ZoyaPatel
Ahmedabad

AMINAINA KO ITA. Labarin cin amanar dangantaka da soyayya labari mai taΙ“a zuciyar mai karatu.


 πŸ’…πŸ’…πŸ’…πŸ’…πŸ’…πŸ’…πŸ’…πŸ’…πŸ’…πŸ’…




🀦🏻‍♂️🀦🏻‍♂️🀦🏻‍♂️



  πŸ’” *AMINAINA KO ITA?*πŸ’”


                          🀦🏻‍♀️🀦🏻‍♀️🀦🏻‍♀️


  


     πŸ™†πŸ»‍♀️ *(BETRAYED LOVE! )* πŸ™†πŸ»‍♀️

         


*Na*



    *Rasheedat Usman*



    *(Ummu Nasmah)*





*MARUBUCIYAR*


*Sauyin Rayuwa*

*Nasmah ko Nasirah*

*Sara da SassaΖ™a*

*Akan Ζ΄ar Uwata*

*Indo a Birni*

*So Bai San Jini ba*

*Hatsabibiya Saude*

*RuΙ—anin zuciya Biyu*

*Doctor Hassan*

*Ƙauyemu*


   And now *AMINAINA KO ITA?.*



   *SADAUKARWA*


Na sadaukar da wannan littafin ga Ummana Momy Hassana marigayiya Ubangiji ya jiΖ™anki da rahama yasa mutuwa hutuce a gareki, ina roΖ™on alfarma ga duk wanda ya samu damar karanta wannan littafin daya sata cikin adduar

Sa rabbi shi mata rahama ya yalwanta haske gami da ni'ima cikin kabarin ta.



 *SPECIAL GIFT TO*



*MY SON AHLAN* rabbi ya albarkaci rayuwarka, Allah ya dauwamar da Ζ™auna da tausayi gami da jin Ζ™ai na iyayenka I love You My Son.




*Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…*


 *____________________________________*


 *πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*

*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*

 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*____________________________________*


*Warning* Ban yadda wani ko wata ya juya min labari, ta kowacce siga ba tare da izina na ba yin hakan kuskukure ne.



*Tsokaci* wannan labarin Ζ™irΖ™irarren labari ne ban yishi don cin zarafin kowa ba, duk wacce taga yazo dai-dai da halinta labarin ne kawai yazo da haka domin kuwa labari ne mai Ι—auke da salon zamani wanda ya taΙ“o abubuwa da dama da suke faruwa a halin yanzu labari ne mai taΙ“a zuciyar mai karatu.




Ina farawa da sunan Allah, Allah ka tsare harshena ga rubuta abinda bazai amfani al'umma ba.




*Shafi na Ι—aya*




_______ Cikin gaggawa take Ι—aura agogon hanunta tasan yanzu haka Allah Atiku Naira yana hanya, bata gama tunanin ba, taji ringin Ι—in wayarta, kallonta ta mayar kan screen Ι—in wayar, *ALH ATIKU NAIRA* Ι—an murmushi ta saki tare da saka hanu ta Ι—auki bag Ι—inta tare da Hijabin ta, niΖ™af ta Ι—aura, ta jefa wayarta shima cikin jakar, wasu plat Ι—in takalmi ta saka kalar ja ruwan kayan jikinta, hanyar waje ta nufa, Ƙanwarta Nazifa da tun Ι—azu take zaune tayi tagumi ta zubawa Ζ΄ar uwar tata idanu cike da Ζ™yamar Ζ™asΖ™antacciyar rayuwar da ta zaΙ“awa kanta,  dakatar da ita tayi ta hanyar kiran sunanta.

 " Aunty *NAFEESAT*!!!"

 Tsayawa NAFEESA tayi tare da juyowa ta amsa kiran.

 " Na'am uwar Ζ™orafi, yau kuma wacce da'awa zaki bani wanda ban santa ba"

Numfashi Nazifa ta sauΖ™e tare da runtse idanunta cike da jin haushin Ζ΄ar uwarta tace.

 " Dan Allah Aunty karki fita kibi wannan Alhajin, kin san dai abinda kike aikatawa haramunne ko? sam bai dace da rayuwarki ba."

 TaΙ“e bakinta NAFEESA tayi ta ce.

  " Tatsuniyar taki kenan da kullum kike maimaita min ita koda karatu ne yaci ace zuwa yanzu na haddace, Nazifa nasha faΙ—a miki cewa ki cire idanunki a kaina kin kasa ji ko, to Wallahi na kusa naci ubanki muddun baki fita sabgata ba, kaji min yarinya da shegen shishshigin tsiya, to uwata ma da ta haifeni bata saka min wannan idon da kika saka min ba, nasha faΙ—a miki neman kuΙ—in da zan rufawa kaina asiri nakeyi na Ι—aukewa kaina takaicin da ubana ya kasa Ι—auke min dan haka ki kiyayeni."

 Tayi Maganar cikin faΙ—a tana nuna Nazifa da yatsa, shuru Nazifa tayi tana kallonta sanda ta gama sannan Nazifa cikin siririyar muryarta tace.

 " Allah ya baki hkr Aunty gaskiya na faΙ—a miki, wannan ba ita bace hanyar neman kuΙ—i meyasa bazaki nemo koda Ι—auken atamfofi bane kk kasa kaya ki sayar ba, saiki samu kuΙ—in ta hanyar da ta dace hanyar halak, Aunty NAFEESA muna da Uba fa mu ba marayu bane ubanmu yana da dukiyarsa dai-dai gwargwado yana bamu ci da sha, me kika rasa Aunty da har zaki maid......."

  "Dakata dallah malama ya isheni haka, abubuwan dana rasa a cikin gidan nan suna da yawa kuma kema kin sani, Ban rasa ci da sha ba, amma na rasa sutura masu tsada da kuΙ—in buΖ™atun duniya na more rayuwa, ni macece kuma budurwa kinsan dole ina buΖ™atar Ado na Ζ™yale-Ζ™yalen zamani kuma duk na rasasu saboda Allah ya haΙ—ani da mungun Uba wanda bai damu da rayuwar jin dadi na iyalinsa ba, mai kuΙ—in lukudu wanda bazasu amfane kiba bare kuma ni ABBA kansa kawai ya sani babu ruwan sa damu, kinga kuwa tunda ina buΖ™atar jin daΙ—in rayuwa dole naci karena babu babbaka."

 Girgiza kanta Nazifa tayi cike da rashin gamsuwa da maganganun NAFEESA tace.

 " Aunty Wannan ba hujj......"

 " Kee!!! Dallah wannan soki burutsun naki ya isheni yanzu ba lokacin Ι“ata yawuna bane ina da abu mai mahimmanci da zanyi ki bari Allah ya dawo dani lafiya sai mu Ι—aura daga inda muka tsaya, idan Mama ta dawo kice mata na fita."

 Ta dakatar da Nazifa tare da juyawa ta fice numfashi Nazifa ta saki tare da cije leΙ“enta tana kallon ficewar Nafeesa.

" Hmmm!!! Allah buwayi gagara misali, kowa da tasa Ζ™addarar mu kuma tamu kenan ta rashin samun uwa ta gari, tabbas da Mama mai kulace da Rayuwar Aunty Nafeesa bata lalace haka ba Hmmm!!! Allah ka shirya Aunty Nafeesa"

 Duk zancen zuci Nazifa keyi tare da miΖ™ewa ta kwanta a saman gadon nasu zuciyarta duk babu daΙ—i.



 Ita kuwa Nafeesa tana fita, tayi bayan layin gidan su, tana dube dube sai da ta tabbatar babu kowa a wajen sannan tayi saurin shiga cikin motar Alhaji Atiku Naira, numfashi ta sauΖ™e tare da cewa.

 " Sannu da isowa Alhajina, kayi kyau sosai tamΖ™ar Ζ™aramin yaro."

Ta Ζ™arisa Maganar tana kashe masa Ido tare da Ι—aura hanunta saman cinyarsa, ta kwanto jikinsa, dariya Alhaji Atiku yayi cike da Sha'awarta ya jira hanunsa cikin rigarta yana dariya yace.

  " Duk kyauna ban kaiki ba, ina tsantsar Sha'awarki, anya kuwa yau ba'a cikin motar nan zamu kashe arnan nan ba kuwa, dan na zaΖ™u."

 Dariya Nafeesa tayi tana saka hanunta ta cire nasa hanun daga cikin rigarta tace.

  " Rufa min asiri tsakiyar unguwa muke ja mota kawai muje Amada hotel yafi min rufin asiri domin kuwa ana ganina da mutunci, ni ai taka ce tunda kana biya min buΖ™atuna kuΙ—i enough daga ni har jikina ai naka ne."

 Dariya Alhaji Atiku yayi yana lakace mata hanci yaja motar suka fita daga cikin unguwar.






  🏬. *AMBASSADOR AHMAD GIWA FAMILY ESTATE*. 🏬




 Hommm!!!! Hommm!!! Hommm!!! Ƙarar motar da ta doki kunnen Ι—an sandan dake gadi a bakin makeken get Ι—in, koda jin sautin motar tamkar zai doki get Ι—in ya shigo hakan ya tabbatar masa da cewa *HAIDAR* ne, sanin zafin zuciyarsa ya sa sargent Samuel tashi da sauri ya wangale get Ι—in hancin motarsa ya danno fara tas gwanin sha'awa ita kanta motar abun kallo ce Ζ™irar *MERCEDES BENZ C300 MODEL* wacce kuΙ—in ta zai kai kimanin 7million hanu Sargent Samuel yake Ι—aga masa wanda shi HAIDAR baima lura ba, dreving Ι—insa kawai yake, a parking space dake cikin estate Ι—in Yayi parking, hanu yasa da niyar buΙ—e motar ya fito sai yaji ringin Ι—in wayarsa, dubansa ya kai ga wayar Helina da kamar bazai Ι—aga kiran ba, sai kuma ya saka hanu ya Ι—aga wayar tare da maida kansa ya jingina jikin sit Ι—in motar shuru yayi ba tare da yayi magana ba, daga can Helina tace.

  " My Man where are you going."

 Tamkar baya son maganar ya amsa mata da cewa.

  " Meye matsalarki da inda nake, kina bina bashi ne wohoho Helina kin matsawa rayuwata da yawa, na faΙ—a miki idan ina buΖ™atar ki nida kaina zan nemeki?"

 Ya jefe mata tambayar cike da gatsali, Helina shuru tayi jin yan iskan nasa suna kansa kafin cikin kwantar da murya tace.

  " Sorry My Man, ina son ganinka ne, 2dys bamu haΙ—u ba, ni kuma gaskiya ina matse da kai bazan iya haΖ™urin yau ba tare da kaiba kasan son da nake maka."

 Ta Ζ™arisa Maganar cikin marairaicewar murya, HAIDAR tsuka yaja ba tare daya kuma ce mata komai ba, ya katse kiran hanunsa yasa ya buΙ—e motar ya fito, numfashi mai sanyi ya sauΖ™e tare da kai dubansa ga tarin ma'aikatan gidan dake tsaye suna jiran fitowar sa, murmushi HAIDAR yayi tare da miΖ™a musu hanu Ι—aya bayan Ι—aya sukayi musabaha kasancewar sa mutum mai tsananin daraja Ι—an adam komai talaucin sa, baya taΙ“a Ζ™yamar mutum, Ga kuma uwa uba kyautar da yake dashi, kuΙ—i ya basu rafa guda, kafin ya danna kansa cikin wani Ζ™aramin get da zai sadasa da part Ι—in *INNA JAMMA* wanda take haΙ—e da su *UMMI* tun daga bakin Ζ™ofar da zai shigar dashi Babban falon yake jiyo hayaniyar su Minal, da Sallama ya shiga da gudu Minal ta faΙ—a jikinsa, tana.

 " Oyoyo Yaya Haidar welcome"

Dariya Haidar yayi tare da Ι—aga Minal sama yana cewa.

 " Oyoyo my princess"

Ya Ι—agata yana Ζ™oΖ™arin shiga cikin falon, Afnan ma dariya tayi tace.

 " Sannu da zuwa yaya Haidar, tun Ι—azu Daddy ke jiranka, yanzu yake cewa zai tafi kawai ba lallai kazo ba maybe uzuri ya riΖ™eka."

 Murmushi Haidar yayi ya sauΖ™e Minal tare da cewa.

 " Ai kuwa kamar Daddy ya sani wallahi na biya Company ne, akwai kayan da aka kawo wanda gobe muke so a fitar dashi garmany, shine ya tsaida Ni na tsaya munyi lissafi, Ina *AL'AMEEN*."

 " Yaya Al'ameen yana Bedroom Ι—insa bai fito ba, ko breakfast baiyi ba, maybe ma Ina ga bai tashi daga bacci ba."

Murmushi HAIDAR yayi tare da cewa.

 " Okay Afnan kije ki tada sa, kice zamu shige da Daddy yayi maza ya fito, bara ni na Ζ™arasa wajen Daddyn."

 " Shikenan Yaya Haidar bara naje na tashe san."

 " Wannan ai yaudara ce baΖ™ar cuta taya zaka shigo gidan nan baka fara nemana ba a matsayina ta uwar gida"

 Inna Jumma tayi maganar tana riΖ™e kunkumi, da sauri Haidar ya kai dubansa ga Inna Jumma, kyakkyawar tsohuwa fara tas mai tarin annuri a fuskarta, murmushi Haidar ya saki tare da miΖ™ewa tsaye ya nufi Inna Jumma sanda yazo daf da ita ya tsaya yace.

  " Ai koda idanuna sun makance, dole zuciyata sai ta kalleki, uwar gida sarautar mata, wai ma ya akayi yau naga kin koma min yarinya Ζ΄ar 19yrs kinyi kyau fa Zuciyata."

 Ya yi mata maganar cikin raha cike da Ζ™aunar kakar tasu Dariya Inna Jumma tasa za tayi Magana taji muryar *FARUQ* daga bayansu yana cewa.

 " Ina kyau anan jiki duk ya tattare tsufa ya gama awun gaba ita, fata duk ta jeme, kai dai malam faΙ—a mata gaskiya ya akayi kaga ta tsofe ta jeme tamkar Ζ΄ar 140yrs"

 Dariya Haidar yayi yana maida kallonsa ga Faruq dake shigowa, taΙ“e bakinta Inna Jumma tayi tare da cewa.

 " To fa, ai kaga inda matsalar take kai ALIYU duk sanda kazo gidan nan sai wannan Munafukin UMARU Ι—in ya biyo ka, bari kaji aini tsufana yazo da kyau ka jira na uwarka da ta ubanka ka gani bazasu sami kyawun tsufata ba"

 Dariya dukkan su sukayi Haidar na rungume Faruq yace.

 " Haba dai Inna Jumma kin taΙ“a ganin inda mota ta tashi babu inji ko kin taΙ“a jin inda Ι—an Adam ya rayu babu jini, Momy ai kunfi kusa Ζ΄arki ce."

 Inna Jumma cike da Ζ™aunar jikokin nata tana dariya tace.

 " A'a Umaru ban taΙ“a gani ba."

 Haidar still dariyar yayi yace.

 " To kuwa ki saka a ranki duk inda kikaga Haidar sai kinga Al'ameen Da Faruq domin kuwa tsintsiya ne maΙ—auri Ι—aya, kaga Faruq rabu da Inna Jumma haura ka tashi wannan Ι—an son baccin tsiyar ni bara nayi wajen Daddy time na Ζ™urewa."

 Ya Ζ™arisa Maganar yana sakin Faruq ya haura step Ι—in cikin hanzari Faruq ido ya kashewa Inna Jumma tare da ce mata.

  " Aje a zauna a cigaba da zaman jiran bazawarin tsoho HAIDAR dai ya tsere miki anga sabon jini ana neman liΖ™ewa."

 Yayi maganar yana dariya Inna Jumma itama dariyar tayi ta saka hanu zata jawo Faruq ya ruga da gudu ya nufi part Ι—in Al'ameen, murmushi Inna Jumma tayi ta furta.

 " Ja'iri Ι—an nema, hmmm Alhamdulillah!! Har cikin raina ina jin daΙ—in yanda kan jikokina yake haΙ—e suna Ζ™aunar junansu Allah ka tabbatar da Ζ™auna da zumunci tsakanin su har abada."

 Tayi adduar tana zama cikin Ι—aya daga cikin kujerun dake falon kusa da Minal dake famar game da system Ι—in Maimu.


  

 Hankalinsa kwance yake baccin sa cikin blanket Ι—in, ga sanyi ac daya gauraye Bedroom Ι—in gami da Ζ™amshin turaren Ι—aki, Afnan da ta shigo ne ta zauna bakin bed Ι—in tana tashinsa a hankali.

 " Yaya Al'ameen!! Yaya Al'ameen!! Yaya Al'ameen."

 Jin sautin kira cikin kunnuwansa ya sashi buΙ—e idanunsa a hankali yana ambaton.

 " Bismillahillazi ahyana ba'ada ma amatana wa ilainnushur"

Ya Ζ™arisa adduar tare da sauΖ™e sexy eyes Ι—insa masu kalar ruwan toka Ash color tamkar idanun mage ya zubawa Afnan ba tare da yayi magana ba, kasancewar sa miskilin gaske wanda shi kwatakwata bai cika magana ba, koda da iyayensa maganarsa bata yawa, mutum ne mai wuyar gane halinsa wanda idan bakasan halinsa ba, sai kace yana da wulaΖ™anci.

 " Yaya al.........."

Hanu ya Ι—aga mata ba tare da ta Ζ™arisa Maganar ba, ya nuna mata hanyar Ζ™ofa alamun ta fita, babu musu Afnan ta fita domin kuwa tasan halin Al'ameen sarai zai ma iya maketa, idanunsa ya Ι—aga ya kalli makeken agogon bangon dake manne cikin Bedroom Ι—in, 11:30am Ι—an Ζ™ara ware idanunsa yayi yana kallon agogon tabbas yau ya makara.

 " Daddy."

Ya furta a hankali tare da tashi da hanzari yana sauΖ™e Ζ™afarsa Ζ™asa takalmin dake gefen bed Ι—in ya saka tare da miΖ™ewa tsaye daga shi sai gajeren wando da bes, daidai da shigowar faruk, da Sallama juyawa Al'ameen yayi yana kallon Faruq sai kuma ya saki murmushi ya amsa sallamar, zama Faruq yayi bakin bed Ι—in tare da cewa.

 " Meyasa wai kake hakane taya zaka kori yarinya bayan aikota akayi ta tashe ka."

Kansa Al'ameen ya kauda gefe tare da nufar tollet ba tare da yayiwa Faruq Magana ba, shima Faruq sanin hali ya sashi taΙ“e bakinsa, kusan 30 minute kafin Al'ameen ya fito daga tollet Ι—in kunkumin sa Ι—aure da towel ya rayata Ι—aya kuma a kansa yana tsame ruwan dake jikinsa kan dest Ι—in dake jikin dressing mirror Al'ameen ya zauna, Faruq ya kalla da hankalin sa ke kan wayarsa cike da nutsuwa Al'ameen yace.

  " Hmmm!! Har abada baka taΙ“a fuskanta ta, Faruq sai kace ba tare muka taso ba, sanin kanka ne, na haramtawa Afnan shigowa Bedroom Ι—ina amma tsabar ganganci kuka turota, muddun baku daina aikota cikin Bedroom Ι—in nan ba, ina tabbatar maka wata rana sai dai ku shigo ku Ι—auketa a karye."

  Faruq dake kwance saman bed Ι—in Al'ameen yana jinsa yayi shuru bai kulasa ba, tamkar baya wajen, Al'ameen ganin Faruq bai tankasa ba, yasa shima yayi shuru, sai da ya gama shiryawa cikin wata Ι—anyar gezna baΖ™a wacce ta Ι—auki fatar jikinsa kasancewar sa farin mutum Ζ™al, gashin kansa ya gyara ba tare daya saka hula ba, ya manna siririn glass Ι—insa a Idanunsa.

  " Muna iya tafiya."

Ya furtawa Faruq tamkar bai son maganar murmushi Faruq yayi ya Ι—auki wayarsa tare da dukan kafaΙ—ar Al'ameen yana dariya.

 " Shege Abokina, wannan kwalliyar kuwa anya ba wajen budurwa zaka ba."

 TaΙ“e bakinsa Al'ameen yayi tare da furta.

 " Kaine suke gabanka har kake tuna su, ni ko kaΙ—an basa gabana, Faruq Ζ™waΖ™walwata bata shirya Ι—aukawa kanta damuwa ba, domin kuwa mace matsala ce."

 Murmushi Faruq yayi hanunsa na kafaΙ—ar Al'ameen suna tafiya yace.

 " Anya kuwa Al'ameen aljana bata aureka ba, wannan Ζ™yayyar da kake yiwa Aure yayi yawa, gaskiya ya kamata a fara nemo maka magani, naga kai ko kaΙ—an mata basa burgeka duk kuwa kyan mace da adonta, abokina kana da matsala duk yanda akayi."

 Murmushi Al'ameen yayi ya Ι—aga kansa ya kalli Al'ameen tare da cewa.

  " Aljani baya taΙ“a kusantar mai yawan ambaton Ubangiji, ko ta nan ya kamata ka fahimci nafi Ζ™arfin jinni."

 Yayi Maganar daidai sun shigo tsakiyar falo, wannan karon babu Inna Jumma a falon da alamun ta shige Bedroom Ι—in ta, sama suka haura Wajen Daddy, da Sallama suka shiga shiga cikin Bedroom Ι—in, wani kyakkyawan tsoho mai kimanin shekaru 75 zaune idanunsa manne da farin glass ga wani farin saje daya zagaye fuskarsa yana sanye da farar shadda duk da Ι—an tsufar da yayi hakan bazai hana kaga tsantsar kama dake tsakanin sa da Al'ameen ba, HAIDAR ne zaune gefen sa yana tausa masa Ζ™afarsa *AMBASSADOR AHMAD GIWA* kenan adalin tsoho mai matukar tausayin talaka da taimakon su Wakilin Nigeria na Ζ™asar *AMERICAN* tsohon Ι—an siyasa daya riΖ™e manyan maΖ™amai cikin Nigeria. Fuskarsa Ι—auke da murmushi ya amsa sallamar tasu, gefen Haidar suka zauna Al'ameen a hankali ya furta.

 " Good morning Daddy hw ws th dy"

 Har yanzu fuskarsa Ι—auke da murmushi ya amsa.

  " Fine My Son, sai yanzu gari ya waye kenan, da har zan tafi ba tare da munyi sallama ba, sai naji bazan iya tafiya bamu gana ba dalilin kenan da yasa na dakata da tafiyar sai tomorrow in Allah ya kaimu."

 Murmushi Al'ameen yayi yace.

   " Sorry Daddy na Ι—an makara ne, amm Daddy sai yaushe kenan zaka dawo idan ka tafi."

 Murmushi Daddy yayi tare da kallon Al'ameen yace.

   " Just one years kawai zanyi, sannan ina son na sanar daku cewa da Faruq zan tafi yau saboda ayyuka sunmin yawa ina buΖ™atar mai taimaka min kuma sai naga faruk ne ya dace daya tallafa min idan yaso kaida Haidar sai ku kula da Companyn mu dake nan."

 Kusan a razane Al'ameen da Haidar suka Ι—ago kansu cike da mungun mamaki.

 " Whattt!!!!" Suka furta kusan a tare shi dai Faruq kansa yana Ζ™asa kasancewar yasan da zancen tafiyar tun jiya da safe Daddy da Papa suka sanar masa tare da hanasa sanar dasu Al'ameen gudun sasu cikin damuwa, murmushin manya Daddy yayi cikin kwantar musu da hankali yace.

  " Dama dole nasan hankalin ku zai tashi dalilin kenan da yasa na hanashi ya sanar daku, tafiyar ta kama dole dashi ne shiyasa zan Ι—aukesa sannan nima ina buΖ™atar mai tayani hira, hmmm ana tare dama dole wata rana a rabu, sannan ai tafiya ba mutuwa bace, muna zamanin da waya kan sada zumunci, facebook twitter Instagram Whatsapp telegram etc gasu nan dai da yawa hanyar da zaaga juna ta video call da kuma magana ta chart, dan haka ku masa fatan alkairi kawai baku tada hankalin ku ba."

 Numfashi suka sauΖ™e tare da furta.

  " Shikenan Daddy Allah yasa hakan yafi alkairi, zamuje muyi breakfast Daddy."

 Murmushi Daddy yayi cike da Ζ™aunarsu yace.

 " Okay kuje Allah ya muku albarka."

 Da ameen suka amsa tare da miΖ™ewa suka fito Ζ™ofar Bedroom Ι—in Ammi ya nufa Haidar ya dakatar dashi da cewa tana bacci fasa shiga sukayi suka fito daining, har zasu zauna Haidar yace.

 " No ni bazan zauna ba zan shige Companyn Gum Arabic ya iso yanzu zanje na duba ingancin sa, dan a yau nake son a shige dashi Egypt."

 Al'ameen kansa na ga wayarsa yace.

 " Har kayan sun isowa jiya naji aka ce suna gashuwa harsun iso kenan.?"

" Eh sun iso tun cikin dare shiyasa ma yau nayi sammako zuwa Companyn Ƙaron sunyi kyau sosai da alamu zasu kawo kuΙ—i, jiya Sadam ya kira ni yake cewa akwai waΖ™en sa buhu 60  yana buΖ™atar kuΙ—i, sai dai ban yanke hukunci ba, nace masa sai munyi shawara, idan kun Ζ™araso Companyn sai muyi magana."

 Numfashi Al'ameen ya sauΖ™e tare da zama yana jawo wata farar kula ya buΙ—e Chief Ι—in dankali ne soyayye, spon ya Ι—auka da plat ya Ι—ebi daidai wanda zaici sannan ya cewa HAIDAR.

 " Babu wani shawara da zamuyi kawai kace masa bazamu sayi kayan ba."

 FARUQ ne yace.

" Saboda meyasa kace baza'a saya ba, bayan kuma muna buΖ™atar wake sanin kanka ne suna cikin list odern da za'ayi zuwa Tailan."?

 Haidar cewa yayi.

 " Ko kaima zaka tambayesa."

Murmushi Al'ameen yayi tare da cewa.

" Saboda Sadam bashi da amana ya cucemu sau biyu ya samu asaran maΖ™udan kuΙ—aΙ—e ta hanyar yaudarar mu da saka magani cikin waken sa, wanda su kuma Ζ™asar waje basa buΖ™atar wake wanda yake da sinadarin magani, Ζ™arshe mukayi asaran wannan waken KAFIN ya dawo gida Nigeria tuni ya Ι“aci da Ζ™wari sannan Tailan suka daina sayan waken mu, dan haka bazamu sayi nasa ba yakai wani Companyn."

 HAIDAR ne yace.

 '' But amma......."

Hanu Al'ameen ya Ι—aga masa.

  " Karkace komai kawai bazamu saya ba na yanke hukunci."

 Numfashi Haidar ya sauΖ™e tare da ficewa yana cewa.

 " Okay sai kun iso"

 Al'ameen da Faruq tare sukayi breakfast suna Ι—an taΙ“a hira sama sama.


 Haidar Dreving Ι—insa yake hankali kwance ya kunna waΖ™ar Auta mg boy mai taken sai dake, yana sauraro cikin nutsuwa, hango wata mabaraciya ya sashi tsayawa gefen titi yayi parking, inda Nafeesa ke tsaye tana jiran adaidaita sahu, tunda yayi parking Nafeesa ta zirawa motar Ido sosai motar ta mata kyau koda gani ba Ζ™aramin kuΙ—i motar zatayi ba, duk cikin zuciyarta take wannan zancen, idanunta kuma na kan motar tana jiran ganin wanda zai fito daga cikin motar, Haidar cike da nutsuwa ya buΙ—e motar tare da ziro kafarsa, tun daga takalmin sa, take Ζ™are masa kallo har samansa, ko kaΙ—an Haidar bai kula da ita ba, kansa tsaye ya nufi mabaraciyar tare da miΖ™a mata Naira dubu goma, ya juyo, Nafeesa murmushi ta saki cikin zuciyarta ta furta " wannan damar bazata wuce ni ba, domin kuwa da ganin wannan bawan ba Ζ™ananan kuΙ—i bane dashi, dole na Ζ™ulla alaΖ™ar zuciya dashi domin babban jari zai zamo min" tayi zancen zucin tana nufar motar sa cikin hanzari ta zauna jikin motar, tare da danna Ζ™ara tana muΖ™urΖ™usu, ta riΖ™e cikin ta gam da zummar yana mata ciwo sosai take muΖ™urΖ™usu harda riΖ™e cikin ta, idanunta rufe gam...................






Vote

Share

And comment.





Wannan littafin na kuΙ—i ne akan farashi Naira 200 kacal, guda biyu ne daga AMINAI BIYU UWAR AHLAN a cikin littafinta mai taken AHLAN, 


Idan kina son duka biyun zaki biya 300 naira guda Ι—aya 200 Naira


Zaki biya kuΙ—in ta wannan asusun bankin 0006064512 Rashida Usman Jaiz Bank.


Ko katin waya mtn Card ta Ι—aya daga cikin waΙ—annan numbobin wayar tamu.


 08147537180

 0816 555 0116




*ALƘALAMIN RASHEEDAT USMAN*






     *UMMU NASMAH*

Mumbai
Kolkata
Bangalore
Previous Post Next Post