*🗯️🗯️DACE DA JUNA🗯️🗯️*
*MALLAKIN HADIZA D AUTA*
*WATTPAD PRINCESSDIJA246*
*TAURARI WRITTERS ASSOCIATION*
*SADAUKARWA GA ƘANWATA KHADIJA MUHAMMAD MRS BASAKKWACE👌🏻*
*Alhmdllh Allah da ya nuna mani na fara ɗora Alƙalamina da sunan fara rubuta wannan littafi, yanda na fara cikin sa'a Ubangiji yasa na ƙare cikin nasara, ƙagaggen littafi kuma gajere ne ban yarda kowa ya juya mani shi ba, ta kowace siga ba tare da izinina ba👌🏻*
*1-5*
Zaune take kusa da mahaifiyarta dake toya ƙosai, sai zubawa mutane ƙosan take yi a takarda tana sakawa leda, cikin sauri take miƙawa masu siya tare da fatan ta sallami kowa, cikin zafin nama take aikin saboda gurin ayi a gama ta sami damar zuwa Makaranta cikin lokaci, itama Mamar tata sai faɗin take yi
"Nauwara ki tashi ki je ki barni nace zan ƙarasa aikin mana"
Matshiyar buduwar da aka kira Nauwara ta ɓata fuska tare da turo baki gaba tace
"Don ALLAH Mama ki bari mu ƙarasa duka ai an kusa siyarwa ma"
Mamar ta ci gaba da jefa ƙullun ƙosan cikin ruwan man tana cewa
"Idan kika haɗu da Malamin naku mai zafi ai sai ki san me zaki sanar da shi yau in kika je, ni dai na fita haƙƙinki don bana so a ci zarafinki a kan hakan ina da ikon hanawa, amman tun da kin kafe ai shi kenan idan mun kammala sai ki je Allah yayi maki Albarka"
Nauwara ta washe baki cike da jin daɗi tace
"Ameen Mamitah!, Ai ma yau ba mu da lecture ɗinshi sai gobe, kin ga goben ai sai in je da wuri"
Mamar tana ci gaba da jefar ƙullun ƙosan tace
" Allah ya nuna muna goben lafiya to"
Da Nauwara da wasu yara da matasan da ke tsaye suna jiran ƙosan duka suka haɗa baki wajen faɗin "Ameen Ameen Mama"
Haka suka ci gaba da aikin sana'arsu har suka kammala, Nauwara ta kira almajiran da ke kwasar masu kayan aiki ta ɗora masu, sannan ta bi bayansu zuwa gidan da suke zama, in da ta bar Mamar tata a nan bakin titin tana kai wasu kayan da suke ajiyewa a wurin wani mai shagon da ke kusa da su, waɗanda suke bari a nan sai gobe idan sun zo su karɓa, kayan da suka danganci tasar toya ƙosan, da kujerar zama, da kuma murhun da suke aikin da shi.
Nauwara tana cikin shirin zuwa Makarantar ne Mamar ta shigo ɗakin nasu ta zauna, bayan ta gama gaisawa da wasu matan da ke tsakar gidan suna aikace aikacensu, cikin fara'a tace da ita
"Har kin yi wankan kenan?"
Tana fesa turare a jikinta tace
"Ai dole Mama saboda yau nayi latti sosai fa"
Mamar ta maka mata harara cikin sigar wasa tace
"Ai kuma ke ake ji, daman na san laifin lattin duka kaina zai ƙare yau, bayan na yi ta koroki ki dawo kina maƙalewa"
Nauwara ta ɗauko jakarta ta rataya tana faɗin
"To ai Mama ni bana so kina daɗewa wajen ne shi yasa, haka kawai mutane su yi ta kallonki kina toya ƙosai a titi, gara kawai in san na tayaki kin baro wajen da wuri a huta, don ma kin ƙi ni Allah da kin bar sana'ar nan kawai, sai ki samo wata mu fara na gaji da ƙosan nan wallahi Mami"
Ta ƙare maganar cikin shagwaɓa tare da muryar kuka, Mamar kuwa cikin murmushin ƙarfin hali, ta buɗa jakar kuɗin cinikin da suka yi ta ciro ɗari biyar tana miƙa mata tace
"Yanzu dai karɓi kuɗin ni dai ki je kar ki ƙara yin wani latti, Ubangiji ya kare mani ke ki je lafiya ki dawo lafiya"
Nauwara ta karɓa cikin damuwa tace "Ameen na gode Maminah" har fice ɗakin ta dawo tana cewa
"Mami yau baki ce nayi kyau ba?"
Mamar ta bita da kallo cikin shauƙin son ƴar tata tace "Kin yi kyau sosai Nauwarata! ALLAH yayi maki albarka"
Bakinta a washe kuma fuskarta ɗauke da ɗauke da murmushin jin daɗi tace
"Ameen Maminah! sai na dawo kin ji?, idan yayana ya dawo ki ce ya siyo man ice cream ɗin kar ya manta fa?"
Mamar ta bi bayanta da kallo tana goge wasu hawayen da suka sirnano mata a fuska ba shiri, sannan cikin sanyin jiki ta yada haƙarƙarinta akan gadon ta kwanta, zuciyarta cike da damuwa tana ta nazarin wasu abubuwa da suka shuɗe, waɗanda suka kasa goguwa gaba ɗaya a cikin zuciyarta.
Nauwara kam tun da mai Napep ya ajiyeta cikin harabar Makarantar tasu, ta sauko take takunta cikin ƙasaita kamar kullum, wadda tafiyar ta riga da ta zame mata jiki yayin da wasu suke ɗaukar hakan a matsayin kuri ko yanga, sai dai ko kaɗan ba hakan bane amman mutane da yawa sun kasa gano hakan a zahiri.
Tun daga nesa dandazon samarin suke kallonta har ta wuce ta gabansu, ƙamshin turarenta ya doki hancinsu suka fara yi mata fito suna yi mata kirari, amman ban da hannu da ta ɗaga masu tana murmushi ƙanzil bata ce da su ba, wani ɗaya daga cikin Samarin ya buga tsaki cike da jin haushinsu, ya miƙe tsaye yana kallonsu ɗaya bayan ɗaya sannan yace
"Wai ku har yaushe ne zaku gano cewa wannan yarinyar bata kai matsayin da zaku lalace kanta ba?, Idan ma gayunta ne yake ɗibarku to kun yi a banza tunda ita ta kasance ƴar wulaƙanci, don ni wannan yarinya da za'a barni da ita da tuni na yaga mata rigar mutumci WALLAHI, saboda na tsaneta sosai haushinta nake ji, musamman idan naga kowa yana lalacewa a kanta tana iskanci, to me tafi sauran mata ne wai ma da har kuke yi mata irin wannan kallon? mitssss!"
Ya ƙare maganar tare da fisgar littafanshi ya bar wajen zuciyarshi cike da jin haushinsu duka, sauran abokan nashi kuwa suka fara yafitar juna suna ƙumshe dariya, wani ɗaya daga cikinsu yace
"Ni fa na fara hango wancen guy d'in an ya ba son Yarinyar cen yake yi ba?"
Dukansu suka fashe da dariya don wasu da yawa sun gasgata, yayin da wasu suka ƙi gamsuwa da hakan duba da yanda yake mayen mata amman ita ko kaɗan bata gabanshi.
Ɗanɗano daga littafin DACE DA JUNA👌🏻
*DAGA ALƘALAMIN HADIZA D AUTA✍🏻*
