*🥙BASAKKWACE'Z KITCHEN🥙*
07092021
*MACARONI BECHAMEL*
INGREDIENTS
Macaroni
Flour
Madara
Nikakken nama
Butter
*METHOD*
Dafarko zaki dafa macaroni ki ajiye a gefe saiki daura pan awuta kizuba mai albasa tafarnuwa saiki soyasu kikawo Nikakken namanki kuxuba akai kijuya sannan kisa tomato paste kizuba ruwa kadan yanda zai karasa dafa miki naman saiki saka maggi gishiri dadai abinda kikeda bukata na kamshi da dandano saiki rufe kibashi minti 5 zuwa 10, saiki dora wata tukunya a wuta kisa butter ko mai kadan saiki zuba flour Kamar cokali biyu saiki juya suhade jikinsu saiki kawo madaranki ta ruwa kijuye Kan hadin butter da flour dinki saiki zuba maggi da dandano da kamshi kadan saikiyi ta juyawa har yayi kauri
Amman ba can ba , Yana daukar lokaci kafin yayi kauri ba'ason kibar wajen saboda zai Iya Miki guda guda koki rage wutar saidai kina zuwa akai akai kina dubawa, Bayan yayi kauri saiki dauko abin gashinki wanda zakiyi baking saiki zuba hadin flour kadan da macaroni saiki juya sosai step uku zakiyi saidai hadin naman shine tsakiya saiki juye wannan ragowar hadin flour din akai ki tabbatar tarufe macaroni din saiki kawo cheese ki barbada a Saman kiyi baking dinshi saidai Saman baya daukar lokaci Kamar kasa wannan akwai dadi sosai yar uwa kigwada yima oga kullun saiyace kiyi masa.
08167151176
_MRS BASAKKWACE_