*By*
*Oum Hairan*
*Bismillahir rahamanur rahim*
*Paid book*
*Free 1-2*
Ƙirrr! Ƙirrr!! Ƙirrr!!! Wayar dake aje saman Centre table ɗin dake tsakiyar parlourn ta fara bugawa alamun tana neman agaji, wata matashiyar budurwa da shekarunta bazasu gaza 22 ba takai hannu ta ɗauki wayar “baƙuwar number?" Ta faɗa da sigar tambayar kai batakai da bawa kanta amsa ba kira na biyu ya shigo ta ɗaga ta kara a kunnenta cikin zullumi da tunanin abinda zata ji a daidai wannan lkcn da take zaman jiran tsammanin ko ta mutu ko ta rayu.
A ɗaya ɓangaren taunar cingum ta karaɗe kunnenta dadai lkcn da akayi niyyar magantuwa bayan an gama yauƙin da cewa “Hye yarinya sunana Diamond Hindu akwai haduwa tsakanina dake a yau ɗin nan da misalin 3:30pm a LA'SULTANA bana buƙatar sanin kowa bayan ke ɗaya sannan ni kamar ajali nake bana African time domin duk second na rayuwata yanada matuƙar amfani gareni"
Ƙit ta kashe wayar ta ajiyeta tare da miƙewa tsaye da cup na lemo a hannunta tana fadada murmushinta tace “ Senator Bashir kazo hannun Diamond Hind zanyi wasa da hankalinka kamar jaririn kuikuyo a hannun mafarauta zan tabbatar maka dani ba ƙawar yara nace"
Kayan jikinta ta cire ta ɗaura towel ta nufi bathroom da nufin wanka wayar ta ta ɗauki ruri ta juya ta dauka ta duba sunan dake yawo saman sensor ɗin ta ta dannn answer a ɗayan sashin akace “gajiyarki hutun wasu Diamond kinfi hanun yaro wancan tsamin fah ya shigo gari tun 1:23pm" murmushin gefen baki tayi tace “shashashan labari sai yanzu zaka sanar dani shigowarsa bayan yaje gda yayi wanka ya kwanta ya huta oya ware makwakwe bakada amfani....."
Jifa tayi da wayar ta fada bathroom ta sakarwa kanta shower tana karkaɗa dogon gashinta da yaci ƙananun kalba da aka ƙawata da duwatsu farare masu sheƙi, ta jima tana sille jikinta sannan ta fito ta ɗauki wani towel ɗin tana goge jikinta wani kiran ya shigo a wata wayar daban ta matsa jikin gadon ta ɗauka tana watsa gashin baya tace “duk wani mutum dare yaka hutawa ba mutum ba hatta dabba amma kai daren shine sa'ar ka yau akwai fita ka faɗawa yara su zama ready" “ok babbar yarinya muna da party na babyna yau da dare a central misalin 11:00pm zuwa 1:00am"
Taɓe baki tayi tace “bana fita da sauran haske talatainin dare yana farawa ne daga 1:30am zuwa 3:00am anan nasara take sannan bana zuwa gdan da yake da me tsohon ciki da me goyo mace damuwa ce aharkarmu namiji kenwar Lami ne so ku rinqa bin doka domin kunsan meye target na team ɗinmu"......
Jinjinawa basirarta yayi yace “komanki cikin tsari amma kinsan waɗancan askarawan suna farautarmu?" Wata muguwar dariya tayi tace ”shine me sun dade basu faraucemu ba dalilin da yasa naji a raina zanbi ayari muje operation ɗinnan tare kenan kudai kuyi abinda nace bana faɗuwa akan duk abinda nasa a gabana, am kafin ka waske ka sanarwa yara banson kisa duk wanda ya kashe hukuncinsa kashewa"
Aje wayar tayi ta ɗauki mai lotion saman madubi ta shafa ta ɗauki wasu riga da sikelt ta sanya ta ɗora baƙin glass tare da haɗe kalbarta ta daure ta yafa wani siririn mayafi ta dubi kanta a madubi tayima kanta murmushi ta zura takalmin ta ta fice a ɗakin wata mota ta nufa ƙirar Jeep ta matsa mata remote ta buɗe ta shiga ta zauna tare da zube wayoyinta saman dashboard ta duba agogon hannunta 3:11pm motar tayima key ta fice daga hotel din batare data saurari kowa ba ta nufi inda ta nufa tana tafe tanabin waƙar dake tashi a motar lkcn data isa gurin 3:28 ta samu guri me kyau tayi parking ta buɗe murfin motar ta zuro ƙafarta ɗaya tana ƙarewa yanayin gurin kallo uku saura ƴan sakanni wata ƙaramar mota ƙirar focus ta shigo tayima kanta matsuguni a bayan tata aka buɗe aka fito matashiyar budurwar ɗazu ce tana ta waige waige bayan Diamond ta gama nazarinta tayi mata horn tare da bude mata sashin me zaman banza.
Nufar motar tayi tana yabawa da haɗuwarta ta suka kalli juna kallon rashin sani Budurwar ta zubawa Diamond idanu a zucci tace “haƙiƙa Allah ya cika duniya da alatunsa wannan halitta dole ki tsula tsiyarki a duniya kowa ya kalleki" a zahiri kuma zama tayi Diamond taja numfashi ta furzar da iska tace “a gurguje Hany aiki zamuyi dake a yau daganan ki nufi Taufiƙ hotel ɓangaren yamma sashin hagu akwai wani guy mai suna Saddeeƙ inason ki isa gareshi da fuskar tausayi duk yanda zakiyi kada ki baro gurin saikin samomin number Harees a gurinsa idan kika ɓatamin aiki shakka babu zan bataki wannan shine kawai aikin ki duba secret account dinki nasa miki 2 millon idan kin gama zan qara miki 3 millions"
Nuna mata hanya tayi ta fita taja motar ta a mugun guje ta fice daga park ɗin, wani gurin hutawa ta nufa tayi parking ta fito ta nemi kujera me zaman mutum biyu ta zauna tare da baje wasu takardu a saman table na gabanta ta fara duba su a nutse tana murmushi tana ɗige ɗigen maker a wasu ɓangarori na taswirar tana tsaka da wannan aikin taga inuwa a kanta ta ɗago ta sauke idanunta akan mutumin dake tsaye samanta ta zare glass ɗin fuskar ta tare dayin baya tayi miƙa.
Wata yaja ya zauna yana me dubanta yace “aikinki yana kyau Diamond Amma fah akwai matsala kwalawan nan sun buɗe wuta nemanmu suke yi a kowacce kusurwa ta 9ja" janye mayafinta tayi gashinta ya baje a bayanta tace “Bobbo guy to wai dole ne zaman 9ja ɗin gareku ni karku damu dani banida matsala ba ayini don tozarta ba kamar yanda na gagari ƙasata Ghana to 9ja ma saidai ta barni banson cinye lkcn akan aikin banza kaje ka fara shirin ko ta kwana wannan itane taswirar aikinmu akwai risk a lamarin ka zuba jami'an tsaro sosai don tabbatar da aikinmu yayi kyau.
Wayarta ta dauka ta shiga wani guri tayi wasu yan qananun bincike tayi murmushi tace “akwai mazan kuɗi a hannunsa cikin wannan baƙar jakar" karkatawa tayi ta nuna masa yayi zooming nata sosai ya ƙare mata kallo taci gaba da cewa “bata hannunsa tana dakin matarsa tana da wani yanayi na kafiya idan taƙi bada haɗin kai zaku iya harbinta a gaɓar da kukasan bazata mutu ba"
Ɗagowa yayi ya dubeta yace “wai meye damuwarki ne da mutuwar mutum ko rayuwarsa matuƙar buƙatarki ta biya?" Ɗagansa hannu tayi ta miƙe tana tattare takardun tace “duk abinda kaji nace kada ya faru gaɓar faruwarsa ce batazo ba kada ku ɓatamin aiki sirrin nasarar mu yanada alaƙa da rashin taɓa rayuka domin bamu mukayisu ba" murmushi tayi masa tace “kayi aikin cikin Lucky inayi maka fatan nasara sai zuwa gobe zamu iya haduwa kafin nabar ƙasar"
Bata jira cewarsa ba ta nufi motar ta cikin takunta na isa me daukar hankalin kowanne namiji tayima motar key ta fice.
Bata koma masaukinta ba saida ta gama saita ayyukan ta ta kowanne bangare sannan ta koma ta kwanta domin yin bacci baccin ƙin zuwan mata yayi saboda yanayin da take ciki na jiran tsammani can wajen goma da rabi na dare saqo ya shigo wayarta tana dubawa taga number ce tayi wani tsalle ta rungume wayar tace “akwai alamun nasara Harees dama ka daina bibiyata bazaka ganni ba sai naso"
Da wannan tunanin ta fice daga masaukin nata domin isa mahaɗarsu gdane ƙarami me dakuna uku a wata unguwar talakawa mara cikowar mutane wadda hankali zai ɗauke daga kansa ta buɗe ta shiga sun kwana biyu basu shiga gdanba komai a hargitse yake, ba wannan ne a gabanta ba guri ta samu ta zauna tana taunar cingum tana duban agogo tare da kora lemo ta ɗauki wayoyinta ta kashe ta watsa su a Aljihun rigar jikinta.
Kwanciya tayi bacci ya ɗauke ta mai ƙarancin nauyi tanayinsa ne a yanayin tunanin aikin dake gabansu duk da bata wani ɗauki aikin me wahala ba amma dole ne aikin yana buqatar nutsuwa.
Kamar wacce aka jorner mata alert ta tashi ta fice daga gdan daidai lkcn da motar su Jagwa tayi parking ta buɗe ta shiga sukaja suka bar anguwar a mota kowa ya shirya zura baƙar riga da abin rufe fuska baƙi shigar ninja dai ta gaske komanta baƙi ta ɗaura wani baƙin agogo a hannunta a slow suka rinƙa shiga unguwar duk irin manyan karnukan dake area Amma shiru kake ji basu ko motsi wannan tsarinsu ne Indai suka shiga guri hatta sauron yankin ranar bazai motsa ba.
Ƙwararru ne kuma fitinannu ne a duniya sun gagara sun fantsama sunyi shuhurar da suka buwayi duk wani mahaluƙi da karansa yakai tsaiko kowa tambayarsa idan ya buɗe baki Diamond! Diamond!! Diamond!!! Suwaye wadannan dame suke taƙama meye madogararsu akwai wani yanki ma na mutane da suke ganin Diamond's team ba mutane bane domin aikinsu baya kama dana bil'adama su kadai sun buwayi yanki mabambanta ƙarfin ikonsu akan duk abinda suka sa a gaba ya game ko ina a yankin African babban abinda yafi razana mutane da duk mgn sai ace jagorar team ɗin mace ce kowa tambayar da yake wa kansa itan wacece waye ɗaurin gindinta a duniya?
Ɗago manyan idanunta tayi tace “ku tsaya anan tsayawa sukayi daya motar ma ta tsaya suka fita ta dubi kowa ta bashi side ɗinsa ta dubi wani a cikinsu tace “ku shiga zamu tsaya nida Ifritu a waje idan mun ji wani motsi zamuyi muku alama kudai ku rinƙa Ankara da na'urar hannunku idan kuka kuskure kanku zata kware Diamond Bata rafkanuwa".........
BOOK 1&2
AMOUNT #600 VIP
REGULAR 300
DOMIN SHIGA A DAMA DAKU ZAKU IYA BIYA TA WADANNAN HANYOYIN ACC 0255526235 GTBANK
EVIDENCE OF PAYMENT TA 09013718241 KO KATI MTN TA 09013718241 PLEASE BANSA VTU DON ALLAH ONLY DIGIT NUMBER NA KATI TA WHATSAPP A NUMBER CAN TA SAMA.
MUTANEN NIGER ZAKU TUNTUƁI WANNAN NUMBER DOMIN BIYAN NAKU KUDIN CIKIN SAUƘI 94775574
*Oum Hairan*
