Rayhan zaune bayan mota tana duba magazine, direba na tuka ta, ta dago ta kalli Direban "ya kake tuki kamar mace, ka ja mota da karfi, kara gudu Direba ya yi, wani tsaki ta ja ta cigaba da kallan magazine, gida suka iso inda Direba ya faka a motor park, bude kofar ta yi ta fito bata nufi ko'ina ba sai falon Chief General, ba shi kadai ta same shi ba, yana tare da wani dan matashi da ba zai wuce shekara Ashirin da bakwai ba, wankan tarwada ne, yana da tsayi da farfadar kirji, kana ganinshi kasan tsayayyan namiji kalar da mata suke so, sanye yake da kakin soja, ya kame a tsaye alamun girmamawa
Rayhan ta karaso wajen Dad dinta ta zauna gefenshi
"My Dad yakake?"
"Lafiya lau, ya aikin?"
"Aiki na tafiya yadda ya kamata"
General ya nuna Aliyu "ga DOGARI, shine garkuwarki daga yau, shi zai koma kula dake"
Kallonta ya koma ga Aliyu, ta yatsine fuska "baka iya gaisuwa bene, ko bakin ka na ciwo ne?"
Aliyu kanshi na kasa amma sai daya saukar domin ya kalli Rayhan, Rayhan wankar tarwada ce, tana da kyau sosai ga diri da daukar ado cikin kananun kaya
General ya kalleshi "baka ji abinda ta ce ba?"
Ran Aliyu ya baci sosai, sosai ya ji haushin Rayhan, ba yadda zai yi dole ya gaishe ta, bata amsa ba ta mike tana fadin "Dad da alamu DOGARIN nan zai yi taurin kai, ka fada mishi sharada na bana son raini, Sannan dolensa ya girmamani
Aliyu y kara dagowa a karo na biyu ya kalleta
General ya ce ai kuwa Aliyu bai da matsala duk cikin bataliyarsu shi nafi so kuma hankalina ya fi kwanciya dashi, sai yasa na dakko shi domin ya zame miki garkuwa, nasan idan dashi a tare dake ko kuda ba zai zo kusa dake ba
"To Dad naji, amma ka fada masa ina son girma"
Ta fada tana barin falon, General ya kalli Aliyu "karka damu da ita, wallahi Aliyu Allah ya jarabceni da soyayyar Rayhan, tunda mahaifiyar ta ta rasu duk wachca zan aura saina sake ta dalilin Rayhan har nazo na hakura da auran"
Aliyu bai ce komai ba, har yanzu a kame yake
Rayhan dakinta ta shiga, ta wuce bayi ta watsa ruwa Sannan tazo tasa kaya marasa nauyi, ta zauna bakin gado tana tuna Aliyu "DOGARIN ya hadu, irin wanda nake so ne amma ya min yaro, nafi son 30 above" tsaki ta ja "to me ma yasa nake tunaninsa" tashi ta yi ta je ta bude fridge din dakinta, ice cream ta dauka ta dawo bakin gado ta zauna tana sha
Ta bangaran Aliyu masaukinsa da General ya nuna mishi ya nufa, Boys quarters ne, zama ya yi yana tunanin shi mai saurin fushi taya zai iya jure wulakancin Rayhan, Aliyu nada fushi sosai, idan har ya yi fushi sai ya aikatata wani abu kafin ya samu sauki a zuciyarsa, haka dai ya cigaba da tunanin taya zai iya hakuri da Rayhan
Washegari Aliyu ya shirya tsaf cikin kakin sojarsa, ya tsaya gefen motan Rayhan yana jiran fitowarta, can sai gata ta fito, ta yi ado cikin wani riga da wando, ta yi kyau kuma dirinta ya fito sosai, Aliyu ya sha'afa da kallanta harta zo gab dashi
"Heee, lafiya, me kake kallo? surata ko kyau na, na yi maka kyau ko, to let me tell you ka yi sauri ka cire ranka ko wani tsammani daga wurina, wane kare da fatar kura, kai yaro ne ni kuma babba ce"
Aliyu kara kallanta ya yi sosai, kalmar yaro data kirashi dashi ya yi masa zafi, kuma yasan ba girmansa ta yi ba don ba za ta wuce shekara ashirin da biyar ba
Katse me tunanin ta yi "baka gaishe ni ba"
"Ina kwana" bata amsa ba, ta yatsine fuska "to bude min mota na shiga, na gaji da tsayuwa"
Ya danne zuciyarsa ya bude mata ta shiga cikin isa Sannan ya rufe ya dawo bangaransa ya shiga ya ja motar suka tafi
Suna tafiya kan hanya "ka kunna min sauti"
Aliyu ya kai hannu ya kunna sautin motan
"Wannan ya yi high ina bukatar cool one"
Aliyu ya danne zuciyarsa ya ya canza mata wani daban
" kai yaro ya dai kana tafiya damu kamar a tsutsa, Inji ni a sama"
Wani zuciyace ta debi Aliyu tsananin jin haushin kalmar yaro data kirasa dashi, idanunsa sun canza Kala tsabar fushi, taka birki ya yi ya bude motar ya fito, ya bude gidan baya inda Rayhan take, tsorata tayi yadda ta ga tsananin bacin rai a fuskarsa, ya mika mata hannu
"Ban wayarki?"
Ta shiga rarraba idanu bakinta na rawa "me zaka min da waya"
Daka mata tsawa ya yi a karo na biyu "na ce ki bani wayarki"
Ta tsorata sosai jikinta na rawa ta dauki wayarta ta bashi, rufe ta ya yi, ya shiga motar ya ja, ya canza hanyarsu, zaro ido ta yi
"Ka canza hanya, ina zaka kaini?"
Bai tanka ta ba ya shiga gudu da motar kamar zasu tashi sama, sunyi tafiya mai nisa Sannan suka kawo wani wuri daga gani tsohon gidan gona ne, Aliyu ya faka motan ya fito Sannan ya bude gidan baya
"Fito"
Kuka ta fara yi "don Allah karka cutar dani, wallahi ban taba yin sex ba"
Jawo ta ya yi waje Sannan ya cincibe ta a kafada tana ihu tana rokwanshi amma bai kulata ba har sai da suka isa dakin dake cikin cikin gidan gonar, ya direta kan gado ya tsaya yana kallanta
Kuka take yi sosai tayi jina jina fa hawaye
"Don Allah karka cutar dani, bana sex, ba zan kara maka laifi ba
"Ni na ce miki zan yi Sex dake, kawai so nake na banbance tsakanin ni da ke waye yaro, sai kinyi tsirara a gabana na ga girmanki"
Rayhan ta zaro ido "na shiga uku, don Allah ka yi min rai, wallahi kai ba yaro bane, ka girme ni"
"Kin san Allah yau sai kinyi tsirara a gabana na ga girmanki"
"Wayyo Allah yau na mutu" ta kara fashewa da kuka
Rayhan idanunta sun rikide sunyi ja sosai tsabar kuka
"Wallahi ba zan kara ba, daga yau tsakanina da kai girmamawa ne"
Aliyu ya ce a'a ba girmamawa kawai mu zuba rashin mutunci, mu ga ni da ke wa zai yi nasara
Wallahi na tuba
"Ba zan gane kin tuba ba sai kin yi tsirara ko kuma mun zauna dake anan na sati daya, sai ki zaba"
"Ta kara fashewa da kuka wai kai baka da imani ne, na fada maka na tuba wallahi"
"Au nine ma bani da imani, to ya yi kyau" fita ya yi ya dawo falo ya zauna yana wasa da wayar hannunsa, fitowa ta yi ta zo ta sameshi ta tsaya gabanshi
"Yanzu idan na fadawa mahaifina duk abubuwan daka min wani mataki kake tunanin zai dauka a kanka, ina baka shawara ka yi maza ka mayar dani gida"
"Ok zaki fadawa mahaifinki ko, to bari na gwada miki ni tantirin dan bariki ne"
Fisgota ya yi jikinshi ya rungume ta tsaf, zata yi ihu ya toshe bakinta da wani kiss mai zafi, tun tana kokuwar amsar kanta sai ta yi lukui alamun ta ji maza, sa hannu ya yi ya matsa mata breast sai ta danyi wani kara "Wayyo Allah na"
Ya banbareta daga jikinta, sunkuyar da kanta ta yi kasa alamun ta fara jin kunyarsa "yanzu idan kin je fada masa, sai kice nasha bakinki sannan na matse miki nono, ta kawar da kanta alamun ta ji kunya
Aliyu ya ce juyowa zaki yi ki kalle ni Aunty Rayhan ko kuma na ce Baba Rayhan ko Inna Rayhan, to bari na fada miki ko kin ninka haka shekaru da girma nafi karfin ki ce min yaro, zan iya natsar dake, na kwanta dake har nayi miki ciki
Ya mika mata wayarta "gashi wayraki" ta amsa batare da kallanshi ba
"Mu tafi"
Fita suka yi suka je inda mota yake, Aliyu ya shiga ya zauna, Rayhan a tsaye
"Ba za ki shugo bane?"
"Ina tsoron na shiga baya ka ce na yi maka raini"
"Karki damu, shiga kawai" ya yi yar karamar murmushi ya ja motar suka wuce babu wanda ya kara yiwa daya magana har sai da ya kawo ta wurin aiki
Da kanta ta bude kofar motan ta fito shima ya fito ya tsaya, bata ce masa komai ba ta yi wucewar ta, shi kuwa yana tsaye a wurin ba zai je ko'ina ba har sai ta tashi aiki
Wata yer matashiya ce da ba za ta wuce shekara ashirin ba tazo wucewa sanye take da hijabinta dogo har kasa, kanta a sunkuye, tafiya take yi cikin natsuwa
"Irin matar da nake so kenan" Aliyu ya fada a zuciyarsa "baiwar Allah dan tsaya ina da tambaya"
Tsayawa ta yi ta juyo ta kalleshi "malam wani irin tambaya?"
"Sunanki nake son sani, da kuma gidanku"
"Me zaka yi dasu?"
"Ina da tabbacin nine mijinki, auranki nake son na yi"
murmushi ta yi ta Juya zata wuce ya yi sauri ya tare gabanta
"Ina tsoron kakin soja"
"Zan cire na ajje a gefe"
"Me kake bukata, bana son tsayawa kan hanya"
"Number wayanki"
Nan ta shiga fada masa yana rubutawa bayan ta gama ta yi wucewar ta yabi ta da kallo, murmushi ya yi
"Yes Aliyu, ka yi dace"
Rayhan ta shiga Office ta zaun, ta kasa tabuka komai, tuna soyayyar da Aliyu ya gwada mata ta shiga yi, tana murmushi, lokaci guda ta ji soyayyar Aliyu yana ratsa ko'ina a jikinta, fadi take a zuciyarta "ina sonka Dogari na wallahi, ba zan iya auran kowani da namiji ba sai kai" ta cigaba da tunani tana murmushi
Shukrah ta shugo gidansu Meenat babu sallama fadi take kawata fito ki ji wani labari
Meenat ta fito suka zauna tsakar gida "fada min ya aka yi ne?"
Shukhrah ta janye hijabinta ta rage daga ita sai sai skintie da singlet, kitson gashin doki ne a kanta, ya yi tsawo har duwawu, zama ta yi ta kalli Meenat
"Yau nayi hadaddan kamu kawata, wani Guy na samu, ya hadu sosai"
"Dagaske Shukhrah?"
"Kin ga yadda ya rikice kuwa? ya ganni cikin hijabina ina tafiya kamar mutuniyar kirki, wai kawai ya ga matar aure"
"Ki ce yana ruwa"
"Kuda da kada kuwa"
Sahabi ne ya shugo
"Ina kike je nazo ban ganki ba?"
"Na je gyaran kai ne"
"Kin ga dai bana son kina fita bakya fada min, yanzu dai bani dubu daya a wurinki"
Ciro dubu daya ta yi ta mika masa amsa ya yi yana kallanta "da kudi kenan anje anyo wani harkan kenan"
Harararsa ta yi ya fita abinshi ta ce mara amfani kawai
Meenat ta ce yana da amfani mana tunda shine kawai yake shiganki ki ji ki dai dai
Shukhrah ta ce
Wanda na hadu dashi yau da alamu zai fi Sahabi komai, zan ji shi sosai
Suka tafa suna dariya
Aliyu ya kasa samun natsuwa, tunanin Shukhrah ya dabaibaye masa zuciya, Rayhan a natse ta karaso ta same shi jingine jikin mota ya yi nisa cikin tunani, bata katse shi ba kallan fuskarsa ta shiga yi soyayyarsa na kara ratsawa ilahirin jikinta, a hankali ta katse shi
"Na tashi aiki" ta fada cikin sanyin murya, ya juyo a hankali ya kalleta
"Ok, to shiga mu tafi" da mamakinshi ya ga ta shiga gaba, kallanta ya tsaya yi
"Nan ne wurin zamanki?"
"Daga yau nan ne wurin zamana, ba zan kara zama a baya ba" ta fada cikin wani yanayi ta bude kofar motan ta shiga, murmushi kawai ya yi shima ya shiga ya tada motan,
Suna tafiya Rayhan na satan kallanshi, ji take kamar suyi ta tafiya karsu tsaya, shi kuwa tunanin Shukhrah yake
Da suka karaso gida, Aliyu ya bude mota ya fito ya zagayo ta gefen Rayhan zai bude mata, Rayhan ta yi saurin budewa, ta fito fuskarta dauke da annuri, ta kalleshi shima kallanta yake, tsantsan kaunarsa ce kawai a idanunta, kulle kofar motan ta yi ta tsaya kallansa, daga mata gira ya yi
"Yen mata lafiya?"
"Ina neman wata alfarma ne daga wurinka"
"Ina sauraranki"
"Ina son ka zama babban abokina, me bani shawara"
Tsura mata ido ya yi na wani lokaci kafin ya ce ni bana abota da mace
"Ka taimaka min"
Yayi shuru yana tunani kamin ya ce zan yarda amma na wucen gadi, abotan sati daya kawai zamu yi
"na yarda, daga yaushe abotan zai fara"
"Duk yadda kika ce ya shugabata"
"Yanzu muna matakin abokai ne, amma kasan wani abu kuwa?"
"A'a sai kin fada"
"Kana kyau sosai a cikin kakin soja"
"Ko?"
"Kwarai da gaske"
Duba agogon hannunsa ya yi "la'asar, bari na je na yi sallah"
"To, ka yi mana addu'ar, sannan idan ka dawo zuwa dare ka shirya cikin kayan gida zamu je yawo
"To" kawai ya ce ya wuce itama ta wuce
General zaune a falonsa Rayhan ta shugo cikin farin ciki ta zauna gefensa
"Yata yakike?"
"Lafiya lau Dad"
"Kina cikin farin ciki, miye sirrin"
"I am in love Dad"
Farin ciki ya baiyana a fuskarsa "fada min waye ya sace zuciyar yata"
"Sirrine Dad, zaka sanshi amma ba yanzu ba"
"Meyasa ba yanzu ba"
Mikewa ta yi tana fadin Dad ba yanzu ba idan lokaci ya yi zaka sani, tana gama fada ta wuce ya bita da kallo yana murmushi
Dakinta ta shiga ta fada kan gado tana tuna yadda Aliyu ya kama bakinta yana tsotsa, da yadda ya matsa mata nono, bata taba shiga wannan yanayin ba, ta tsinci kanta a bakon yanayi, tunda Rayhan take wasan banza bai taba shiga tsakaninta da wani namiji baji take yi dama ya kara yi mata, a hankali sonsa nata kara girma a zuciyarta, tunani ta fara yi ta wani hanya zata bi ta sace zuciyar DOGARI
Aliyu masallaci ya je ya yi sallah sannan ya dawo, bangaransa ya wuce ya shiga bedroom dinsa ya fada kan gado yana lallatsa wayarshi, Shukhrah ya kira, kiran farko ta dauka
Barka da warhaka ma'abociyar natsuwa, bautan Ubangiji, sanin ya kamata
Ta bangaran Shukhrah tare take da Meenat jin sabon saurayin da ta yi ne ya kirata yasa tasa wayan a handsfree Meenat na ji
"Ko zan so na ji sunan malamar?"
"Sunana Shukhrah"
"Ni kuma sunana Aliyu, ba zan boye miki ba, na kamu da tsananin kaunarki kuma ba komai yasa kika kwanta min a rai ba sai shigarki ta mutunci da natsuwarki, kawai yanzu dama nake nema a wurinki, ki bani zuciyarki, zanzo neman auranki, bana son auranmu ya dau lokaci
Shukhrah suka kalli juna da Meenat sukai dariya mara kara
"Na baka dama, zaka iya zuwa wurina kowani lokaci, kuma hanya a bude take na neman aure na"
"Nagode nagode sosai, idan na shirya zuwa zan kiraki sai ki tura min address"
"To babu damuwa saina jika"
Ta katse wayan,
Aliyu ya manna wayar a kirjinsa yana samun kwanciyar hankali, a wannan yanayin Rayhan ta fado ransa yana tuna zakin miyaunta da ya sha dazu, ya fara tsintar kanshi a cikin tsananin sha'awarta
Fadi yake "tabbas wannan ita ce matar aure, na tabbata namiji ko taba hannunta bai taba yi ba, idan na aureta nine farkon wanda zata fara sani,
Ya cigaba da magana a zuciyarsa
Meenat da Shukhra tafawa Suka yi
Meenat ta ce lallai kana ruwa
"Kusa da kada kuwa"
"To yanzu miye abin yi?"
"Kawai mahaifina ya rasu zan fada masa, saina kaishi wurin magajiya a matsayin Mamata"
"Kuma kin kawo shawara"
"Ke bari naje na yi bachci don yau akwai kwanan club"
"Ya kamata, ni yau ina tare da Oga ba maganar club"
Tashi Shukhrah ta yi ta shiga dakinta, daki ne guda daya, akwai Katifa a kasa sai kafet shimfide a dakin, bangon dakin zagaye da labule, kwanciya ta yi kan katifar har bachci ya fara daukarta Sahabi ya shugo ya fada kanta
"Haba Sahabi bachci fa zanyi"
Ta juyo tana magana ya manna bakinta da nashi ya shiga tsotsa
tureshi ta yi "ka barni bachci nake ji"
"Ke wai kwana biyu shuru baki kawo mana kwastoma ba"
"baka da hakuri watarana wallahi, nifa aure zanyi ma"
Ya watsa mata wani kallo "da raina uban wa kika isa ki aura"
Murmushi ta yi "taya zan barka bayan kasan banda wani da namiji da nake jin dadinsa daya wuce kai, kawai auran jari zanyi na dinga kawo maka kudin kana ci"
Murmushi ya yi "sai yasa nake kara sonki, to wani asararre kika samu zai aureki"
Ta tabe baki "wallahi wani gara ne, soja nefa, daga gani babban soja ne ma"
Ya zaro ido "Soja fa kika ce, ba'a wasa da Soja, idan muka shiga hannu ba za mu ji dadi ba
"Kwantar da hankalinka dan samari, nifa mace ce, zan juya sojan kamar waina"
Ta kai karshen maganar tana rungume shi,
"Baby zan sha nono"
Ya fada yana kallan breast dinta
"Ni kuma zan sha banana🍌" ta kama bananan sa da sauri duk suka fashe da dariya
Da daddare Aliyu ya so zuwa wurin Shukhrah amma babu dama saboda fitan da zasu yi da Rayhan, kwalliya ya yi cikin kananun kaya jeans baki, red T-shirt, ya yi kyau matuka
Da fitowar sa ya samu Rayhan harta fito tana jiransa amma ta juya baya bata san ya fito ba, ta yi kwalliya cikin wani party dress Golden colour, dogo ne har kasa amma babu hannu sannan ya tsage a gefe, sai kyalli yake yana daukar ido wal wal, gashinta anyi masa ado sosai, sannan kafarta takalmi ne mai tsini
Aliyu cak ya tsaya yana kallan bayanta, hadiye miyau ya yi, yana ji a ransa kamar ya je ya rungume duwawukanta, ya yi ta shafa, ji ya yi banana 🍌 na motsi, juyowar da ta yi yasa shi dawowa hankalinsa, kara rikicewa ya yi da ya ga kwalliyar dake fuskarta, da kyar ya karaso
"Na yi kyau" ta fada tana masa fari da ido, wani yarrrr ya ji, hankalinsa ya kara tashi, daurewa ya yi ya ce "sosai kuwa"
Zuwa ya yi bangaransa ya bude ya shiga, itama ta bude nata bangaran ta shiga
Yaja motar suka fita, dakyar Aliyu ke tuka motar hankalinshi na kan Rayhan, itama satan kallanshi take yi, wurin wani hutawa suka je inda masoya suke zama, anan suka zauna, Aliyu ya je ya yi odan kayan ciye ciye da shaye shaye, Rayhan ta tambayeshi kudin
Kallanta ya yi "muna matsayin abokaine yanzu, nina biya kudin"
"To kenan next ni zan biya"
"Idan kin ga dama"
Sunyi hira sosai daya kawo shakuwa a tsakaninsu, daga nan sai suka wuce Cinema suka sha kallansu bayan nan suka dawo gida
Aliyu ya bude kofa ya fito, itama Rayhan bude ta bude ta fito, Aliyu ya zagayo ta wurinta ya tsaya
"To sai da safe kenan ko"
Mika tayi "harka gaji da kawarka"
Hankalin Aliyu tashi ya yi sanadiyar mikan da ta yi bai san lokacin daya rungume ta ba, tsayawa ta yi cak sanadiyan wani bakon yanayi daya ziyarceta
A hankali ya kai bakinsa dai dai nata, idanunsa na kallan nata idanun
"Ba kiss zanyi miki ba, kawai I hug you saboda ke kawata ce, kuma ai ba laifi bane"
Lumshe idonta ta yi, bukatar ya sumbaceta amma sai ta ga ya sake ta, "ki je ki kwanta sai da safe"
Ya juya har ya fara tafiya ya juyo ya kalleta
"Ya kika tsaya, ko akwai wani abu ne, idan rungumarki da nayi a matsayin abokinki na yi laifi, to ki gafarce ni amma ina son zan fada miki wani magana, duk wani abu mai daraja a killace yake, a matsayina na abokinki zan baki shawara shigarki bata dace dake ba, ina son mace mai killace jikinta da adana shi"
Yana gama fada ya yi tafiyarsa, Rayhan ji ta yi ba dadi, kallan jikinta ta yi, ji ta yi ta tsani shigar da ta yi, a sanyaye ta taka ta tafi ciki
Na Maryam Muhammad Hasheema (M jaruma ce) 09049493054
Mu hadu a page 2
