai kai ni asibiti ba kenan? Ko sau d'aya yau na shak'i iskar waje? Na shiga uku ni Zubaida"



  Saurin tallabo ta ya yi ganin ta daina motsin,sai ya yi zaton suma ta yi


"Zubaida! Zubaida!". Ya fara nanata sunan da k'atuwar muryarsa ya na jijjiga ta


 Ita kuwa ta na ji ta yi banza da shi,ta na jera masa Allah ya isa a cikin zuciyarta.



 Babu jimawa likitan ya shigo cikin gidan,Alhaji ya yi masa iso har falon,ya zo ya tsuguna a inda ta ke



  Ta d'an kyallo ido ta kalle shi,sai ta ga hannunsa rik'e da wannan abin da su ke sakawa a kunnen su,sai ta maida idonta ta rufe.Ta na jin ya d'ora mata abin a k'irji sai ta d'auke numfashin ta cak,wai ita a nufinta har sai ya d'auke za ta saki numfashin,amma sai ta kasa,ta sake shi da k'arfi ganin za ta mutu,sai ta dinga d'auke numfashin ta na saki.


  Likitan ya ce"Alhamdulillah,numfashin ta ya dawo,sai dai bai daidaita ba,menene ya faru da ita ne Alhaji?"



 Alhaji ya sauke ajiyar zuciya ya ce"wallahi ban sani ba,dawowa ta kenan na tadda ita a haka"


 Likitan ya ce"ayya! Yawanci damuwa ce ta ke kawo irin wannan ta farat d'aya,yanzu zan yi mata wata allura sai na rubuta mata magunguna,tun da dai ba ta farka ba,bare mu san abin da ya haddasa hakan ko?"



   "Wallahi zaman kad'aici ne". Su ka ji muryar Zubaidan babu zato



Likitan ya ce"Alhamdulillah! Madam ya jikin?"


  "Ahhhh! Wayyo zuciyata!" Ta fad'a ta na dafe k'irjinta.



 Hankalin Alhaji ya d'an tashi,ya zo ya d'ago ta,ya ce"me ya sameki Zubaida?"


Zubaida ta fashe da kuka ta ce"haba Alhaji! Wannan zaman ya isheni haka! Ko akuya ta na buk'atar kulawa,amma ka kimshe ni a cikin gida,kai ba ka d'ebe min kewa ba kuma ba ka ba ni abin d'ebe kewa ba,wallahi nan ba da jimawa ba zuciyata za ta fashe!"



  Cikin takaicin maganganun ta Alhaji ya saketa,ya tashi ya na cewa likitan ya je gobe zai ji alert, likita ya kwashi kayan aikin sa ya fita da tausayin Zubaida.




  Bayan tafiyar likitan Alhaji ya kalli Zubaida ya ce"dama rashin lafiyar k'arya ne? Ai kuwa in dai hakane ki ke tunanin zai sa na canza ra'ayi na, to sai dai ki mutu!"



 Bai jira cewarta ba ya yi shigewar shi d'aki.



  Zubaida ta tashi zaune,ta ci kukan ta,kafin ta koma d'akinta ta kwanta da tunanin wata mafitar,don ba za ta kashe kanta ba tabbas sai ta samarwa kanta mafita.

[8/29, 8:42 PM] Mai Zafafa: *GAJEN HAK'URI*

 



BY

    *SADIYA ABDUL(Mai zafafa)*



*☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️*



SADAUKARWA GA K'UNGIYATA😘



PAGE   12




    Yau Alhaji ya na fita ita ma ta yafa mayafi ta d'auki jaka ta fito,ta dad'e a tsaye kafin ta k'arasa bakin get d'in,saboda ita dai har zuciyarta tsoron wannan me gadin ta ke,dafe k'irji ta yi ta runtse ido,a k'ok'arin ta na saka wa kanta jarumta ta had'e rai ta fara taku cikin isa,kanta a sama ta nufi bakin get



Ko kallon inda ya ke zama ba ta yi ba,zuciyarta na ta bugu ta nufi k'ofar,har ta ta'ba za ta bud'e ta ji muryarsa


"Hajiya fita za ki yi ne?"


  Sai da Zubaida ta d'an razana,don a zaton ta hana ta zai yi,amma ta dake ta ce"eh! Zan shiga mak'obta ne"


"A dawo lafiya" Ya fad'a ya na zama kan kujera.


  Wata sassanyar ajiyar zuciya ta sauke har da dafa k'irji,ta shiga kallon tafka-tafkan gidajen unguwar,ko ina a kulle babu hayaniyar komai,gidan da ya ke kallo gidanta ta nufa.


Cikin d'ari-d'ari ta k'wank'wasa,me gadi ya lek'o ya ce"sannu hajiya,wurin wa ki ka zo?"


 "Matar gidan" Ta fad'a kanta tsaye.


 "Ta san da zuwan ki?" Ya tambaya.

 

 Cikin k'osawa Zubaida ta ce"bawan Allah ba ni hanya mana"


 Ya d'an yi jim kafin ya ce"a'a,bari na sanar mata"


Ya rufe gidan,ya bar ta tsaye cikin takaici.Bai jima ba ya dawo ya bud'e ya ce an ce ta shiga


   Shiga ta yi da bismillah,ta na kallon yanayin gidan,ya yi kyau sosai duk da bai kai nata had'uwa ba,k'ofar da ta ke kyautata zaton nan ne falo ta nufa da sallama,a ka amsa a na bata izinin shigowa.



  Wata matashiya ta gani,wadda ba za ta wuce shekarun ta ba,black beuaty ce, ta ci kwalliyar ta,ta na zaune ta na bawa d'anta abinci a kofi,gefe guda kuma ga wata kyakkyawar yarinya kan kujera,ta bada hankalin ta wurin tv.


 Zubaida ta kuma yin sallama a karo na biyu,matar ta amsa da murmushi ta na cewa"k'araso mana".



  Ta k'araso,ta zauna cikin d'aya daga cikin kujerun falon ta na gaishe da matar


Matar ta na dariya ta ce"to! Ai ni ce zan gaishe ki,ina kwana?"


  Zubaida ta yi murmushi ta ce"lafiya lau,ya yaran?"


 Matar ta ce"ga su nan k'alau"


Zubaida ta ce"amm...mak'obciyar ki ce, gidan da ya ke kallon naki"


"Ayya! Gidan Alhahi Sunusi ko? Sannu da zuwa"


Matar ta fad'a, ta na tashi,ta d'akko mata abin sha ta ajiye a gaban ta.


  Nan dai su ka sha firar su,Zubaida ta na ta yiwa yaran wasa,sai da sha biyun rana ta yi sannan ta koma gidanta,sai ta ji ta rage damuwa sosai ta ji dad'in zama da matar,sai ta ji sha'awar haihuwa ko ba komai yaran za su d'ebe mata wata kewar.


   Washegari ma haka ta koma gidan,su ka sha firar su,sun saba sosai,duk Alhaji bai san wainar da a ke toyawa ba,tunda da safe ta ke zuwa.Sai wata rana da har ya fita sai kuma ya ji ba ya jin dad'in jikinsa,hakan ne ya sa shi dawowa gida saboda ya kwanta,ya na shawo kwanar layin ita kuma ta na k'ok'arin shiga gida,da gudu-gudu ta afka,kamar za ta tashi sama ta shige d'aki ta na fatan bai ganta ba


  Ba k'aramin mamaki Alhaji ya yi ba,na ganin Zubaida ta dawo daga waje,da sauri ya k'araso cikin 'bacin rai ya kalli Tiger ya ce"kai! Dama matata ta na fita ko yau ta fara?"


  Tiger ya ce"eh,Alhaji ai kullum ta na fita,na yi zaton ma da sanin ka".


 Alhaji ya ja tsaki ya ce"ka san inda ta ke zuwa?"


 Tiger ya ce"e...to,ranar farko dai bayan ta fita na lek'a,sai na ga nan gidan me kallo wannan ta shiga".


  "To ka bud'e kunne da kyau ka ji! Daga yau kar ka sake barin ta,idan kuma ta sake fita wallahi sai na yi shari'a da kai!"



 Cikin rawar jiki Tiger ya ce"a yi hak'uri Alhaji,ba zai ma faru ba".



  Ya na shiga falon ya tadda Zubaida kwance a falo ta na baccin k'arya,kallon ta ya yi na sakanni ya yi guntun tsaki ya wuce


Zubaida ta tashi,ta na murmushin k'arfin hali ta ce"Alhaji sannu da zuwa,lafiya kuwa ka dawo da wuri haka?"


  Ko juyowa bai yi ba,bari ya kula ta


 Ta bi shi d'akin nasa ta na cewa"ga shi ban d'ora girki ba,me za ka ci?"


 Juyowa ya yi rai a 'bace ya nuna mata k'ofa alamar ta fita.


  Ta fita cikin sanyin jiki kamar za ta yi kuka.Kitchen ta shiga ta d'ora girki ta na ta tunanin mafita a kan zaman ta da Alhajin,sam ta rasa inda auren su ya dosa,sai kace wanda a ka yi wa auren dole?


  

  Ta na zaune a kan abin sallah bayan ta idar da sallar la'asar ta ji fitowar shi


"Alhaji ga abinci a dining" Ta fad'a ta na tasowa


Bai kalli inda ta ke ba,ya je ya bud'e k'ofar falon ya fita,bai jima ba ya dawo hannun sa rik'e da leda,mik'a mata ya yi ya na cewa"ki saka ki fito ki sameni a mota".


Da rawar jiki ta kar'ba,sai ta ga lik'ab ne a ciki da k'aton hijjabi,haka ta zumbula ya rufe ta ruf,don ko k'afarta ba a gani,ta d'aura lik'ab d'in ta fito.Shiga motar ta yi ya ja su ka fita,ta so tambayar sa inda za su je,amma ganin yanda ya had'e rai ya sa ta yi shiru


 Tafiya kad'an su ka yi ta ga ya yi fakin a wani wurin siyayya,ta fito ta na rarraba ido ta cikin nik'abin.



   "Ki duba ki d'ebi abin da ki ke so,kin tsaya ki na kalle-kalle kamar y'ar k'auye".


  Ya fad'a ya na yin gaba.


 Zubaida ta tsaya ta na bin wurin da kallo,saboda ta ga kusan a kwai komai a gidan,sai ta rasa abin da za ta d'auka,ta shiga kwasar kayan ciye-ciye.


  Tsaki ya ja ya na kallon ta da takaici ya ce"malama koma mota,kafin ki sa na ji kunya,y'ar k'auye kawai!"


Sim sim ta fita daga wurin,ta koma mota ta zauna,ta na jin haushin yarfin da ya ke yi mata


  Ba a jima ba ya fito, tare da ma'akaitan wurin,da su ka rik'o masa manyan ledoji,bayan sun zuba a both ya ja motar su ka tafi.


 

  Mamaki sosai ta yi na irin uban kayan da ya zabgo mata,kayan sawa kala-kala,kayan kwalliya turaruka,mayuka,babu abin da ya bata takaici kamar takalmi da jaka da ta gani har kala biyar


Cikin zuciyarta ta ce"ko uban me zan yi da takalmi da jaka oho!"


  Ta na nan zaune ta na kallon kayan,ya shigo d'akin nata,envelop ya ajiye mata ya yi ficewar sa.

[8/29, 8:42 PM] Mai Zafafa: *GAJEN HAK'URI*

 



BY

    *SADIYA ABDUL(Mai zafafa)*



*☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️*



  *Mom Asad  ga kyautar shafi guda Alhaji ya ce na baki,ke kad'ai*👌🏻



SADAUKARWA GA K'UNGIYATA😘



PAGE   13




    Da sauri ta d'auki envelope d'in ta bud'e, hannunta har karkarwa ya ke yi.Saranda ta yi ta saki baki da mamaki ganin abin da ke ciki,ta bi kud'in da kallo ta na sakin murmushin da ba ta san ya kufce mata ba,a iya rayuwarta ba ta ta'ba zaton za ta samu irin mijin da zai dinga d'aukar kud'i masu nauyi haka ya na bata ba,ta so a ce Alhaji ya na da halayya irin ta Musa tsohon mijinta,da kuwa tabbas ta gama dacen miji,ga kud'i ga kula da soyayya.


  Adana su ta yi,ta shiga wanka ta na jin farinciki har cikin ranta.Bayan ta fito ta ci kwalliyar ta cikin irin shigar da ya ce ya fi so,don a ganinta ya fad'a ne kawai don ya ji dad'in bakinsa,tunda ina ma ya zauna a gidan bare har ya ce zai wani za'bawa matarsa kayan da za ta saka? To ko ya na gidan ma ita fa ba ta ga wani kallon ta da ya ke ba,ta na sakawa ne kawai saboda umarni


  A falo ta tadda shi ya na kwance ya na danna waya,har da canza tafiya kafin ta k'araso inda ya ke


"Sannu da hutawa Alhaji" Ta fad'a ta na zama a kujerar da ta ke kallo tasa.


  "Yawwa" Ya fad'a ya na tashi zaune.


Ya kalle ta na sakanni kafin ya ce"a kwai wani abun ne?"


  Zubaida ta yi wani murmushin d'aukar hankali ta ce"e...dama godiya na zo na yi maka,Allah ya saka da alkhairi ya k'ara maka bud'i"


"Ameen" Ya fad'a ya na janyo laptop d'insa.


 Zubaida ta d'an matso dab da kujerar sa ta wani karya harshe ta ce"um...Alhaji idan ba za ka damu ba,don Allah zan rok'e ka wata alfarma ne"


 "Ina jinki" Ya fad'a ya na maida hankalin sa a kanta.


 "Dama cewa zan yi,da zaman kad'aicin nan da na ke yi,me zai hana ko da y'ar aiki ce ka samo min? Ka ga zan d'an rage zaman shirun,ko ba komai zan dinga jin motsin ta,ina ganinta?"


 

 Lokaci d'aya ya sake murtuke fuska,ya maida hankalin sa a kan laptop d'in sannan ya ce"idan aikin gidan ne ya yi miki yawa sai ki fad'a a canza miki gidan?"


 Ta ce"a'a,shikenan Alhaji"


Ta na fad'ar haka ta mik'e ta ce masa"sai da safe"


 "Ki shiga d'akina,ki jirani" Ya fad'a ba tare da ya kalleta ba.



  Ba ta ko juyo ba,ta shiga d'akin nasa ta kwanta ta na jin wani bak'inciki a cikin ranta.




  Washegari bayan Alhaji ya fita,kamar kullum ta fara shirin fita ita ma,har da d'aukar leda ta zuba alawowin da ta za'bowa Humaira jiya,wai za ta kai mata.Kanta tsaye ta doshi bakin get d'in,ba tare da ta kalli inda me gadin ya ke ba,har ta ta'ba k'ofa ta ji ya ce"Madam oga ya ce daga yau kar na sake bari ki fita"


  Zubaida ta ji wata fad'uwar gaba ba kad'an ba,don duk a zaton ta jiya Alhajin bai ganta ba,shi ya sa bai yi mata maganar ba,ashe ya ganta basarwa kawai ya yi


  Ta wani had'e rai a k'ok'arin ta na nuna masa bai isa ya bata umarni ba,ta d'ora hannunta a kan k'ofar ta ji ya ce"kee! Wallahi ki ka ta'ba k'ofar nan sai na had'a ki da kare"



  Ya na fad'ar haka ya bar wurin.


  Tsaki ta ja,ta na jinjina rainin hankali irin nasa,ta na bud'e k'ofar ba ta kai ga fita ba kuwa ta jiyo haushin kare,juyowar da za ta yi ta hango karen ya na tunkaro ta,ta zaro ido ta k'walla k'ara,don ba k'aramin tsoron karen ta ke ba,ganin haka ne ya sa Tiger yi wa karen magana sai ya tsaya da tunkarar ta d'in



   Zubaida da ta fara wata sand'a cikin fargaba,k'irjinta sai dukan uku-uku ya ke yi, ta na ganin ta wuce inda su ke ta tattare doguwar rigarta ta kwasa a guje,ta na shiga falon ta kwanta a nan k'asa ta na sauke numfashi,sai kuma ta fashe da matsanancin kuka


Ta fara magana cikin kukan"wannan wace irin rayuwa ce na ke yi? Anya wannan abin da Alhaji ya ke yi min so ne kuwa? To gaskiya na gaji,wallahi ka dawo a yi wadda za a yi!"



  Haka ta yi wunin ranar cikin k'unci da takaici,kuma ta gama yanke hukuncin k'watarwa kanta y'anci.Ta na zaune a falo ta na sak'a da warwara har k'arfe goma sannan ya dawo,ko kallon shi ba ta yi ba sai da ya wuce ta bi bayan shi,ya na zaune ya na amsa waya ta same shi,don haka ta nemi gefe ta zauna had'i da 'bata rai.


  Ya na gamawa ya tashi ya fara k'ok'ari cire kaya,ba tare da ya kalli inda ta ke ba.


"Ina son magana da kai" Ta fad'a ta na kallon gefe.


  Ya zauna gefen gadon ya ce"ina jinki".


 Zubaida ta aro dauriya,ta danne tsoron da ya ke shirin yin tasiri a zuciyarta ta ce"idan ka na lissafi yau wata na biyar kenan a gidanka,don haka a cikin satin nan na ke so na je gida".


  Alhaji ya ja wani dogon tsaki,ya tashi ya shiga wanka ba tare da ya kuma kallon inda ta ke ba.Wani takaici ya turnuk'e Zubaida,don haka ta tashi ta d'auki wayarsa da ke kan gadon ta fice daga d'akin,ta na shiga d'akinta ta saka mukulli ta kulle ta nemi gefen gado ta zauna ta na share hawaye.


  Danna wayar ta yi,da nufin ta nemi number mahaifinta,ta fad'a musu halin da ta ke ciki,amma sai ta ga wayar da password, ta ji wani sabon takaici ya kuma rufe ta,ta wulla wayar kan gadon ta kwanta ta fashe da kuka me cin rai.



  Turus! Alhaji ya yi da mugun mamaki,ganin bai ga wayarsa a inda ya ajiye ta ba,kai tsaye d'akin Zubaida ya nufa ya k'wank'wasa k'ofar cikin fushi.Ta na ji ta yi banza da shi don wani mugun haushin sa ta ke ji,ya kai kusan minti goma sha biyar ya na jiran sunanta tare da k'wank'wasa k'ofar,amma ba ta ko motsa daga inda ta ke ba


Iya 'bacin rai yau Alhaji ya kai mak'ura,don haka ya je ya dubo inda sauran mukullan su ke,amma sai dai kash! Babu na d'akin nata,su na cikin d'akin,haka ya koma d'akinsa ya kwanta zuciyarsa na tafarfasa,bacci kad'an ya yi a ranar saboda 'bacin rai.


  A 'bangaren Zubaida kuwa kashe wayar ta yi ganin ba za ta yi mata amfani ba,ta yi kwanciyar ta,ta na jin wani kaso na damuwar ta ya tafi,tunda ta san ta k'untata masa shi ma.



 Washegari ta d'akko wayar ta zo ta ajiye ta a falo,wai idan ya fito ya d'auka,kitchen ta shiga kai tsaye ta fara had'a abin da za ta karya da shi. Fitowar Alhaji don neman ta yanda zai samu wani mukullin ta yi daidai da fitowar ta daga kitchen, hannunta d'auke da kofi da farantin indomi,cak ta tsaya hannunta ya fara karkarwa nan take tsoro ya dira a zuciyarta,ganin tsantsar 'bacin rai a fuskar Alhajin



  Daurewa ta yi,ta zo za ta wuce ta gabansa,ba tare da ta bari sun had'a ido ba,k'irjinta na tsananta bugu.Ta na zuwa daidai inda ya ke ya fizgo ta har kayan hannunta su ka zubo musu a jiki ita da shi d'in,bai damu da zafin da ya ji ba,ya d'aga k'aton hannunsa ya sharara mata wani gigitaccen marin da ya dakatar da jinta na tsawon minti biyu.


  Cikin wata murya da ke nuna tsantsar 'bacin rai ya ce"ina wayata?"


  Zubaida da bakinta ya gaza ba ta had'in kai wurin bud'uwa,da hannu ta yi masa nunin inda ta ajiye ta,ta na karkarwa.


 

 Alhaji ya war'bar da ita ta fad'i a gefe,ya d'auki wayarsa ya koma d'aki.Har ya yi wanka ya fito ta na nan kwance a inda ya barta,sai dai ya na jiyo sautin kukanta a hankali hakan ne ya tabbatar masa ba suma ta yi ba, kallo d'aya ya yi mata ya wuce,ya fita daga gidan.


   

  Sai da ta shafe awa biyu kafin ta bawa kanta hak'uri,ta tashi daga wurin kai tsaye d'akinta ta shiga,ta yi wanka ta dad'e ta na kallon kanta a mudubi kafin ta shirya ta d'akko babban akwati ta shiga loda kayanta a ciki,sai da ta saka komai da ta ke ganin za ta buk'ata sannan ta d'auki hijjabi ta saka ta d'akko kud'in jiya da ya bata ta janyo akwatin ta fito.



Duk da ta na mugun tsoron Tiger da karen da ta gani jiya,amma hakan bai hana ta tunkarar shi ba.Tiger ya na hango ta ya had'e rai,duk da dai ya cika da mamakin ganinta da akwati


  "Sannu" Ta fad'a gabanta na fad'uwa,don ita ta kasa gane shi d'in musulmi ne ko arne



 "Yawwa,Madam ya a ka yi?" Ya fad'a ya na kallon akwatin.


  "Garin mu zan tafi,Alhaji ne ya sakeni" 


Ta yi maganar ta na share k'wallar da ta zubo mata.


  Tiger ya d'an kalle ta ya na nazarin ta,kafin ya ciro wayarsa daga aljihu ya ce"to ki tsaya na tambayi Alhaji na ji gaskiyar magana"


  

Ganin ya fara danna wayar Zubaida ta ce"a'a don Allah ba sai ka kira shi ba,bar shi, tsaya mu yi magana"



"Ina jinki" Ya fad'a ya na mayar da wayar aljihu.


 Zubaida ta zaro rabin kud'in ba tare da ta k'irga ba,ta mik'a masa ta na cewa"ba saki na ya yi ba, gajiya na yi da zaman,ka kar'bi kud'in nan don Allah ka bud'e min na fita".


  Tiger ya kalle ta da tausayi ya ce"a'a Madam,ni ba zan ci amanar Alhaji ba,domin na san ba ni da riba,ki koma ki cigaba da hak'uri har Allah ya kawo miki mafita".



  Babu irin magiyar da ba ta yi masa ba amma ya ce shi magana d'aya ya ke yi,ba zai bud'e mata ba


Ganin haka ne ya sa ta cewa"to don Allah ka kar'bi kud'in nan ka siyo min waya da sim card"


 

Tiger ya d'an yi nazari kafin ya kar'ba ya ce"to zuwa gobe sai na kira k'anina ya zo ya siyo,amma kar ki cewa Alhaji ni ne,don na ji tausayin ki ne kawai zan yi miki wannan taimakon".


Zubaida ta ce"ba zan fad'a masa ba,na gode sosai Allah ya saka".



  Ta ja akwatin ta ta koma gida ta kwanta ta na share k'walla.

[8/29, 8:42 PM] Mai Zafafa: *GAJEN HAK'URI*

 



BY

    *SADIYA ABDUL*

_(Mai zafafa)_



*☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️*



SADAUKARWA GA K'UNGIYATA😘



PAGE   14



  

   Washegari a ka siyo mata wayarta babba har da sim da memory,ta yi farinciki ba kad'an ba,tuni ta had'a ta ta saka caji a d'akinta.


  Bayan ta cika sai ta kunna ta shiga tunanin yanda za ta tuno number mahaifiyar ta ko a idonta ne,amma ta kasa sai ta fara hawaye ta na nadamar rashin damuwa da haddace number. Haka ta yi tsawon kwanaki uku ba tare da ta samu mafita ba,Alhaji kuwa tun daga ranar da ya mare ta bai sake ganinta ba,don kullum ta na d'aki a kulle,ganin idan ya shiga kitchen ya na ganin alamar an yi girki shi yasa bai damu ba,ya san k'alau ta ke,watak'il ta yi fushi ne,sai kuma  ta d'an bashi tausayi,amma ya share a k'ok'arin sa na nuna mata kuskuren ta.


  Rana ta hud'u ne ta je d'akinsa ta fara k'wank'wasawa bayan ta ji shigowar sa gidan,ya ce"a bud'e ta ke ki shigo mana"


  Ta turo k'ofar ta shigo jiki a sanyaye,kallo d'aya ya yi mata ya kauda kai,ta zauna gefe ta ce"dama so na ke na gaisa da mahaifiya ta"


  Bai ce komai ba ya d'akko wayarsa a kusa da shi ya daddanna ya mika mata,ta kar'ba hannunta na karkarwa,so ta ke ta kalli number sosai,don haka ta k'aro k'arar wayar su ka gaisa ba tare da ta saka wayar a kunnen ta ba,kallon number kawai ta ke yi,ba su jima ba ta katse kiran ta mik'a masa wayarsa,sai ya kar'ba ya bita da kallon tausayi ganin duk d'ari-d'ari ta ke yi da shi.


  Da sauri ta koma d'akinta,ta saka sakata tare da d'aukar wayarta,da kyar ta samu ta saka number Umma don kuwa da ido ta haddace ta ba da zuciya ba, ta danna kira cikin fargaba,lokaci d'aya kuma gabanta ya bada rass! Ta sulale ta zauna tunowa da ai babu kud'i a wayar,sai ta katse kiran ta kwanta lamo.


  Washegari bayan ya fita sai ta zari dubu d'aya ta fito don aiken Tiger ya siyo mata kati,a zaune ta tadda shi ya na cin abincin da ya siyo a waje,cikin d'ari-d'ari ta k'arasa ta ce

"sannu".


Ya ce" yawwa Madam,ai dai wayar babu matsala ko?"


Zubaida ta ce"e,k'alau ta ke,amm...kati za ka siyo min zan yi kira".


 Ya d'an yi shiru na d'an lokaci,ya na nazari don ya fara tunanin wata rana fa za ta iya aiken sa ta gudu daga gidan,sai ya kar'bi kud'in ya ce"to bari na yi waya a kawo kin san ba na fita ko ina,idan an kawo zan mik'o miki".


 Zubaida ta yi godiya ta ba shi kud'in ta koma cikin gida.Bayan ta koma Tiger ya fita ya siyo mata katin ya k'wank'wasa k'ofar ta kar'ba ya koma bakin aikinsa.


  Har ta na karkarwa ta saka katin,ta fara kiran number Umma,ta na shiga ta d'aga da sallama,Zubaida ta ji wani farinciki sai ta fashe da kuka,Umma ta tashi tsaye cikin firgici ta ce"Zubaida ce?"


"Ni ce Umma" Ta yi maganar cikin kuka.


  Umma ta ce"to kukan me ki ke yi? Ko dai mijin naki ne wani abun ya same shi?"

  

Ta ce"a'a,wallahi Umma na gaji da auren sa,tahowa gida na ke son yi kuma ya hanani"


 Cikin tashinkanli Umma ta fara magana"ashe ba ki da hankali? Ko dan ba ki san irin hidimar da ya ke yi mana ba? Har fa gidan ya sa a ka rushe ya siyi gidan marigayi malam Idi ya had'e a ka tamfatsa mana gini.Ke bari ki ji Alhaji bai tsaya  a nan duk wata sai ya zo da kansa ya gaishe mu ya kawo mana kayan abinci, har da kud'in cefane,idan ba ki gode masa ba ai kuwa ba za ki butulce masa ba!"


  Zubaida ta ji kamar an zare mata laka,lallai Alhaji ashe ya san ya siye iyayen ta,shi ya sa ya ke mata abin da ranshi ya so


Ta na cikin tunanin ta kuma jin muryar Umma ta na magana cikin fushi"to wallahi ki san abin da ki ke yi Zubaida,shi zawarcin abin so ne? Ko kuma kin san gidan da za ki fad'a idan kin fito daga nan d'in?"


Zubaida ta kashe wayar ba tare da ta bata amsa ba.Nan ta zauna ta na ta kuka kamar hawayen ta zai k'are,ita yanzu Hafsa kawai ta ke son samu ko ta waya ne,ta san ita ce kawai za ta bata shawara me kyau,haka ta yi wunin ranar damuwa fal zuciyarta.



    Tun daga ranar kullum sai ta kira Umma a waya sun gaisa,amma ba ta kuma yi mata zancen matsalar Alhaji ba.Mu'amular ta da shi ta sake yin baya sosai,don yanzu sai ta yi kwana uku ba ta saka shi a idonta ba,idan kuwa ta san ranar Lahadi ne da ya ke wuni a falo,tun ranar Asabar ta ke d'ibar abin da za ta ci ta shige d'aki ,ba ta fitowa gabad'aya ranar,bare ya saka ran za ta yi girki.


  Yau ma ta kama ranar lahadin,tun safe ya ke zaune a falo ya na aikinsa a laptop, lokaci-lokaci sai ya kalli k'ofar d'akinta ko za ta fito,amma har izuwa yanzun k'arfe biyu da rabi ba ta fito ba,lemo kawai ya ke korawa ya na mamakin sabon halinta.


  Wannan watan ma,haka ya yo mata siyyayyar uban kaya, har da lesuka da atamfofi,kuma ya bata kud'i kamar wancan watan.Ta'be baki ta yi bayan fitarsa ta na bin bayan sa da harara.


  Yau haka kawai ta ji ta na sha'awar ta fara chatting, saboda haka ta fito don ta tambayi Tiger ko ya na da WhatsApp ya tura mata,turus ta yi ganin babu kowa a wurin zaman shi,ga kuma k'ofar d'akinsa a kulle,sai ta yi tunanin ko ya shiga band'aki ne,har ta tsaya jiran fitowar sa,sai kuma ta zaro ido lokaci d'aya ta kwasa da gudu ta koma cikin gidan,kai tsaye d'akinta ta shiga ta janyo k'aramar akwati ta zuba kaya kala uku a ciki,ta d'auki kud'inta da wayarta ta zuba a jaka ta saka hijjabi ta fito cikin sauri.


  

  Sai dai kash! Ta na fitowa ta hango Tiger zaune ya na cin abinci,ta yi saurin komawa ta na dafe k'irjinta,ta fara hawayen takaici,sai yanzu ma ta fara tunanin inda Tiger ya ke samun abinci, tunda ta san ba ta bashi.


"To kenan fita ya ke ya na siyowa?"

Ta yi wa kanta tambayar.


  Sai ta jijina kai ta na murmushi.



Washegari haka ta zo windon falo ta zauna tun safe,har sha biyu ba ta ga ya fita ba,don haka ta tashi ta shiga kitchen ta yi girki mai sauk'i ta ci ta yi sallah.Ta na idar da sallah ta dawo ta zauna ta cigaba da lek'e,k'arfe biyu daidai ta ga ya fita daga gidan,ai kuwa ta duro daga inda ta ke,ta shiga d'aki cikin sauri ta d'auki akwatin ta saka hijjabi ta fito,gabanta na tsananta fad'uwa.


  

  Wata ajiyar zuciya ta sauke bayan ta fito daga gidan, sai ta fara waige-waigen ta inda za ta bi,cikin sa'a ta ga mak'obciyar ta ta fito a mota tare da mijinta.Ta d'aga musu hannu alamun su tsaya,su ka tsaya ko gaisawa ba su yi ba ta ce"maman Humaira don Allah ku sauke ni a hanya"


  Ta ce"to shigo"


Zubaida ta shiga ta na sauke ajiyar zuciya,bayan sun gaisa mijin maman Humaira ya ce"ta ina za ki bi?"


 Ta ce"kawai idan an fita titi zan sauka,tasha zan je"



  "Ganin gida za ki je?" Maman Humaira ta tambaya


  "E wallahi" Zubaida ta amsa da saurin ta.



  Baban Humaira  ya yi mamaki,saboda ya san irin arzik'in mijinta, amma bai ce komai ba,ya kai ta har tashar,sai da ta shiga ya biya mata kud'in mota sannan su ka tafi inda za su je.


  Zubaida ta dinga hamdala a zuciyarta ganin direba ya d'auki hanya.Sai kuma ta saki murmushi da ta tuna yanda za a kwashe tsakanin Tiger da Alhaji.

[8/29, 8:42 PM] Mai Zafafa: *GAJEN HAK'URI*

 



BY

    *SADIYA ABDUL(Mai zafafa)*



*☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️*



SADAUKARWA GA K'UNGIYATA😘



PAGE   15





     "Assalamu alaikum". Zubaida ta yi sallama cike da zumud'in ganin gida, ba dan Umma ta kwatanta mata yanda a ka maida gidan nasu ba,da bai zama lallai ta gane shi ba,saboda yanda ya yi kyau sosai duk ya haska unguwar.


 Umma da ke zaune ta na daka yaji,ta tashi da sauri har ta na yarda ta'barya ta washe baki da fad'in" muryar wa na ke ji kamar Zubaida?"


 "Ni ce Umma" Ta amsa da farincikin da ya kasa 'boyuwa.


 Umma ta ce"amma shi ne babu sanarwa? Ina shi Alhajin,ko ba shi ya kawo ki ba?"


 Lokaci d'aya fara'ar fuskarta ta d'auke ,ta ce"ni fa bai san na taho ba,ai dama na fad'a miki na gaji,kuma wallahi idan kun ga na koma gidan Alhaji to a can ajalina ya ke"


 Ta na fad'in haka ta yi shigewar ta d'aki.


Umma ta koma kujerar ta zauna ta na jin fad'uwar gaba,lallai sai yau ta san Zubaida ba ta da hankali,yanzu ya za su yi da wannan lamari da ta ke son 'bullowa da shi,jiki a sanyaye ta k'arasa ta zuba abinci a kwano ta shiga d'akin da Zubaidar ta ke ciki.


  Zaune ta tadda ta,ta na game a waya babu wata damuwa tare da ita.Umma ta zauna ta ajiye mata kwanon ta na kallonta ta ce"ci abinci sai mu yi magana".


 Zubaida ta ce"a k'oshe na ke Umma,sai dai zuwa dare"


 Umma ta ce"meye dalilin dawowar ki gida? Kuma meye amfanin sa?"


 Zubaida ta ce"Umma ai na fad'a miki tun a waya,wallahi na gaji ba zan iya irin rayuwar da mu ke yi da shi ba,shi kwata-kwata fa bai san meye rayuwar auren ba,na gaji gaskiya".


  Umma ta ce"amma dai ai ya na baki ci da sha ko?"


"Sosai"  Ta amsa a tak'aice.


 Umma ta gyara zama ta ce"to kuwa babu abin da zai hana ki komawa gidansa,ai yanzu rayuwa ba za ka ta'ba cewa sai abin da ka ke so za ka samu ba,ba zai yiwu ba,a zamanin nan in har namiji ya baki ci da sha to ko babu sutura ki zauna kawai..."


Zubaida ta katse Umma da fad'in"a'a fa Umma,ni ma a da na yi zaton haka ne,amma yanzu kam na fahimci ba ci da sha da sutura ne kwanciyar hankali a aure ba gaskiya".


 Umma ta yi shiru ta na nazari,idan ta fahimce ta dai kamar Alhajin ba ya iya biya mata buk'ata ne,shi ya sa ta gaji,sai ta rasa ma me za ta fad'a mata kawai ta tashi ta fita.


 Zubaida ta kwanta ta na fad'in"za ku yi ku gama,amma wallahi babu tsautsayin da zai maida ni wannan bak'ar rayuwar".




    Koda Tiger ya dawo daga siyan abinci, sam bai ga wata alama da za ta nuna masa Zubaida ta fita ba,don haka ya cigaba da aikinsa hankali kwance.



 K'arfe goma da rabi na dare Alhaji ya dawo gidan,dama ya san ba zai same ta a falo ba,don haka ya yi shigewar sa d'aki.



  Da daddare haka mahaifinta ya saka ta a gaba da tambayar dalilin ta,shi ma ta fad'a masa ta gaji ne,kuma ta tabbatar masa ba za ta koma ba,nan ya hau ta da fad'in ya na fad'in dole ta koma tunda dai ba sakinta ya yi ba,don haka duk ranar da ya zo sai ta bishi sun koma,Zubaida ta shige d'aki ta dinga kuka,ta na me jaddada k'udurin ta na barin auren Alhajin.


  

Washegari ma da safe bai ji motsin ta ba,kuma bai bincika ba ya yi ficewar sa.Haka a ka dinga yi har tsawon kwana biyar,sai a na shidan ne ya san ba ta gidan


  Ranar Asabar ne bai fita aiki ba,ya fito falo zai zauna kan kujera,sai ya lura kamar da k'ura a kujerar,ya d'an yi mamaki,amma sai ya bar shi a duk cikin fushin ne ya sa ta daina gyara gidan, ya goge ya zauna ya na ta aikinsa,tun sassafe ya ke zaune amma bai ga ta fito neman abin kari ba,har a ka kira azhar,shi kad'ai ya dinga mamaki,ya je d'akinsa ya yi sallah ya dawo falon, shiru dai ba ta fito ba ya na nan zaune a ka kira sallar la'asar,ya je ya yi ya dawo amma Zubaida shiru, sai ya fara tunanin to ita ba za ta ji yunwa bane? Don haka ya yanke shawarar lek'ata ya gani.


  Ya na tura k'ofar d'akin ta bud'e,sai ya ga babu kowa ya yi zaton ko ta na band'aki ne,sai ya shiga d'akin a karo na farko tun zuwanta gidan,ya zauna gefen gado ya na jiranta


"Anya kuwa ina yi wa yarinyar adalci? Ta dinga rayuwa ita kad'ai alhalin da ba ta saba da hakan ba?"


  A zuciyarsa ya fara wannan maganar,cak! Ya tsaya da tunanin sakamakon hango kwalin waya a kan mudubi. Ya tashi da sauri ya je ya d'auka ya na jin fad'uwar gaba,kai ya jinjina ya na kuma tabbatar da rainin da ta yi masa.


  Ya bud'e kwalil wayar da sauri,sai ya ga babu wayar a ciki,ya d'auki takrdar ciki don ya duba ranar da a ka siyi wayar,kwatsam sai ya ga sunan Tiger a matsayin wanda ya sayi wayar.Don a lokacin sunan sa a ka saka,tun da shi dai bai san sunan Zubaidar ba.


  

  K'irjin Alhaji ya bada ras! Tuni wani mugun 'bacin rai ya turnuk'e shi,ai kuwa ya je ya fara bugun band'akin da k'arfi,amma ya ji shiru babu ko motsin ta,ganin za ta 'bata masa lokaci ne ya sa shi bud'e k'ofar, ga mamakin sa sai ya ga wayam babu ko alamar ruwa ya zuba a yau,cikin mamaki ya fito daga d'akin ya fara lek'a ko ina ya na dubawa amma babu alamun ta,daga k'arshe dai Alhaji har k'ark'ashin gado da cikin sif ya duba babu Zubaida babu alamar ta.


Alhaji ya fara gumi gabansa ya na fad'uwa,karo na farko da ya ga laifinsa na hanata rik'e waya,da tuni yanzu ya kirata ya ji inda ta ke.


  Sai ya nufi wurin Tiger rai 'bace


"Barka da fitowa Alhaji" Tiger ya fad'a ya na mik'ewa.


  Alhaji bai bi ta kan gaisuwar sa ba ya ce"kai ina matata!?"


 K'irjin Tiger ya bada wani dumm!  Cikin inda-inda ya ce "Alhaji ai ba yanda za a yi na san wannan amsar"


 Kafin ya rufe baki Alhaji ya wankesa da wani wawan mari ya ce"ina ka kai min matata!?"


  Tiger ya fara zare ido,izuwa yanzun ya fahimci abin da Alhaji ya ke nufi,lallai Zubaida ta shammace sa ta gudu kenan?


"Alhaji a min afuwa,wallahi ban san lokacin da ta fita ba". Ya yi maganar jikinsa na rawa.



  "Wallahi da sa hannunka a 'batan ta,tun da na ga har waya ka siya mata!" Alhaji ya fad'a ya na dank'o wuyan rigarsa.



  Tiger fa ido ya fara raina fata,cikin rawar murya ya ce"Alhaji mu zauna zan yi maka bayanin gaskiya".


  Alhaji ya sakesa ya na yi masa mugun kallo


Tiger ya kwashe duk yanda abin ya faru ya fad'awa Alhajin,kuma ya d'ora da fad'in shi bai san ba da sanin Alhajin a ka siyo wayar ba.


 "To uban me ka ke yi ta fita daga gidan nan?" Cewar Alhaji cikin 'bacin rai me tsanani.


Tiger ya ce"babu mamaki na fita siyo abinci lokacin,don Allah a yi hak'uri, tsautasyi ne".


Ya yi maganar ya na wani karya wuya,wai a dole ya ji tausayin sa.


  "Ubanka kai da tsautsayin! Cin abinci ka zo yi ko aiki?"


Alhaji ya yi maganar ya na k'ara sauke masa wani marin.


  Tiger dai ya yi shiru babu bakin magana,Alhaji ya nuna masa wuri ya ce"zauna a nan! Idan na kira waya a ka tabbatar min ba ta je gida ba,to wallahi kai ne ka sace ta,kuma sai ka fito da ita ko uwarka za ka je ka siyar!".



   Tiger ya zauna gumi na karyo masa,har k'walla ta cika idonsa.Alhaji ya kira wayar Umma,bayan sun gaisa ya ce"Zubaida ta na kusa?"


Umma ta ce"e,bari na bata"


  Sai ya sauke wata ajiyar zuciya,ya na nunawa Tiger hanyar fita.Ai kuwa ya tashi cikin sauri,ya shiga d'akin ya tattaro kayan sa ya zo ya fice,ya na tsinewa Zubaida a cikin zuciyarsa.



   Umma ta mik'e mata wayar ta ce"ga mijinki nan".


 Ta wani had'e rai sannan ta yi sallama. 


Ya amsa ko gaisawa ba su yi ba ya ce"me ya fitar da ke daga gida?"


"Gajiya na yi da zaman gidan,kai ba ma iya zaman gidan har da auren ma ya isheni haka".


 Alhaji ya jinjina kai ya ce" haka ne?"


 Ta ce"tabbas!"



  Cikin takaici ya ce"ke da kin san kin gaji,amma shi ne ki ka kasa fad'a min tun tuni?"


Ta yi shiru ba ta ba shi amsa ba.


  Ya ce"to yanzu me ki ke buk'ata?"


"Ka sakeni" Ta fad'a a dake.



  "Na sakeki saki d'aya" Ya fad'a ya na kashe wayarsa.

[8/29, 8:42 PM] Mai Zafafa: *GAJEN HAK'URI*

 



BY

    *SADIYA ABDUL(Mai zafafa)*



*☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️*



SADAUKARWA GA K'UNGIYATA😘



PAGE   16





     Zubaida ta bi wayar da kallo gabanta na fad'uwa,don ba ta yi zaton Alhaji zai iya rabuwa da ita tafarat d'aya ba, duk a zaton ta hankalin sa zai tashi ne,ya tambaye ta dalili,idan ta fad'a masa kuskuren sa sai ya gyara su fara rayuwa irin ta cikakkun ma'aurata,amma sai ta ji kai tsaye ya saketa.


"Da ma shi ma ya gaji da ke"  Zuciyarta ta fad'a mata.


  Sauke ajiyar zuciya ta yi ta ce"tabbas! Allah ya sa haka ne ya fi alkairi"


 Jiki a sanyaye ta fito tsakar gidan,ta tadda Umma ta na alwala,sai ta tsaya ta kasa magana.Umma ta kalle ta ta ce"kin gama? Ya ku ka yi?"


  Zubaida cikin jin nauyin maganar da za ta fad'a ta yi k'asa da kai ta ce"ya sakeni"


Umma ta wani zaro ido ta fara jero salati kafin ta ce"mun shiga uku! Kin gani ko Zubaida? Yanzu wa gari ya waya? Me ye amfanin zawarci?"


  Ita dai ta yi shiru ta kasa magana.Umma ta yi k'wafa ta kar'bi wayarta ta shige d'aki,da daddare bayan mahaifin ta ya dawo a ka sanar da shi,shi ma ya shiga damuwa sosai,ya yi ta surfa mata masifa ita dai ba ta ce k'ala ba,ta bi su da ido.


   Sati biyu da sakin Alhaji ya aiko da kayan Zubaida cike da manyan motoci,don har kayan gadon da kayan kitchen duk da shi ya siya amma sai da ya bar mata.Zubaida ta yi farinciki ba kad'an ba,don dama ta na ta tunanin ta yanda za ta samu kayan sawar ta,ita sam ba ta saka ran zai bata komai ba bayan na sawar


Da yake yanzu gidan a kwai wadatar d'akuna,sai a ka zuba kayan a ciki,da ta ce a siyar sai Umma ta ce ba za a siyar ba tun da ba su yi komai ba,idan ta tashi wani auren sai ta tafi da su.


  Sai da Zubaida ta yi wata d'aya a gida sannan Hafsa ta zo jajanta mata,ranar ta na kwance ta na baccin rana ta ji an d'aka mata duka,ta tashi ta na murza ido,sai ta saki murmushi ta na gyara zama saboda ganin Hafsa.


 Hafsa ta had'e rai ta na kallon Zubaida da ga sama har k'asa ta ce"wato har ma wani baccin rana ki ke iya yi ko?"


 "A ni kuwa me zai hanani baccin rana Hafsa? Wai sai yau ki ka samu labari ne?"


Zubaida ta yi maganar ta na hararar Hafsan.


Hafsa ta ta'be baki ta ce"wallahi tun ranar Alhaji ya sanarwa da mijina,takaici ne ya hanani zuwa,ke dai Allah ya shirye ki Zubaida"


 Zubaida ta ce"ke ba na son wulak'anci,me na yi da ki ke nema min shiriya?"


"Meye ma ba ki yi ba? Idan ban da wawiya waye zai Shiva cikin daula ya fito? Kai! Ke dai na rasa irin tunanin ki wallahi"


  Zubaida ta ce"to Hafsa ya ki ke so na yi? Wallahi wannan mutumin ya wuce zatonki,ni na rasa irin sa,kwata-kwata bai d'auke ni a bakin komai ba fa,wani irin zama mu ke yi kamar wanda a ka yi mana auren biyayya".


  Hafsa ta gyara zama ta ce"ba ya zama a gidan ne ko kuwa? A waje ya ke kwana?"


 Zubaida ta ce"a'a rana d'ai-d'ai ne ya ke kwana a wurin aiki"


 Hafsa ta ja wani dogon tsaki ta ce"kuma shi ne ki ka kasa daidaita shi?"


Zubaida ta ce"duk a bar tuna abin da ya wuce,don kin san Alhaji ba mayar da ni zai yi ba".


Hafsa ta ce"to yanzu nawa ne a cikin account d'inki?"


Zubaida ta ta'be baki ta ce"tabb! Ni ina na ga wani account? Ni da ko waya bai bar ni rik'ewa ba?"


Hafsa ta zuba tagumi da duka hannu biyu ta na kallon Zubaida ta ce"Allah ya yaye miki ciwon da ya sameki"


"Kamar ya? Wane irin ciwo?" Zubaida ta tambaya da mamaki.


 Hafsa ta ce"ciwon toshewar basira na ke nufi,da wauta da shirme da shiririta,wannan duk cuta ce Zubaida"


  Zubaida ta had'e rai ta ce"wai ke meye hakan? Ba na son irin haka"


  Hafsa ta ce"na ji,yanzu dai bani labarin zaman ku da Alhaji na ji irin kwamacalar da ki ke tafkawa".


 Tiryan-tiryan ta zayyane mata yanda zaman su ya kasance da Alhaji,da irin k'uncin da ta shiga na zaman kad'aici.Hafsa ta sauke ajiyar zuciya ta ce"gaskiya dole ki shiga damuwa"


"To kin gani? Ai rabuwar ita ce mafita"


Hafsa ta ce"gaskiya ki ni ce ba zan iya cigaba da irin zaman ba,amma takaici na d'aya da ba ki mallaki wasu kadarori ba,kamar Alhaji Sunusi amma ki tsaya sanya? Gaskiya Zubaida kin bani haushi"


Nan dai su kai ta fira har Umma ta zubo musu abinci,Hafsa ta ke fad'a mata ta na da cikin wata hud'u,Zubaida ta yi mata murna.Ta ce idan ta gama idda za ta zo su tattauna


Hafsa ta ce"ai dole mu yi zaman tattaunawa Zubaida kin ga yanda ki ka k'ara wani kyau kuwa? Wallahi yanzu talaka ma tsoron tunkarar ki zai yi,don yaro ma ya san matar auren sa!"


 Zubaida ta yi wani murmushin jin dad'i ta ce"Allah ko Hafsa?"


"Hmm! Zauna shiririta dai" Hafsa ta fad'a ta na tashi don tafiya.


  


    Lokacin da ta kammala iddarta sai yayanta ya zo mata da zancen abokinsa wai ya ganta ya na sonta,nan ta ke Zubaida ta ce  bai yi mata ba.


Nasiru da mamaki ya ce"tun kafin ki gan shi?"


"Ai na san ma ba zai yi min ba,ba dai abokin ka bane?"


Ba ta jira amsar shi ba ta shige d'aki.


Babu jimawa kowa ya san Zubaida, don yanda ta zama wata ajebo,ta na baza kalarta,samari kuwa sai tutuwa su ke yi,amma ba su ishe ta kallo ba,don yanzu wani ji da kanta ta ke,sutura iri-iri wanda da ba ta san tsadar su ba da ta na gidan Alhaji yanzu duk ta sani,shi yasa kanta ya ke kuma fashewa.


  A na cikin haka su ka had'u da wani mutumi a wani shopping mall,ya ce ya na sonta,ai kuwa ta aminci don da ganin shi ka san ba k'aramin mutum bane.


  Washegari ya zo gidan su,ya yi mata bayanin kan shi.Sunan shi Usman,ya na da mata da y'ay'a uku duk maza,dalilin da ya sa ya ke son k'ara aure,matar sa ba y'ar nan bace,y'ar Ghana ce wata rana ya je kasuwancin sa su ka had'u da ita,y'ar masu kud'i ce sosai kuma ita ma ta na mugun son shi,don har ta fi damuwa da shi


Sanda ta bayyana shi a matsayin wanda za ta aura sai iyayenta su ka ce ba ta isa ta auri d'an Nigeria ba, ita kuwa ta dage ta ce shi d'in ta ke so,idan ba su yarda ta aure shi ba za ta shiga duniya.Da k'yar su ka amince a ka yi auren su na matuk'ar jin tsanar sa.


 Bayan auren sai su ka fara samun matsala,saboda sam Fatima ba ta da kunya,ta tashi a sangarce shi kuma ba shi da hak'uri ko kad'an,don haka zaman nasu ba wani dad'i ya ke yi ba, duk da tsananin son da ya ke yi mata.A haka ta samu ciki wanda tun ya na k'arami mahaifiyar ta ta zo ta tafi da ita can Ghana har sai da ta haihu ta kusa yaye d'an sannan ta yarda ta dawo.


  Tun daga nan kuma Fatima ba ta sake zaman wata biyar a gidan mijinta ba,da mahaifiyar ta ta bushi iskar ta sai ta zo ta tafi da ita ,sai ta shafe watanni za ta dawo,har ta yi haihuwa uku.


Ganin ana tauyewa yaran karatun su ne ya sa shi tashi tsaye ya ce dole ta dinga barin su,idan ta tashi tafiya,sai da a ka kai ruwa rana sannan ta yarda ta bar yaran,ya kai su gidan mahaifiyar shi ta ke rik'e su,kuma ta takura masa sai ya k'ara yin wani auren, ba don son ranshi ba ya fara neman matar da zai aura,saboda son da ya ke yi wa Fatima ba ya son ya mata kishiya.


  Zubaida ta ji wani dad'i bayan ta gama jin labarin sa,don ta san ta na shiga idan ya gaji da iskancin Fatima sakinta zai yi,ita kuma ta mallake sa ita kad'ai.


  Ba da jimawa ba kuwa a ka saka ranar aure wata biyu kacal,tuni Zubaida ta fara shirye-shiryen aure sai wani rawar kai ta ke yi,ita za ta shiga gidan me mata.


Hafsa ma ta kuma k'arfafa mata guiwa,ta na fad'a mata ai ta na shiga zai saki Fatima,ita kuma ta kafa tata gwamnatin.

[8/29, 8:42 PM] Mai Zafafa: *GAJEN HAK'URI*

 



BY

    *SADIYA ABDUL(Mai zafafa)*



*☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️*



SADAUKARWA GA K'UNGIYATA😘



PAGE   17




     Yau ya rage saura sati biyu auren Zubaida da Usman,babu abin da ba ta yi ba na shirye-shirye,sai jiran lokaci kawai,sosai ta ke k'aunar Usman saboda irin mijin da ta ke fatan samu ne,gani ta ke kamar ma burinta na duniya ya gama cika. Kullum ita ta ke tashin shi da safe,ta hanyar kiran shi a waya,ta ce kar ya makara zuwa aiki,soyayya su ke sha babu kama hannun yaro.


  Yau su na zaune su na fira da Usman ,cikin sigar bugar cikinsa ta ce"ya anti Fatima kuwa? Allah ya sa dai za ta d'auke ni kamar matsayin y'ar-uwa,kamar yanda na d'auke ta,mu zama abu d'aya saboda mu baka cikakkiyar kulawar da ka ke buk'ata,hankalin ka ya kwanta"


  Usman ya ji wata nutsuwa da halin Zubaidan, da murya me nuna jimami ya ce"Fatima ba ta nan,ta na can gidan su kin san na fad'a miki ba ta fiya zama a nan ba,kuma wallahi ko zancen auren har yau na kasa yi mata,don ina gudun 'bacin ranta"


 Zubaida ta danne kishin da ya taso mata ta sanyaya murya ta ce"ayya! My Usi ai ba a yin haka,rashin sanar da ita ma zai zama wani laifin kuma,kishi ya zama dole kuma in sha Allah ba za ta tada hankalin ta ba"


  Usman ya sauke ajiyar zuciya ya ce"to! In sha Allah yau zan fad'a mata".


  Da haka su ka yi sallama ya tafi,Zubaida ta shiga gida ta na tunanin ta yanda za ta fara nuna masa Fatima ta raina masa hankali,ko Allah zai sa ya gane ya d'auki mataki a kanta.



   Kamar yanda ya d'auki shawarar Zubaida, haka ya sanar da Fatima halin da a ke ciki,ai kafin ya k'arasa ta yi tsalle ta dire ta ce wallahi bai isa ba! Sam ta k'i tsayawa ta saurare shi sai zage-zage ta ke yi ta na fad'in duk me tsautsayin da ta aurar mata miji sai ta yi nadama. K'arshe dai sai kashe wayar shi ya yi,ya na ta tunanin mafita,baccin shi kad'an ne a wannan daren.



  Kwana uku da sanarwa Fatima zancen ta tashi hankalin y'an gidan su,ta ce ita gidan mijinta za ta koma,dan dole mahaifiyar ta ta hak'ura ta tafi,har ta fara ramewa,saboda son da ta ke yi wa Usman ba na wasa bane,kuma ko a mafarki ba ta yi zaton zai k'ara aure ba,shi ya sa ta sakankance.


  Ranar da ta dawo kuwa Usman ya ga tijara ganin idon shi, don kuwa har cin kwalar shi ta yi wai sai ya kai ta gidan su Zubaida ta ci ubanta,da kyar ya samu ta sassauta ya na ta bata hak'uri, ya samu ya bar gidan da muguwar fargaba,sai ya ji dama bai d'akko zancen auren ba,su zauna lafiya da Fatin shi.



  Washegari da sassafe Zubaida ta doka masa kira,don ta tashe shi daga bacci.Fatima da ke zaune saman gadon tashin ta daga bacci kenan,duk da ba isar ta ya yi ba,tunda jiya raba dare su ka yi ta na ruwan bala'i,to yunwa ce ta tashe ta a lokacin,ta ja doguwar hamma ta na mik'a


K'arar wayar Usman ce ta katse mata mik'ar ta,ta yi saurin tashi ta je ta d'auki wayar ta na kallon screen d'in, _Amaryata_ sunan da ta gani kenan a rubuce,sai da ta kalli wurin da ya ke a kwance ta ga har lokacin bacci ya ke,ta buga masa wata harara ta fice daga d'akin.


 "Assalamu alaikum, haba my ango ina ka shiga ka manta da amaryar ka?". Zubaida ta yi maganar bayan ta ji an d'aga wayar.


  Fatima ta wani zaro manyan idanunta da tsananin mamaki,ko ba a fad'a ba ta san Zubaidan wayayyiya ce


"Kin ci ubanki ke da angon,za ki yi aure a lahira a can za ki yi angon"


Fatima ta fad'a cikin gur'batacciyar hausar ta.


Zubaida ta tashi tsaye ta na sake kallon wayar,don a zaton ta wrong number ta yi, sai ta ga tabbas number Usman ce,cikin inda-inda ta ce"don Allah da wa na ke magana?"


 "Ki na magana da matar Usman! Wadda ya aure ta,kuma zai ta auren ta har su mutu tare su biyu,babu wani shegen da zai shigo,k'arya ya ke wallahi".


  Fatima ta fad'a, a k'ok'arin ta na nuna ta ji hausa har ta k'oshi.


  Zubaida ta kwashe da dariya don ka na jin yanda Fatima ta yi maganar za ka san ba ta k'ware a hausar ba


  Ta na cikin dariyar ta tsinkayi muryarta" banza wawa mara d'a'a,ba ku da mutunci ba ku da daraja,to mijina ya wuce ki,idan ba ki yarda ba ki shigo ki gani!"


  Zubaida ta kuma sakin dariya ta ce"au dama kin san meye daraja,amma shi ne ba kya daraja mijinki? Ki ke tafiya ki bar shi da matse filo? Ke tukunna ma wai me ye ya dawo da ke?"


"Ubanki ne ya dawo da ni,shegiya y'ar iska me neman mijin wani,kuma aure babu"


Ta fad'a ta na huci,kamar za ta dank'o Zubaida ta cikin wayar.


Zubaida ta kwashe da dariya har da rik'e ciki ta ce"ke bagwariya,ki fara koyar hausa kafin ki zo kan k'wato miji,kuma aure kamar an yi an gama,zan zo na koya miki yanda a ke kula da miji kin ji y'ar gwari?"


Ba ta jira amsar ta ba,ta katse kiran ta ajiye wayar a gefe,wata ajiyar zuciya ta sauke ta na dafe k'irji ta ce"oh! Ni Zubaida, yanzu da wannan masifaffiyar za mu zauna? Lallai dole na d'aura d'amarar k'watar y'anci,tunda ya na mugun son ta".


Ta na kallo wani kiran ya na sake shigowa ta yi banza da wayar ta shiga sabgar gabanta.


  Fatima kuwa rufe ido ta yi,ta shiga zazzagawa Usman masifa,wai Zubaida ta kirata ta zazzage ta,da mugun mamaki ya ke kallon ta kafin ya ce"ita a ina ta samu number ki da har za ta kira ki?"


  "Ga shi a wayarka!" Fatima ta fad'a ta na wurga masa wayar.


 Saura kad'an ta same shi a fuska,ya tare ya na fad'in"to wa ya ce ki ta'ba min waya?"


  Fatima ta ce"na ta'ba d'in, ka yi yanda za ka min!"


Sai kuma ta fashe da kuka,ta zauna ta na ta yi. Ya taso cikin damuwa ya duk'a a gabanta ya shiga rarrashin ta,kamar ba ita ta yi masa laifi ba.

Post a Comment

ADS HERE
ADS HERE