ADS HERE
Posts

EGG OMELETTE ROLL (ƘWALELEN KA MAI MATSE ALJIHU)


 *🥙BASAKKWACE'Z KITCHEN🥙*



01092021


   *EGG OMELETTE ROLE*

 

Aslm alkm barkanmu da warhaka yau muna tafe ne da wani salon girki na ƙwai da kayan miya wanda wannan girkin yana da matuƙar ɗanɗano da amfani musamman wajen karin lafiya da gina jiki ko kuma yana da kyau a yawaita yiwa kananan yara domin samun kuzari da annashuwa a koda yaushe

 


INGREDIENTS

1- Kwai 

2- Chips 

3- Albasa

4- Lawashi

5- Tattasai 

6- Attaruhu

7- Man gyada

8 Madara ta ruwa

9- Gishiri da Maggi

 


*METHOD*

Uwargida ta samu kwano mai faɗi ta fasa ƙwai kamar uku a ciki sai ta ɗauko gishiri ta zuba kaɗan sannan ta ɗauko madara ta ruwa kamar rabin gwangwani ko wacce bata kai rabin da kaɗan ba sai ta cakuɗa ta juya sosai.

 


 

Daga sai ta ɗauko tattasai da attaruhu da ta yayyanka ƙanana sosai sai ta zuba a ciki ta cakuda, sai ta dauko albasa ta yayyanka ƙanana sannan ta ɗauko lawashi shima ya wanke yayyanka shi ƙanana sai ta juye su a ciki sannan ta ɗauko maggi ko roycow ko mr.chief na dunkule bare daya ko biyu ta barbada yadda dai ɗanɗanon zai yi daidai sai ta cakuda sosai sannan ta ajiye a gefe.


Sannan sai ta ɗauko kasko ta dora a wuta ta ɗan zuba mai kadan sai ta dauko haɗin kwan ta ajiye sai ta ɗauko chips  ta zuba daidai misali sai ta jujjuya amma anaso chips din ta zuba mai laushi sosai amma in ya wanda ya bushe ne sai ta fara zuba shi a haɗin da farko bayan ta zuba madara a kwan.

Bayan nan sai ki ɗebo haɗin da ƙaramin ludayi ta zuba a kaskon kamar yadda ake soya wainar fulawa

 

08167151176


*MRS BASAKKWACE*

Post a Comment

ADS HERE
ADS HERE