ADS HERE
Posts

SHINKAFA MAI HAƊIN KWAKWA


 *🥙BASAKKWACE'Z KITCHEN GROUP🥙*


08092021


*SHINKAFAR KWAKWA*


Yana da kyau uwargida ta san yadda ake dafa nau'ukan shinkafa. Kada ta tsaya a shinkafa fara da dage-dage ko jalof ɗin shinkafa kawai. Yana da kyau idan za ta dafa shinkafarta, ta ɗan ƙawata ta da su ganye domin ƙarin jini da lafiya a jiki. Idan a sati kina dafa shinkafa ba tare da yi mata wani haɗi ba to tabbas ne abincinki zai fita daga ran maigida.


 

INGREDIENTS

Garin kwakwa ko markaɗaɗɗiyar kwakwa

Shinkafa

Karas

Koren tattasai

Koren wake kanana Peas

 


*METHOD*

Da farko zaki  ɗora ruwa a wuta. Idan ya tafasa sai ki zuba shinkafa har sai shinkafar ta tafasa na tsawon minti 15 sannan sai ki wanke da ruwa ki sa a matsami a ajiye.sai ki kankare karas, sannan a wanke kamin a yayyanka shi ƙanana. sai ki wanke tattasai da koren wake da koren kanana Peas sai ki yayyankasu amma banda Peas ɗin.''

Bayan kin kankare bayan kwakwar kin markaɗa farin, sai ki zuba ruwa sosai. Da ruwan kwakwar za kiyi sanwar dahuwar.

ki zuba ruwan kwakwar a tukunya bayan ya tafasa sannan ki zuba wannan ajiyayyen shinkafar idan ta kusa dahuwa sai ki zuba yankakken koren tattasai da karas da koren wake da kuma koren wake ƙanana Peas a rufe da murfi a rage wutar girkin.


Bayan mintuna biyar, sai a gauraya wannan shinkafar a sauke. Shikenan an kammala._ _Ko da maigida ba mai son cin shinkafa bane zaki ga ya fara sha'awar cin irin wannan girkin. Za a iya hada wannan girkin da miyar kaza ko miyar kifi


08167151176


_MRS BASAKKWACE_

Post a Comment

ADS HERE
ADS HERE