DOGARI PAGE 2
*DOGARI*
Na
*MARYAM M HASHEEM*
*M JARUMA*
PAGE 4
*_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
Aliyu kwance yana tunanin surar Rayhan, sha'awarta nata girma a zuciyarsa, rungume filo ya yi yana nishi sama sama, natsuwa ya samu daya tuna da shukrah nan ya dauki wayarsa ya kirata
Rayhan kuwa ta kasa bachci, tana tuna kalaman Aliyu "dama baya son shiga ta, dama shigata bata birgesa" haka ta cigaba da tunani da kyar ta samu bachci ya sace ta
Washegari Aliyu ya shirya tsab cikin kakin soja, ya yi kyau sosai, fuskarsa na fitar da annuri sanadiyar dadewan da suka yi suna hira da Shukhrah jiya da daddare, fitowa ya yi harabar gida inda motar Rayhan take parks, ya jingina jikin motan yana jiran fitowar Rayhan
Can sai gata daga nesa tana zuwa, sanye take da doguwar rig, yayi matukar kyau da tsada, sannan doguwar rigar yana da hijabi, tsawan hijabin bai wuce kugunta ba, ta yi kyau sosai, kamar irin matan larabawan nan, ya sha'afa wajen kallanta, ta karaso wurin motan
"Barka da safiya, dafatan ka tashi lafiya"
"Lafiya lau, kin ganni kuwa, shigarki ta yi min kyau sosai"
Ta ji dadi kamar ta yi tsalle
"Ya kasaka uniform bayan kasan yanzu muna matakin abokine"
"Akwai dalilin da yasa na saka"
Tana murmushi "fada min dalili, ina jinka"
"To tunda ke Kawata ce, ai zan iya fada miki sirrin zuciyata, budurwata kuma abar kaunata tana son ta ganni cikin kakin soja, saboda ita na saka, yau zan je wurinta"
A tsorace Rayhan ta kalleshi, zuciyarta ya shiga bugawa yana mata zafi, bakinta na rawa ta shiga yin magana "dama kana da budurwa?"
"Tabbas ina da budurwa"
"Kana sonta sosai?"
"Ina sonta kamar rayuwata, amma akwai wani matsala ne, maiyasa kike tambayata?
Bata bashi amsa ba ta bude kofar mota ta shiga gami da goge hawayen daya sauka kumatunta
Tabe baki ya yi ko oho, shima ya bude motar ya shiga, ya jasu suka wuce suna isa wajen aikinta ta bude kofa ta fito batare da ta ce mishi komai ba ta wuce, ya fahimci akwai damuwa amma daya tuna da Shukhrah sai ya yi biris ya ji wani farin ciki, ya ja motar ya yi wucewarsa
Rayhan data shugo Office dinta ta zube gwiwowinta a kasa tana kuka mai matukar taba zuciya
"Wayyo Aliyu, shikenan na rasaka, ya zanyi da soyayyar ka, ya zanyi da kaunarka"
Ta cigaba da kuka tana biga hannayenta a kasa, ta yi kuka har ta gaji ta bama kanta hakuri, kuma ta yi alkawarin ba zata taba bari Aliyu ya gane tana sonsa ba, zata barshi ya auri wachca yake so
Aliyu kuwa kwatancen da Shukhrah tai masa yabi, tsayawa ya yi a kofar wani gida, kwatan kofar gidan ya cika sai wari yake
Shukhrah sanye da dogon hijabinta ta fito kanta a kasa alamun tana jin kunya, murmushi ya yi yana binta da kallo hatta karaso wurinsa cikin natsuwa
"Ina wuni"
"Lafiya lau matata to be insha Allah"
Ta rufe fuskarta alamun ta ji kunya
"Na sameki kalau, ya Mama?"
"Lafiyarta kalau"
"Ko zan iya shiga na ganta"
"Babu damuwa"
Shukhrah tai masa jagora har cikin gida, magajiya sanye da hijabinta tana zaune kan taburma Aliyu da Shukhrah suka shugo, Shukhrah ta zauna gefenta, Aliyu ya durkusa
"Ina wuni mama"
"Lafiya lau dan nan"
"Shukhrah jeki amso masa ruwa da abin sha"
Ya yi sauri ya ce mama ki barshi kawai
"A'a yaro ba za'a yi haka ba"
"Mama wallahi ki barshi, babu damuwa"
"To Allah ya yi albarka dan nan"
"Amin mama, mama dama ina son a bani dama, zan turo manyana ayi maganar aurena da Shukhrah"
"Allah sarki, to shikenan zanyi magana da kannan mahaifinta, duk yadda muka yi sai na fada maka"
"Ai kuwa mama nagode"
"Babu komai"
Sa hannu ya yi a aljuhu ya ciro kudi da kimaninsu zasu yi dubu ashirin, ya aje mata a gefe
"Mama ga wannan ba yawa"
Tasa hannu da sauri ta dauka, Shukhrah gabanta ya fadi ta juya tana kallan magajiya tana kyafta mata ido
"Dan nan nagode, Allah ya yi albarka"
Ta bude lalitanta ta zuba kudin
"To mama ni zan wuce"
"To sai anjima ka gaida gida
Aliyu ya mike ya fita Shukhrah tabi bayanshi tana ma Magajiya nuni akan ta ajje kudin, suna fita magajiya tai dariya
"Kaji yer banza" ta fito da kudin ta rabashi biyu ta boye rabi ta mayar da rabi lalitarta
Aliyu da Shukhrah jingine jikin mota suna hira, Aliyu na kallanta yana magana
"Kasancewarki matata zai sa yayana su samu tarbiyyar addini, yayana za suyi alfahari dani na zaba musu uwa ta gari mai alkunya"
Shukhrah ta danyi murmushi ta kalle shi
"Ka yi min alkawari ba za ka taba bari na ba kome ya faru"
Murmushi ya yi "na amince ba zan taba barinki ba komai ya faru"
Suka cigaba da hiransu, ya sha'afa gabadaya zai je ya dauki Rayhan a wurin aiki, lokaci har ya wuce sai daya ga kiranta, ya kalli Shukhrah
"Zanje na dakko madam dita"
"Madam kuma, kana da mata ne dama?"
"A'a, ba matata bace, ni me tsaronta ne, ni DOGARIN tane"
"Na fahimta"
"Ni zan wuce, tana jirana"
Ya shiga mota, ta tsaya tana kallansa ya ja motar ya wuce saita shiga gida ta samu magajiya zaune ta fito da goranta da sigarinta
Ta tube hijabin "zafi ya ishe ni wallahi" riga da wando take sanye dashi, ta zauna
"Bani kaso na"
Magajiya ta bude lalitar ta ta ciro kudi ta rabashi biyu ta mikawa Shukhrah, Shukhrah bata amsa ba ta tsaya tana kallan magajiya
"Amsa mana"
"Wallahi ba abin da ya baki kenan ba"
"To nawa ya bani, cutanki zanyi?"
"Magajiya haka zamu yi dake?"
"To shikenan tunda baki yarda dani ba karki kara kawoshi gidan nan"
"A'a abin bai kai haka ba, kawai a share maganar"
Shukhrah ta dauki sigari ta kunna tana sha tana busar da hayakin, magajiya ta kalleta
"Gama sha ki bani kudina"
"Au sigarin ma sai na biya?"
"To me kike nufi?"
"Babu damuwa, zan biya"
Rayhan ta jima sosai tana jiran Aliyu can sai gashi ya karaso, ya bude kofa ya fito da sauri
"Ki yi hakuri, ina wurin budurwata, na sha'afa da hira da ita"
Ta tsaya tana kallanshi ta jure ta ce "ya kabar ta?"
"Na barta lafiya lau"
"Yaushe zaka kaini na ganta?"
"Miye huriminki da ita?"
"Kai abokina ne, ina da wannan hurumin"
"To shikenan duk ranar da kika shirya"
"To weekend, ya yi?"
"Eh ya yi"
Tai murmushin karfin hali suka shiga mota suka yi wucewarsu
Koda Rayhan ta dawo General ya ga alamun matsala a fuskarta, ya yi kokarin sanin meke damunta amma ta boye, daga karshe ya tambaye ta dawa take soyayya, ta tabbatar masa da wannan maganar babu, komawa dakinta ta yi ta kwanta, sai ji ta yi zazzabi na son rufeta, mai aiki ta turo kofa ta kawo mata abinci, ta umurci mai aikin ta mayar da abincin, bayan mai aikin ta fita kuka ta shiga yi, kallanta ya kai kan hotan mahaifiyarta dake manne jikin bango, tashi ta yi ta je wurin hotan ta tsaya tana kara kuka kasa kasa
"Mamata Allah ya jikanki, ta jingina jikin bango ta cigaba da kuka
Shukhrah na dawowa gida ta shiga daki ta tarar da Sahabi kwance kan katifa, yana ganinta ya tashi zaune
"Tuntuni kin bar ni da yunwa, ina ta jiranki kizo ki bani kudi"
"Wai kai Sahabi baka iya fita ka nema ne, nafa fara gajiya wallahi"
"Au hakama zaki ce, to shikenan zan yi tafiyata, sai kowa ya kama gabanshi"
Ya tashi kenan ta rungume shi
"haba my Sahabi daga wasa sai ka dauka da gaske, kasan dai ba zan iya rayuwa da wani ba idan ba kai ba, kiwanka kadai ya karbe ni"
Ya dan kalleta "to bani kudi sai magana ya wuce"
Kudin da magajiya ta raba ta bata nata kason ta damka masa gabadaya, ya amsa yana murmushi
"Ina sonki masoyiyata"
"Nima haka masoyina"
"Bari na je na sayo abin da zan ci"
Sahabi ya fice, Shukhrah ta zauna kan katifar dakin
Aliyu Kiran gida katsina ya yi ya fara shaida musu ya samu matar aure, murna suka shiga yi suna wa Allah godiya, daganan ya kira babban abokinsa Ahmad ya shiga bashi labarin Shukrah, har Ahmad ma ya kosa ya ga Shukhrah tsabar zuzuta ta da Aliyu yake yi, babu wanda Aliyu bai sanarwa labarin Shukhrah ba, bayan ya gama ya fito falonsa ya bude fridge ya dauki goran ruwa ya bude yana sha, tunanin surar Rayhan yake yi yana murmushi, a halin da yake ciki ji yake kamar yanzu ya ganta tsirara a gabanshi, sha'awarta nata tsananta a zuciyarsa
"Zan gwada neman jikinta, nasan zan samu, da ganinta yer hannu ce, zan samu duk abinda nake so a wurinta, amma Shukhrah ta virgin ce, na tabbata babu wani namijin daya taba kama hannunta"
Ya yi murmushi ya cigaba da kurbar ruwa
Washegari Rayhan ta tashi gefen kanta na mata ciwo, tasha panadol sannan ta fito falo ta samu General ya gama shirin tafiyar da zaiyi zuwa NDA dake barin kaduna, domin yaye sabbin sodojin kasa
"Barka da safiya Dad"
"Yauwa, Angel"
"Harka gama shiryawa kenan?"
"Eh na gama shiryawa, zaki je wurin aiki kuwa yau?"
"A'a yau na tashi da ciwon kai, kawai zan huta"
Hankalin General ya tashi "meya kawo miki ciwon kai?"
"Kawai gajiya ne, sai yasa ma yau na sauke zuwa wurin aiki"
"Ayya! Sannu ko?"
Tai murmushi "yauwa Dad"
Tayi wa Dad rakiya har harabar gida inda motoci da sodoji ke jiransa, nan Aliyu ya shugo ya dawo daga jugging, ya kame a gaban General yana gaishe shi cikin yaran sodoji, General ya yi murmushi
"So funny, ni zan tafi kaduna, ka kula da Rayhan sosai"
"Babu damuwa Sir"
Nan dai suna kallon General ya shiga motarsa dake tsakiya, motocin suka fita a jere
Aliyu ya kalli Rayhan, kallo irin na tsananin sha'awa, yana murmushi "kawata an kara bani rikon ki, ya kenan, har yanzu matsayin abota ne ko kuma zan koma matsayina na me kula dake"
Ta dago ta kalleshi, tana kallan kyakkyawar fuskarsa, ta kasa kau da kanta, wani soyayyarsa da kaunarsa na kara mamaye mata ilahirin jikinta, bata san lokacin da ta ce "muna matsayin abota har yanzu"
Ya yi murmushi "da kyau yer gari, yanzu zan dauke ki muje yawo, yau zan baki kulawa na musamman a matsayina na abokinki, jeki yi wanka ki shirya nima bari naje na shirya"
Kawai lumshe idanunta ta yi, ya fice ta bishi da kallo, ta fara tunani a zuciyarta
"Ina matukar sonka Aliyu, bana tunanin zan iya auran wani ba kai ba" a take ta tuna fa yana da budurwar da yake so, sai hankalinta ya tashi ta bar wurin da sauri, dakinta ta shiga ta fada kan gado tana kuka ta dade tana kuka, karan ya shugo wayarta alamun message ya shugo, ta janyo wayan tana kallan allon wayar "My bodyguard" ne a rubuce ta bude message din ta shiga karantawa kamar haka
"Baby na gama shiryawa, ina jiranki"
Ta maimaita kalmar "Baby" ta cigaba "to meyasa zai kirani da Baby, kodai yana sona ne, a'a taya zai soni bayan yana da wachca yake so"
Jiki a sanyaye ta tashi ta shiga bayi, ta yi wanka sannan ta fito ta shafa mai ta shirya cikin wani riga da siket na leshi, ta danyi light makeup, ta yi matukar kyau sosai, ta feshe jikinta da turare sannan ta fita a sanyaye
Aliyu jingine jikin mota yana waya da masoyiyarsa Shukhrah, yana cikin nishadi da farin ciki, tsayawa ya yi cak yana kallan tahowar Rayhan, yana kallan yadda ta yi wani irin kyau, hankalinshi ya tashi, sha'awarta ya kara tsananta, har wani hadiye miyau ya yi, ya katse wayar dai dai lokacin da Rayhan ta karaso ta tsaya gabanshi
"What a pretty girl"
Lumshe ido ta yi "gaskiya baby kinyi kyau sosai"
"Meyasa kake kirana da Baby?"
Murmushi ya yi "laifine idan nakira kawata Baby?"
Rayhan ta yi shuru Aliyu kuwa sai kallanta yake cikin sha'awa fadi yake a zuciyarsa "A hankali zaki shugo hannu na Yarinya"
Rayhan ta bude mota ta shiga, shima ya bude ya shiga, ya jasu suka tafi
Kofar wani super market Aliyu ya yi parking, Aliyu ya kalli Rayhan, sannan ya kalli hannunta data ajje gefenta, hannun ya bashi sha'awa sosai, kumbunan sun bashi sha'awa, kai hannunsa ya yi ya dora akan nata, ta juyo da sauri tana kallanshi shima kallanta yake, ya kashe mata ido daya, sai ta kawar da fuskarta, gabanta ya fadi, ta kasa janye hannunta sai ya shiga murza mata hannun
"Baby mu shiga ciki ko"
Bata ce komai ba ta janye hannunta gami da bude kofa zata fita ya yi sauri ya riko hannunta, bata juyo ba ta tsaya cak
"Baby juyo ki kalle ni mana"
Kunya ya kamata, wani dadi da farin ciki suka ziyarceta, Aliyu ya fahimci haka saiya sake mata hannunta, daya fito ta kasa kallon fuskarsa
"Muje ciki ko"
Bata bashi amsa ba suka shiga cikin super market din, Aliyu ya fara yiwa Rayhan siyayya, Rayhan kawai kallan Aliyu take yi tana mamakin yadda yake bata kulawa, haka ya gama mata siyayyar kayan zaki kamarsu chocolate da sauransu sannan suka fito, daganan suka tafi wani wurin hutawa
Zama suka yi a kujera na musamman suna kallan junansu suna shan ice cream, Aliyu ya kalleta cikin wani yanayi
"feed me Baby"
Ta rufe fuska cikin kunya
"Ya kike hakane, karfa kiyi wani tunani daban, ina matsayin abokinki ne fa"
Ta tsura masa ido
"Ya budurwarka?"
Ya yi wani murmushi da hakorarsa suka baiyana
"Allah sarki my Shukhrah, my wife to be kenan"
Zuciyar Rayhan ya yi wani bugawa, wani zafi take ji a zuciyarta amma ta jure
Ya ce tana nan lafiya, ina sonta kuma kema kawata ina bukatar ki
Jikinta a sanyaye ta ce kana bukata ta? Me haka yake nufi?
"Ina nufin ina sonki"
Rayhan ta kasa yarda da abinda ya ce, ta shiga fadi a zuciyarta "ya ce yana sona kuma ya ce yana bukata ta, me haka yake nufi, wani irin so yake min?
Ya katse mata tunani sanadiyar hura mata iska da ya yi a fuskarta, ta tsura masa ido
"Ki bani labari"
"Ni banda labari sai dai kai ka bani labari"
"To bari na baki wani labari"
Ta natsu tana sauraransa, ya shiga bata labari, haka ya yi ta bata labarai iri iri, tana ta dariya tana nishadi, sun dade a wurin hutawar kamin suka bar wurin, ranar yawo suke ta yi Aliyu dai nata faman cusawa Rayhan soyayyarsa da bai san ma tuntuni ta kamu ba, har dare basu dawo gida ba Cinema suka je suka yi kallo sannan suka dawo gida
A harabar gida suka tsaya suka yi shuru, Rayhan ta kalleshi
"Bana son rabuwa da kai, yau ka sani nishadi sosai"
Yai murmushi "nima bana son rabuwa dake"
"Toya zamu yi, sai da safe"
fadi yake a zuciyarsa "daga gani sha'awata take ji, idan na nemata ma Yanzu nasan zata bani hadin kai, bari na gwada"
Harta fara tafiya ya tsaida ta
"Kona raka ki ne?"
Ta juyo tana kallanshi "idan har ba zan takura maka ba"
"Ai babu takura, taimakon juna ne" ya daga mata gira daya, ta ji wani yarrrrr, suka jera suka shiga ciki
Da suka shugo falo duk suka tsaya suna kallan juna
Aliyu ya ce akwai wani magana ne?
A'a, bari na shiga ciki na watasa ruwa, cikin wani yanayi ya ce zan raka ki, ta danyi shuru tana kallanshi sai kuma ta ce to, jerawa suka yi har dakinta
Aliyu ya zauna bakin gadonta yana mata wani irin kallo, zata shiga bayi ya dakatar da ita
"Haka zaki shiga wanka baki tube ba kin dora tawul"
Ta sunkuyar da kai "yau bana jin dora tawul"
Mikewa ya yi "to mu je na yi miki wanka"
Ta zaro ido "wanka kuma? A'a ka barshi"
Kafin ta kara wani magana ya jawota jikinsa da karfi ya rungume ta, kirjin Rayhan ya shiga dukan uku uku, sumbatarta yake yi yana nishi sama sama alamun yana samun sauki daga tsananin sha'awarta dake addabarsa
Ya kai hannunsa kan breast dinta yana matsawa, Rayhan ta kasa dakatar dashi saboda yadda take jin dadin romance din, ya kula tana jin dadi sai ya fadar da ita kan gadonta ya haye jikinta ya cigaba da romance dinta
A take Rayhan ta shiga tunanin fa Aliyu ba mijinta bane, kuma bai da niyyar auranta, hasalima yana da wachca yake so
Aliyu yana kokarin cire mata kaya, ya ga tana kokarin kwatar kanta tana hanashi, ya shiga sa mata karfi sai ta fashe da kuka
Aliyu ya tashi daga jikinta da sauri ya tsaya yana kallanta sai kuka take yi kamar ranta zai fita, ya shiga kallanta cikin jin haushi yana fadi a zuciyarsa "ji min yarinyarnan kamar bata san komai, tana min wani munafurci"
A zahiri kuwa cewa ya yi
"Yi hakuri, kar kiyi tunanin komai, ke kawata ce sai yasa nake miki haka, idan ba kya so to shikenan bari na wuce"
Bata ce masa komai ba ya tashi ya fita daga dakin, ta cigaba da kuka, tana ji a ranta kamar ta tsayar dashi amma ta jure
Aliyu bangaransa a boys quarters ya wuce ya zauna falo yana ajiyar zuciya, sai kara tuno dadin miyaun Rayhan yake yi, da tattausar nonuwanta, sha'awarta ya kara girma
Ya furta da karfi "wallahi sai nabi duk hanyar da zanbi na dandani zakinta"
Kira ne ya shugo wayarsa ya dauka ya duba "Wife to be" a rubuce, sai ya ji wani nutsuwa, sai da wayar ya gama ringing sannan ya kirata, ta bangaran Shukhrah kwance take a jikin Sahabi yana matsa mata nono, tasa wayar a handsfree yana jin maganar Aliyu
"Matata ya kike?
"Ai yau ina fushi da kai, ka manta dani gabada"
"Habadai Babyna, taya Sarki zai manta da Sarauniya, ai hakan ba zai yuhu ba"
Sahabi suka kalli juna da Shukhrah suna yer dariya mara kara
Haka Aliyu ya cigaba da zubawa Shukhrah Kalaman soyayya amma Shukhrah da Sahabi dariya suke ta yi masa, sun dauke shi sakarai bai san abinda yake yi ba, hakadai suka raba dare suna waya
Washegari Rayhan zaune falo tana shan shayin da me aikinta ta kawo mata, amma bata tantance dadin shayin, tunaninta na wurin Aliyu, tana tuna wasan daya mata jiya, wani shocking ke ratsa ta, tana jin dadi, sannan sonsa na karuwa a zuciyarta
Karan bude kofa ta jiyo, sai shugowan mutum, koda bata juya ta duba waye ba tasan Aliyu ne, don kamshin turarensa baya boyuwa, gefenta ya zo ya zauna yana mata wani irin kallo, itama kallanshi take yi
"Ina kwana"
"Lafiya lau Baby"
"Abokina na rasa dalilin daya sa kake kirana da Baby"
Yay murmushi "kina mantuwa ni abokinki ne, kuma ni a ganina aboki kamar saurayi ne"
Bata ce komai ba ta dauki kofin shayi ta kai baki ta kurba sannan ta ajje a kan center table, Aliyu ya dau kofin shayin ya kai bakinshi dai dai inda tasa bakinta ya kurba, ta bishi kawai da ido, ta kasa gane me Aliyu yake nufi
Da Aliyu ya shugo bai rufe kofar falon ba, General ne ya shugo ya tsaya a bayansu yana kallansu, Aliyu ne ya fahimci akwai mutum a baya sai ya yi sauri ya mike gami da yin salute, yana jinjina masa
General fuskarsa babu yabo babu fallasa ya amsa gaisuwar, Rayhan ta tashi ta je da sauri ta rungume shi "welcome Dad"
Yay murmushi "na yi missing dinki, dafatan dai Aliyu yana kula dake yadda ya kamata"
Rayhan ta kalli Aliyu "sosai kuwa, shiya sani farin cikin da ban taba yi ba, yana mantar dani maraicin mahaifiyata"
General ya ji wani farin ciki ya ziyarce shi ya kalli Aliyu
"Ka yi babban aiki Aliyu, wanna aikin da ka yi yafi min zuwa daji yaken yen ta'adda, yanzu kai ba Captain bane, na kara maka matsayi, amma yata ce zata fadi matsayin da zan baka, matsayi mafi girma da daukaka"
Wayan Aliyu ya shiga ringing bai motsa ba, yana jiran izinin mai gidanshi
General ya ce zaka iya amsa wayarka
Sai yanzu Aliyu ya motsa "thank you sit"
Ya fita yabar falon domin amsa waya, Rayhan tana cikin farin ciki sosai ta kalli Dad
Aliyu sai daya jira kiran Shukhrah ya tsinke sannan ya kirata bugawa daya ta dauka, yana jin muryarta wani farin ciki ya dabaibayeshi, Soyayyar ta nata kara girma a zuciyarsa, sun dauki lokaci suna waya kamin suka yi sallama, Aliyu ya katse wayan yana murmushi
"I love you my Shukhrah"
Bangaransa ya wuce
General da Rayhan zaune a falo suna tattaunawa
"A ganinki wani matsayi ya dace da Aliyu"
Rayhan tai murmushi "ina sonsa da babban matsayi"
General ya tsurawa Rayhan ido "da alamu kina jin dadin DOGARIN ki?"
"Sosai kuwa Dad, like kar ya yi nisa dani"
Dad ya yi murmushi "dakyau yata, ni kuwa zan baki mamaki, zan kai Aliyu matsayin da bai isa ya kai ba don kawai farin cikinki yata
Rayhan ta yi murmushi "Lieutenant colonel"
"Matsayin da kike so na bashi kenan?"
Ta lumshe idanunta "eh Dad"
"to an gama my lovely daughter"
Rayhan ta fita domin fara yiwa Aliyu albishir amma bata same shi ba sai ta wuce boys quarters bangaransa
Aliyu zaune kan kujera yana latsa latsan wayarsa Rayhan ta shugo cikin farin ciki, hankalinsa ya kai kanta
"Yen mata ya aka yi ne"
"Kalau"
"Baki taba shugowa bangarena ba"
"Laifi ne idan na shugo bangaran abokina"
Ya yi wani murmushi dashi kadai yasan ma'anarsa "dakyau yen mata, da alamu kin fara shiga tarko na"
Ya kai kallansa kan kirjinta daya cika fam, kamar zai fasa rigarta ya fito, wani sha'awarta ya shiga addabansa, ya fara jin banana 🍌 yana motsi, ta karaso inda yake ta tsaya
"Albishirinka"
"Goro"
"Menene tukwicina?"
Ya yi shuru yana tunani "me kike so?
"Kawancenmu ya kara karfi"
Ya mike dai dai saitinta yana kallanta sama da kasa, sai ta ji wani yarrrr, ta dukar da kanta, jawota ya yi ya rungume ta, yay wani dan nishi "ah" Rayhan ji ta yi wani abu ya tokareta, da alamu banana 🍌 ne, jikinta ya fara rawa, ya kai bakinsa dai dai kunnanta "Kawancenmu dake ya kara karfi, "to fada min menene?"
Ta banbare jikinta daga nashi tana kallan kasa, ya tsura mata ido yana yer murmushi
Muryarta na rawa ta ce Dad dina zai canza maka matsayi daga Captain zuwa Lieutenant colonel
Aliyu ya zaro ido, ya kasa yarda da abinda kunnuwansa suka juyo masa
"Wasa kike min ko?"
"Taya zanyi maka irin wannan wasan, I am serious"
"Wow! Rayhan gaskiya na yi farin ciki"
Tai murmushi "abin daya kawo ni kenan, sai anjima"
Ta juya ya bita da kallo yana murmushi "idan kuwa da gaske ne daga matsayina na Captain na koma Lieutenant colonel wannan abin farin ciki ne, Allah yasa da gaske ne"
Rayhan ta dawo ta tarar da Dad har ya je ya canza cikin jallabiya, ya kalleta ya yi murmushi
"Har kin je kin yi masa albishir kenan"
"Eh! Dad ya nuna farin cikinsa, ganin farin cikinsa da na yi nima yasa ni farin ciki"
General ya kalli Rayhan ya ce kodai kodai kuna soyayya dashi ne?
Rayhan ta girgiza kai da sauri alamun a'a
"Yata fada min gaskiya, karki boye min komai"
Rayhan ta ce a zuciyarta, ni ina sonsa amma shi yana da wachca yake so, sai dai ba zan raba shi da wachca yake so ba, a zahiri kuma ta ce gaskiya nake fada maka Dad babu soyayya a tsakaninmu, sai dai na shaku dashi sosai, ina jin dadin kasancewa dashi
General ya yi murmushi "Allah sarki yata"
Suka cigaba da hirarsu
General ya kira Aliyu ya tabbatar masa da matsayinsa na Lieutenant colonel, Tuni Aliyu ya kira can katsina ya sanar dasu sunyi farin ciki sosai, suka fara shirye shiryen yin walima don nuna farin cikinsu, haka dai aka yi bikin karin girman da Aliyu ya samu aka gama cikin farin ciki, amma Rayhan ta roki mahaifinta alfarma akan ya barta tare da Aliyu kada ya kaishi wani wuri da zai yi nisa dashi, General ya amince da alfarmarta
Rayhan da Aliyu shakuwa ya kara shiga tsakaninsu sosai, koda yaushe suna tare, Rayhan tana jurewa bata taba yarda tabar Aliyu ya gane tana sonsa ba, shiko Aliyu kullum cikin neman sa'an Rayhan yake, jira kawai yake ta gama shiga tarkwansa, kuma kullum sha'awarta karuwa yake a zuciyarta, tsakaninsa da Shukhrah kuwa magana ya yi girma, yana jin soyayyarta kamar rayuwarsa,
Sahabi hayan wasu dattawa ya yi akan sune iyayen Shukhrah, shi kuma yayanta, Aliyu ya zo ya kawo musu gaisuwa, kuma ya yi alkawarin turo manyansa cikin satin, Aliyu ya shirya zuwa katsina ganin gida, Rayhan ta dage sai dai ya tafi da ita, ya yi mata duk wani dabara amma taki yarda, General ya ce ya ta fi da ita babu damuwa
Aliyu ya tafi katsina tare da Rayhan,
Aliyu dan asalin kankiya ne, kuma mahaifinsa shine sarkin kankiya, Rayhan ta yi mamaki da ganin ashe Aliyu dan sarauta ne, abin ya birge ta sosai
Aliyu da Sarki Mahmud sai mahaifiyashi Haj Amina, Aliyu shine babba a dakinsu sai kaninshi Umar sai mai binshi Fatima amma tana aure a cikin garin katsina, sai Habib sai autarsu Ameera
Da ganin Rayhan sunyi tunanin ita ce Shukhrah, Aliyu ya ce dasu ba ita ba ce, Shukhransa ya barota a Abuja, Rayhan yer me gidansa ce, Ameera ta ce ni nafi son Aunty Rayhan kawai ka aure ta
Aliyu ya kalli Rayhan itama ta kalleshi ta yi, sannan Aliyu ya mayar da kallanta ga Ameera
"Aunty Rayhan Kawata ce fa"
Ameera ta shagwabe fuska "nidai ina sonta Yaya, ka aureta ta dawo wurinmu da zama"
Rayhan ta yi murmushi tana jin dadi a zuciyarta, sai ta ji Ameera ta shiga ranta
"Ameera ki kyale Yayanki da farin cikinsa"
Ameera ta yi kamar zata yi kuka "nidai ku yi aure kawai"
Sai suka fashe mata da dariya
Cikin kwana biyun da Aliyu da Rayhan su ja yi a kankiya, babu wanda bai shaku da Rayhan ba, Maman Aliyu ji ta yi a ranta dama ita ce surukarta amma ba yadda zata yi tunda dan nata yana da farin cikinsa
Kamar ba za'a rabu ba haka Aliyu da Rayhan suka baro kankiya, Rayhan harda kukanta, Aliyu sai dariya yake musu
Dawowansu Abuja bada dadewa ba, iyayen Aliyu suka zo suka nemawa Aliyu auran Shukhrah, aka biya sadaki da komai, lefe kadai ya rage
Shukhrah ta yi kuka har ta koshi amma bata bari Aliyu ya gano halin da take ciki ba, sai dai tana ta ramewa a tsaye, sannan Genaral bai da masaniya akan Aliyu ya biya kudin Shukhrah
Haka rayuwa ya cigaba, har zuwa wani rana da Rayhan tana zaune, me mata hidima ta shugo ta shaida mata mahaifinta na son ganinta, Rayhan bata bata lokaci ba ta wuce Bedroom din General, ta same shi kwance likita na tsaye yana gwada Dp dinsa, ta karaso da sauri
"Dad jikin ya tashi ne?
"Eh my daughter Jikina ya tashi"
Tuni kwalla ya fara fitowa daga idanun
"Darling me zai saki kuka?"
"Dad ina tausayawa kaina, ina jin tsoron na rasa ka a wannan duniyar, ina zan bi na samu farin ciki"
"My Angel ba zan barki ba haka har sai na kaiki dakin mijinki"
Ta girgiza kai "taya zan samu wani da zai kula dani kamar kai, duk duniya babu, kai kadai ne kawai gata na"
Ya dan shafa kanta yana murmushi "haba yata kamar banda dangi, kannaina a suna sonki, hakama dangin mahaifiyarki"
Ta cigaba da kuka
"So kike ki sani cikin damuwa, kukan nan da kike yi zai iya karamin rashin lafiya"
Sai ta yi shuru ta zauna gefenshi, Aliyu ne ya shugo, dai dai likita ya gama abinda zai yi ya fita
General ya kalli Aliyu, ya yi murmushi
"Karaso Aliyu"
Aliyu ya karaso ya tsaya cak cikin girmamawa
"Aliyu ina son na roke ka wata yer alfarma, nasan zan samu, Ina da wannan tabbacin"
"Ka roke ni kowani alfarma, insha Allah zanyi maka biyayya"
General ya yi murmushi ya kalli Rayhan
"Kai kadai ne zaka iya kulawa da yata, na yarda da kai Aliyu sai yasa tun farko na zabeka a matsayin DOGARIN ta, ga amanar yata, ina so ka aure ta"
Aliyu ya zaro ido cikin tsoro da firgici, Rayhan itama zaro ido ta yi, ta kalli Aliyu shima ya kalleta
Mu hadu a page 3